Murucin Kan Dutse

Chapter 141 of 146

ma dai ba yar goyo ba.
Don ba don ke ba waye zai iya rike ta irin yadda taso mayar da kan ta a baya abin ya damay ni sosai a lokacin ban da yadda zanyi ne kawai idan nagan ta a lokacin.
Ba laifin ta bane nace dashi akwai kurciya da kuma zugi ana fada mata maganganun da ba zasu fisheta ba ita a ganin ta ta dauka so ne.
Yanzu ai ta gane gaskiya ita da bakinta ranan naji suna hira da mama Altine irin maganganun da sukai ta fada mata ba don Allah ya gyara ba ai lalata suka so yi kawai.
Amma shi yaro ina yasan wanan irin raayin da sukai ta koya mata kan taki ubanta da yan uwan ta.
Nifa shiyasa Nasir da jinior har gobe nake son rayuwan su don tun uwar su na raye basu taba nuna min ko diyana wani banbanci ba dama shi da namiji haka rayuwan shi yake sai kalilan ne ake samu da wani halin na daban.
Bar ni dasu ai zasu sha mamakina don koda ita marigayiyar take a raye may suka mayar da ita a cikin su in ba suna son abin hannun ta ba zasu zagayo ta.
Daddy ba zamu bi ta nasu ba azama daya zan kaita anjima idan an gama kamu sai ta kwana a wurin su zuwa gobe ko jibi ta dawo kaga ai an dai wuce wurin ba shike nan ba.
Yace idan kinga hakan ba matsala shike nan amma ni naso ne kawai a share su, nace kada ku zama daya dasu daddy bari dai kawai nakaita da dare gidan anty Amina sai gobe kuma na tura taje can babban gidan ta wuni masu.
Yace yayi idan ba zai kawo matsala ba nace insha Allahu ba komai shigowan hindatu falon ya dan katse hiran da mukeyi taje cewa ashe kina nan ne nace da ita eh kawai.
Na fara tattara kayan da yaci abincin don na basu wuri sai naji tace ashe yau zulfa zata dawo gidan shine ba a fada muna ba.
Hindatu kina da hankali kuwa ko kuwa raini ne ya kawo hakan tsakanin mu matana don zata dawo zaki ce wai sai na fada maki ke lokacin da kika tafi wana fadawa cewa zaki dawo gidan.
Ko akwai wace ta biya min sadakin wata a cikin ku ne fice min daga falin yar rainin wayon banza kawai.
Ni dai ficewa nayi ina jin yadda yake zagin ta a raina nace wanan kuma ta daukowa kan ta wani sabon fitina a zaune kalau.
Na koma na samu wasu bakin sun shigo gidan nan muka baje ana hira su Zarah na ta faman shirin buki da za ayi da karfe biyar na yamma ranan.
Mun kai wani lokaci sai ga su anty Amina da anty maryam sun shigo nan muka tare su a cikin mutunci na sa Gajiye ta kawo masu abin tabawa.
Barshi inji maryam ta fada cikin rashin damuwa nace a dai kawo masu su taba anty Amina yau fa a gidan ki Amira zata kwana nace da ita.
Tace cikin ya tsune fuska ai mu darajan mu bai kai ace za a kawo muna yar mu gare mu ba don yanzu kin fi iko da ita ai.
Nace haba anty nina isa don dai kawai bamu kusa ne kin san aikina ba lokaci ke gare shi ba ita kuma Amiran tana karatune kun sani.
Yanzu dai bashi ba mun zo ne muji abinda ake ciki tunda mu matsayin mu baikai na anemay mu ba mu san komai akai.
Mun ga idan mun kyale ki zakiyi muna rufarufa ba zurfine ki rubda ciki ga komai don kina ganin kin fi kowa wayau.
Nace haba dai anty may yai zafi haka kuma ai abin baikai can ba duk abinda ake ciki ina kiran anty Asamau na fada mata komai balle ni ai komai shiya saya da kan shi ya kuma tura a gyara mata dakin ta can bauchi.
Bakaji ba ina ruwan an haifa maki jari ashe har jere kin saka ai mata bamu sani ba mu inji anty maryam ?
Tace anty ai saiki tashi mu tafi don wanan ta riga da ta mamaye komai ba komai zamu gane ba sai dai shi may gidan ya kamata mu gani.
Sai dai ki sani duk cin amanan da kikewa yaran nan a kunnuwar mu yake in zalunci abinyi ne sai ki hau ki zauna ga yaran nan kinwa uwar su ma data kafaki balle mu din.
