Murucin Kan Dutse

Chapter 145 of 146

cikin tsawa kuje gun grandpa sai suka tafi ya rugumay su a jikin shi yana dan hira dasu na tambaye shi lafiyan jikin yace dani Alhamdullahi.
Ai abin yazo min da sauki tunda ina samun kulawa daga gare ku keda mijin ki Allah dai ya saka maku da alheri.
Nai murmishi tare da fadin amin baba ya juya gun Suwaiba yana cewa ashe kina gunta haka nake son ganin ku da baku biyewa wanan uwar taku da har yanzu bata san Annabi ya faku ba hassadan ta a kullun kamar karuwa yake a zuciyar ta .
Na rasa ko wata irin mutum ce Laure da bata girma kullun jiya iyau take Suwaiba tace baba ni yanzu ai ba zan taba yarda mama ta hadani da kowa ba tunda na gane halinta bana kai mutum ga alheri bane ko yaushe.
Nace tashi mu shiga mu gaida su mama mu wuce zuwa sauran gidajen sai dai kafin na shiga saida muka leka mama Altine bata nan ta fita zuwa unguwa.
Kamar kullun yadda mama Laure ta saba tarona babu yabo ba fallasa hakan ne ma yau a fuskan ta don tunda tace a, a mutanen birni ne yau a gidan namu bata sake bi ta kan mu ba sai Suwaiba ce ta shiga ta dauko tabarma ta shimfida muna a waje cikin yar rufar dake daga kofan ta da akayi.
Amaryan baba tafito da murna tana muna sannu da zuwa na karbi danta dake goye a bayan ta take cewa jiya mukaji labarin kin shigo kin dawo da yaya a wurin mai kuli.
Nace mun shigo mama aiki ne ya dan yi min yawa da mutanen dake shigowa yasa bamu samu shigowa wurin ku ba a jiya din.
Tace to yaya hanya andawo lafiya Allah yasa abinda akaje nema ya amfana ga kowa ai kina da kokari wallahi duk da baki kasan amma aike ko yaushe baya katsewa a gare mu.
Nace kai mama ai hakan ya zama dole nayi mata gaisuwan mahaifinta da na samu labarin ya rasu bana kasan .
Dama haka ake so ai a dinga bin masu hannu da maiko idan sun shigo kamar za a fadi ana ladabin shegu gare su.
Na dauka ma dani take sai naji amarya na cewa bakin halin wasu kuma bai bari hassada ya sa suci arziki ai gara nabu naci arziki dana zauna hassada ya kashe ni a daki.
An girma ba a san an girma ba har yanzu mugun hali ya hana a tuba a koma ga Allah sai yawon bin boka da malam a ka iya.
Nace da yarana su mike mu tafi na mika masu tsaraba da bazo masu dashi harda yaran amaryan babana sai kuma mama ta hau fada wai har yanzu ina nuna mata kiyayya a fili.
Ita may yasa ban ban ta wani abu ba kari akan wanda nabata amma na uya sakowa kannena har da agolan gida tsaraba.
Allah sarki dadi inji barawon takanda an daiji kunya wallahi ai sai ki bari diyan ki da kika hana su nuna yara jinin su ne amma ba wacce hassadan ki ya zamawa taki ba a duniya.
Don rashin ta ido wai yau har kina fada kan tsaraban hajiya ina nan a bayan ta babu irin zagin da bakiyi mata har fadi kike wai ta magance kowa a gidan mijin sai abinda ta ga dama take masu a gida.
Kin ce ita da uwarta ne ai sukai wa yaran ki asiri suka lalace babu mai mayar da sufe wuta yanzu kuma abinda taiwa yan uwan ta ya tsone maki ido Albarka take nema shiyasa kike ganin ta ko yaushe a haka don babu hassada a zuciyar ta ita da uwarta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE BA A YAFE BA, , , , ,

109

Naji dadin dan lokacin da na samu kwana biyu na zauna a gida tare da yan uwa na da iyayyena don naga matsalolin su na taimaka wa wanda zan iya taimakawa a nan kafin na koma na sake shiri a kai.
Suma hakan don sunji dadin kasancewa da mu a lokacin don sun nuna muna so da kauna iya a dadin saboda yadda daga ni har yaran mun sake jiki sosai da kowa a cikin su.
Sai da na share sati biyu cur a gida muka shirya dawowa Abuja don aikin da ake nemana akan shi idan ba haka ba yadda daddy baya kasan da sai na share kusan wata daya a gida tare da yan uwa da iyayyena.
