Murucin Kan Dutse

Chapter 17 of 146

inda yake shiga banan yake shiga ba yana fadin ba zai lamunci ina wa mama rashin mutunci ba a gidan shi in har nace ban auren Jatau to nafito da wanda nake so yai min aure don shi ba ai mai dogon zawarci a gidan shi.
Inna tana daki tana jin duk yadda muke kwasa da babana a tsakar gida na shigo daki ina kuka ina cewa ban san abinda naiwa baba da mata suka tsaneni ba haka ?
Inna tace bake suka tsana ba yarinya nice suka tsana a gidan nan har ya shafe ki an riga an dasa mashi kiyayyan mu a ran shi tuntuni.
Nace Inna irin wanan abinda baba yake min wani lokaci har tunane nakan yi nace anya kuwa shine mahaifina kuwa ?
Tayi shiru ranta a bace yana mata suya da takaici cikin bacin rai tace dani idan bashi bane uban ki waye yarinya ?
Tsaban rashin tsoron Allah da makoma ne dai ke damun su daga shi har ita din.
Karasa wacce zaka dinga kuntatawa sai yar cikin ka ko yaushe ita yaya nata haukan kishine ya rufe mata ido take haka akan mu.
Don kullun burinta shine taga bacin raina a gidan nan idan taga haka shine farin cikin ta a gidan nan.
Ki dai yi hakkuri ko yaya yake mahaifin ki ne daga su har mu bamu isa muja da ikon Allah ba idan kuma Allah ya kaddara shima wanan din mijin ki ne babu tsimi babu dabara sai kin aure shi.
Yanzu abinda nake so dake shine ki daina wanan rashin kunyan da kika dauko mata kici da yi mata biyayya a matsayin ta na uwa a gare ki don matar uban ki ce kullun ina fada maki haka.
Ina zaune ina jin duk nasihan da Inna ta take min naso na daure amma kuma kukan da nake dan newa ya tsanan ta min zuciyana ya kasa daurewa ita kanta Inna ganin yadda nake kuka gwanin ban tausayi bata san sanda kukan ya kwabce mata ba.
Can dau inna ta daure take ce min yarinya yanzu ba kuka ne abin yi ba gare mu dole ne musan mafita ga wanan zancen naki.
Muryan baba ne mukaji yana cewa duk abinda zakuyi sai dai kuyi dana ai nasan kece mai daure mata gindi tanayiwa mutane iya shige a gidan nan.
Inna tana jin haka tamike tafito daga dakin tana cewa ai dama nasan duk maganan yarinya idan ya taso akaina yake karewa a gidan nan don rashin adalcin da ba ai muna.
Idan bani da ita ba wa ake wa wanan ikon haka a gidan nan ya kyale sai dai mu da aka raina muna kuran mu kawai.
Baba ya dinga kallon Inna da mamaki yasan duk lokacin da ta va da ansa ga zance a gidan to abin yakai karo ke nan ba dadi.
Ido kawai ya tsura mata ya kasa tabuka komai a kan ta sai muryan mama ne daga bayan su take cewa ai har da daurin gindin ka da suke samu suke ganin kamar wuyan su ya isa yaka yanzu a gidan
In bashi har yau Rahama take da zatace wai ga zabinta bayan wanda kai mata don ta samu dauri daga uwarta ko ?

****** ********* ******
Da sassafe sai ga Larai kawar mama ta shigo gidan wurin mama lokacin Inna tana dama muna koko da zamu karya dashi don ina daki dun kule har lokacin bana jin dadin jikina.
Da dariyan ta suka gaisa da mama take cewa a, a lauratu kice min kuma yar ki ta kara maku babban kamu ne agidan kuma ?
Lalai kun iya jefa fatsa a ruwa ko yaushe sai manyan kifin garin kuke kamawa, yarinya ta zama ma uwarta jari a gari don ko shi wanan din kada ku bari ya sullube maku.
Don nasan yo Allah na tuba ai kaman wancan din za, ayi tunda shima sai a hankali kinga kun kara samun wani gadon kuma ku haye ai.
Da farko Inna taso tai banza da su da suka taba ita da mama sai kuma taga indan tai shiru ta kyale su sun sha da ita.
Don ko gobe dawowa zatayi ta kara gasa mata wani don taci riban na farko din da tazo tayi.
Inna ta dago kai inda suke ta dube su tana murmushi ace hakane fa kedai Larai.
Kuma kin sab jahili shike gagawan yanke hukunci amma shi mai ilimi kullun yana kyautata zaton sa gurin ubangijin sa ne domin shine mai azurta bawan sa a duk lokacin da yaso hakan.
