Murucin Kan Dutse
Chapter 20 of 146
haban zanin ta tana mika mai kallon kudin yake a cikin mamaki yake cewa na maye wanan din tace dama yar tawa ce tace a baka kayi hakkuri dashi ba yawa.
Sai da ya dan juya yana kallon kofan shiga gidan shi baiga kowa ba yai sauri ya karba yana fadin an gode ya shige gida har yai dan nisa mama ta juya zata shiga gida taji yace ki dai ja mata kunne ta kula da rayuwan ta a can Allah ya tsare tace amin nagode da karamancin da kai min.
Da tashigo ne take fada min yadda sukayi da baba nake cewa Allah sarki baba abin nashi akwai daure kai a ciki wallahi yana son iyalin shi amma tace ta raba shi dasu da karfi da yaji.
Mama tace ba abinda ya bani dariya sai waigen da yakeyi kada angan shi yana karban kudi yasan idan ta gani yau basu kwana aljihun shi.
Da dare muka tafi sallaman inna ta nan mama tai mata bayanin komai mama tace wa inna ta ina rokon ki Asiya ki bari yadda mahaifinta ya bari ta tafi ke ma kibarta Allah kuma yasa hakan shine Alheri ga rayuwan ta.
Don ni zaman ta gurin Saade zaifiye min zamata a kauyen nan ko bazan ta kara sanin duniya.
Inna tace ni na isa in hanaki yadda kike so da yarinya tsakanin mu dake sai fatan alheri da neman gamawa da duniya lafiya.
Allah yasa yarinyar nan gurin ta na karatun da take son yi ya cika ta wanan hanya.
Mama tace zata barni mu dan gana na kwana a gurin ta don sai zuwa gobe da rana zamu tafi in Allah ya yarda taima mama godiya takawo sakin Inna rabata tana godiya.
Bayan tafiyan mama inna sai faman nasiha take min na kama kaina na zama ya ta gari abin alfahari ga kowa nan gaba don wata rana sai labari.
Naji matukar dadin nasihan Innata ga albarkan da take ta saka min yafi a kirga
Kwana nayi ina tunanen yaya rayuwana zai kasance a gurin anty Saade ko baba zai yarda ya barni nakai ga samun cikan burina a rayuwa.
Da safe na shirya zan tafi gida gurin mama inna takawo adduoi tabani tace na fake na kula da yin su ko yaushe don suna da falala da faida nai godiya naiwa kakannina sallama nafice gidan tare da jaddawa Innata zancen karatun kanne na kada a bari ya dakata masu.
Shiko baba sai da zai bar gida ne washe gari yake fadawa mama cewa kinji wai Altine zata birni da yarinyar nan.
Wani uban ashar ta lailayo ta watsa ma mama Altine tana cewa munafuka makira dama ta fahinci duk itace mai hura muna kunne akan halin da muka tsira yanzu ni da uwata .
Da sauri tace kai may kace mata kan magan tafiyan da ita ?
Yace may zance da ita banda Allah yakai lafiya idan na barta nan din wani abu zatai min ban da karin bakin cikin da zata jefani ciki kawai.
Jin haka tace malam kakoyi tunane kafin ka bada bakin tafiya da ita birni tana nan ma bamu inmata ba balle rashiga birni idon ta ya bude ai watarana ma sai tace bakaine ubanta ba don raini.
Don haka wanan magana ajeye shi babu zancen tafiya gare ta ba inda zata tafi tana nan cikin mu dadi da wuya haka zata zauna garin nan.
Yace yanzu kan sai anjima in na dawo nai mata bayani don na makara kada mota ya wuce ni na rasa.
Abinda ita dashi basu sani ba yaune tafiyan mu zuwa burni sai dai baba ya dawo ya samu labarin tafiyan mu kawai gurin jama, an unguwa.
Komai na amfani mama ta dauka takai makwabtan ta boyo kayana dake gidan ta tasa an kwashe ankaiwa inna ta gurin su.
Haka yasa na fahinci tafiyan namu mai dadewa ne don ban taba ganin haka ba wani bako ta dauko da matarshi da suke yawon neman gida tace ya zauna a dayan dakin dake gidan da iyalin shi.
Sha biyu da rabi na Rana hamza driver na kofan gidan mama ba bata lokaci muka kama hanya.
Da zamu shiga mota yara sun fadawa mama lauratu sunga motan birni kofan gidan mama Altine sai gata tafito daidai mun fito zamu shiga mota.
