Murucin Kan Dutse

Chapter 143 of 146

yadda kika ga dama dashi, idan kina son kafa doka gina raminki da kan ki sai ki zauna a ciki amma ba ramin da wata ko wasu suka gina ba kizo kice zaki shige ki mamaye.
Idan kina son ki san ko ni wacece tambayan shi kice dashi uwar diyan shi takwas ne ta kira layin shi don haka kibawa kan ki amsa dani dake wake da mijin yanzu ?
Ina fadin haka nai sauri na katse layin nawa ban staya sauraren abinda zata fadi ba a lokacin don kada ta jefo min mai zafin da yafin da yafi wanda na fada mata din.
Sai dai tana cikin kunduma zagi daddy din yafito daga ban dakin yana goge ruwa a kansa tambaya ta yake tare da kai idanuwan shi aka wayan shi dake hannun ta yana fadin keda waye haka ?
Take cewa wata banza ce ta bugo layin ka shine nake fada mata kada ta kara kiran layinka a wannan lokaci sai kawai ta kai min zagi ,
Ko wacece zamu hadu da ita don bata san wace ta zaga ba ke nan dan ni bana ba da bashi ko kadan,.
Bata ma san ya kawo bakin gadon ba sai ji tayi ya wafci wayan shi a hannun ta da karfi yana duba wanda ya kira layin nasa sai yaga ai nombana ne na nan gida Nigeria na kira shi dashi.
Watau ke nan da Rahama wanan take cin mutunci haka ko, sai dai gaskiya bata kyauta mai ba don ba haka yaso ba da zancen don shi so yayi sai na dawo muyi maganan.
Batare da ya damu da tana gurin ba, ya kira layin nawa kamar kada na dauka dai na dauka yake cewa kina ina ne naga nomban nigeria kika kirani dashi ?
Nace ina lagos yau six days kenan da dawowan mu gobe zan iso Abuja insha Allahu sai dai nakira ka wata yar iska naji ta dauki waya har tana min barazana wai wayan mijin tane wanan na daina kiran ka a wanan lokacin haka .
Ita din wacece daddy kardai nace kana hurda da matan banza ne kuma abinda ban san ka dashi ba a baya ?
Yace bar wanan zancen idan kin iso zamuyi magana akan sa ina yaran suke ne mu gaisa nace dashi yanzu suka fita da doctor Hauwa zuwa cikin gari.
Mukai sallama dashi ya kashe wayan tare da sauke ajiyan zuciya tana furzo iska daga bakin shi ya lumshe idanuwan shi a hankali don bai san ta ina zai fito min da zancen ba.
Muryan tane yaji tana fadin wai wata yar iskace a cikin matan naka har zatace dani wai na gina ramin kaina wanan ramin ba nawa bane naje gaba ?
A hasale yace da ita matar nawa zaki zaga da yar iska a gabana ita bata zage ki ba sai kece mai zagin ta a gabana matar da nake da zuria da ita fiye da kowa a duniya matar da, , , , ,
Haba malam ya isa haka ko ba a fada ba nasan wanan yar iskan likitar matar takace da ake fadin kana ji da ita don naga alama tunda gashi ka rufe ido a kanta kana son ci min mutunci.
Yace idan kika sake maimaita zagin da kikai mata a gabana yanzu ranki zai baci dani a wurin nan.
Ki shirya yau Abuja zamu koma don Rahama ta iso Nigeria gobe zata shigo Abuja din ita da yaran da ta tafi.
Yana fadin haka bai tsaya bin ta nata ba ya fara shirya kayan shi nan ya barta da mamakin wanan irin rawan kafan da kaduwa da yayi akan matar shi .
Wai wacece wanan da yake wa rawan kafa haka ita dai taga matan nashi ba wani abin kai gida a kan su balle ace wai wata tafita a cikin su.
Shiryawa yayi ya fita daga dakin yana fadin zai je ya dawo kafin ya dawo ta shirya yana fita taja uban tsuki wayan ta ta jawo tana fadin ni za a kawowa iskanci akan wata banza can wai Rahama ?
Kawarta ta kira take fada mata komai har take cewa ba inda zata don kano yace zasu tafi amma yanzu ya canza saboda wata wai su koma Abuja.
Kawar tace wallahi Samira kibi a hankali kin dai san ko shekara nawa muka kwasa wurin samun hankalin shi kafin ya yarde muna don haka ki rufawa kan ki asiri kibishi ku tafi.
