Murucin Kan Dutse

Chapter 103 of 146

damu ko school muka tafi sai ta dinga muna abinda taga dama yanzu ma saboda ita late mukeyi zuwa schoool da safe.
Daddy yace may yasa baku fada min ba tunda ta fara hakan yace kira min ita dakin nasu sai yaron ya mike tafi gun kiran ta.
Tare da uwarta suka fito falon inda uwar kecewa dashi kadawo ashe yace eh kawai ya juya kan ihisan yana cewa may yasa kowa na falo a na hira kika shige daki ke ?
Yanzu nake jin duk kwanakin nan bakya fitowa da wuri sai kin sa yan uwan ki yin late a school daga yau kada na sake jin haka daga gareki.
Sai uwar take cewa wata sabuwa yau kuma Ihisan ce akaiwa kulli bani ba babu dai yadda zakuyi damu gani nan bari nan wallahi.
Yace ke dakata wani irin magana ne wanan kuma haka sokike abarta tana cutawa yan uwan ta kullun ta sa su makara ko may aida ba haka takeyi a baya tare suke fitowa su wuce.
Inda nake tajuyo tace yanzu Rahama baki ji kunyan fadin wanan maganan ba wa karamar yarinya zakiwa hadi wurin ubanta.
Murmushi nayi nace da ita cikin dariya Allah sarki Rahama mai dadin suna yanzu kuma nice na fada mai don ina bakin ciki da Ihisan ko may ?
In ba bakin cikin ba may zai sa ki mata hadi gun ubanta hira banda kilibibi may kike koyawa yaran suyi in ba gulma ba.
Wai hindatu may yasa baki da tunane ne ina ruwan Rahama a cikin wanan zancen yanzu da ita ake zuwa school din ko may wai ?
Ta juya gun Nasir tace kune kilababbun da kuke cewa haka ko zaku hanata zama da uwarta ne ko may yan bakin ciki da sukai gadon mugun abu a gurin uwar su.
O my god wai may nene haka kike yi hindatu na fa fada maki bana sin irin haka so kike karnaiwa ihisan fada ko may idan tayi ba daidai ba ?
Wanan cin amanan nata da kukaitayi don bana nan yanzu nazo babu wanda zai saka min ya a gaba da mugun manufa in yarda don da baifi da ba
Ihisan dai ba yadda zakuyi da ita don ta zamay maku kashin bakin tunkuya ta Allah bata ku ba ta juya ta wuce fuu zuwa ciki.
Yarinyar ta samu wuri ta zauna a takure yayin da falin yai tsit bayan wucewan ta ciki sai Nasir ne yace dani mum yau ki muna wanan miyar bindin saniyar da kafan shi mana please ?
Nace Nasir an barka a tasha sai dai ka fadawa maman ihisan tai maku don yau itace da girki sai yaran suka bata rai yace ni yau shi nake son ci wallahi.
Nace bari banda gobe sai nai maka duk abinda kake so sai uban yace saboda may baza ki masu ba tunda shi suke so sai nai shiru nasan yin zai iya jawo man matsala gun matar shi.
Yaran suka ce daddy yace ki muna shi inji jinior nace kaida baka azumi ina ruwan ka da abin shan ruwa na masu azumi ne kawai wanan.
Aisha tashi ki ciro min ki dan saka a ruwa ya sake kafin na taso kin san wuyan dahuwa ne dashi.
Ihisan ce ta mike zuwa dakin su nasan ko ta fadawa uwar ne sai gani nayi ta fito ta shiga kitchen din a lokaci sha daya na rana lokacin yin abin buda baki baiyi ba.
Amma haka ra babake kitchen sin wai tana aiki nikan ganin ta shiga banyi yun kurin tashi zuwa abinda zanyi ba din.
Ba ita ta gama ba sai bayan uku da wani abu na rana na shiga na dora masu girkin sai gata tafito daga daki tana shiga naji tace may aka dorawa wuta haka kuma ?
Bayan wanan uban abincin dana dafa sai an kara dora wani kuma again wanan ai ya zama barna ko ?
Nace abinda diyan masu gida ke so shine zan dafa masu tace haka za a kare wurin yiwa diyan kishiya bauta babu gode balle na gode.
Gyara dai maganan ki ko kin manta nima ina da masu ci a ciki ne da zakice hakan.
A dai bari su girma kamar kowa mu gani ba wanan ya ta tsitsai din ba da ba a san da su ba a gidan.