Sai da na kwana uku a kano nagama komai da nake bukatan yi na bar garin da dare muka shiga abuja don haka kowan mu a gajiye yake a lokacin.
Wanka sukayi yaran suka kwanta ni da su Atika muka dan yi abin da ya kamata muka kwanta muma.
Washe gari monday haka da gajiya na shiga wurin aiki don meeting din da muke da shi a ranan wanda ya zama min dole da sai na halarce shi dole.
Bamu fito ba sai karfe uku na rana don haka ban tsaya ba na nufo gida kai tsaye don nai wanka da sallah na samu dan abinda zanci a gidan.
Wanda nayi sa, a an gama abincin wanka na fada nafito na tayar da sallah a gurguje don na makara sosai da sallah da ban samu nayi ba a cikin lokacin sa.
Sai da na idar da sallah na shirya na fito falon wurin su mama da yara na zauna nan kowa ya fara kawo min korafin shi na baida abu kaza na komawa school.
Shigowan maman ihisan yasa yaran dan tsagaita min da damuwada suka sakani gaba dashi wanda bai hanani cin abincina ba a tsanake.
Mun gaisa da ita take tambayana mutanen gida nace da ita duk suna lafiya tace dani kun sha gida wanan karon kan ?
Nace wallahi kamar kada mu dawo da sauri tace dani kauye din kike cewa kamar kada ki dawo maman Haidar ?
Da sauri na dan kallota nace inane asalina maman ihisan ai kowa yabar gida gida ya barshi da kauye da birni in dai da wadata ai duk daya ne ga bawa.
Tace hakane aini nayi dana sanin rashin tafiyana da kuka tafi kuka barni don wanan mara mutuncin matar tashibhaka tazo min da wasu irin tika tikan mata a gidan nan wai suna meeting a wurin ta bakiga iya shegen da sukai muna ba a gidan nan wallahi .
Dariya ne ya subuce min nace da ita ashe kun sha kallo tace kallon takaici ko may abu tun sha biyun rana suke abu daya har muka kwanta ni dai ban san watsewan su ba ranan.
Nace wata sabuwa ke nan kuma yazo muna gidan ke nan gara da bana nan nasan da nawa ya samay ni don dani kowan su zata shigo gidan ranan.
Tunda ni suka saka a gaba tace ko kina nan ai bazaki kula su ba don babu wasu itin kilakan mata ne dasu.
Nace ko ajikina tunda ba a guna suke alamarin su ba sai dai wacce duk ta kulani shine zasu jini kin san ai saniya bata sani ana son ta kauce sai an tokari bayan ta ko ?
Kai kema dai wallahi kawai dai don baki gari ne kawai nace ai gani sai su kara dawowa in don ni dama sukai taron su gani.
Tace dani aini ranan naga ikon Allah zakice gidan nan ko wani wurin sai da motane don irin yadda suka baje motocin su ke da ganin su babu mutanen arziki a cikin su wallahi.
Nace ai in mutum bai mutum ba bai gama ganin duniya ba mu kuma irin namu kaddaran ke nan da muke gani ko wace da nata irin sallon da take zuwa muna.
Tace bari maman haidar wallahi ni har mamakin wanan mutumin nake ji irin wanan rayuwan haka ga yara mu na tasowa suna bude ido da abubuwan barkata a gida suna gani.
Don duk wacce zata shigo da nata irin sallon iskancin da zata zo muna dashi a gidan gida ya koma muna kamar gidan yan iska.
Nace da sauri ga wanda ya damu da abinda suke ciki ba nifa ban damu da kowa ba balle lalurar mutum ya damay ni.
Tace zulfa fa suna lafiya nake cewa da ita suna lafiya ina ga karshen sati mai zuwa zasu dawo nan din itama yadda mukayi da ita.
Tace dani kuma again nan din ita ma zata sake dawowa da zama nace ba anan din take ba dama may ye amfanin zamata a can da takeyi ita kadai ai gara ta dawo a hade yafi.
Allah ya kyauta tace dani tare da mikewa tsaye tabar falon ran ta babu dadi a raina nace kishi kumalon mata ke nan koni ai ba taki na bar gidan ba ta zauna ita kadai kamar yadda ko wace mace ke bukatan ganin ta ita kadai a gidan mijin ta.
Amma ni may zaisa na wahal da kaina ga haka ni da na shiga cikin mata uku na zo a ta hudu shine zan sakawa raina wani kishin banza can.
