Murucin Kan Dutse

Chapter 104 of 146

ne wai haka ?
Tace haka zakace yace may kike son nace nama kuka rasa a gidan ko may da wanan zai kawo maku fitina haka don baku da tunane na gane abin naku hadin bakine don kawai kuci min mutunci ku hanani kwanciyan hankali.
Ta juya a hasale tana fadin keda keda tsiyar nama sau ki hada da namu duk ku cinye ina ruwan dan baka saba ba da ganin hakan.
Nace ni dake yanzu ai sai a banbanta wanda ya nuna zalamar shi ba ki dai kwaruwan mu kan.
Duk da ta wuce tsaye nayi aka kasa shi daidai sai kason mu ni da ita yafi na sauran yawa nace Aisha ta kai mata nata.
Can ta koroto da naman tace muje mu kara mu da ya zamawa bakon gani a gare mu tadawo min dashi nace ta saka a freeze ta aje mata.
Nan suka shiga gyaran shirgin naman da yake yaran na da hazaka zuwa goman dare har sun gama komai suka saka a wani katon roba mai marfi suka kawo dakina.
Da dare sai ga anty ta bugo min waya tana min godiya wai taga yara sun zo da abin arziki nai murmushi kamar tana gabana nace haba dai anty ai wanan ba komai bane ni ina zan iya abinda akai min.
Tace to adai ta hakkuri don kin san zaman hindu wurin ku ba alheri bane da biyu ta zabi zama can din yaran nan sun fada min irin zaman da kuke acan din kina ma da kokari Rama in nice ai da na bar mata gidan na dawo inda nafi karfi.
Nace a raina yanzu kuma haka ke son dawowa tsakanin mu bayan ta riga taba da kafa an muna dariya ta jima tana min hiran rikicin su da Zulfa tace tana ganin hadin baki sukayi akan hakan.
Nace anty ni dai nasan ban na shiga hakkin kowa shiga nawa ne dai ba zan dauka ba tace to a kara hakkuri mukai sallama ta kashe wayan ta bar ni da mamakin ta.
Washe garin sallah koda goma yayi duk mun gama komai na abincin da zamuci tunda ba wasu zamu aikawa ba sai makwabtan mu da ba musulmai ba na sawa abinci da soyayyen nama da abin sha na aika masu dashi.
Natura Aisha ta fada mata an gama abinci yana saman dining idan sun tashi ci bata ki ba ta turo yar ta ta diban mata itama ihisan din nan falo ta zauna taci nata.
Ranan da daddy zai dawo sai gashi yazo mata da wata yar aiki sai dai bai dawo da yaran ba zasu tsaya can suyi hutu a wurin uwar su ne.
Dawowan daddy babu abin da ya canza a tsakanin don har yanzu baya iya aiwatar da komai idan muna tare dashi sai dai idan da sauran matan shi yake zai iya gudanar da komai normal yadda ya saba.
Tun abin baya damun mu har ya fara yi min magana sai gashi wai laifina zai gani kan haka wai ni ban ma damu da halin da muke ciki ba ni dashi din.
Na idar da sallah asuba na zauna a wurin na fara tunane may ke kawo muna wanan matsalar ne haka tsakani na dashi don gashi har mun fara samun matsalan zama kan hakan dashi.
Na kira Zarah abokiyar shawara na nake fada mata halin da muke ciki ban ko kai karshen magana na ba ta katse ni da fadi cikin tashin hankali Rahama kina ko da hankali kuwa ?
Kina cikin wanan babban matsalan haka kika zauna tsawon lokaci mai tsawo haka abuna damun ki.
Nace Zarah ni may kike so nayi ne wai tace kin ko san abinda ke damun ku daga ke harshi bafa karamin abu bane wanan don asiri ne da akeyi tsakanin na miji da mace da hausawa ke kira da dan baka.
Ba zai taba samun natsuwa dake ba sai idan wanan asirin ya bar aiki a tsakanin ku tunda da sunan ku akayi shi amma dai anyi shuuman mata anan don yanzu ba zamu cewa ga wacce tai maki wanan abin ba tunda kina da kishiyoyi da yawa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A TAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
80
Tun bayan waya na da Zarah sai hankalina ya fara tashi don ba karamin tsoro kalamin ta ya bani ba.
Ni lafiyana shine yafi min komai a rayuwa na in dai zasu barni da lafiya ina iya bar masu mijin su a zauna lafiya.
Amma ta ina zan fara wana san yai muna wanan shamakin a tsakanin mu ni dashi don duk kishiya kishiya ce dai.
