Murucin Kan Dutse
Chapter 105 of 146
hannuna dake rike da nashi din.
Tambaya na ya sake yi na sunkuyar da kai na kasa wani irin abu nakeji a zuciyana kuka kawai nake da bukatan yi a lokacin ko zanji sanyi.
Ya sake ni ban tsaya ba na shige dakina na rufo yakai minti talatin sai gashi dakin ya shigo yazo ya tsaya kaina ya dan jima a tsaye ba tare da yai magana ba.
Sai zuwa can yace nasan kina cutuwa Rahama nima abin ya fara fin karfina don ni kadai nasan halin da nake ciki a zuciyana.
Nace ni bashi ke damuna ba gida nake son zuwa kawai na kwana biyu ko zan huta sai naji yai murmushi yace cikin wata murya Rahama kina nufin kije gida ki fada masu matsalar da muke ciki ko may ?
Muryan shi ya ban matukat tausayi a yadda yai magana yace kina ganin idan sunji wanan matsalar da muke ciki zasu barki ki zauna dani ne haka Rahama ?
Ban sake magana ba sai kukan da nakeyi shima din bai min magana ba yana dai tsaye a wurin kawai can naji ya sa kai ya fice daga dakin a gurin Aisha nake jin wai daddy ya fita.
Mikewa nayi na shiga bandaki nai wanka tare da dauro alwala na sallah raka,a biyu nakai kuka na ga Allah.
Nan na zauna naci gaba da lazumi da jero adduoi sai tunanen abubuwa da dama dayazo min a raina na zamantakewa na a gidan daddy wanda a kullun da irin matsalar da nake fuskan ta a gidan.
Nake tunane shin haka sauran mata masu kishiya suke zaune a gidanjesu dama ake ganin kamar wani dadi mace ke ji idan anga tafito tana tunkaho a waje.
Ni kan gaskiya da muguwar rawa gwanma kin tashi da a illanta min rayuwana kan kishi gara kowa ya kama gaban shi a huta hakana.
Don in anci gaba da haka watarana inaji ina gani akan rayuwana za, a koma wama ya sani ko ana hakan nice dai ban gane hakan gare ni.
Da kyat na iya tashi na shirya na fito don duba girkin da Aisha ta riga ta dora muna ba laifi na samu taimin shi yadda nake so sai dan abinda baza, a rasa ba kawai nayi.
*** *** ***
Tun bayan fitan shi daga gidan abin duniya ya damu zuciyar shi ya rasa wa zai fadawa wanan magana sai bashir ya fado mashi a rai don ya fishi sanin irin matsalolin hakan nan.
Sun gaisa sunyi komai yace Bashir wallahi akwai matsala bashir din yace subbahanallahi matsala kuma Gentle yace wallahi babba kuwa.
Nan dai yake koro mai komai har yagama yi mai bayani Bashir din ya nisa yace lalai babban matsala ne wanan.
Yace sai dai gaskiya ko ka yarda ko kada ka yarda zan fada ma gaskiya wanan abin sihiri ne wanda mata keyi a tsakanin su.
Sai dai banyi tsanmanin yanzu wayewar kai din nan ashe an saura yin irin shi abune mai wuyan sha, ani sosai don dole sai ka nemi makarun shi.
Yace a ina zan nema Bashir kafa san ni ba wai na iya irin abubuwan nan bane a rayuwana asalima naki jinin alamari da sihiri shiyasa ma ban yarda da shi ba ni.
Yace to shike nan tunda baka yarda ba Allah ya sauwaka ko yace kamar ya ban yarda ba ai magana nake fada ma yanzu kan ai dole na yarda tunda ya faru dani.
Sunyi magana yace idan ta shigo kano akwai inda zasu tafi tare dashi aji ko may yakawo hakan sukai sallama ya kashe wayan.
Monday tunda safe na shirya don zuwa inda ake neman mu wurin interview din da za, ayi ban tafi da haidar ba gida na barshi gun Aisha na dauki mota na fita.
Koda na isa na samu wa yanda aka neme mu tare sun hallara a wurin ko na shiga don gaisawa da mutanen arzikin mu.
Ban dade da zuwa ba aka kirani na shiga ba wani tambaya sosai akai min ba don sun riga da sun san mu dama don haka bamu sha wani wuya ba sun dai karbi takardun mu kawai.
Sai bayan mun dawo ne Aisha ke fada min ai akan fitina daddy sunyi fada da maman Ihisan nan dai ta labarta min komai.
Sai da na huta nafito falon don bata ma san dawowa na ba gidan sai ganina tayi falo zaune muna kallo.
