Murucin Kan Dutse

Chapter 122 of 146

so.
Ni dai ina jin ta nasan koni haka akaita zagina a baya ban ma sani ba ko yanzu ai ban debe tsanmani don kishiya sunar ta kishiya ai.
Ranan Laraba da ya zagayo ya kwashi yara ya fara kaiwa shi da Sani da motocin mu da duk wanin abinda za, a bukata sai mu da bamu tafi ba mun tsaya sai an kwashe kayan kowa a gaban idon shi.
Bayan an gama ya dauke mu shida zulfa a gaba ni da hindatu muna baya sai hadiyan rai takeyi ban san may ya bata mata rai ba a lokacin tundai safe take hakana a gidan.
Gida ne babba mai kyau ga tsari shigen ginan mu na na can kano sai dai wanan din ya nuna mai aikin wayewa da akayi na zamani.
Mun shiga da addua da godewa Allah yaran ne suke nuna muna ga inda daddy yace namu ne duk komai iri daya ne har ginan wanan dai dakunan da aka kara biyu sune banbancin mu.
Amma bayan hakan komai iri daya ne kowan mu zata tashi da dakuna biyu a bangaren ta.
Abin yaiwa kowan mu dadi sosai nace Zulfa ta fara zaben inda take so sai bayan ta zaba na farkon ta dauka ni kuma na dauki wanda ke daga ciki ni yafi min sauki ma don hayaniya da ban so sosai idan ina resache.
Wata sabuwa Hindatu ce tazo tana fadin kuji min wanan tsohuwar wofi din duk sai muka waiga gunta muna kallon ta sai take cewa wai fa Raliya ke fadin ita bazata zauna part daya dani ba sai dai wai a hada ta da Rahama su zauna wuri daya watau mu tsofin mata ya hade mu wuri guda ke nan.
Kuji min tsohuwar banza mai mayar da kanta baya don Allah wai kamar Raliya ke cewa wai mune tsofin mata jifa don Allah.
Dariya zulfa tai mata tace haba haba dai ke da mutumiyar taki kuma za a ji kan ku ai bai dace ba haka ku dai sasanta kan ku acan.
Tace bari Zulfa matar nan ta bani haushi wallahi bata san ina dakin ha ta bugo mai waya tana wanan maganan.
Ai ban bari takai karshe ba nace ke tsohuwar banza wace bata san may takeyi ba wa ye tsohuwar bake ba ke ba a gujeki ba shine ke zaki guji wani.
Dariya ta bani sosai har na kasa hadewa sai da na fasa shi nace da ita amarya ce fa maman Ihisan tace kai amma dai ke amaryan may can.
Haihuwar ta hudu fa har da bari tace min wanda ma aka sani ke nan fa na boye wayasan su.
Tunda shima uban aiki bai san hakan ba sai daga baya don ta boye mai komai da farko akan zancen diyan nata.
Nace kai hudu fa kikace tace wallahi Allah ko kuma dasu zata dawo nan gidan wai da sauri Zulfa tace wani gidan ?
Tace ai sai kiyi tunda uban aikin ya yarda mu may zamuce na san dai akwai tsiya kan a gidan nan don ban yarda agola sufi min diya na.
Dariya sosai muke mata har taji haushin mu tace ai dole kuyi mun dariya tunda baku aka taba.
To maman ihisan aiko mu ba a bari ba don gidan gaba daya ne kila tsarin zaman a tare bai mata ba ta bullo ta wanan tsigar kuma.
Kuma wallahi dole ta zauna ba tunda ba fin kowa tayi ba ta zo a zauna in kasa akaci a kwaba tare a hade shi.
Zulfa ta kallo inda nake tai min signal da idon ta wai nai shiru nace yanzu dai ai gamu gani ko tunda dai namu dama idone mai daki shiyasan in da ruwa ke mai yoyo.
Ta dan jima tana ta tonon asiri har ta gaji ta koma wurin ta Amira tace wai mummy ku baku san tana da yara bane dama ?
Nace nifa ban san komai bz a kanta kin san ba ta dade ba na tafi germany shiyasa ban ma damu da nasan komai ba akanta.
Tace wai danta ya girmay ni nisa ba kusa ba wallahi baki gan shi gudan babba dashi fa ya kusa kai daddy tsayi muka kwashe mata da dariya kawai.
Yanzu mun samu hutu da rage fitina don kowa akwai kitchen a part din ta sai daga baya nake ji ranan a wurin sani wai sayen gidan yayi ashe da kudin shi ba haya bane.