Wasu hawaye ne suka zubo min nace cikin kuka haba anty maryam ban taba zaton irin wanan sakamakon a gareku ba wallahi.
Muryan Zarah ne naji tana fadin may ye na kuka a nan doctor da har zaki tsaya kina zubar da hawayen ki ga banza diyan da aka bari ai ba a ke kadai aka bari ba.
Wa ya nuna nashine har yasan da zaman su a gun ki sai yanzu ne da ake ganin sun zama mutane aka san dasu ko may da za a zo ana fadawa mutane wani magana can mara tushe.
Ke kuma a suwa wai wakike a cikin maganan ko karan kada miya baki kai ba ga zancen nan don haka ki ja bakin ki kiyi shiru ga maganan nan.
Aikuwa nan fada ya tashi a tsakani sai ga suwaiba ta fito daga daki itama ta saka baki aja su aja su anty Amina din fada suke sosai da gori a tsakanin su.
Sai ga Amira ta fito da abokan ta don jin hayaniyar da yai yawa tana ganin ina kuka ta nufe ni bata nufe su ba tana fadin.
Mummy may ya samay ki may my ya faru hakane kuma ina dazun nan kike cewa zan tafi gidan su na kwana.
Sai nace ba komai Amira ina share hawayen dake fuskana ba komai kamar ya uwayen ki ne sukazo suna zargin ta wai ta kakace komai ta hana su shiga har kan bukin ki inji suwaibana take fadin hakana a hasale.
Kamar ya ta daga kai tana kallon inda suke tsaye suna fada take cewa dama wa ake son yai min wani abu bayan mummy ina da wata uwace data fi min mummy ne yanzu.
Nifa yanzu ba zan yarda ba don yanzu ba irin da bane da ake fadawa mutum magana yana yarda amma may mummy ta rage mu dashi a duniya ni da yan uwa na ?
Ke rufa muna baki shanyayun banza kawai daku da uban naku duk an shanye ku baku dana fadi a kan ku.
Duk dukiyar uwar ku da ta bar mai an handamay wama ya sani ko yanzu babu komai da ya saura gare ku.
Haba mama Amina wanan bai dace ba gaskiya kudin dama kuke magana ai ba a hannun ta yake ba kuje ku samu daddy mana shi da komai ke gurin shi amma za a zo a saka mum a gaba da wanan magana haka ?
Kai kai wai may ke faruwa haka ne a nan anyi taron arziki za a kawo muna fitina kuma ana zaune kalau wai may ke faruwa ne wai ?
Gasu nan gara dai da ka shigo don wannan abin baiyi ba gaskiya yarinya tana iya kokarin ta da yara amma babu kunya kuzo muna da zancen wai dukiyan yara idan an baku dukiyan may zakuyi dashi baku za a yi ku rike ko may ?
Mama Altine ne da ranta ya baci take fadin wanan maganan cikin bacin rai da damuwa daddy ya juya gun su yace dukiya wani dukiya kuma ?
Maryam tace na yaran mana da mukaji ance wai an fitar masu kwanaki shine muke son ji idan wanan mai wawason bata wawaahe masu ba ?
Ke kuma tsohuwar munafuka Altine da kike wanan magana don an shan ye ki an gama daku ana baki na goro idon ki ya rufe har kike wai ana zaune kalau.
Kai ku dakata don Allah ba wacce zata shigo min har cikin gidana tazo taba son ciwa iyalina mutunci a zauna kalau.
Dama ai na fada maki keda kike daukan su wasu tsiya ko yar uwar nasu dake da rai yaya ta kare dasu sai yanzu ne kuka san ta bar baya a duniya ?
Wa ya taba zuwa da sunan yazo gidan nan don ya ga yaran da ta bari sai yanzu to bari kuji na fada maku.
Idan ba girma da arziki ne zai kawo ku wurin wanan sha a nin ba na rokeku da ku zauna a gidajen ku daga yau idan yaran suna so zasu tafi inda kuke amma ba a gidana ba .
Ku fice min gida idan fitina ya kawo ku ai akwai hukuma sai kukai karana a can ina jiran sanmacin ku.
Ya nuna masu hanya da su fice mai a gida nan suka fara sake mai bakaken maganganu suka fice daga gidan a fusace.
Suna fita hajiyan harka tana shigowa nan take samun labarin abinda ke faruwa a gidan tace kayya ai dama ace tana gidan haka ya faru da sun ji magana.