Nace a wwurin ki ne yake amma agun wanda ya yanka masu rago yasan dasu kin san ance mai karami watarana shi keda babba insha Allahu.
Magana take so yai nisa na fahince ta sai na sharer ta naci gaba da aikina sai naga yaa dace na hada tuwon farar shinkafa aci dashi ba bata lokaci na dora na fara aikin shi sai dai ba yawa sosai.
Da muka sha ruwa shi muka ci muka bar faten doyan da tai muna wanda har ya yi karfi ko don yin shi da akai da wuri.
Koda daddy ya shigo ya samu yaran a falo suna cin abincin su a zaton shi shi aka girka a gidan saida ya gama ya fito ya zauna cin abinci ya na budewa faten ya tare shi a fuskan shi take ranshi ya baci.
Da karfi ya kwala mata kira don kwance take tun shan ruwan ta jikin ta yai mata nauyi ta mike ta fito kai babu dan kwali ba wani kwalliyan da tayi.
Tans zuwa yace may ye wanan saboda Allah yanzu hindu abinda zanci ke nan a gida na a matsayina na wanda yai azumi kko may ?
Tace may kuma yayi don Allah kai mutum baima gwanita ka gode mai yace may ye abin gwaninta anan a faten doya ke kullun ba zaki iya yiwa mutane abincin kwarai ba don kiuya kawai kada ki motsa jikin ki komay ya kawo haka.
Ni gaskiya ba zan lamunci hakan ba wanan ai cutawa ne gare mu may aka rasa a gidan nan da baza a girka muna abincin kwarai ba ?
Ni shi na iya kuma shi nayi ba zan wahal da kaina ba don a yabe ni ko wani abu mutum na fama da azumi yai aiki ya gaji a kawo mai wani korafi can kuma ?
Ya ce yayi kyau za a ko jimu a gidan nan dake idan wanan abincin zaki dinga girka muna tace iin hakane sai dai naiwa mama waya akawo min wata yar aikin don ba zan iya wanan wahakan ba gaskiya.
Yace yanzu dabara ya rage gareki ai idan tazo sai ta girka iya bakin ki don ba zan auro mace ba tace bata iya min girkin da zanci.
Ya kwalawa jinior kira yace kira min mummy ku a dakin ta yaron yazo kirana ina ba haidar nono na ce gani tafe yaron bai gama shan nono ba na mikawa Atika shi na fita.
A zaune na samay su yadda na ga zaman su yau yasa nasan akwai matsala ke nan na karso ina mai barka da shan ruwa ya karba min a dakile yace ina abincin da naga kinyi ?
Na kai idona kan faten dake gaban shi fari nace nabawa yaran yace babu ko kadan a bani nai dan shiru can nace akwai shi yace a bani don Allah ?
Na juya na koma daki na dauko mai cikin wanda za suyi sahur dashi na kawo mai har miyan da komai.
Na aje ban tsaya ba zan wuce tace indai kili bibi abin yi ne sai mu zuba mu gani dama sherin da kike son kulla min ke na yasa kikai wani girki.
Ban iya sheri ba ni da bakin maigidan naiwa yaran girki ki wacce ta fada baki bata fada maki daidai bane dazun yadda akayi.
Tace wakike nufin ta fada min nace wacce kika hana karban abinci ai tazo ta karba taci duk da kin hanata ci din.
Ya isa haka please yana kai loma abincin a bakin shi daga haka bai kara cewa komai ba yaci gaba da cin abincin shi na juya zan wuce yace jinan.
Sai na juyo yace ku saurare ni daga yau girki a hade za, a dinga yin shi ban yarda a kara raba tunkuya ba a gidan nan ba.
A zato ita zata fara korafin saboda may amma sai naji tace ya dai fi don bazan iya wahakan ba kaitan banza abincin ba haka.
Nace baida matsala ta fadi haka ni may zance na bada kaina duk da nasan mune zamu cuto ba zatai komai ba ita na sani.
Tun wanan rana muke komai a gidan tana daki kwance da yar ta sai in an sha ruwa sune farkon diba ni dai bance komai ba a kan hakan da yai muna din.

********* ********* *********
Nidai ranan ina barci bayan na falkane Aishs ke cewa dani wai sun fita shida hindatu din.
Ban kawo komai ba sai da suka dawone naga anata shigowa da kaya irin na raba ma dangi din nan da karshen azumi.
Aikina nake banbi ta kansu ba sai da dare ne ya kiramu nazo na zauna yake cewa kayan da za, a bawa mutane na sallah ne sai kiyu list din wa yanda kike sin abawa a part din ki.