Amma wa zan zarga a wanan matsalan shin hindatu dake nan zaune tare da mune ko kuwa wa yanda ke gida ne sukai min hakan wai ?
Nan dai na zauna ina ta faman tunane wanda har na gama ban iya gane komai va daga ciki abinda dai na yake da ga karshe shine zan dukuma nafi da kaimi wurin kai kuka na ga Allah dayai min tsari akan duk mai bina da wani mugun manufa.
May na tare masu da har yai zafi haka sukai muna wanan mugun asirin da sai jahili zai iya shi.
Sannu a hankali na fara rama a tsaye gashi bayan zarah aminiyata ban iya fadawa kowa wanan zancen don da kunya aji shi a bakina haka.
Muna cikin wanan halin ne ranan sai ga massage ya shigo a email dina asibitin da nai bautan kasa suna neman mu muzo interview wurin su.
Murna farin ciki duk ya kamani a lokaci daya daddy kawai nake jira ya dawo na fada mai naji may zai ce akan zancen.
Koda ya dawo nice da girki ranan don haka na tsara kwalliya na dana bata lokaci wurin yin shi ga lafiyayyen abincin dana girka don shi a ranan.
Bai shigo ba sai yamma lis ya dawo gidan ina dakina ina bawa yarona nono naji muryan shi Atika na mikawa yaton bai koshi ba ya dan sa kuka nace fice dashi zuwa dakin ku don Allah,
Tana fitowa dashi uban yaji kukan shi yace kai Atika ya akayi ne yake kuka kawo shi nan ta mikawa uban yoron ta nacewa wai bai koshi da nono bane shine yake kuka.
Daddy yace ita nonon nata na sayarwa ne ko may zatayi dashi da bazata bashi ba ya sha ya koshi da kyau.
Daga kofa ina fitowa nace cikin wani murya najan ra, ayi nace wallahi daddy ya faye tsotso shi bai koshi da nono.
Ya dago yana kallo na na tabbatar shigan tai mashi kyau don ni kaina na sani saboda kayan ya fitar min da kurciyana a fili.
Yai murmushi yace nawa za, a sayar muna a bashi ya sha ya koshi yadda yake so na sake cewa daddy don Allah barshi yanzu Aisha zata kara mai da abincin shi yasha.
Wallahi Rahama kiji tsoron Allah in baki son Allah ya kama ki da laifin daukan alhakin wanan yaro yaro dan wata shidda da kai ace bai sha nono ya koshi ba sai wani abinci can na bature.
Ban so ba namika hannu ina karban yaron a wurin shi nace jishi dan Allah sai dan banzan tsotso dashi aikai ka baci da ci wallahi.
Komawa mukayi daga ni har shi muna dan hira yaron na shan nono yace ina yaran nace sun fita wasan ball sukace.
Yace kai yaran basa ji wallahi nace to maza ne ba a raba su da irin haka tunda ba mata bane sai dai a saka ido ga muamulan su kawai.
Sai dai haka din amma ba kwar ba dai kan don an wuce wurin kwaliyan da ba biyan kudin sabulu ai aikin banza ne yin shi.
Gaba daya muka juya inda take tsaye tana magana cikin tafiya zuwa kofan baya shi dai na dauka bai fahinci maganan ta ba amma ni sai na fara zargin anya ba daga hindatu muke samun matsala ba kuwa ?
In ba shi ba yaya tasan abinda ke tsakanin mu ni dai na san daddy ba zai taba fada mata komai ba a tsakanin mu duk yadda suke kuwa don shi ba namijin dake zama yai maganan wata matar shi da wata ba.
Tafe take tana waka mai kama da habaici kamar an dauke ta an rada a kasa ta fadi kasa tim a tsakiyan falon.
Ba karamin buguwa tayi ba ga wanan faduwan shine yace innalillahi may ye haka ya akai haka kuma sannu tashi.
Bai mike ba yana zaune inda muke yana cewa may kika taka kuma haka ya kada ke wanan faduwan haka ai sau ki karye ko ?
Allah ai ba azzalumin bawa bane don shi ba ai mai gadara in daukan alhaki abin yine kadan mutum ya fara gani a rayuwan shi.
Ina fadin haka na mike na bar wurin ban mata sannu ba ta mike da kunya ta nufi dakin ta tana cewa ban san shege yaron da ya zubar da ruwa ba a saman ties din nan kuma ?
Bai jima ba ya tafi sallah sai bayan ya dawo ne na fito don bashi abinci mun zauna yana ta latsar wayan shi har na zuba mai abincin na aje a gaban shi ya kalli abincin yace duk ni zan cinye wanan Rama ?
