Murucin Kan Dutse

Chapter 119 of 146

kodai har da karatun kishi kika koyo ne can ?
Nace dama aina iya ina dai binku sannu ne don biyayya kuma yanzu naga kamar kuna ganin tsoron ku nake ji ban iya daukan wa kaina incin hakan ?
Yace musan kin iya ai har kin wuce wuri tunda har da yaran mun kin hana muga abin sai labe labe kika barmu dashi kawai.
Daga karshe muka juya kan hiran karatuna yake cewa gaskiya na godewa Allah abin kamar a mafalki wallahi Allah.
Nace a ro ai baku so hakan ba dani ku yace haka dai kikace ko mu wuce ace muna mijin doctor ai dadin mune ko.
Da zai tafi ya kawo alheri yabawa yaran nace haba harda wani guzuri kuma yace ai wanan ba komai bane ni dai naji dadin mutuntanin da kikayi ai.
Yanzu yaushe ne zaku koma can din ku bar nan don na sani kafin natafi in ma da hali ki gobe ne sai nazo na kai ku da kaina kafin na wuce ai ?
Nace kai haba dai kamar wacce ta matsu sai na shirya may be nan da wata ko fiya da hakan dai .
Yace a, a don Allah k bar wanan zancen mana ko so kike abokina ya samu hawa jini ai wanan horon ya isa hakana don Allah.
Nace horon may kuma sai kace wanda baida wasu matan a tare dashi dai don Allah barni har na shirya a tsanake please ?
Ya daure fuska yace to naji amma insha Allahu nan da Saturday mai zuwa zan zo na kaiku gidan da kaina nace da sauri a, a ni bani hurda da Saturday ai don nasan aibun yin abu a wanan ranan sai dai Laraba mai zuwa na sama ko Friday din ta.
Yace yadda kikace hakan za, a yi rankishi dade aiko hakan ma mun gode sosai wallahi don zan tafi da kwarin gwiwa ai.
Nace amma fa ia sani gidan nan zamana yakeyi ba zan sake shi ba muddin naga baiyi yadda mukai alkawari da kai ba wallahi wallahi sai dai ku wayi gari na dawo nan din kuma bazan taba kara yarda da ku ba har abada.
Yace insha Allahu ma zaki samay mu da cika alkawari da yardan ubangiji kada ki damu yi muna dai fatan alheri mu samu mu fita daga tarkon ku na mata tunda haka Allah ya nufe mu da gani a kan ku.
Har bakin mota na raka shi ya wuce yana min godiya na koma ciki na zauna sai lokacin hiran mu dashi ke dawo min a raina nai mamaki yadda na amince mai da bukatan shi haka ?
Ina fa jin tsoron kada sai na koma daddy yace bai san da zancen ba yazo ya karya alkawari sai gabana ya fadi dam a lokaci guda.
Na dauki waya nai dialing din nomban shi kira daya biyu gana uku ya dauka ina jin yana magana yace hello nace yaya Bashir sai kaga na kira ka kuma yace eh wallahi ko kinyi mantuwa ne dai ?
Nace kamar ka sani nace wallahi yaya Bashir kada na koma gidan daddy da zama yazo yace baisan da zancen hada mu wuri daya ba daga baya.
Na rantse da Allah idan yai min haka sai nayi inpiching din ku a kotu daga kai harshi daga baya kada kuce ban fada maku ba.
Yace subbahanallahi Rahama may ya kawo wanan zancen kuma haka kodai kina shawara da watace ban sani ba ?
Nace aini ba haka nake ba banda yawan kawaye haka kuma ban sharing din matsalana da kowa sai idan naso na dai kirane kada na koma yaga na koma yace zai min wullakanci kan hakan ba zan dauka ba.
Yace kada kiji komai kwantar da hankalinki ashe daddy yana kusa suna tare yana jin may nacewa Bashir din ya kada kan shi kawai.
Sai da muka gama wayan yace Bashir yanzu na gane dalilin wasu maza da basu yarda mace tai ilimin zamani bayan secondary.
Wai yau Rahamane ta zare haka don Allah yarinyar da ko yatsa aka sa mata a baki bata ciza shi idan ba taso ba amma jita yanzu don Allah.
Yace nima abin har tsoro yake bani ai sai da mukai wanan maganan da ita bashir din yace wallahi ba komai bane sannin ciwon kan ta tayi yanzu kawai duk shi ya jawo hakan ba komai.
Sai dai gaskiya sai kayi da gaske don akwai magana babba idan sun hadu a wuri daya dadin abin kasan halin kayan naka ka iya zama dakowan su ko.