Wa ya hanavzaman lafiya a tsakanin marigayiya da Rahama ba su ba ta kasa gane va son ta suke tsakani da Allah ba a kullun cikin zuga ta suke da tai rashin mutunci a dakin ta don suna hassada da bakin ciki da samun ta cikin su.
Ina kafin ta mutu ta gane gaskiya nan ta mutu ba kunya suka wawashe abin da ta bari a dakin ta yanzu kuma sun dawo dan abinda ya saura ga yaran su kuma wawashe shi a tsakanin su.
Nace wallahi hajiya ni ban taba kai zuciyana a irin wanan abin ba a rayuwana duk abinda zanwa yaran tsakanina da Allah nake masu don ina kwadayin samun lada a kan su balle Allah na tuba har anty zata bar baya na ce ni Rahama wai na gaji dasu ko na watsar dasu don ina butulu ko may.
Kuma duk abinda zanyi fa tare da sanin anty Asamau nakeyin shi gidan nan don kafa sheda irin haka dama.
Ko ba sheda fa Rahama sai makiyin Allah zai ce ga sherin ki akan yaran nan a gidan nan wallahi.
Sai da lokacin fita yayi aka sasauta maganan daidai lokacin kuma hajiyan daddy ta shigo gidan kan maganan ita ma tace zata tafi har gida ta samay su tai masu tas yara dai nasu ne su da yar uwar su ta mutu suka kasa rikewa har suna da bakin zuwa yin wani magana yanzu don basu da kunya ko may ?
An dai bata hakkuri na hada mata duk wani abinda za a raba gun kamun a ka kai mata a mota suka tafi.
Ko ba komai dai naji dadi don dani kadai suka sama ba wani abin da zan iya yi a lokaci sai kuka don takaici amma Allah ya rufa min asiri a gaban mutane suka zo min kuma sunji magana sosai ranan.
Anyi kamu anci ansha komai yayi kyau yadda ya dace ayi an tafi da dadin rai a gidan an barmu yan gida muna ta kawar da kayan da aka fitar.
Da dare misalin karfe tara sai ga su anty Asmau sun shigo gidan sunzo bada hakkurin abinda ya faru don ashe daddy ta tafi wurin wani kanin mahaifin su ya fada mai.
Shine ya kira su daya bayan daya yana masu kashedi akan gida daddy tare da fada masu abinda su anty Amina suka zo sukayi.
Sun bani hakkuri nace babu komai ai zama tare ne ya kawo hakan take cewa don Allah abawa daddy hakkuri don tana ma jin nauyin shi da kunya su hada ido don basu da bakin magana akan zancen din an riga da an bata zance ko.
Da haka dai da zasu tafi suke cewa sunji ance za a taimaka akai masu amarya ta kwana don Allah kada abi ta zancen nasu.
Na aika aka kira Amira tazo sai dai tana zuwa ta nuna bazata tafi ba da lalashi da komai ta shirya suka tafi da ita.
Su suwaiba na fadin wai don may zan bari a tafi da ita yin haka kamar na nuna jin tsoron su ne ai, nace haba hakan ai ba komai bane diyar suce fa a barta ta san iyayen ta ta san darajan su tun yanzu don yan uwan uwa ba wasa bane.
Dama sune suka watsar da yaran har haka yakai ga faruwa amma ai tasan anty Asamau don idan muna waya tana kusa nakan bata su gaisa da ita ta dan tambaye ta wasu abu gamay da rayuwan su .
Sai gashi kuma bayan tafiyab su da yarinyar washegari daddy ya samay ni da nashi fadan don may zan tura Amiira wurin su tunda basu da mutunci.
Hakkuri na fara bashi nace daddy yar su ce fa dole ne ko yaya ne su san su don jinin su ne yaran, yace dani cikin bacin rai ke dakata Rahama.
Sai nai shiru ido rufe ya hauni da fada akan naje na dawo mai da yar shi kafin raina ya baci inda yake shiga ba nan yake fita ba sai da mama Altine ta bashi hakkuri tare da fadin bari ta tafi ta dauko Amira din tin da safe.
Abubuwa duk sun taru sun min yawa a kaina ta ko ina babu dadi a gareni kan wanan magana don daddy ya rufe idanuwan shi yai min tas akan yan uwan anty Saade.
Yadda mama ta fada hakan akayi don tunda safe ta shirya nasa driver ya kaisu ita da mama Abu matar maigari da gwagon daddy da take zuwa gun mu akai akai idan muna kano.