Sai naji tace an dawo ta zubar dama an saba ana mazuru ana shaho may zai sa a iya zama gida tunda an riga da ansaba hurda da wasu maza.
Take naji raina ya baci sosai sai dai Allah ya taimake ni ban tankata ba tunda na gane hassada ne abin nata ba komai ba.
Sati biyu sai ga shi anturo muzo mu karbi appointment letter din mu ya fito ban bata lokaci ba na tafi na karbo inda sabon wata zamu fara aiki dasu din .
Wanan dalilin yasa na matsawa daddy kan son zuwa gida na dubo su yaso ya hana amma da na matsa yace mu shirya idan zai shiga ya sauke mu.
Take na fara shirin tafiya tsaraba sosai na hada tunda safe muka kama hanyan kano tare da shi.
Banzo da yaran ba don suna school dagani sai Aisha da baba da haidar mukazo kawai anty tai mamakin ganin mu don bata san zan shigo ba.
Duk da halin da nake ciki amma ita a idon ta taga na mata kyau ne sosai na sake na zama wata classic lady dani.
Ban dade ba a gurin ta na fita zuwa part dina inda na samu duk yayi kura dayake dare ne inda zamu kwanta muka dan gyara tunda safe muka shiga gyaran wuri da taimakon gajiye muka gyara ya zama neat.
Nan take min hira wai yanzu ai anty ta karaya sosai tana son janta a dawo irin da can baya amma ita gaskiya tana tsoron hakana don wanda ya zarge ka a baya bayan yasan halinka amma ya rufe ido yai ma sheri ita bazata zauna da ita ba.
Tace takan dai dan taimaka mata wani lokaci can ba, a rasa ba sai da nai kwana biyu a kano na shirya muka wuce gida.
Mun isa da wuri don haka kafin wani lokaci akasan da zuwan mu nan yan uwa da abokan arziki suka dinga shigowa taron mu sai dai naje washe gari Allah yaiwa Jatau mijin Suwaiba na rasuwa muka tashi da wanan tashin hankalin kuma a gare mu.
Koda naje gidan abin ba dadi ruwa ma babu shi a gidan ko kadan nasa akira masu ruwa suka cika duk wani kayan dake gidan take na bada kudi aka sayo masu abinci sai dai suwaiba ke cewa dani ai rabawa akeyi kowa yai nasa nace ba matsala tabar masu sai a kawo mata nata.
Ban samu zama ba don kwana uku a gidanta muke wuni sai dare nake dawowa gida don haka ban samu kebewa da Innata ba.
Sai ranan da aika sadakan uku bandawo ba saida na wadata Suwaiba da duk wani abin bukata suma kishiyoyin nata nai masu nasu irin alherin gwargwadon hali na dawo gida ban kai dare baranan gidan .
Da dare muna zaune muna hira da Aisha uwarta ta kirata bayan fitan ta ne Inba ta ke cewa dani wai niko yarinya lafiya kuke kuwa don naji ance wanan hatsabibiyar kishiyar taki takoma can inda kike da zama yanzu ?
Nace a sanyaye lafiya muke inna sai dai dan abinda ba a rasa ba can kuma ba kullun bane tace to Allah ya kyauta a daita hakkuri da jama, a don Allah.
Nace insha Allahu Inna sai na boye mata don ban san yadda zan iya fada mata komai dake faruwa ba a tsakanina da daddy din.
Sai wurin Attu ne da naje cikin hikima irin nasu na manya take tambaya na na sake jiki sosai ina fada mata matsalar dake damuwar mu tsakani na da daddy din.
Take naji yar tsohuwar ta saka min salalami tana tafa hannayen ta tace yar nan tun yaushe hakan ke faruwa na fada mata tace to kin fadawa uwar ki da kikazo nace haba attu ko nasha giyar wake yaya zan iya fadawa inna wanan maganan kuma.
Ko ke dai daurowa tayi da har na koma bazaki ji shi ba a bakina ba tace ki koma ina cikin wanan irin laluran haka na ai banga ta zama ba .
Dole ne na bazama wurin masana a walwale maki wanan sihirin don idan ba walwale shi ba ku ba zaman lafiya ko zaman aure a tsakanin ku tunda akwai cutawa ga hakan.
Wunin da banyi ba ke nan don Attu ta fita tabar mu don haka na wuce uguwar mu na gaida mama Altine da matan babana.