Amma dai ayi a sannu ayi adalci don Allah a tsakani kaga wanan daukan wacce bata girki ka fita da ita don Allah a daina tunda suna da motan su kowa taje gashin kan ta don ba kowa fa zai iya hakkurin abinda yarinyar nan kai mata ba.
Yace ni may ne mata illa kishi data saka a ranta kuma duk haka suke ai da bakin kishin junan su yace dashi ai dai ba a taba ji ba sai yau din nan ko ?
Nan dai suka tattauna daga karshe suka shiga gari don yin wani harka daya shafe su can.

********* ********* *********
Ban fadawa yaran batun tashin mu ba gidan sai ana saura kwana biyu mu koma can muna falo dasu mun barbaje nace dasu.
Tau yau dai saura kwana biyu mubar gidan nan dai sai duk sukayo min ido caaa akaina sai Aisha ce tace dani anty ina zamu koma kuma bayan nan din , ?
Na bisu da ido nace daddy yace bai yarda da zaman mu nan ba dole mu koma gida mu zauna can wirin shi.
Har suna hada baki wurin cewa inda mama ihisan take nace can din kuwa kai kai inji Nasir yace wallahi ni haka bai min dadi ba nace ina ruwan ka kai da kake namiji baka zama gida kuma kwana nawa ya rage maku ku tafi ku barmu nan din.
Kowa ya dinga fadan albarkacin bakin shi nasan dan freedom din da muka samu yanzu akwai matsala idan ance za ai muna abinda akayi a baya zama ba sakata ba wali a can din.
Basu so ba haka dai na kwantar masu da hankali muka shirya ba komai muka dauka ba don wacin gadi zamuje yi mugani ga watauna ba san mu dai shiga din ba agani.
Dogon motar su na wurin aiki ya turo muna ta kwashe mu da kayan mu zuwa gidan ni da yarana da yan matana ras har su uku don ko wace ta girma yanzu.
Mun shiga da sallaman mu babu kowa a falon sai tv dake faman aiki a wurin kawai shi kadai.
Ban tsaya ba muka wuce part din mu a rufe yake na dauko ke daga bag dina nabawa Aisha ta bude muna suka fara shiga da kayan da mukazo dasu ciki.
Jin motsi yasa ihisan fitowa tare da yar aikin su sai taga muna suka juta da sauri suna fadawa hindatu din tace wa Rahama fa a gidan nan yai daidai Aisha ta fito falon tana jin su.
Ta koma tana fada min nace tasan abinda tayi kila kada na dawo yar iska wacce bata tsoron Allah ga alamarinta.
Aiko kamar ai aiko mata da sakon kayan ta har muka gama shiga da kayan mu ciki ba wanda ya leko falon cikin su.
Dama munzo da abincin mu da zasu ci don haka bamu damu da rashin girka muna komai ba.
Sai bayan wani lokaci daddy ya dawo gidan ina zaune na idar da sallah la, asar naji shi da yaran sukan Haidar da Abdul sukayo daki da gudun su da suka gan shi.
Ina may nene wai haka ya bude labulen dakin ya shigo yana cewa ikon Allah daddy kuma kuke tsoro.
Daga yaron nayi ina kwashe salaya na nace dashi sannu da dawowa fuska a daure yace yauwa kun dawo lafiya.
Alhamdullahi na bashi amsa dashi ya nufo yaran suna kokarin shige min a jikina basu son ya dauke su wai .
Yai murmushi ta re da kadan kanshi yace baku sanni ba ko maman ku ta hana ku sani na ko ?
Ni dai banyi magana ba na bude wardrobe na ciro wani dogon riga nawa Abdul ya rike min kafafuna nace kai tsaya dan Allah ni kada ka kadani kasa kaji.
Ya zo ya duka har inda muke ta dauku yaron ya fara kuka zai fita dashi shiko haudar duk yabini ya make shima nace kubi daddy ya sayo maku ice cream ba zaku sha ba yaran suka kada kai nace to kuje gun daddy ya sawo maku biscuit da sweet yanzu zaku dawo da big bros zaku tafi cewa Nasir sai suka yarda suka bishi.
Bai jima ba ya fice dasu har jinior da Nasir din suka fita tare yan matan suka dawo guna suka zauna muna hira.
Sai gab da magariba suka dawo gidan hindatu na falo taga shigowan shi dasu tace bissimillahi diyan gwal sun dawo ke nan bamu da hutu yanzu gidan nan balle aiyi lokacin mu.