Tunda fatsar mu ya iya kama babban kifi ko yaushe idan kamu banza ne wasu sukama koda karami ne mugani .
Don ita killa wanan karon kifin da zata kama ba irinsa a wanan ruwan sai na gaba zata kamo.
San nan ku sani shi sheri kare ne don mai shi yake bi hassada ga mai robo ko yaushe ai taki ne da ace ko wancan din ansan haka zai zama muna alheri da wasu sun kai nasu sunci.
Amma daya abin rabone daga Allah sai sheri ya juye muna alheri a rayuwan mu.
Sai gashi a filin Allah an dawo ana hassada akan mu kinga ko ai bamu ga kaico ga kamun manyan kifi don isa ne wani ko uwar ruwa yajefa fatsan shi ko kwai bazai kamo ba.
Take suka hasala matuka gaba dayan su don sun fahinci inda maganan Inna ya dosa gare su don kowa na da manyan yan mata a dakin shi.
Don idan baki yasan abin fadi baisan ansan da zai samo ba sai suke ji kamar Inna ta watsa masu ruwan zafi ne da safen nan.
Nan suka kama masifa da kumfan baki gareta sai ashar da mugun kalamai suke watsowa ita dai inna ta shige daki abinta tana dariya.
Bata san baba na gida ba sai muryan shi taji yana cewa haba haba Laira wanan ba girman ku bane kizo har gidan mutane kina masu shagube.
Idan ma an kaiki gurin maigari baki da gaskiya anan din babu ruwanki cikin zancen kishin su.
Nan suka juya kan baba da fadan suna fadin dama ai baka taba ganin laifin su kamar Asiya ce har zatai muna gori wai namu diyan ko samarin kirki basu dashi.
Dama ai nasan duk munafunci ne kokai baka kaunan wanan zancen akan ta sai in yai dadi ne kake fin kowa cinyewa.
Idan ma asirin su ne da suka iya yaka ma ka sai dai ya tsaya a kan ka don ni bazasu iya komai dani ba.
Yace maza Larai ta fice mai a gidan shi tunda ba alheri ne ke kawo ta ba gidan sai hadin hasumi a tsakanin iyalin shi.
Simi simi larai ta juya tabar gidan tana fadan karya inda tasan yana gidan lokacin da batai gigin shigowa ba lokacin.
Tana fita ne baba ya juya gurin mama yana cewa ke kuma in kina kama girman ki ki kama don wanan ba halin arziki bane gareki.
Mama dai sai faman haushi takeyi wai tana fada an mata gori ita da diyan ta a gidan.
Indai don auren tsofin da nakeyi ne inna take ganin kamar wani fin diyan ta nayi su zuba haka zan kare rayuwana a wahalce gidan Jatau.
Don duk yadda zatayi shige da fice sai tayi ko bama so sai na tafi gidan nan nai masu bauta su ma kamar yadda na saba yi a gidan garbati bakin ciki shi ya dade bai kashe Inna ba dani.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA DON NAUYI GARESHI YAR UWA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH, , , , , ,

15
Da taimako na muka kanmala aikin girkin rana da muka samu anty ta dora don muna cikin hira na mike don jin kaurin abinci danaji.
Kofan danaga ta nufa dazun dauko muna abun sha na nufa sai dai ina shiga kaina ya daure yadda naga kayan girkin zamani ya cika kitchen din ta ko ina.
Na rasa yaya zan duba abincin da naji yana nuna alaman ya dahu a lokacin.
Gurin gas din na nufa da tsoron tabawa fal a zuciya na don ban taba amfani dashi ba sai dai cikin karfin hali na bude tukunyan dake saman wuta.
Na samu abincin har ya tsotse na sauke sai dai ban iya kashewa ba ganin kayan miyan da tai blandinga cikin blander na juya na dora a wutan sai kamshi ne ya ziyarci hancin su a falo lokacin kuma suka fahinci bani falon tun dazun da sauri anty ta mike zuwa kitchen din ta samay ni a tsaye.
Cikin mamaki take cewa dani Rama dama kin iya girki da gas ne ?
Kaina girgiza mata tare dacewa yau ma na fara ganin shu ai, tace min kiyi a hankali nan take min bayani kan komai na kitchen din muna aiki a tare da ita har muka karasa tana gwada min komai sannu a hankali har na fara fahinta har muka gama aikin na zubo ma mama dani , mukaci mukasha muka koshi.