Nan ta buga kasa tana fafin ba inda mama zata dani don ubana ya hana tafiya dani mama tace da ita kin makara don ni ubanta ya riga ya sallama min ita kamar yadda kika bukaci yai masu ita da uwarta to tun jiya mun gama magana dashi ko.
Nan taje har da tare gaban mota ta baje hannayen ta wai sai taga yadda za, a tafi dani birni.
Tana jin hamza driver yasa giyan mota tsoro ya kamata ta ruga da gudu gefe tana Allah ya isa tsakanina dake mai kuli kuli.
****** ********* ******
Mota na tashi nabi kauyen mu da kallo hawaye na zubo min a idona una tuna rabuwana da mahaifiyata da yan uwan haihuwana.
Biyu da rabi shaf muna cikin garin Kano ta Dabo jalla babban hausa yaro koda may kazo anfi ka .
Sai bin garin nake da kallon mamakin ikon Allah gine gine kamar ba mutane ne sukayi shi ba da hannuwan su.
Abin hawa tun ina girgawa har bakina da zuciyana suka daina aiki sai binsu da kallo kawai nakeyi.
Mutacan mu wuce nan driver na ta aikin tukin shi sai ga mu wani katon unguwa mai gine ginen zamani kala kala.
Muryan mama ce ke cewa dani ikon Allah Rahama yau gaki birni a kanon dabo tunbin giwa yaro ko da may kazo anfika.
Nace mama harda maita da sata sunfi kowa tace yarinyar sawasa kin ganki mayan ka.
Nace aiko har na koma gida bazan taba fitowa waje ba balle a sace ni tace ce Allah kin tuba fita kan ai sai randa babu rai kuma.
Wani irin katon gida ne naga driver ya karya kwana ya shiga damu yai horn maigadi ya wagale kofan muka shige.
Daidai lokacin ne na sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi mama tace barka da arziki yar nan Allah ya rabaki da rigiman uwarki lauratu da masifan jatau kin huta.
Mun fito da yan kayan mu dake cikin ghana most go don sai dana cika jakata da tufafina masu kyau tsufin nabarwa Inna ta su a gida.
Anty tana zaune a mamakeken falon su kafata harde a cikin daya ga remote din tv rike a hannun ta tana jin sallama mu ta mayar da hankalinta gare mu.
Tana fadin lale marhabin da Ramana yau gani ga Ramana a gidana Allah nagode maka daka nuna min wanan ranan gare ni.
Da gudu na naje na rugumay ta naji tace waisshi Allah yi a hankali anty taki rubabace na dago kai nace wayo sannu anty ta dafa min kai tana cewa Sannu Ramana sannun ku da zuwa.
Dukawa nayi da kaina sai hawaye shar tace da sauri subbahanallahi ko baki son zuwa ne aka rabo ki da gida ?
Sai lokacin ne ta dago kai tana cewa sannu mama mama take cewa ai dole na tsaya har ku gama shirmayn ku ko.
Wani bata son zuwa shirmay ta daine wai taji dadin ganin ki ke nan take wanan kukan haka.
Nan muka zauna a falo tare da ita tace bari ta dauko muna abinsha kafin abinci ya sauka.
Mama tace ina yan aikin naki kuma keda baki jin dadi tace cikin murmushi wai mama yaushe rabo ai duk an watsa su saboda fitinan matan gidan nan.
Gulma yai yawa ga fitina yaki ci yaki karewa dole aka sallami kowa daga mu sai halin mu yanzu a gidan.
Mama tace naji gidan shiru ina sauran yan uwan zaman ki da maigidan kuma murmushi tayi ta mike da kyat zuwa kitchen sai gata da kayan sanyi da sauri na mike naje na karbo mata kayan na kawo gaban mama na dire su.
Sanyi lemon ya hanani sha Anty ta kalle ni tace kisha mana Rama nace sanyi anty sai ya huce zan sha suka sa min dariya
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,
IDAN KIN BIYA KI RIKE AMANA DON AMANA NAUYI GARE SHI YAR UWA DON ALLAH MU KULA PLEASE, , ,
17
Zan iya cewa tun dawowan matan gidan har zuwa yau kwana biyu ke nan da cewa sun dawo gidan amma banji duriyan su ba har wanan lokacin
Ni dai a bangaren mu zan iya yiwa anty na aikin komai da duk wani abinda yaka mata na kula dashi.
Sauran matan gidan sai mamaki sukeyi yadda suka samu yaran su ga kuma gidan a gyare tsab kamar yadda da farkon shigowan su gida .
