Murucin Kan Dutse

Chapter 146 of 146

bayin sa masu dogaro a kan shi suna yawan kai kukan su a gareshi ko da yaushe.
A nan Allah ya taimakeni a kan Samira don haushin ba nawa bane ni kadai don ya shafi kowan mu saboda ta shiga wurin shi ta samay shi tare da zulfa suna soyewan su washegari da ta koma kuma ta sake samun shi tare da hindatu .
Sai haushin nawa ya rage ya koma a kan su take cewa da kawarta dama hakane ana zaton wuta a makera sai a samayta a masaka.
Don haka tai muna bugun dan kade gaba dayan mu tace mune mukai mata wani sihiri miji ke ganin bakin ta haka daga dawowan shi.
Ranan da girki ya dawo a kaina ne muka kwasa da daddy din don har lokacin ina a kan bakana na rashin yarda dashi da banayi.
Ya kirani a waya yake fadin nazo na samay shi ya dawo nan na shirya na samay shi a falon wuri na samu na zauna daga nesa kada dashi tare da gaida shi da dawowan shi.
Ya amsa min ba tare da ya dago kan shi ba yace maman Jinior ke nan wai ni ban fahinta ba ya fadi yana kokarin rufe takardan dake a hannun shi.
Ya dago yana mai kallona cikin mamaki nake cewa dashi na may fa ke nan daddy don da zaran ya kirani da wanan sunan na maman jinior nasan da akwai magana ke nan daya taso a kaina.
Yace wai har yanzu kina nan akan bakarki ne na kina guduna ina da cuta ko may ?
Nace ni bance kana da cuta ba daddy kawai dai don na fahinta da irin auren nan da kake a yanzu ko a kai tsaye ne ko da binciki gama yadda duniyar nan ta mu ta koma a yanzu.
Murmushi yayi yace dani yayi shine har yakai bana samun kulawan da aka saba bani ko kadan kamar baya.
Nace ba haka bane wanan kawai dai dorowa ne don ni ban ma san ka dawo ba gidan ai.
Yace dani karbi wanan na mika hannuna na karba a cikin ladabi tare da budewa sai naga ai form ne na wani makaran ta a kasan saudiya dake garin madina.
Ga kuma sunayen yarana a jere a ciki su hudu a form din na gani da dan wurin zulfa guda, da sauri na dago kai cikin mamaki ina kallon shi tare da son jin na may ye wanan form din kuma daddy ?
Yace dani kin karan ta aiko ?
Nace na karanta sai dai ban fahinta ba yace ok yaran nan nake son akai su can suyi karatu dukkan su.
Nace dukkan su daddy yace ko baki ra, ayin hakan ne ke nace a, a ni may zance abinda ka zartan ai shine nawa.
Yace good ina da raayin yarana su fahinci addini sosai a rayuwan su tunda Ubangiji ya hore min abinda zan iya daukan nauyin su a hakan dashi.
Masha Allahu nace dashi yace na gama komai akai saura tafiyan su idan lokaci yayi Allah ya kaimu nace tare da fatan Alheri ga wanan tsarin.
Yace haka nake son ji wanan halin naki yasa nake kara son ki a raina ko yaushe Rahama don biyayyan ki a gare ni sai dai kuma gashi ana yabon ki ga sallah kina son kasa yin salati kuma.
Nai murmushi nace ni din kuma daddy may kuma nayi baiyi magana ba ya miko min wani takarda dake gefen shi again yace karan ta wanan mu gani kuma.
Na karba na bude sai naga takardane na test da aikai masu shida Samira din wata shidda da suka wuce a baya.
Hakan na nufin ayi test din ne kafin su daura auren su dashi kuma a sibitin mu ne akai masu wanan gwaji din da nake son gani.
Ina kai karshen takardan na sauke ajiyan zuciya tare da dago kaina na dan kalle shi ina kokarin mika mai takardan.
Ya karba tare da fadin kin gansu da haja yanzu ko akwai sauran wani abinda kike son ji kuma don naga kina daukana ban san abin da nakeyi ba ne ko ?
To ki sani ni jarabar tawa bata kaini ga har na dinga yin abu a ido rufe ba haka yadda kike nufi nakeyi din.
Na dan musguta zamana kadan cikin jin nauyi da kunya ina cewa dashi ni abinda doka ya tabadar nake magana a kai, bawai nace kakai ga hakan bane ai.
Ya ware hannaye shi tare da fadin what ever d case dai yanzu kin gani a zahiri dama na kyale kine naga iya gudun ki.
Murmushin yake nayi tare da dan dagawa na kara mika mai takardan nace abinci fa akawo yanzu ne ko sai anjima.
Yace idan an tausaya min abani don tun karyawan safe danayi ne a cikin nan nawa har yanzu.
Mikewa nayi da nufin zuwa dauko mai abincin nasa sai naji yace dani ki turo min zulfa tazo idan kin tafi na ansa da to na fice falon.