Nace a raina lalai alamarin daddy ya bunkasa sosai ke nan har ya iya sayen wanan katon gidan haka a garin Abuja don iyalin shi.
Saura kwana hudu a tashi da azumi daddy ya shigo muna zaune a falin mu Abdul na saman jikina yana rikici wai sai na goya shi bai son na kowa sai ni.
Tun daga main falo yake jin kukan yaron na tashi ya shigo bayan ya sallami bakin shi sun tafi yana fadin.
Wai may ya samay shine haka yake kuka daidai ina dukan shi don ya isheni da fitina tun safe yake hakana a gidan anyi lalashin duniya yaki yarda da kowa.
Nace fitina yake ji yau haka kawai ya tashi haka yanzu wsi shi sai na goya shi yace to may zai hana ki goya shi din yaro jeka ta goya ka kaji Allah ya taimake ka kai ba wanda ya hana ma bayan ma.
Ni wai ban gane ba fa har yanzu naji shiru in dai ba planning kike yi ba Rahama kin dai san bani kaunar wanan abin ko kadan.
Murmushi nayi nace Allah dai ne ya tausaya min don wanan dan fitinan idan ina zan iya dashi haka.
Take naga ran Zulfa ya baci har ya lalashi yaron ya dauke shi zasu fita baitai magana ba a raina nace kishiya ke nan baki da tabas ai dama sai dai a tafi a rufe kawai na ciki na ciki dama.
Ya kai kofa ya juyo yana fadin yau Raliya zasu dawo fa ina fanin don tace dani sun taso dazun.
Ita dawa zasu dawo naji kace zasu dawo inji zulfa da sai yanzu tai magana dashi tun da yai min maganan samun ciki a gaban ta.
Yace idan tazo ai zaki gani tace aiko gamu gani din Allah ya kawo su lafiya mu sha kallon yan birni.
Ya dai fice da yaron abinshi daga falon bai tanka ta ba nima don ta san na fahinci may take nufi sai na share ta na ci gaba da karatun wani takarda dake hannuna.
Haka har muka watse don ra san na gane manufanta amma kada abin yai nisa sai naji tace dani ashe yau Rahama kina da baki ke uwar yaya.
Nace gaki uwargida ina ni ina wani kwashe kwashe can kedai zata dinga barwa yaran idan zata tafi ai tunda kece uwar gida sarautar mata.
Tace a ina uwar gidan take nan kudai da kuke jin lokacin ku ai sai daku gashi yanzu har yana maki tuni kin dade baki haihu ba hakana.
Murmushi nayi ba yanzu zan bata amsa ba na kira Aisha nace ta dauki min magani daki na ba baba har Abdul din dake rikici idan an dawo dashi.
Bayan ta kawo min maganin ne na matse yaron na bashi yasha sai dan wirin Zulfa hanif yazo wai shima na bashi nace dashi allura dai zan maka sai yaron ya gudu can kuma ya sake dawowa ta nace wai sai na bashi maganin ya sha.
Uwar tace wallahi hanif zan doke ka yanzu kuwa dannema ina faman kafa kafa da ku kace a dinkira ma magani lafiyan ka kalau kuma.
Nace nima ai ba mahaukaciya bace da zan bashi magani don nasan illar yin hakan fiye da kowa.
Bance zaki hashi ba ai shi nake ma fada nace a, a bashi ba dai aiko kana dasu da yawa baka cutawa wani don baidasu yana kafakafa da abinshi.
Shiru tayi bata sake magana ba sai kallo mukeyi kowan mu yayi shiru yaron yazo ya lafe saman kafana na dauke shi na aza a saman jikina yai barci.
Haidar na ganin haka yasa rikici wai ya tashi tace yaki tashi ai ba uwarka bane kai kadai in kana son dauka zo na dauke ka nan mana.
Sai yaron yace baiyi na hawo shi nace kyale mama kaji bari in yai barci sai na sauke shi ka hau kaima.
Wani hira ta dauko min da haka muka wayance zancen kowa ya manta da abinda akayi muka basar dama shine kishin ba komai ba.
Sai wajajan shida ga Jinior ya shigo yana hakki yace mummy kin san may nace a, a jinior tace wallahi ga matar nan matar nan mai sallon nan ta zo harda wasu yara ana shiga masu da kaya wurin maman Ihisan.
Addua na fara a bakina na neman kariya da tsarin ubangiji Allah akan zaman da zamuyi da ita a gidan.
Ba wanda ya shiga don dama Allah ya taimake ni yarana basu da irin wanan shige shige na wasu dakuna ba wanda ya tafi inda suke.