Kada fa nai kiba kizo kice dani na tsufa maki nan gaba ki fara dan kwanaye kwanaye kuma kina baki son zama da tsoho.
Nai dan dariya mai kama da murmushi nace ai tunda bance ma tsoho ba da farko yanzu ma bazance ba don ni din ma yanzu ai ba yarinya bace.
Muna cikin hiran sai ga ta fito daga daki tace dear kasan na fadi a gaban ka amma ko ka shiga ka dubani kaga ya jikin nawa gashi yanzu duk jikin nawa ciwo yake min wallahi.
Yace ki sha magani mana tace ni asibiti nake son zuwa aduba min kafana don ciwo yake min yace amma ba yau ba kan don dare ya yi yanzu.
Ta wani bata rai bataso haka ba taso ne ta tasa shi a gaba sukama hanya zuwa asibi a cikin daren nan ta nuna man iyakana dashi sai bai biye mata ba yace tasha magani agani zuwa gobe.
Sai da ta wuce nace dama ina son ka huta na fada ma an turo min da sako ana neman mu ranan monday wurin interview asibitin da mukai service.
Yace a, a shine baki fada min ba Rahama wanan ai ba karamin magana bane yanzu zanyi waya da MD naji yaya ake process din abin naku.
Nan a wurin ya kira sukai dan magana yace ba matsala na shigo kawai ranan monday din za a duba ai ina da kwazo sosai sun sani.
Mutum zai iya fahinta yanayin mu a lokacin yadda muke daukin junan mu sai dai ba dama komai don engine bai aiki a kaina ko kadan dan wasan da ma yakanyi da farko idan yayi yanzu sai gari ya waye mai ba lafiya a jikin shi.
Mutum zai gane yana cikin damuwa don sai matsala ya faru zaka san idan mutum yana kaunar ka baka sanin zurfin kaunar sai idan matsala ya gitta a tsakanin ku zaka gane zurfin kaunarva gare ka kasan yadda mutum ya damu da kai.
Hakane yanzu a kullun bakin daddy bai gajiya da kwantar min da hankali yana bani hakkuri kan matsalan dake faruwa damu din.
Nakan yi murmushin yake nace haba daddy bakomai mana ai matsala ne kowa yasan ta sai yace Rahama nasan ina cuta maki sosai sai dai hakkurin ki bai bari a fahinci muna da matsala ni dake.
Don da watace da yanzu duniya ta fahinci halin da muke ciki ko ansan muna da matsala wurin wanan fannin.
Wanan kwantar min da hankalin da yake yasa ban dauku matsalan nakaishi can kasan zuciya na ba sai ma kara kaimin da nayi wurin kyautata mai fiye da koda yaushe yadda wani ba zai iya fahinta ba.
Ina shiga dakin shi kullun nake da duty na kwana a ciki indai ba mun dan samu matsala bane nai fushi dashi.
Don a dakina nake yaji bana fita bana kai kara gun kowa yadda naga sunayi ban taba kai karan shi a wani ba duk zaman mu dashi na aure.
Yau ma na shirya tsab nabi bayan shi zuwa dakin hindatu da ban san may yasa idan ina duty zata dauki lokaci zaune afalo wani lokaci sai na shige zata bar falon.
Yau ma tana ganin na shige ta mike ta fada dakinta ta jawo wani roba fari can kasan kayan ta inda ta boye ta dauko wani abu mai kama da baka ta hada shi yadda takeyi kullun.
Ina shiga dakin ya fito daga wanka yana tsaye yana fesa turare a jikin shi na shigo dakin da sallama na.
Jin sallama na yasa shi dan juyowa gare ni yana murmushi yace har yaran sun kwanta ke nan nace sunyi barci tun dazun ai.
Karban turaren nayi naci gaba da fesa mashi sai bina da kallo yake yana murmushi da kada kai kawai.
Nace daddy lafiya ko naga sai wani kallo kake min ko yau injin ta samu service ne ban sani ba daidai da nake mayar da turaren a mazaunin shi yace .
Da haka zai kasance gare mu yau din aida nafi kowa farin ciki ko yaushe burina da fatana naga wanan matsalan ya tafi a gare mu.
Yace Rahama ni har yau na kasa kai karshen fahintar ki nace namay fa daddy ?
Yace baki ganewa ke kina da wani baiwa da ba kowa ne Allah keyiwa shi ba ke kanki baki sanin kina dashi sai dai na tare dake ya sanar maki da hakan.