Kafin zaman gidan nasu ya canza kala, don ko wace daga cikin su tana ji da kanta bata iya gyara gida in general sai dai ta gyara daidai part din ta kawai ba ruwan su da sauran part din gidan haka zai dauki lokaci a cikin datti.
A da suna da mai aiki har mutum biyu da tsohuwa da yar matashiyar budurwa sai ya kasance gulma yai yawa kowan su na kokarin jaye mai aiki ta koma katkashin shi haka ya kawo fitina mai karfi har ya kai maigidan ya sallami duk yan aikin ya ce.
Yau da safe anty ne ta shigo dakin mu ina zaune ina gyara kayan yara ina ganin ta na gyara zamana da kyau tare da gaishe ta don nasan ba kasafai take shigowa dakin ba, dakin da muke ni da yaran nata.
Bayan na gama gayar da ita ne ta samu guri a bakin gadon Nasir ta zauna tana cewa na fa gane kunfi dasawa da Nasir gidan nan Rama.
Murmushi nayi mata kawai nace anty ai shi na daban ne a gurina yana bukatan a ja shi a jiki sosai.
Baki ta tabe tana cewa wanan ai halinsa sai shi don baida yadda sam wallahi ina mamaki ma yadda ya amince dake haka da sauri.
Tace cikin dan sake, tsaki tare da cewa dama nazo ne naga idan baki aiki ki shirya ki rakani wani gurin don fitan ma dole ne zanyi shi, su Amira ya damay ni na je ni tun jiya yake damuna na akan maganan.
Ban bata lokaci ba gurin shiryawa don anty dama da shirinta tazo dakin namu don mu tafi a lokacin.
Mun nufo kofan fita daga gidan na hango wata mace shigowa daga ciki kai tsaye yadda nagan ta tafe yasa na fahinci watace daga gidan don yadda take tafe a gadarance.
A karo na farko da na fara saka daya daga cikin matan gidan a idona ke nan tun bayan dawowan su gidan daga yajin da suka sha.
Wace nagani doguwa ce yar fara ba can ba tana shigowa gidan sabale da gyalen ta a kafadan ta tana kada yan makullaiyan motar ta a hannnun ta.
Waya take a cikin sakin fuska amma tana hango mu take annurin fuskan ta ya gushe mata ta hade rai a lokaci guda.
Tana ganin mu ta wani bata fuska tare da kawar da kai gefe daya ta nufo mu gadan gadan babu alaman kauce muna gare ta.
Hakan yasa naga anty ta dan kauce gefe daya gudun kada su hade su buge junan su.
Kai tsaye kamar ban ma san da ita a tafe ba saida kafada na da nata ya gogi juna ko gezau ban yi ba itace ma naga ta dan yi kamar zata tangada don buguwan da junan da mukayi.
Kam kaza tace tare da juyawa tana fadin, ke wata irin bagidajiyar ina ne wai kina tafe kamar dabba dake baki iya kaucewa mutane ?
Kamar ba dani take magana ba don ban juya inda take tsaye ba a lokacin.
Don idan na tsaya zan gwada mata ni yar tallah ce a kauye a baya don bani shayin uban kowa inda ta ganni.
Kada na tsaya bata amsa na batawa anty farin cikin ta yasa na dake na wuce ban bata amsa ba don da taji amsa daga bakina sosai.
Motan anty muka shiga batare da tace dani komai ba din ban ma yi zaton taga abinda ya faru a tsakani na da hindatu kishiyar ta din ba a lokacin.
Tafiya mu kadan yi mai dan nisa kadan daga uguwar su sai gamu a wani irin katon gida mai wani irin wawakeken get mai girma.
Horn tayi har sau biyu sai ga wani mutum daga ciki ya bude kofan ta danna kan motar muka shiga daga ciki.
Abinda idona ya gane min ban san lokacin dana sauke ajiyan zuciya ba har sai da anty ta dan juyo inda nake tana murmushi
Wani guri na hango an tara motoci har kusan hudu sai sheki suke suna walkiya kamar an tara dawakai kosassu a gurin.
Ta juyo inda nake tace dani bisimillah ko Ramana fito mu shiga daga ciki mu duba ban tsaya ba kamar yadda ta fita nima haka na fita daga motan.
Ko kasan gidan ma abin kallo ne a lokacin don ko ina yaji grass carpet a gurin kore shar da shi gwanin ban sha,awa.
Direct wani kofa muka nufa sai gamu a wani katon fili da ya raba sassan gidan kashi biyu ga wani katon part a tsakiya dake nuni hawan bene ne gurin.