Ko dakin Zulfa da muke kusa wuri daya basu shiga idan ba ya kama dole ba ka tsare yaran ka wuri daya alheri ne a wanan zamanin da muke ciki don kariyan kai.
Yaron ka in yana wanan halin zai iya shiga wani hali baka sani ba haka ma za, a iya zarga mai wani sheri ba tare dz kaika sani ba ko yaron.
Shiya ka zamo abokai da diyan ka shine kawai alheri d mafita a wurin ka don yanzu lokaci ya canza kowa nashi ya sani ba kunya a kan hakan.

********* ********* *********
Har suka kwana suka wuni ni dai ban sasu a idona ba daga ita har yaran nata data zo dasu wurin yar sa idon shiyan mune ma nake jin wai yaran ashe duk manya ne dasu.
Ni dai na jawa yara na duka kunne kan su iya kan su daga uwar har yaran ba ruwan su da kowan su nasan kuma insha Allahu zasu ji magana na.
Balle ma Amira da taki jinin ta kamar yunwar cikin ta bata ko son ai mata zancen Raliya sam taci uwar bari gunta ko.
Ban san tana falon ba na shigo a cikin shiri na, nazo na roke shi zan kai yara gun baba daga csn idan an gama masu zamu dan je nakaisu yawo.
Ganin ta baisa na fasa abinda ya kawo ne ba kai tsaye na nufi kujeran da yake zaune akai na dan zauna ina cewa sannun ku da hutawa shi kadai ya amsa min nace daddy don Allah ina son zan kai yara gun baba daga can zan dai kaisu su sayo abu yan matan.
Gaba daya ke nan zaku fita dasu ko nace eh ba iya tafiya biyu shiyasa nace su shirya mu tafi.
Kada ku bari yamma yai maku a waje kin san bana son hakana dai nace nima ina da abinyi idan mun dawo, ba zamu kai har yamma ba ai.
Na mike ina fadin mun tafi yace kudin askin yaran fa ko an yafe min ne na barshi nace zasu shigo ai su karba nazo fada ma zamu fita ne dama.
Daga haka na sa kai na fice falon ba wanda yaiwa kowa magana a cikin mu ina fita taja tsuki tare da kawar da kanta kishin ya motsa ke nan.
Nima hakane dana samay ta a fslon sai da naji nawa kumzllon ya zaburo min daurewa dai nayi na hade shi ya koma inda ya taso.
Bayan kamar minti goma sha sai gamu mun fito tare da yaran suna gaba ina bayan su muka shigo falon har lokacin tana nan zaune a falon.
Nan suka kewaye shi kowa na fada abinda zaije yi Amira taje gefen kujeran da yake zaune ta lafe a bayan shi tana fadin daddy kudi zaka bamu muje shopping yau.
Harara take watsawa sai gani na shigo ina gyara hijjab din dake jikina nace au zama ma kuka yi Aisha dake gabana tana cewa daddy ina wuni yace a, a Aisha duk wanan kwalliyan haka na fita ne ?
Tace daddy ai ban yi kwaliya ba tunda da anty zamu fita kasan ita ustaziya ce yace lalai ke kuma fa ?
Helen ce ta katse masu hiran su da Aisha da yake mata wasan barkwanci idan yaso don ba kullun yakeyi ba sai idan yana son nishadi.
Ya sa hannu a aljihu shi yana ciro kudi yake cewa ku yan mata sai a dan baku mai yawa ko don naga ance yau shopping ne za, a da mummy.
Ya mikawa kowa kudin har yan samarin da zasu wurin aski sai da ya basu nasu yadda zasu sayo abu a can Ihisan ce ta shigo daga karshe tana cewa mummy bana ce zan tafi ba.
Nace ayya ai na dauka ko kina barci ne tace yanzu nunu ke fada min taga kun fito ai, jinior shine mai alaman rashin kunya irin na yara yace bazamu dake ba ke ma ba kina fita da maman ki ba ki barmu.
Kai jinior zan buge bakin nan naka yanzu ashe ba anty bace ko kake mata haka bana hanaka yiwa yannen ka rashin mutunci ba ko .
Ya ja baya yana magana ciki ciki na ce mu zamu tafi ihisan karbi kufin ki gun daddy mu tafi muka juta muka barsu a nan yana bata kudin ta.
A kofan gida na ga wani sauri zaune kallo daya nai mashi na kawar da kaina ya na charting a wayan shi.