Nace daddy wani irin baiwa ce wanan kuwa dani ban san da shi ba haka sai kai ka san shi a gare ni ?
Ya murmusa yana nufar gado yace ba yanzu zan fada maki shi ba sai nan gaba idan komai ya daidaita tsakanin mu.
Sai ya zauna a bakin gadon yace Rahama ina tausaya maki ina cutar dake a shekarun ki baki cancanci wanan hukuncin ba haka a wanan lokacin.
Rama ba zan iya boye maki ba ina tausaya maki matuka kuma don abin nawa a kwai son kai a cikin sa na kasa sama muna mafita a matsalar mu idan wani yaji haka tsawon lokacin da muka dauka a matsalan nan sai a ga na faye zama mai son kaina da yawa.
Nace haba daddy saboda may zakace haka kuma ai komai mukkadari ne daga ubangiji mutum bai dorawa kan shi lalura ai.
Yace nasan haka Rahama amma irin hakkurin da kikayi a dan tsakankanin nan ba kowa ne zai iya daure wanan irin matsalar ba haka.
Gashi ke kinyiwa wanan matsalar kankantar dauka da ace shekarun ki ya haura hakane nasan ba matsala zaki iya jure hakan har lokacin da Allah zai kawo muna mafita.
Nace ni ban damu ba daddy Allah dai ya bamu lafiya yace kwsnan zan tafi wani guri da nake kyautata zaton kila a shawon kan matsalan a can idan na tafi.
Nace daddy ban son kasawa kan ka tunane akan wanan matsalar saukin abin ma bani kadai bace a gun ka kana iya zuwa wani wajen wata kila acan ka dan samu kadace kayi.
Ni dai burina na zama mai cin wanan jerabawan da ubangiji ya aiko muna dashi bana zamo cikin masu kasa daurewa da kaddara ba.
Murmushi yayi gami da girgiza kan shi yace hakane amma wani lokaci abubuwa da dama sukan zowa bawa da sanadi don ai a gunki ne kawai wanan matsalan yake faruwa dani.
Nace dani da sauran duk a hannun ubangijin mu muke shi kadai ne kuma yasan dalilin yi hakan a gare mu don haka ka cire wanan damuwan a zuciyan ka kawai mu koma ga Allah ya kawo muna saukin alamarin.
Haka mukai ta hiran matsalar yana kankamay dani yana wasa da gashin kaina da yasha relexzer ya kwanta baya har barci yazo ya dauke mu bamu sani ba kowa da abinda zuciyar shi ke saka mai kan maganan.
Ina jin saukan numfashin shi alamar barci ne ya dan dauke mu na lalaba na mike daga saman gadon na shiga ban daki can na darji kuka na don na fahinci shima daddy yasan akwai matsala a wani wuri kamar yadda zarah ta fada min ranan.
To wa naiwa laifi yai min wanan mumunan hukuncin haka da sai mara imani zaiyiwa dan uwan shi haka a rayuwan zaman duniyan nan na dan lokaci kalilan.
Gashi na kasa fadawa inna ta matsalar da nake ciki kada hankalinta ya tashi na rasa wanda zan fadawa bayan Zarah da itama da kyat na iya fada mata komai.
Inna ce ya kamata na fadawa kuma ina jin nauyi da kunyan fadar irin magana haka a tsakanin mu ta yaya ma zan iyace mata wai miji baya iya kwanciya dani.
Don ni da farko banyi zaton wanan matsalar babba ne haka ba sai yanzu dana fahinci abin kamar ba mai karewa bane muna tunda yana iya amfani da yan uwa na ashe nice dai muke da wanan matsala din tsakanin mu.
Haka naci kuka na da tunanena nafito na koma na kwanta ban farka ba ga dan barcin dana samu sai bakwai na safe ashe hindatu nace ta kasa ta tsare taga fitowana daga dakin don haka take min wanan dabian kullun nake da girki.
Haka na daure na ci gaba da alamura na kamar kullun sai dai daddy yazo karyawa da safe sai naga ya kura min ido ban yarda mun hada ido dashi ba sai naji yace Rahama na amsa a sanyaye ban dago na kalle shi ba.
Naci gaba da abinda nakeyi yai shiru yana nazari na nazo wucewa ya riko hannuwa na abinda yasa ni dagowa na kalleshi ke nan yace dani.
Sai naga idon ki kamar kin yi kuka a daren jiya ko?
Ban tanka mashi ba sai kokarin wucewa da nake son ya sake ni nayi kawai nake da

Download complete TXT · Novel page