Murucin Kan Dutse

Chapter 21 of 146

ke ta bata amsa ba gaisuwan ki nazo nema ba zuwa nayi don inji dalilin ki na saurin daukan wanan part dina matsayin naki?
Shiko ke kina ganin cewa su sauran ba mata bane sai ke kadai ce macen auren a gidan nan don kina takama kinfi har mijin naku shekaru zaki iya mai wayo yadda kika saba.
Anty dai tana duke yayin da mama Altine dake ballan goro ta dakata tana sauraren hajiyan.
Idan ba kaddara ba ke har yaushe Alhaji karami zai auro sa, auroki a matsayin matar shi ya aje a gida haka tsofai tsofai da ke.
Baba inda yaran nan zasu tafi suna gidan nan daram kamar yadda baki so shigowan su gidan ba sai ki ta zama ke kadai a dole kin samu gida kin mike kafa daga ke sai diyan ki a gida.
Ni dai ban san yaya akayi ba ko maganan matar ne yai min yawa a zuciya ta yadda take faman aibanta min Anty na.
Sai ji sukayi nace kai amma dai wasu girma kawai sukafi mutum ba wayo ba.
Duk babban da bai gyara tsakanin maurata ba baikamata kuma ya bata ba har mutum ya zauna ya na aibanta macen aure wai dama yin haka shine wayewa ?
Ni na dauka ai duk abinda dan ka ya dauko yazama naka tundai ga uwaye mata .
Abin danka naka ne ba bambanci tsakanin matan shi sai dai kai babba ka hada hankalin iyalin danka ka nuna ma babba matsayin shi haka shima karami yasan matsayin shi shine girma.
A ko wani gida wanda aka san tarbiya da mutunci ansan uwargida itace kan gida dole itace mai fara zaban abu kafin na baya su zaba.
Kamata yayi uwa ta godewa Allah idan ya bata dan da yasan shimfida adalci a tsakanin iyalin shi bai kauce wa addini.
Amma wanan magana ba girman ki bane da darahan ki ba hajiya ace kina zuwa gurin matan dan ki kina raba daya biyu a tsakanin su don suna karkashin ki kawai kema fa uwa ce hajiya tunda nasan kina da diys don haka, ,
Tau ke kuma fa karamar mara kunya daga ina haka ke kuma wacece a gidan nan da dan tsugunin ki zaki tsaya ki dubi fuska na kina fada min magana ba kunya ba tsoron Allah.
Nace hajiya ba haka bane ni naga ke uwace a gurin mu ba girman ki bane da mutuncin ki yadda kike hajiya ace aji wanan irin kalamin na aibanta matar dan ki daga bakin ki.
Mutuncinki da kimarki yafi karfin aji haka a gare ki koda ace tsohuwar ce yake aure ai bai dace ba ke aji daga bakin ki kina aibanta abinda yake mallakan danki ne kuma abinda yake so.
Cabdi Sa,ade a ina kiia debo wanan fitsararar yarinyar haka mara mutunci mara kunya da ita ?
Wai ma waya baki ikon aje ta a cikin gidan nan ne har take ganin ta samu guri da kamar wanan yar zata kalli tsaban idona tana fada min maganan da wani mahuluki bai taba tsayawa a gabana ya fadi ba.
Anty saade na fadin hajiya yi hakkuri yarinyar ce shiyasa ,
Hajiya sannu da zuwa mukaji ance daga bayan mu ashe maigidan ne tunda nake magana da hajiya yana tsaye a kofan daki.
Ya karaso yana fadin hajiya kaunan Saade ne tazo kuma kinga abinda nakewa gudu ke nan a koda yaushe idan kina fadin magana na aibanta Sa,ade kada ya fada a kunnen yan uwan ta.
Gashi kuma yau karamar yarinya tana mayar maki da martanin maganan ki na kullun akan saaden.
Ke nan ran ka bai baci ba ga abinda tai min ba ke nan a gaban ka yace hajiya ai wanan maganan ku ne na mata ni bai shafe ni ba.