Wai ma akan wani mijin zan zauna ina kishi mijin da ko yaushe baya nuna an mashi daidai a cikin kwashe kwashen mata yake da yawan aure a gidan.
Na ja tsuki tare da kiran Hadiza tazo ta kwashe kayan abincin da naci a gabana tare da mike kafafuwana a saman dan stoll din dake a gabana na dafe kaina da hannu daya ina tunanen maganan da hindatu ta fada min nace a raina Allah ya kara hadani dasu wata rana zasu san allura ma karfe ne ba abin banza bane shi.

********* ********* *********
Kamar yadda muka barar da zulfa hakan ne kuwa a karshen satin ta dawo Abuja sai dai tun dawowan ta ban samu zama ba don yara na dake damuna suna fama da lolayin ciki kowan su.
Idan na gama da wanan wanan zata kirani da nata korafin kuma haka suka raba min hankali ga aikin da ya taso min a gabana kuma ban da hutu ta ko ina a kaina.
Ranan jumma,a maigidan zai dawo kasan don haka a bangaren kowan mu sai shirin taron maigidan akeyi kowa na nuna nata bajin ta akan dawowan shi kamar yadda ko wani gida haka mata keyi idan miji ya dan yi nisan balaguro da gida na kwana biyu.
Ashe mu duk shirmay mukeyi a bangaren mu bamu sani ba sai ranan ds zai dawo yai waya zasu iso da karfe sha biyun rana yakuma ce ba sai mun je taron shi ba da yan aikin su yake tare.
Ina dakina ina shiri Atika ta shigo tana ce wa dani ga Anty Amira da Aisha sunzo na ce kai sunzo min da matsalan su ke nan daga mai miyau sai amai a cikin su dariya tayi ta fita daga dakin.
Sai gasu sun shigo tun daga kofa suke kwala min kira da mummy mummy nace ya salam wanan kiran fa na tashin hankali haka fa for god sake ?
Suka fada min a jiki da murnan su muka shiga gaisawa dasu nan Amira take cewa dani mummy wani buki kukeyi ne a gidan yau naga gidan ya cika da motoci mana haka barkatai.
Cikin mamaki nace motoci kuma a ina na mike tare da leka window dakina aiko matane na hango suna shige da fice a bangaren amaryan daddy din.
Nace kun san mun samu yan bidi,a a gidan yanzu kila wani abin sukeyi kuma a nan ashe ni ban sani ba wai duk dawowan daddy akewa wanan shirin haka .
Sai isowan shi gidan ne mukajiyo hayaniya ta ko ina a gidan da shewa wai suna mai sannu da zuwa.
Sai dai kamar hadin baki don babu ko mutum daya daga cikin mu mamaki wanan abin ya bashi don haka yayi zaune a cikin mota yaki fitowa daga ciki.
Suna tsaye sai iskanci suke zubawa irin na manyan mata yan duniya suna wani girgije girgijen jikin su.
Waya ya daga ya kira mu dashi yana fada wai ban mu san ya iso bane kuma wani haukane haka mata suka taru muna a gida haka suna wanan iya shegen haka ?
Nace a gidan nan to banda ma saniya a kan su amma ganinan fitowa yanzu ai.
A tare mu uku muka dinga fitowa daga part din mu nice ta karshe tare da yarana gaba dayan su muka fito shigan mu ma kawai ya isa mutum ya tsaya kallon mu don kowan mu ya kure a dakan sa sosai rike nake da hannun anty da daddy da suka sha irin nasu adon nan kuma kallo ya koma a kan mu duk wanan iya shegen da suke zubawa a wurin.
Motar har lokacin yana rufe haka muka ratsa su har bakin motar daidai lokacin ne ya bude motan tare da sako kafar shi daya waje.
Sai na karasa bude motar tare da rankwafawa gare shi na dan kamo shi da saurin ta ta karaso bakin motar tana bangaje yaran dake murnan ganin mahaifin su har anty na buga bakin ta a kofar motar wai tana kamo shi.
Wani tsawa ya daka mata tare da karasa fitowa daga cikin motar gaba daya yana kama yarinyar yake fadin kina haukane haka komay da zaki ture min yarinya kina gani.
Jaye min daga nan please ya juya gun matan da suka dandazo a gaban mu yana fadin wa yan nan fa kuma daga ina haka suke su ya busu da wani irin matsiyacin kallo na takaici hindatu ta fada jikin shi ya rugumay ta haka ma zulfa tai mashi ban tafi ba shi da kan shi ya jawoni izuwa jikin shi ya kama hannun su jinior muka shiga cikin gidan yana rungumay dani a jikin shi .