Sai da aka kwasa dasu don gidan anty Amina suka fara zuwa tace vaza su ba da ita ba sai gobe zasu dawo da ita din.
Amma mama ta fada masu cewa idan har basu ba yarda yarinyar ba komai ma zai iya faruwa akan maganan.
Haka dai dole suka ce yarinyar tana gidan maryam daga gidan maryam aka kira masu Asmau itace ta bada Amira din suka dawo da ita gida tare da su.
Har lokacin raina ba dadi ga jama, a da suka taru don ni a gidan zakace ko yar cikina ne akewa aure a lokacin irin yadda yan uwa na sukai min kara a bukin.
Sai dai yan uwan marigayiya sun kawo min cikas a rayuwana kan zargin da suke min na wai nayi rub da ciki da dukiyan yaran yar uwan nasu.
Kamar yadda daddy ya dauki zafi nima haka na dauka dashi don ban kara bin ta kan shi ba, tun wanan lokacin.
Ban san may ya gani ba da dare ya aiko kirana ina zaune tare da su mama Suwaiba na ta ta faman hada kayan da za a kai hidan iyayyen mijin Amira na gara a cikin manyan robobi don da safe zasu tafi da kayan bauchi.
Mutum biyar aka zaba da zasu tafi Aisha Sister din daddy da fatiman shi sai Asamau sister din anty don ita kadai tace zata tafi sai Zarah yanzu ga Suwaiba tace zata tafi itama don mota biyu zasuyi amfani dashi.
Sai da na dan bata lokaci na mike na tafi inda na samay shi tare da Zulfa a zaune tare da shi.
Sallama nai masu tare da gaida daddy din sai Zulfan take tambayana yaya naji da jama, a dazun ta shiga ance mun dan fita bana ciki.
Na dan bata rai na nakai zaune ina fadin wallahi fa mun tafi wurin mai aikin cicin ne tana son kawo muna cikas ga aikin bayan munyi da ita a yau muke son mu kammala komai gobe za a tafi dasu.
Take cewa dani ai haka mutane suke wani lokaci basu da alkawari nace ai tayi muna don har ta aiko dashi ko tun dazun yanzu ma hada kayan mukeyi aka kirani.
Tace wai gashi har kin wani fada kin ramay ki na ko samun cin abinci kuwa doctor ?
Murmushi nayi nace da ita ina naga ta zama naci abinci idan banga an kamala komai ba tace ai shine ance rana baya karya sai dai uwar diya tai kunya inji manya.
Wanan uwar diyan kan a tsaye take don tun da safe ban ga kin zauna ba ga jama, a sun taru haka abin tubarkallah wallahi.
Nace gaskiya mutane sunyi kokari sosai wallahi don hakane kawai za ai wa mutum a nuna mai so da kauna yasan cewa shi din da dangi ne ta ko ina.
Mun dai dan taba hira akan bukin da ita t yana ta faman aikin shi bai tanka mu ba sai can naji yace damu.
Naga, har su suwaiban ki ai sun shigo da wuri haka abin ya ban mamaki nace ai dole ne suzo daddy wanake dashi bayan su.
Ranan wuya akace sai naka inji zulfa sai Daddy yace ga wanda yasan da hakan ko naga wasu na jikina ne amma suna ja baya ga bukin .
Sai duk mukai shiru saboda mun fahinci inda maganan shi ya dosa a lokacin da zulfa yake wanan magana din.
Yace dama na kiraki ne naji su waye zasu tafi gobe sai kuma jibi din idab za a kaita da suwa za ai tafiyan kuma ?
Na dan ya mutsa fuskana da babu saki a cikin sa nace tau dama dai ga goben sai na lissafo mai masu tafiyan kai kayan .
Nace jibi din dai ne ban san masu zuwa ba don kowa na son zuwa yaga dakin nata a can yace ba gaskiya bane kin san dai ba za, a kwasa akai masu dawainiya ba can kuma da yawa.
Nace ai yanzu sai ka fada kowa yaji yace ba manya ne zasu tafi ba idan za a je din nace ai yadda kace haka ne za ayi.
Amma maganan yana hannun Aisha da Fatima don sune masu gudanar da komai na gani yanzu don ni ba zan iya ba saboda kowa abinda ya kawo shi ke nan.
Yace to ji nan kada a wuce mutim goma dai kuma a tabbatar da an tafi da mama Laraba da mama Altine idan za a kaita din don

Download complete TXT · Novel page