Baki ko san yaya matar take ba balle har kikai ga daukan mataki a kan ta sai idan kin ganta ne ai zaki dauki mataki a kan ta.
Take cewa hakane kuma fa bari na shirya naje ko ganin yar iska nayi naga nata kalar wanka wata kila ma wata cus ce can ilimin ne kawai a kai.
Sai suka kwashe da dariya a lokaci daya kawar tace koke fa mutumiyar aiba haka kai tsaye ake kama makashi ba sai da kwana kwana.
Nan ta mike ta shiga shiryawa sai dai ranta abace don gani take duk ajin ta da kima ace akan wata zata rushe plain din ta da tayi na zuwa kano ziyarar dangin shi a karo na farko ?
Da yamma suka shiga Abuja kai tsaye part din maigidan ta sauka don nuna isa da gadara ga matan gidan ta nuna ita ta isa ga kowa don hamshakiyace.
Amma sai ya karya mata takon da cewa akan may zata zo nan bayan ga gurin ta can takoma can don a cikin iyalin shi ya shigo.
Duk da ranta ya baci amma dole ne tabi shawarar kawar ta ta lalaba shi taga gudun su tukun.
Haka ta mike a likacin hindatu tashigo suka hade a falon kowa yabi dan uwa da harara da hassada a fili na kishi.
Nan ta fice tabar hindatun na kallon yanayin shi ta fahinci akwai bacin rai a ciki sannu da zuwa tai mashi don har lokacin ba dadi a tsakanin su.
Washegari da safe sai shirin zuwa taron mu akeyi don na bugo waya muna iya port a lokacin da zamu taso daga lagos din.
Tsayawa fadin irin shirin da nayi bata lokaci ne dagani har yaran munyi kyau sosai don zama indiya ba wasa ba gaskiya.
Ban kawo komai ba a raina na cewa zamu hadu da wai wata amaryan shi ni dai daukina kawai shinenaga yarana dana share tsawon watan ni bama tare da su.
Mun kai wani dan lokaci kafin mu tashi don haka sai sha biyu muka sauka a Abuja inda shi da yaran ne suka zo taron mu da hindatu.
Da murna na rungumay yarana ban ko bi ta kan sgi muka kuma rugumay juna da hindatu din sai yaran da suka rugumay mahaifin su don murnan ganin shi.
Jinior yana lake a jikina na dago kai muka hada ido dashi alaman radhin gaskiya irin na maza karara a gareshi nace yallabai mun samay ku lafiya ?
Ya dan murmusa yace lafiya kalau ya karatu da zaman india nace sai hamdala na dauki yar wurin hindatu dake murnan ganin mu.
Mun dan dauki lokaci muka kwasa sai gida ina tare da yarana har muka kawo gida ina maijin dadin ganin yadda yaran ke a cikin walwalan su babu wani mairaicin rashina da suka yi.
Wani abin sai uwa dama abinda nake so ke nan na dage akan sai Inna tazo ta zauna min da yaran duk da kunyan da take nunawa na rashin son nuwa duniya itace mahaifiya na a matsayina na yar fari a gurin ta.
Muna shiga gida na hango wata mace a tafe tana bun kasa a kasa da waya a hannun ta bayan na bude motan kafana kawai na sako a kasa ba tare da na fito ba muka tsaya magana da yaran dake fadan daukar jakana na hannu.
Sai da na raba gardaman na karasa fitowa daga motar gaba daya hankalinta na a gurin mu yayin dana karasa fitowa daga cikin motar gaba daya sandarewa tayi a tsaye inda take tana rayawa a ranta ta ina zata fara dani.
Ga dai Ilimi ga kuma uwa uba kyau da tsari da ta hango muraran a wurina ga wani kwarjini da nai mata a idanuwanta a lokaci daya.
Ban ko koma ta kanta ba na ja yarana muka fara hawa steps din shiga gidan hankalina a kwance.
Sai naji shi yana fadin Samira ga docter ta dawo fa daga india ita da yaran ta yadda tai min wani irin kallo nima haka na juyo nai mata tare da fadin wacece kuma Samira ?
Kafin yai magana sai naji tace wace kike gani a gaban ki nice amaryan maigidan da fatan zaki gane ni daga yau.
Wani kallo nai mata tare da sake shuumin murmushi nake cewa amarya amarya fa ko dai uwar gidan wanan ai ba a kiran ta da amarya don ta haife mu ko ?
Ai sai dai mu bata kambun uwargidan cin gidan gaba daya shi zai fi sauki na fadi haka ne don irin yadda ta mayar min da magana itama.