Nan muka barsu tsaye cikin takaici da mamakin wannan irin cin fuskan da daddy nuna masu a fili gava kowa don su suna ganin duk a inda yar wanan kungiyar take dole tana da razara da matan da ta samu a gidan don zaman su hamshakan mata a gari masu kafafen kungiya na kan su.
Wata da take itace hanshakiya a cikin su ce ta fara magana da cewa asha samira banji dadin ganin haka daga gare ki ba ashe kin san baki shirya ba kika taramu a nan don ganin wanan bakin cikin haka ?
Yanzu wanan cin fuskan da mijin nan naku yai muna kinga kin kyauta muna ke nan ko may da har zai dubemu haka a wullakance yaja iyalin shi ya barmu kamar wasu marasa galihu a gurin.
Daga haka bata sake magana ba ta nufi motar ta sauran ma ganin shugaban kungiya ta nufi hanyan fita suka fara sake magana suna fita daga gidan daya bayan daya cikin kunar rai wai an masu wullakanci an nakasa su.
Hankalin Samira yai matukar tashi sosai daga ita sai kawaywn ta biyu aka watse aka barsu a wurin nan suka shiga magana a kaina.
Na yarda da cewan da malam baushe keyi da neman tsari na jiki idan bana sheri bane yana da amfani sosai ga mutum watarana.
Ga yadda irin zamani ya koma a yanzu duk da malamai na fadakarwa amma zuciyan wasu sai kara bushewa yake wurin aikata aikin kaucewa Allah.
Don dai kawai wani buri ko bukata na duniya akan su irin haka ne ga wanan matan don su a nasu ganin kamar duk wata mace a duniya zasu iya shiga da fice su takata yadda ransu ke so a gidan miji idan sun samay ta.
Don koda mijin da baida mata daya su ta aura haka mai shi zai tabbata a duniya ba wata mace sai su haka kuma idan kishiya ko kishiyoyi suka samu ba zasu dauki lokaci a gidan basu watsi da wanan macen ko matar da suka tarar a gidan ba.
Sai dai duk da haka ba wai kullun ne suke nasara akan ko wace mace da suka sama a gida ba akwai wa yanda kan dan fi karfin su a zauna aita fafatawa dasu a gidan Allah ya tsare mu daga sherin irin wa yan nan mata masu mugun hali na rashin tsoron Allah.
Nasan ba komai daddy yakewa wanan rawan kafa haka ba sai yadda zai ga komai ya daidaita a tsakanina dashi wanan karon.
Yayin da su kuma sauran kishiyoyina suke ganin ai asiri ne nai mashi tare kuma da ilimi da kyau din dake gare ni yake min wanan rayuwan haka.
Wanda nina san ba haka bane alamarine na Allah, sai farko idan ka samu daukaka gun Allah sai ya tsare ka ga komai.
Ke dai yar uwa maida al, amarin ki a gun ubangiji a koda yaushe sai Allah ya tsare ki daga duk wani abin ki a gare ki.
Duk wanda ya nufe ki da sheri Allah yana tare da ke sai ya koma a kan mai shi duk wanan aikin dake gabana bai hana ni kullun tsaida dare abokin hirana ba wurin mika koke na ga ubangijina akoda yaushe.
Rana ce kawai nakan dan samu lokacin aiwatar da rayuwana na duniya a cikin sa don shi tashin dare wani alamari ne dake tafiya da sabo da saka abin a zuciyar bawa.
Fitina ce sosai a tsakanin Samira da maigidan yayin da mu kuma sauran iyalin nashi muke a cikin farin ciki da dawowan shi don mun godewa Allah yadda taso taga mun nakasa a kan shi hakan bai samu ba a gare ta don bai shiga guntaba ma balle ta aiwatar da duk wani shiri nata akan shi balle abin yai tasiri gareshi yadda take so.
Don ba karamin gagarumin shiri tayi ba kamar yadda mata da yawa suke wanan irin shirin ga maigida idan ya kwana biyu baya cikin iyalin shi.
Wanan baiwan ne daga Allah don badon Allah yaba tsare bayin sa ba da wata irin shirin da kishiya take a kanta ko daga kai miji baya iya yi ya kalle ka da suna wai abokiyar zaman ta.
Amma da yake abin daga Allah sai kaga ubangiji yana kare

Download complete TXT · Novel page