Gidan mama Altine na fara shiga duk da mun hadu a gidan Suwaiba da ita amma tana ganina ta shiga ina taka saka dani ta shimfida tabar muka zauna ni da yaran ta kawo ruwan randan kasan ta mai tsabta muka sha.
Tace Rahama har na fara zargin ko don irin halin da uwar dakin naki ta tsiro dashi yasa kike ja baya dani kuma yanzu.
Nace ni kan yaya zanyi na gujeki mama aisai butulu ke mantawa da uwar shi irin halarcin da kikai min duniya ko uwata data haifeni ai ya tsaya nan.
Tace to na gode Rahama nan muka shiga hira tace zata dafawa yaran abinci suci nace barsu mama kada ki wahalar da kanki mama kinga abincin su nan biscuit tace yaran birni ke nan.
Mun sha hira da mama amma ko ta dauki halin da anty take min sai na kawar da zancen nace da ita ai yanzu an daina dama rudin shedan ne kawai.
Sai bayan la,asar na bar gidan na shiga gidan mu tsatsaye na gaidasu mama tsufa ya taso mata kanta yai wani farin gashi gashi a dankare mata ba gyara hakoranta na gaba sun zube.
Tabani tausayi sosai nace da ita idan na koma zan sa ai mata hakoran roba tunda dai batai tsufan da zata rasa hakora ba haka na san dai daya ya fadi wurin fadan su da amaryan ta a baya amma sauran biyun fa ?
Nakawo alheri nai masu nace zan dawo don in gana da babana naga jikin nashi yadda yake yanzu.
Sai gap da magariba nakoma gida inda na samu har Attu tazo nema har sau biyu ban dawo ba sai ta bar sako da magariba zata dawo mu fita.
Na samu yaran sunyi barci koda tazo ban zauna ba muka fice tare zuwa inda zamu nida ita sai kanina Audi da ya raka mu zuwa unguwar da zamu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A TAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
80
Tun bayan waya na da Zarah sai hankalina ya fara tashi don ba karamin tsoro kalamin ta ya bani ba.
Ni lafiyana shine yafi min komai a rayuwa na in dai zasu barni da lafiya ina iya bar masu mijin su a zauna lafiya.
Amma ta ina zan fara wana san yai muna wanan shamakin a tsakanin mu ni dashi don duk kishiya kishiya ce dai.
Amma wa zan zarga a wanan matsalan shin hindatu dake nan zaune tare da mune ko kuwa wa yanda ke gida ne sukai min hakan wai ?
Nan dai na zauna ina ta faman tunane wanda har na gama ban iya gane komai va daga ciki abinda dai na yake da ga karshe shine zan dukuma nafi da kaimi wurin kai kuka na ga Allah dayai min tsari akan duk mai bina da wani mugun manufa.
May na tare masu da har yai zafi haka sukai muna wanan mugun asirin da sai jahili zai iya shi.
Sannu a hankali na fara rama a tsaye gashi bayan zarah aminiyata ban iya fadawa kowa wanan zancen don da kunya aji shi a bakina haka.
Muna cikin wanan halin ne ranan sai ga massage ya shigo a email dina asibitin da nai bautan kasa suna neman mu muzo interview wurin su.
Murna farin ciki duk ya kamani a lokaci daya daddy kawai nake jira ya dawo na fada mai naji may zai ce akan zancen.
Koda ya dawo nice da girki ranan don haka na tsara kwalliya na dana bata lokaci wurin yin shi ga lafiyayyen abincin dana girka don shi a ranan.
Bai shigo ba sai yamma lis ya dawo gidan ina dakina ina bawa yarona nono naji muryan shi Atika na mikawa yaton bai koshi ba ya dan sa kuka nace fice dashi zuwa dakin ku don Allah,
Tana fitowa dashi uban yaji kukan shi yace kai Atika ya akayi ne yake kuka kawo shi nan ta mikawa uban yoron ta nacewa wai bai koshi da nono bane shine yake kuka.
Daddy yace ita nonon nata na sayarwa ne ko may zatayi dashi da bazata bashi ba ya sha ya koshi da kyau.
Daga kofa ina fitowa nace cikin wani murya najan ra, ayi nace wallahi daddy ya faye tsotso shi bai koshi da nono.
Ya dago yana kallo na na tabbatar shigan tai mashi kyau don ni kaina na sani saboda kayan ya fitar min da kurciyana a fili.
Yai murmushi yace nawa za, a sayar muna a bashi ya sha ya koshi yadda yake so na sake cewa daddy don Allah barshi yanzu Aisha zata kara mai da abincin shi yasha.