A hankali muke tafe muka fara shiga side din dake left hand din gidan part biyu ne manya kowani dauke da bed room uku uku a cikin shi mayan an saka gadaje da kujeru baban daban sai muka fito zuwa sashen dayan sai naga ai kamar kayan shi yafi haduwa har dakunan gurin kamar sun dan fi girma sosai part din gaskiya ya hadu.
Muka dawo wani katon falo da yasha gyara sosai a gidan da gani shine main falo na gidan na kowa da kowa banda wanda ke cikin ko wani part.
Anan muka zauna don ta huta saboda ta gaji sosai a lokacin sai da ta dan huta take cewa dani Ramana yanzu zabi ya saura akan mu cikin gidajen nan biyu da muka shiga wani kike gani zamu zaba a matsayin namu a ciki.
Cikin mamaki nake cewa Anty wanab ne sabon gidan naku da zaku tare a cikin sa ?.
Cikin sakin fuska take cewa dani shine Rama baban su Amira ne ya matsa min sai nazo na zaba kuma kin san may?
Wai fa yau din nan yake so mu tare a gidan nan don haka wani kike gani zamu dauka a matsayin namu shiyan ni daku da yara.
Don yace su biyu a dayan part din zasu zauna kowace dana ta ai kin ga ba mai ganin wani a tsakani yanzu kowa yaci gashin kan shi kawai ne.
Ta kara tambayana na rasa ma wani zan zaba daga cikine wai farat nake cewa da ita ni sai nake ganin kamar wanan na ka shen da muka shiga yafi haduwa ai anty don haka shine zamu zaba.
Tace ashe tunanen mu yazo daya dake Rama don nima ya burgeni gaskiya sosai gashi da girma ga shi komai nashi purple ne da milk colour .
Bamu jima ba take cewa mu koma mu fara shiri don haka muka juya zuwa gida .
Kamar yadda mijin ya umurce ta tayi hakan tayi don bamu kwashi wasu kaya ba masu yawa muka koma gidan ranan laraba da dare don girman gidan duk a daki daya muka kwana gaba dayan mun cikin shiyan da ta zaba a matsayin nata a gidan.
****** ************ ******
Sai washe gari sauran mutanen gidan suka tare don ina ganin basu san da zuwan mu ba a daren jiya sai washe gari ne suka ga ana kwasan kayan anty ga wa yanda taba ma kyau cikin yan uwanta marasa karfi.
Suke tambayan mijin yake cewa dasu ai ya fada masu cewa kowa ya koma can tun two days ago.
Suna zuwa suka saka balai wai basu yarda da part din da anty ta zaba ba wai sun zabe shi a matsayin nasu tun farko da suka gane shi.
Mijin nasu ya nuna masu basu isa ba don basu zasu fara zaben guri ba sai anty dake matsayin babba a gare su a gidan.
Hakan bai masu ba sai da zulfa ta daga waya takira hajiyan shi tana kuka take sheda mata wai ana yawan take masu gakkin su a gidan nan don ko yanzu da suka dawo sabon gidan su gurin da ta zaba da farko nan Saade ta shige da yaranta.
Ran hajiya mama mahaifiyar maigidan nasu yai matukar baci ta shiga fada tana neman layin dan nata don taji ba, a sin maganan daga bakin shi.
Can ta lalabo lamban shi da kyat don balain da take kan yi yana dauka yaji ta haushi da masifa tana fadin wai mai sunan Alhaji may kake son mayar da kankane wai.
Mace daya figaga da ita ta hanaka samun sukuni da iyalen ka ta hana ka shakat don son kai irin nata.
Yanzu har wanan gidan ma da kuka koma sai da tai maka iko irin nata data saba don ita bakin hali irin nasa na gado da suka saba.
Yadda take takaman ita matarka ce haka su ma suke a matsayin matan ka ba wai finsu tayi ba
Shi bai kashe wayan ba shi kuma bai bata amsaba don ya san koma ya mata bayani ba sauraren shi zata yi ba.
Suka kashe wayan ya ci gaba da harkokin shi don a lokacin baya gida yana gidan gonan shi.
Washe gari muna part din mu duk muna falon anty din bamu faye zama a dayan part din da tace shine zamu zauna ni dayaran ba amma kayan mu yana ciki sai dai mu dan shiga mu fito mun fi zama a gurin ta.
Babu sallama sai ganin an fado muna kawai mukayi a shiya anty da ke kwance ga cikin ta da yai girma ya tana shirin shiga watan ta na haihuwa tai zubur ta mike tana yan kamay kamay tare da fadin hajiya sannu da zuwa.
Dakata