Suna hira da mama nake fahintar akwai matsala a gidan nasu yadda naji tanawa mama bayanin komai dake faruwa.
Na bu gidan da mamaki gashi da girma da kyau babu ne kawai babu a gidan amma wai zasu bar gidan bada dadewa ba.
Ganin ina zaune a takure na kasa sake jikina yasa ta kallon inda nake tausayi nake bata matuka idan ta kalle ni yadda rayuwa yazo min ina yar karama da ni.
Anty ke cewa na taso ta gwada min dakin da zamu zauna a part din ta nan na kwashi kayan mu na kai dakin sai da na tsaya na gyara shi tas na shiga nai wanka tare da yin sallah.
Don a kauye na tashi amma ina da matukar tsabta sosai naki jinin ganin daki a ya mutse ko kadan.
Kafin wani lokaci nai ma gidan kwal don dama gyara yake so bai samu ba ita gashi tayi tafiya sauran matan gidan kuma ba zama sukeyi ba a gida koma sun zauna basu iya gyara ko kadan don son jiki.
Tun wanan ranan da na zo anty tasan ta rage matsala ta wanan fannin sai misalin biyar saura yaran gidan suka dawo daga makaranta su hudu na gani uku mata daya namiji.
Na sheda yaran anty daga cikin su, don na sansu kwanaki da taje dasu ina gidan garbati.
Biyun yan matan ne ban san su ba sai ranan na fara ganin su don haka nake kyautata zaton diyan maigidan ta ne su din, don akwai dan kama na jini tsakanin su da diyan anty din.
Nan suka kewaye ta suna mata hiran makaranta sai can anty tace bakuga Grandma tazo ba da Anty Rahama.
Gaba dayan su yaran suka juyo inda muke muna masu kallon sha,awa da namijin ne ya juya yana kokarin cire school bag din shi dake goye a bayan shi cikin rashin damuwa da abinda uwar tace mai.
Duk da yara ne an koya masu gaisuwa sai yaran da ba nata bane suke muna wani irin kallon mamaki.
Nasir baka gaida Anty Rama ba fa ya dan juye fuska a daure yace ina wuni ?
Muka amsa mai a tare da mama lokaci daya sai dayan yarinyar ta dan kwanta gefen hannun kujerar da anty ke sama tace mummy are they going to stay with us ?
Gaba daya yaran suka juyo suna son jin amsan da uwar tasu zata bayar a kaina maman tace dasu i think so, cikin jin dadi suka saka ihu lokaci daya suka samu waje suka zauna suna surutu.
Kamar yadda nake wa kannena a gida idan sun dawo school zan sa su tube uniform din jikin su na kwasa na wanke na basu abinci kafin su wuce islamiya.
Tsab na mike daga inda nake na ce da Amira oya Amira zo na cire maku uniform kuci abinci.
Duk sukayo kaina suna rige rigen zuwa gare ni cikin jin dadi a tsakanin su, anty tai murmushi daga inda suke zaune da mama suna kallon mu tace dani ku shiga daga ciki dayan dakin kayan su yanan an kowa ta nuna maki nata aini kin ceceni yau wallahi.
Komai na gama masu har abinci a sama sukace zasuci don haka can na hau dashi sukaci muka gyara gurin kamar basu bata ba.
Cikin kwana biyun da nayi a gidan na dan fahinci abubuwan rayuwa na gidan yadda take gudanar dashi a tsarin ta.
Kaman tashi da wuri da safe a girka abincin yan makaranta ai masu wanka a shirya su a hada masu abincin zuwa makaranta sai rakiya har bakin motan da zai kai su school.
Haka yasa ta samu sauki sosai a dan zuwan da mukayi da nayi motsi kadan zata fara cewa wai Rama na nagode nagode kinji idan naji ta fadi hakan.
Sai dai nayi murmushi nace kai haba anty wanan har wani aiki ne mai yawa ?
Nikan a guri na ai wanan ba wani aiki bane don banga abin wahala ba a cikin sa amma ita sai take ganin babu taimakon da yakai wannan tunda gashi tana samun hutu da yin barci da safe wadattace yadda ake bukata a gareta.
A kwana biyun da mukayi kawai shakuwa ne sosai ya shiga tsakanin yaran matan gidan dani sai Nasir ne har yanzu bai sake jikin shi dani.
Sosai nake mayar da hankali ga taimakon rayuwan anty a gidan ko ina na gidan sai walkiya yakeyi don yana samun gyara.