Wallahi Rahama kiji tsoron Allah in baki son Allah ya kama ki da laifin daukan alhakin wanan yaro yaro dan wata shidda da kai ace bai sha nono ya koshi ba sai wani abinci can na bature.
Ban so ba namika hannu ina karban yaron a wurin shi nace jishi dan Allah sai dan banzan tsotso dashi aikai ka baci da ci wallahi.
Komawa mukayi daga ni har shi muna dan hira yaron na shan nono yace ina yaran nace sun fita wasan ball sukace.
Yace kai yaran basa ji wallahi nace to maza ne ba a raba su da irin haka tunda ba mata bane sai dai a saka ido ga muamulan su kawai.
Sai dai haka din amma ba kwar ba dai kan don an wuce wurin kwaliyan da ba biyan kudin sabulu ai aikin banza ne yin shi.
Gaba daya muka juya inda take tsaye tana magana cikin tafiya zuwa kofan baya shi dai na dauka bai fahinci maganan ta ba amma ni sai na fara zargin anya ba daga hindatu muke samun matsala ba kuwa ?
In ba shi ba yaya tasan abinda ke tsakanin mu ni dai na san daddy ba zai taba fada mata komai ba a tsakanin mu duk yadda suke kuwa don shi ba namijin dake zama yai maganan wata matar shi da wata ba.
Tafe take tana waka mai kama da habaici kamar an dauke ta an rada a kasa ta fadi kasa tim a tsakiyan falon.
Ba karamin buguwa tayi ba ga wanan faduwan shine yace innalillahi may ye haka ya akai haka kuma sannu tashi.
Bai mike ba yana zaune inda muke yana cewa may kika taka kuma haka ya kada ke wanan faduwan haka ai sau ki karye ko ?
Allah ai ba azzalumin bawa bane don shi ba ai mai gadara in daukan alhaki abin yine kadan mutum ya fara gani a rayuwan shi.
Ina fadin haka na mike na bar wurin ban mata sannu ba ta mike da kunya ta nufi dakin ta tana cewa ban san shege yaron da ya zubar da ruwa ba a saman ties din nan kuma ?
Bai jima ba ya tafi sallah sai bayan ya dawo ne na fito don bashi abinci mun zauna yana ta latsar wayan shi har na zuba mai abincin na aje a gaban shi ya kalli abincin yace duk ni zan cinye wanan Rama ?
Kada fa nai kiba kizo kice dani na tsufa maki nan gaba ki fara dan kwanaye kwanaye kuma kina baki son zama da tsoho.
Nai dan dariya mai kama da murmushi nace ai tunda bance ma tsoho ba da farko yanzu ma bazance ba don ni din ma yanzu ai ba yarinya bace.
Muna cikin hiran sai ga ta fito daga daki tace dear kasan na fadi a gaban ka amma ko ka shiga ka dubani kaga ya jikin nawa gashi yanzu duk jikin nawa ciwo yake min wallahi.
Yace ki sha magani mana tace ni asibiti nake son zuwa aduba min kafana don ciwo yake min yace amma ba yau ba kan don dare ya yi yanzu.
Ta wani bata rai bataso haka ba taso ne ta tasa shi a gaba sukama hanya zuwa asibi a cikin daren nan ta nuna man iyakana dashi sai bai biye mata ba yace tasha magani agani zuwa gobe.
Sai da ta wuce nace dama ina son ka huta na fada ma an turo min da sako ana neman mu ranan monday wurin interview asibitin da mukai service.
Yace a, a shine baki fada min ba Rahama wanan ai ba karamin magana bane yanzu zanyi waya da MD naji yaya ake process din abin naku.
Nan a wurin ya kira sukai dan magana yace ba matsala na shigo kawai ranan monday din za a duba ai ina da kwazo sosai sun sani.
Mutum zai iya fahinta yanayin mu a lokacin yadda muke daukin junan mu sai dai ba dama komai don engine bai aiki a kaina ko kadan dan wasan da ma yakanyi da farko idan yayi yanzu sai gari ya waye mai ba lafiya a jikin shi.
Mutum zai gane yana cikin damuwa don sai matsala ya faru zaka san idan mutum yana kaunar ka baka sanin zurfin kaunar sai idan matsala ya gitta a tsakanin ku zaka gane zurfin kaunarva gare ka kasan yadda mutum ya damu da kai.
Hakane yanzu a kullun bakin daddy bai gajiya da kwantar min da hankali yana bani hakkuri kan matsalan dake faruwa damu din.
Nakan yi murmushin yake nace haba daddy bakomai mana ai matsala ne kowa yasan ta sai