Tace ashe kin gane ke nan farin cikin rayuwa na sun dawo duhu ya yaye min banda lokavin kowa yanzu sai su.
Aiko tace dawa Allah ya hadata bashi ba kuma don may zai fada mata hakan ai wullakanci ne ba sai ya fadi ba kowa ya sani ai.
Aikin banza may ye bamu sani ba mu dama ai mun ssn komai shiyasa aka dawo aka lake wani gurin har a gama shirya maka don a samu a mallake mu wallahi duk abinda mutum ya dauko ya kare a kansa.
Munafuncin banza da wofi sai da aka gama ta zubar da bin dangin miji a na rokon su sannan aka dawo muna mu Allah ma dai ya cece mu da ciwo wallahi.
Yace cikin wani tsawa ke hindatu ya isheni haka duk kika kara bude baki kika zagar min mata na ki kikai mata sheri yanzu zan dauki mataji a kan ka.
Eh lalsi shirin ki na kyau wallahi Rahama amma mu zuba dake a gani wallahi sai anga wanda zai raina kan shi.
Ina daki ina jin ta nace ohoni Rahama na dawowa turke na mai cabo dada an fara ke nan kuma amma zan daga mata kafa na iya gudun ta dai.
Shi oan shi yai mamakin yadda na kyale ban tan ka ta ba a lokacin don har lokacin ma ni bata sani a idon ta ba haukan ta dai take kwasa.
Ina jin komai na na dake a dakin bayan sunyi sallah ya fito da yaran suna zaune falo haidar na kuka jinior ya taba mai biscuit din shi sai ga wayan Raliya ya shigo mashi a lokacin.
Ya dauki wayan tana jin kukan yaron tace kana inane haka nake jin kuka yaro kuma ?
Yace ina gida zaune daidai fitowa na daga daki in gaidashi tace gidan ka fa ya sake cewa eh a gida nake zaune mana.
Tace wake kuka yace Haudar ne da Junior ke rikici haidar sun dawo ne ko may sai raji murya ina cewa kai Jinior baban kwabo ne fa naka zaka sha na kanin ka kuma kyale bros sai na dauko nashi ai kasha kaima.
Tace dashi eh lalai na yarda kuwa ashe akwai munafunci ban sani ba haka sai yace muna funcin may sai ta kashe wayan ta.
Kallon wayan yayi yai tsuki tare da murmushi yana girgiza kan shi kawai na fahinci komai amma sai nai kamar banji ba naci gaba da magana da yaran na bar wurin ban sake magana ba.
Tsaye yake yana waya yace Bashir maganan ka gaskiya wallahi na fara fahintar komai a yau din nan da dawowan Rahama gidan nan.
Nan dai yake fada mai komai da yafaru tsakanin shi da Hindatu da Raliya din yace bashir kaji min matan nan yadda taita rokona kan na yarda muyi aure zata kawo min kwanciyan hankali a gidana.
Yanzu gashi na fahinci shigowan ta ma yafi tayar min da hankali fiye da baya can don ko tsakanin ta da sauran babu kauna kullun cikin makirci take wa abokan zama.
Bashir tace kafara ganewa ke nan yanzu sa masu ido da a tsakanin su da kan su zasu fahinci komai akanin kaga am fara shiryawa ai mata ba a shiga tsakanin su sam barsu suyi tayi da kan su.
Ban karbi girki ba sai washe gari nayi girki ba zance komai ba don nasan mai karatu zatace dama ahi nake so eh ko shi din ne ai mutum nake mai jini a jika dole ne nima naso mijina dan yaushe rabo.
Bayan komai ya kammala ya dan rugumoni yana cewa Rahama na amsa a dakile yace na rokeki daga wanan karon kada ki kara nisan ta kanki gareni.
Dariya ma maganan shi tabani nace nina nisanta kaina gareka ko kai kanisan ta damu don kawai baka dauke mu da daraja ba kayi mun haka don ran matan ka yai dadi.
Su sancewa baka damu dani ba, dani da babu duk daya muke a gare ka don kawai ran su yai dadi su san ka wulllakan tani.
Yace bar wanan maganan ke bazaki gane bane ko nai maki bayani sai kiga ai da gangan nai maki hakan.
Nai murmushi nace ni yanzu aikai nake saurare naji hukuncin da zaka yanke wanda zai kawo fahinta a tsakanin mu kowa ya zauna a matsayin shi.
Yace na fahince ki na kuma gane komai yanzu da kike nufi da fatan zaku kara hakkuri da junan ku nace ita Zulfa sai zuwa yaushe ne zata dawo nan garin.