Murmushi daddy tayi daga inda yake tsaye yake cewa shiga dai ki huta kafin muyi magana ko nace magana kuma may ya saura tunda ka gabatar da mu ga junar mu na juya muka shige da yaran ina jin tana fadin.
Duniya na haifa ba ku ba sai ki tsaya ga wanda ya aje ki in kina takama da kurciyane ai ya ganki a gaban shi ya dauko ni.
Ban tsaya ba don nasan su Inna na gidan muka shige ciki nan muka tari junar mu da murna ban sake bi ta kan shi ba ga yarana sun baibaye ni.
Ban samu kaina dasu ba sai da akai kiran sallah na kora su suje sallah na samu na shiga dakina sai dai zuciyana fam yake da tunanen wanan matar.
Bayan nai wanka na sauya kayan jikina sai ga Atika tashigo dakin da murnan ta don bata gida da muka iso tana school muna cikin hira da ita ne daddy ya shigo dakin ya samay mu.
Wani kallo na tsana na watsa mashi yayin da Atika ta gaidashi tafice daga dakin yake cewa dani basu dai barki kin huta ba ke nan.
Nace ba kadai barni na huta ba kai da ka kara jajibo muna wani wahala a gidan kuma.
Wahala kuma Rahama aureb nawa shine wahala nace a lalace aure ina aure a nan ka kwaso muna uwar mata wai kishiya wanan ai a gidan dabe ya dace a ganta ba a gidan ka ba.
Mace haka babu fasali a tare da ita daganin ta ma irin matan nan ne yan safara ba abin kwarai bane don tanayin ta yai kama da yan kano jidda.
Dariya yayi min cikin shuumanci yace duk ita kadai nace ni na rasa gane wanan irin rayuwan for god sake may ye ka rasa daddy a gurin mu da baka da aiki sai auren barnan suna ko yaushe.
Wanan ce zan zauna da ita a cikin gidan nan haka ga yara a haka yara zasu tashi da irin tarbiyan da muke so a garesu.
Ko yaushe suna ganin nauin mata lalatattu iri iri gaskiya ya zama dole a gare ni wanan karon na nisance ka kaje duk abinda kake nema a gun mata kaita nema amma wanan tanbadar badani Rahama ba gaskiya.
Ysi yar dariya yace dake kuwa zaku zauna a gidan nan ba wani gida ba auren da nake may nake rage ku dashi dakuke wanan kishin haka wai ?
Nace kishi kishin wa zanyi wanan ai uwatace ba kishiya ba ni bata a gabana gani nayi kawai a tsaye take tana daukan kanta hamshakiya .
Ya kai zaune tare da kai hannun shi a saman cinyana nai saurin kabe hannun nashi ina fadin kada ka soma don nagaji da wanan halin naka daddy a yau nayi nadamar auren ka da samun zuria da kai a duniyan nan.
Da sauri ya katse ni yana fadin Rahama ni keke fadawa kinyi nadaman aure na da kikayi nace na fada don abin ya isheni haka.
Bai yi magana ba sai naga ya mike ya fice daga dakin ran shi a bace nima na raka shi da haraea tare da tsuki na haye gadona don daukan shi ma nake bai san ciwon kan shi ba kuma.
Mutum ya koma na mamajo haka baida aiki sai aure may ya rasa a gun matan shi da yake muna wanan hakin auren kuma ko yaushe kamar ba aure na kai sake ba idan yayi.
Kai da zakaga matan sai kaji nauyi da kunya don basu dace da ajin shi ba abu dai gashi bai faduwa ga mutum.
Abinda mu ba musani ba shine ashe idan namiji ba mazinaci bane haka wani lokaci yakan kasance dashi ga matan yanzu basu tunkaran namiji sai sun shirya mashi da saddabaru da dan sihiri shi ke saka idan namiji ya yi wani abin kaji wani iri a ran ka.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Kuyi hakkuri masu fadin wai novel din ya dau lokaci anayin sa ba laifina bane yadda labarin yazo ne idan kuma na katse shi yadda na katse tarko nasan bazaku ji dadina ba zan ta samun korafi ne kuyi hakkuri saura kadan mu karasa da yardan ubangiji
Na gode da fatan zaku fahince ni yan uwa kuma kuyi hakkuri dani please rashin waya ya kaimu har wanan lokacin haka.
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , ,

108
Daga wanan fitan bai kara kulani ba nima haka inda na shiga harkokina da yara da abokan arziki masu zuwa yi min sannu da zuwa .