Nace ayya angode don na riga da na saya ko har an kai masu ko ina fadan haka namike na bar wurin ban tsaya ba yabi bayana da kallo kawai.
Na koma daki ina mamakin hali irin na daddy ni may ya dauke nine wai zuwan hindatu fitan su karo na uku ke nan a gidan tare.
Na farko wai sun fita zuwa gidan wani abokin shi a bakin matar mutumin nake jin labari sai na biyu wai sunje sayaya ne a wani plaza na gida.
Sai kuma yau da sukai min wanan rainin wayon babu ko shawara haka kawai don an mayar dani yar tallakawa wai nai list din wanda za aiwa alheri a part dina don muna tallakawa ko may ?
Ban fita ba duk da ni keda girki har ya gama abinda yake ya kwanta sai washe gari ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin.
Ban juyo ba nai mai ina kwana yace wai Rahama may yasa baki son a zauna lafiya ne ke yanzu yadda kikai min jiya kin kyauta ke nan.
Ni dai banyi magana ba sai shiri na nakeyi kawai yace badake nake magana ba ne kin kyale ni ?
Nace kaje ka karawa wacce ta sayo din takaiwa yan uwan ta can ni duk da tallakace bani daukan wullakanci kishiya idan ta mai da kai yadda take so ni ba zata mai dani ba don ba zaman ta nakeyi ba anan balle tace zata zabawa yan uwana abinda taga ya dace dasu watau gana kauye ko ?
To kubar abunku nagode Allah ya kara arziki da budi gaba na juya zuwa wardrobe na fara fitar da kayan da zan sa ajikina.
Yace yanzu nagane nufin ki Rahama watau don muje da hindatu ta tayani zaba shine bakin cikin ki ko ?
Na juyo nace bakin ciki bakin ciki akan may fa akan ka fita da matarka ko may ai ba yau ka fara fita da ita ba ko a kano ya damay ni sai yau zan damu ko may.
Ni dai nasan ban wa kishiya shishigi ba balle ni ai mina ga bara kudi ka bamu kace kowa ya saiwa yan uwan shi kayan sallah sai yanzu ne ita tasan hanyar yaudara ko may ?
Sai yai shiru ba abinda yake tunane sai yasan haka akayi da yai magana nakawo mai wanan shawaran akan kowa ya saiwa nashi da kan shi .
Yanzu ko itace ta bada wanan shawaran kan a saye a rabawa mutane kuma gaskiya wanda tace wai namu din baikai wanda yaga ta zaba ba a bangaren ta.
Yai magana tace kallan ya burgeta ne sosai kuma zai karbi yan uwan ta sosai don suna son kalan.
Yace yanzu dai kina nufin bazaki karba ba nace ba nufi bama bana karba na yafe har ga Allah aba wasu.
Yace to shike nan zaki gane kin min wullakanci ga hakan nace aina saba ba yau bane farau din hakan gareni indai wulakancin ka ne.
Wani abin ance idan bakai magana ba sai ya zama maka ciwo a zuciyan ka don maganan na da amfani saboda idan kai sa,a za a daina.
A bangare na ma maganan yai min rana don ashe wai gajiya sukayi a ranan da harda kayan sallah mu dana yara zasu sayo sai suka gaji suka dawo gida washe gari zasu koma su sayo din.
Yin maganan da nayi ne yasa shi dogon nazari duk da ran shi ya baci a yadda nai mai da farko amma daga baya dayai tunane sai yaga rashin dace wan hakan.
Don inda gaskiya ne ai kamata yayi ya dauke mu mutafi tare a sayo komai dani ba su ware ni ba yadda sukai min din.
Ya kuma tuna a bara yadda akayi saye kowa kudin ta ya bata ta sayo ita da yaran ta da nata.
Washe gari koda tai kai zancen zuwa saye sai cewa yayi da ita ya fasa zaiba wa kowa kudin shi ya saya wanda yake so da yaran shi yadda ya saba yi muna.
Ranta ya baci tace wanan ba shawaran ka bane na sani kodan jiya matar ja tai fushi taki karban kayan yasa zaka canza shawara a yadda muka tsara da farko.
Yace in ma haka din je hakan ne don ba haka na saba yi ba da farko ai tun farko sai da na so kin wanan shawaran naki amma kika kawo min kabbali da ba, adi don haka abar wanan zancen zan bawa kowa kudi yadda na saba ne.