Idan yara sun tafi zan gyara falo har kitchen na dora abincin rana sai na koma part din anty na hada mata ruwan wanka na dan zauna da ita muna hira har ta mike ta shiga tai wanka sai nai saurin gyara mata dakin kafinta fito daga wanka na koma kitchen gurin girkin rana, kafin wani lokaci na gabatar masu da abincin rana ko.
Kafin mu cika sati daya komai na kan gidan nasan yadda akeyin shi zan kuma yi mata shi tsab haka yasa suke samun hutu daga anty har mama sun dan canza a wanan lokacin.
Duk wani abinda nasan bata so ko zai bata mata rai da yaran ta basu so, zan gujewa wanan abin .
Na zomo mai kafa kafa a kan komai na gidan bana shiga shirgin dabai shafeni ba don ko yaushe ina busy ne.
Ganin yadda yanayi na yake bana jin kiwar ko kyashin aiki komai idan ina yi, yawan shi bai damuna don ni a gare ni yar kauye tashin kauye har ina aikin yake anan bisa ga namu na kauye mai wahala sosai.
Sai dai ita anty ko yaushe cikin yi min fada take wai na dinga hutawa sai dai nayi murmushi kawai idan ta fadi hakan mama kan ce ai gareta wanan ba aiki bane.
Tana matukar bani kulawa ta bangaren ta sosai don tana nuna min kamar cikin mu daya da ita idan tana nuna min so.
Yau ma zaune take falo ta mike kafa saman dan stol din katakon dake gefen kujera wanda ta jawo zuwa gaban ta, dauke da waya take hannun ta tanayi tsawon minti goma da fara wayan ta kamar ba kudi ake akashewa ba.
Sai tv ke ta aiki shi kadai a falon don mama da suke zaune tare gyangyadi take yi lokacin a zaune ba kallo ba, ai dole mama tayi gyangyadi, taji sanyin AC na ratsa mata jini yanayi ya sauya sai barci duk inda ta zauna.
Ferfeson kodan kaza zalla tace nai masu yaji kayan yaji don hadin kauye nai masu take kamshi ya gauraye ko ina na gidan .
Na zuba mata shi mai yawa tare da dorawa ga ture da goran ruwa sai dai ba mai sanyi ba nazo gaban ta inda take waya na aje mata kayan abincin naji tunda safe tana cewa tana son cin bread da shi ferfesuf irin dai kwazaban mace mai ciki abinda, bai yuyuwa tace shi take so.
Sai ganin na hado mata shi komai kamar yadda take muradin son cin shi kusan kwana biyu ke nan da take marmarincin hakan.
Ta manta waya takeyi sai cewa tayi kai masha Allah Ramana Allah yai maki albarka duniya da lahira ya kare ki daga sherin masheran ta.
Yanzu abinda nafi kusan wata ina son nayi na zauna naci kamar may shine daga kinji na fada kika hada min yadda nake so.
Murmushi nayi ina gyara aje mata kayan abincin da kyau take cewa anya Ramana idan mutanen gidan nan suka dawo zasu gane ni kuwa wanan irin kulawa dana samu a yan kwanakin nan haka.
Sai da taji dan murya cikin waya yasa ta tuna waya take tun farko abincin dana shigo mata dashi ya katse ta.
Daga cikin waya ake tambayan ta wacece take zukawa albarka haka ne wai ?
Tace bari kai dai heartbeat sister na da suka zo da mama ne ta hada komai na gidan nan ta hutar dani daga barci sai ci sai wanka sai ko kallo.
Yace good da kyau amma ko na gode mata wallahi tayi min maganin ki tace wallahi kamar ka sani, kafin duk na gama barci na, zan samu komai is ready yarinya karama bata jin nauyin jikin ta ko kadan.
Yace kai amma wanan yarinyar ta kyauta min wallahi ki min godiya gurin ta tunda ta kula min da bugun zuciya na.
Dago kai tayi inda nake duke ina zuba mata ruwan miyan a plate tace Ramana kinji ana maki godiyan kula dani ko ?
Murmushi kawai nai mata na fara kokarin zubawa mama nata na mika mata, lokacin kamshi ya tayar da mama dake zaune tana gyangyadi a saman kushin.
Yaran da yake weekend ne na sauko dasu cikin hikima nazuba masu suka zauna ci don abinci bai damuwan su sai dai kayan kwadai kawai shine abincin su.
Ganin Nasir yaki saukowa yasa na diban mai nashi zanje nakai mai murya anty ne dake shan ruwan miya da cibi take tambayana da cewa wanan na waye ?
Cak na ja guri daya

Download complete TXT · Novel page