Yace sai na shirya nace amma daddy baka ganin ana shiga hakkin ta da yawa duk yaran mu suna nan suna samun ingantaccen karatu ita ko tana can an barsu da nata yaran.
Ji nayi ya numfasa yace zan shiryawa dawowan nata nan da yan kwanaki kadan insha Allahu zata dawo amma kin san dole a kwai tsarin daki da zamuyi don nan din dakuna shidda ne kawai a gidan ke kina da biyu hindatu biyu sai nawa dana su Nasirda suke a ciki.
Nace hakane yace amma ba matsala ita Ihisan sai ta dawo dakin da yaran ki ke ciki su zauna tare ko ta koma dakin uwarta da zama sai ta zauna a dayan har mu samu daki araina nace anzo wurin.
Nan inda mukayi a nan muka bar zancen sai ko ga Zulfa a cikin bazata tazo ni dai na dawo aikin dare na samay ta a gidan.
Har dakin da take na shiga nai mata sannu da zuwa na dawo dakina ina cire lab coth dina sai gata a dakin nawa tashigo.
Nace a, baku hutaba kun taso tace ina naga hutawa Rahama matar gida tace bani zama a kusa da ita nai murmushi nace haba dai hakan ko zai yuyu.
Yanzu bari nazo nace da Aisha dake ciro min kaya a wardrobe Aisha yanzun keda su Amira ku koma dakin can na yar aikin maman Ihisan sai ku gyara wa anty wanan da kuke a cikin sa.
Nagama magana sai ga daddy ya dawo daga gun aikin shi yana tambaya suna ina nace magani yaki nema ke nan.
Sun gaisa da ita yake cewa kin kai kaya ki dakin ko tace mai dakin tace bata san da wanan zancen ba a falo ma ta barni zaune tun dazun yanzu da zanyi sallah kagin Rahama ta dawo ne yar aikita tace na shiga nan nayi.
Ya juta zai fita nace dashi da har nace su Aisha su gyara mata wanan da suke a ciki ai su sai su zauna ina ya tambaya cikin fada da dan harara nace su zauna da ihisan din a can .
Yace ba haka na tsara ba babu kuma wanda zai canza min tsari na kan hakan yaran ki su zauna nan kusa dake kina ganin su yafi.
Nan dai suka fice a tare ya ga su Aisha sun fara fitar da kaya su yace su maidashi ciki kawai a wancan zata zauna.
Shi da kan shi ya shiga dakin ya samu mai aikita a ciki yace mata ke koma gun uwar dakin ko ta mai dake dakunan dake baya nan matana zata zauna ta mike tana cewa tau Alhaji.
Ta shiga gun Hindatu ta fada mata sai go gata tafito da saurin ta tana fadin banga wanda zai min wanan ba ni da wurina ace za, a ai min kutse yace gidan ki ko gidana ?
Tace gidan kane amma may zai hana ka kaita can inda Rahama ta zauna do sun fi kusa ai da ita yanzu nagani.
Yace bake zaki tsara min yadda za yi da gidana ba ya juya gun Zulfa ce ga dakin ki nan zaki zauna gobe a shirya yaran su fara shiga school da yan uwan su.
Daga haka ya wuce ance ga kofa aiko ta shiga bakin ta inda take shiga ba nan take fita ba zagi gori ba wanda mu ukun bamu sha ba a ranan gun ta.
Nan dai dole aka dawo da tsari sai dai abinda ke daure min kai shine duk wani abinda ke gudana gidan yana kunnen Raliya tasan komai kamar tana zaune a gidan.
Sai kuma nazo na fahinci cewa yanzu idan zatazo garin sai ranan da zanyi girki tayi na farko na kyale ta sai gashi tayi na biyu again shine na nuna ban yarda bada hakan.
Don ta shigo garin kamar yadda ta saba sai gashi ya dawo ya samay ni a kitchen muna hada abincin dare ya dan tsaya a wurin yaran can ya wuce dakin shi sai ya aiko z kirani naje na samay shi yayi wanka ya sauya kayan jikin shi ko.
Ina karasowa yake cewa har kun gama ne nace da dan saura ya juyo da kyau ya fuskance ni nasan yana da magana sai na fuskance shi nima.
Yace tau gashi kuma yau Raliya tazo garin kuma kinga dole a can zan kwana gunta ke nan tunda tazo ba nan ba.
Nace ok ta shigo ashe yace eh wallahi nima nafito meeting ne na samu called din ta take fada min wai

Download complete TXT · Novel page