Sai da na shiga guri ta na nufi nawa bangaren inda na fara hada mai kayan abincin da na shirya mai da kaina.
Koda na koma na samay su baram baram da ita tace bata yarda da zancen zuwa danta wani kasa ba naji tana cewa ita ba yaran ke gunta da yawa ba da za, a dauke mata dan ta daya akai wata kasa wai karatu.
Ban tanka su ba na shiga shirin abinda nake a gaban shi tare da sauraren maganganun su din.
A cikin fushi ta bar falon sai lokacin nace dashi tunda kaga hankalinta bai kwanta ba don Allah daddy a bar zancen yaron kawai.
A harzuke yake cewa dani akan may itakeda iko dashi ko ni da zance ga abinda nake so har ta tsaya musanta min ga hakan.
Ni naja bakina na shiru daga hakan shima din shirun yayi na dan wani lokaci kada na juya gare shi tare da fadin bisimillah ga abincin nan.
Komai ya koma muna normal a tsakanin mu dashi ba sauran fitina sai dana fita girki Samira ta karba wanda nake gani a ranan ne ma ta dawo gari.
Mu dai da asuba muke jin kururuwan fitina a gidan wanda tun lokacin ban kara biyewa akan su ba.
Ban kuma sake jin duriyar Samira din ba ma a gidan da sannu loiacin tafiya yara na yayi sai naga ashe ba da dan wurin zulfa za ayi ba ashe.
Sai da na kai su kano sukai sallama da iyayyen mu mukai tafiyan da hajiyan daddy da za a kai asibiti saudiya sai ihisan da muka tafi da ita da Atika.
Makaran ta ba laifi a wurin tsaruwa kuma yaro baya dawowa sai idan ya sauka yayi hadda za, a bari yazo gida ya kwana biyu idan yana da bukatan ci gaba da karatu sai ta koma yaci gaba dayi wasu littafai da kuma fannin boko watau secondary di su har digree.
Abin yai matukar bani shaawa sosai don nasan insha Allahu idan Allah ya raya min su nan gaba kadan zanyi alfahari da su, bani ba har da kasata baki daya da yan uwa.
Bayan mun barsu ne mun dawo masauki nakewa daddy godiya da kuma fatan alheri ga yin hakan da yayi.
Akwai kewa amma da yake karuwa ne ga kowa daurewa nayi ga abin na fitar dasu a raina baki daya.
Bayan mun dawo ne nake samun labarin wai ashe ba karanin fitina akayi da zulfa dashi ba har takai gun iyayye yasa ya janye maganan tafiyan yaron nata.
Ga kuma labarin Samira da tazo har gida tai masu tas har tana ikirarin wai sai mun gani da baki dayan mu abinda zatai muna kamar yadda mukai mata.
Amira da Aisha suka haifi diya su duka maza muka sha buki sosai na suna Nasir ya gama karatun shi shima yafito da aninin shi na su na soja.
Zama dai ne na hakkuri har lokacin a tsakanin mu don ba wai an daina zaman kishin bane a tsakanin mu.
Shekara takwas yarana maza sun zama hazifai na addini tako wani fanni sun zo gida kowan su ya girma sosai.
Ida na kalle su sai naga tankar ba nice na haife su ba da cikina mahaifin su ya zama don sosai yanzu kafan shi ya kama kasa ga arziki ga kuma yara sun girma.
Haka yasa ya bukaci da na aje aikin gwaunatin da nake na zauna gida a cikin iyalina ban yi mashi mussun hakan ba na aje kamar yadda ya bukata na zauna gida ina dan duba asibitin daya bude a kano duk da haka ida aiki ya taso muna zaga jahohi muna aiki da gwaunati din don kwarewar mu ga aikin .
Hajiyan daddy ta rasu don haka muka kwasa sai kano a lokacin yarana duk suna gida baki dayan su kowa ya gan mu sai ya yaba muna.
Mun dawo daga gidan hajiya ta gan mu yaba tsaye tare da wasu mutane a kofan gida suna magana mu gaidasu zamu shiga naji mutumin na fadin yanzu kana nufin duk ita kadai ke da wanan yaran haka tubarkallah masha Allahu.
Mun gaida mutumin naji daddy yace dashi ka gan ta nan kyautar Allah ce a gare ni don ga sadaukar da rayuwa Allah ya ba ita takuma zamau min marucin kan dutse a rayuwana yanzu, , , , ,


Alhamdullahi yan uwa wace nabatawa akan wanan novel din ta yafe min don Allah don dan matsalar da aka samu akan tsaikon da mukai ta samu dashi.
Don Allah kuyi hakkuri da zainabun ku yan uwa uwayena da yayyena da kannina sai idan Allah ya nufa mun sake haduwa a cikin wani sabon novel din namu nan gaba kuma don Allah kuyi hakkuri ku yafe min yan uwa, , , , ,

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Download complete TXT · Novel page