Amma idan kai muna haka mu aka kwara ni da zulfa tunda sun fi mu yara ai yace au shine hikimar ki ashe kikai wanan shawaran bafon Allah ba ashe kikayi.
Rahama na da gaskiya ke nan ta fahinci abinda yasa kikai masu hakan ke nan ashe tace da yake ta iya yaudara ba dama ai haka yasa ta hada dayin majuju don ta haifi diyan ta samu garabasa .
Yace ke wa ta hanaki yin hakan ai kin rigata shiga gidan tace Allah ne bai kawo ba kaima ka sani ai.
Yace ashe kin san Allah may yi itama shi din ne ya bata a lokacin da kowa bai zata ba din don haka ban son dogon zance kan maganan na riga na fada maki shawara na don tun farko haka na saba yi maku ai.
Ni dai ban san sanda yaiwa yan uwana da iyayye aike ba sai ji nake suna bugo waya suna godiya amma fir naki tambayan shi abinda ya aika masu dashi.
Yaje kano gun su Anty kwanan shi goma a can gun su anty ya gama abinda ya kai shi ya dawo Abuja gurin mu da aikin shi.
Ranan ya dawo ne ya ban kudina dana yara na har dasu Aisha da Atika da helen dake wurina sai da suka samu,
Haka yasa na fahinci kowan mu haka yai mata sai da zan tashi ne ya sake miko min wasu kudin yace wanan na su Nasir ne da jinior don uwar su tace na kawo maki tunda a nan suke gun ki.
Mamaki nayi sosai yadda anty ta sauko haka ba kamar ya watan nin da suka wuce ba ashe yaran ne kan yawa fada mata komai a waya shine yasa ta kara sakewa a ranta ta dai fahinci ba wani abu a zuciya na kan ta zugin mutane ne kawai yasa ta rudani dama amma ita har yau ba zata iya cewa ga abinda nai mata ba.
Washe gari muka shiga kasuwa da yaran nai masu sayayya sosai yadda ya dace da kowan mu har haidar sai da na dan sayo mai tunda yana dasu dama aje.
Naso muje kano muyi sallah a can har daddy ya amin ce sai hidimar tafiya muke yi gaba dayan mu don baifi kwana uku ba ko hudu ai sallah.
Komai munyi na tafiya amma ranan yana dawowa sai yazo min da zancen ba tafiya mu kano sai dai zai tafi da Nasir da Jinior suyi sallah a can.
Banji dafi ba babu yadda zanyi dole muka hakkura da batun tafiyan na dai san dole akwai matsala ta wani wuri akan haka.
Cake na hada lafiyayye da su donut da sauran snacks da zasu tafi dashi nai kuma saa sunyi dadi sosai don sai kamshin vanilla flavor sukeyi na saka a fararen robobi naba yaran sukai wa anty da Alhajin daddy da Abban anty na sallah.
Washegari zasu tafi ya kira mu yake sheda muna Sani zai kawo muna naman sallah da sauran abubuwan bukata da zamu bukata na hidimar sallah din ya kuma kawo kudi masu yawa yaba kowan mu yai muna sallama suka tafi.
Da yamma sai ga nama mai yawa Sani yazo muna dashi zakace ma Saniya ce suku tum aka yan ka muna an gyara shi tun can iyakar mu dai aikin shi kawai.
Muna shirin fara aiki sai ga hindatu ta fito tana wani ya tsunar fuska tace ke Rahama a raba naman nan biyu a bani nawa nan ?
Nasan tsiya take ji don haka nace kamar ya a raba biyu adai kasa a cirewa kowa ku dauki kasan ku tunda ba mu kadai ne da hakkin shi ba.
Wasa wasa muka fara rikici kan hakan ta dauki waya ta kira maigidan cikin masifa lokacin yana falo can ma ana wani rikicin tsakanin anty da zulfa kan abin sallah din.
Sai da ya gama sauraren ta yace kisa wayan nan a handsfree muyi maga taji, ta dauka ya goyi bayan ta ne sai tace a fusace yace ki saurare shi kiji abinda zai fada nace ai gani tsaye ina jin ku.
Yace Hindatu ta ansa ya kira nawa sunan nima na karba yace a kasa abakowa dake gidan har maigadi tunda abin naku tsiya ne, yace ai gaskiya ta fada abinda aka saya don anfanin bukin salla zai kawo fitina kuma wai may ke damun kan kune haka please da wani kuke son naji

Download complete TXT · Novel page