Yana ganin yan mata naga ya tsura masu ido yaron bai min ba na tsaya ban fita ba sai da naga kowa ya shiga mota nima na shiga muka wuce
A mota na muke tafe duk motar ta dauke mu harda Nasir da bamuyi niyar fita dashi ba a lokacin amma ya nace sai ya bimu ya dauki Haidar da hanif shi kuma jinior yana tare da ni.
Mun kaisu gun baba sai da suka dan bata muna lokaci muka samu akai masu muka nufi wani babban store na kaya nan suka shiga kashe dan kudin da aka basu karshe ma sai dana cika masu muka dawo gida tun daga nesa na hango wanan yaron zaune again.
Nace wai waye nan zaune tun dazun na ganshi da zamu fita sai ihisan ta ja tsaki daga bayan motta tace dan matar nan ne fa wai shima a gidan nan zai zauna.
Sai shegen kallon mata wallahi ni haushima yake bani gashi kamar mugu idan ka gan shi ni wallahi ban san may yasa aka kawo muna su gida ba wallahi.
A raina nace akwai matsala kuwa gani da wa yan nan yan mata haka kuma wanan yaron dagani dan zamani ne irin yaran nan ne da ba kwabo.
Ga wani shegen aski da yayi a kan shi wandon shi irin yadda hitsararun matasan nan kayi wai sagin nace dasu to ku saurara dakyau wallahi gaba dayan ku kuyi hankali dashi kunga dai bamu san tarbiyan shi ba ko ?
Ina shiga ciki da mota naga yan matan su biyu a waje wai suna selfi a cikin huranin gidan sai ihuce ihuce sukeyi abin su.
Nace Allah ka cece mu wanan rayuwa haka akwai aiki kuwa gaskiya kowa tasha dogon wandon pencil da matsatsen riga a jikin ta.
Da suna muna wani yauki amma muna fitowa sai suka bimu da kallo don basuyi tsanmani akwai zukakan yan mata haka ba a gidan.
Kowa ya shiga gida da kayan shi niki niki har ihisan a falon mu muka tsaya da ita ana duba abinda kowa ya sayo a wurin.
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
93

Ganin yaran nan da nayi bai min dadi ba sai dai ba zaka aibanta dan wani ba sai addu,a da fatan alheri ga dan kowa shine adduan ko wace uwa tagari ga ko wani da tagani.
Don haka ni dai na dinga kafa kafa da yarana tare da masu adduan neman tsari daga sherin shedan.
An tashi da azumi kowa ya dauki niyya sai wa yanda aka sahelce masu yin azumin kamar yara tsofi marasa lafiya da sauran su.
Muna ta kokarin hada abinda zamu sha ruwa dashi a part dina ni da yara ko ina ya dauki kamshin girkin da suke tayi kowa da abinda yake son ci idan ya sha ruwa.
Zulfa ta shigo tana cewa a, a wanan kamshin yau duk na masu buda bakine haka ko may ?
Ina daga kwance nace da ita ai duk hadama ne irin tasu yanzu karshen ta ma da an sha ruwan nan zasu barni da abincin a kitchen.
A, a mummy nikan nawa tas zan cinye shi ai daidai cikina na soya muna ma Atika dariya daddy ya shigo falon namu.
A, a da alama dai ku azumin bakwa jin shi yau wanan dariyan haka da kuke kwasa kamar an maku bushara.
Yaran nan dai mukewa dariya sun hada abinci kamar masu shirin taron baki wai duk na shan ruwa ne haka .
Amira ta dauko kula tana fadin daddy yau dz abincina zakai buda baki ko na hada delicious mai dadi,
Murmushi yayi kawai nace yau kan kin makara don daddy gun maman Ihisan zai buda bakin shi sai yarinyar tace shitty wallahi na dauka a gun mummy ne ko maman baby da kaci dahuwana.
Murmushi yayi yace ku bari idan su mummy naku za suyi girki sai na zauna naci har sai na koshi.
Ya juya yana cewa Sani zai shigo maku da kayan shan ruwa don mun makara bamu samun lokacin zuwa kasuwa ba da wuri.
Ni dai ban mayi magana ba don ina fama da Abdul mai fitina wai orth din da aka bashi akwai zafi har ya gama ya fita wurin mu.
Ba a dauki lokaci ba Sani ya iso gidan da kayan cikin wata mota haka mai girma duk kayan da ya shigo dasu almost a part dina ya tafi.
Don suna suna aka bi aka sayawa kowa kayajn shan ruwan har helen d bata sallah sai da aka

Download complete TXT · Novel page