Ba wai share junan da mukayi baya damuna bane a a na dai yi niyar daukarwa kaina matakin da ya dace ne don abin nashi ya fara bada tsoro a zuciya na.
Tafiyan wata uku kacal sai aure a bayana daga mutuwan anty yai auren Raliya, Raliya tana fita ba a dade ba ya dauko Niima itama ta debi rabonta tai gaba.
Nisawa nayi a fili nace mijin bahausa ke nan ke mace baki da tabbas zama da mata daya ko biyu zuwa uku sai ranan da rayuwa ya kare wa bawa.
Mun koma bakin aikin mu bayan sati daya ga Inna sai shirin komawa take kano don zaman nan ya kai mata ko ina don bata saba ba zaman dole takeyi.
Ranan da na fara fita na dawo a gajiye don yan aiyukan da nayi a office wanka nayi na shirya nafito zuwa dakin da su inna da mama suke na gaidasu.
Suna zaune hiran su suke na shigo da sallama na dakin tare da masu barka da gida suka amsa min cikin kulawa da kauna.
Na samu wuri na zauna tare da kallon kwanon abincin da aka aje a gefen su basu ci ba har lokacin nake cewa dasu sai naga kamar baku taba abincin ba mana ?
Mamace tace dani Rahama in ba so kike mu fashe ba da wanan irin dadin da kuke bamu haka Allah dai ya baku hakkuri zama da mijin ku.
Inna tace ai mai kuli wanan mutumin ba abin da za, ace dashi sai fatan alheri ku dai ta hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi duniya balle ni banga wani abin gazawa a gare shi ba akan ku.
Baida maraina akan iyalin shi ko kadan tunda duk wani nauyi da hakkin daga matan har yaran shi yana saukewa kai bama iyalin shi ba har masu aikin dake karkashin shi bai barsu a baya ba dubi gajiye yadda ta koma matar mai gadi fa kawai ba wani ba can.
Kin kai nisa ai inji mama ninan fa yar uwar matarshi ce amma ji yadda yake min tankar mahaifiyan shi ce ke a gidan sau goma zai shigo sai ya shigo nan ya duba ni tare da tambayar banda matsala dai ko ?
May yafi wanan dadi Asiya a duniya ai irin mazan nan ko wace mace na fatan samun iri su a duniya.
Murmushi kawai nayi na gyara zama na araina nace wanan kuka sani ku may yafi bacin rai kullun namiji sunan kuna zaune kalau amma baida aiki sai na kadin aure.
Kamar wanda bai samun jin dadi gun iyalin shi irin wanan ma ai sai duniya ta zagi mutum don baza mu fita sai ace mune bamu gamsar dashi ga wanda bai san halin shi da raayin shi ba.
Sai naji Inna tace kinga ta nan tun dawowan ta na fahinci ba dadi tsakanin ta da shi don ko yawan shigowan da take dubamu ya rage.
A, a haba dai Rahama may kuma kike so a duniya yanzu ilimi da daukaka Allah ya baki ga miji na gwadawa tsara kin samu ga zuria dayyaba Allah yabaku a tsakani may kuma kike nema Rahama ?
In dai don wanan auren da yake yawan yi ne sai ku barshi da halin shi tunda auren nasa bawai yana takura maku bane ko wani abu.
Gaskiya in har hakane abinda uwarki ta fada baki ko kyauta ba don banga abin damuwa ba ga wanan dai.
Bafa a kan ku matan ke zama ba ke ku godewa Allah ma da ba irin mazan nan bane da idan sun dauko wata a gida ke ra gida dake da babu duk daya kuke a wurin shi.
Iya hakkuri bawan Allah nan yana dashi a gare ku iyalin shi ki duba irin tsiyar da yaran nan hindatu da zulfa ke shuka mai amma yana hakkuri yana takewa yana kuma zaune dasu lafiya.
Duk masu shigowan nan ni a ganina kaddaran aure ne a tsakanin shi dasu inba ita wanan daya aura mara tarbiyan ba bayan mutuwan diyana waya haihu dashi ?
Balle ita wanan uwar guzumar daya kwaso yanzu ai ba batun haihuwa a gare ta ma mufa a zamanin mu bamu kishin komai inba na haihuwa ba ki zuba in zuba kowa ya cika gida kuma babu wani abindake ga namiji in dai ba wanan din ba.
Nace mama ni ba wai auren shi bane ko wani abu

Download complete TXT · Novel page