Yanzu ma nazo fitane naga motan ki a waje shine yasa nasan kina gidan na biyo ki nan don nasan kina nanan din.
Tace eh ina nan din don nazo ne kan zancen shiyan da ta mamaye na yan uwan ta.
Mu hadu a falo a hajiya nan akwai mutane a gurin sai muyi magana a tsanake.
Ba taki ba suka kwasa zuwa falo gaba dayan su har anty sa,ade din tabi bayan su don jin may za, a fada a falon.
Zaune suke kallo daya zakai masu ka fahinci kowan su a falon a cike yake a lokacin.
Cikin fushi hajiyan ta ke magana tana cewa ka taramu ka barmu a zaune ko kuma wani sabon wulkancin ne yin hakan.
A fusace ya ke don daya dago fuskan shi gaba dayan su sai da hankalin su ya tashi don ganin yanayinsa.
Sai da yakai kamar minti uku kamar yana nazarin wani abu can yace ina son na fara da tambaya anan ?
Don Allah ko a cikin ku gurin nan akwai wanda yasan yadda na samu aiki har na kai ga tara abinda ke gare ni a yanzu har nai wanan ginan da muka shigo.
Shiru sukayi gaba dayan su ba wanda yai magana sai hajiya ce can tai karfin halin cewa .
Don bamu san yadda ka samu ba shine zai hana mu yin magana idan kayi rashin adalci ko may ?
Yace hajiya may ye rashin adalci anan don na bawa uwargidana zabi akan girman da Allah ya bata a gidana.
Nakuma bata zabi amatsayin ta wacce ta taimaka ma rayuwana tun ban san ko mai ba na hanyan neman kudi har yakai ta fara lurar dani yadda zan zamo mai dogaro da kaina har zuwa wanan lokacin.
A fusace hajiyan shi, take cewa kace ma da kudin ta ka zama haka a yau.
A gadarance yace kusan hakane gaskiya don kudin ta da nawa ne muka hada nasai form na sai sauran abubuwan da ya sace nayi kafin na samu na kai ga appointment dina.
A lokacin hajiya ke kin sani Abba bai yarda da zancen aikin da nake nema ba yafi da son na kama kasuwanci kawai.
Ashe don haka hajiya yau komay nai ma sa,adatu kaman ma ban mata komai bane daga cikin gudun mawan da tai min a rayuwana.
Don haka yau hajiya a gaban ki ina son kowacen su ta sani cewa Sa, ade da suke gani ba abin da zanyi wasa ko sakaci da ita bane arayuwa na.
Don haka wace zata iya zama dani da mata ta zauna don a tare kuka gan mu da ita auren mu va zai sa na watsar da mata na mai tausayina mai sona da kauna na wace ta san zafina da tausayawa rayuwana.
Hajiya ta cabe da cewa ai ka karasa kace wace ta haife ka ta san zafin cikin ka da goyon ka.
Aa hajiya bata kai can ba amma dai ina son su fahinci darajan ta a guri na yafi karfin yadda suke tsanmani a yanzu don naga suna son su wuce limite din su agidan nan.
Duk wace bata iya zama a gurin da na ajeta hanya a bude yake gareta zata iya komawa inda tafito don babu dole a gareta.
Matata dai ce ba zan taba wullakanta taba akan ko wacen su insha Allahu.
Kuma ina son ku sani hajiya da kuke kai karana kona matana a gare ta ga hajiya ga ku duk wace ta kara kai karan dayan mu gurin hajiya a gidan nan kan al,amarin da ya shafe ni ko Sa,ade.
Mace ta sani kuma ta rike a kanta zan bata mamaki kwarai ga irin matakin da zan dauka akan ko wacece a gidan.
Haka ya isa please ban san may kuke so dani ba kowacen ku nan tasan zamana da matana tun farko haka kuma kuka amince da zaku iya zama damu a hakan da muke ban auro ku don na wulakanta matana ba don ina son abina kowan ku kuma ta sab da hakan ta amice don haka yanzu kune kma kuke son bi ta hanyan mahaifiyana don ku cuta mata kuma cutawa mahaifiya don Alhakin yarinyar mutane ya haukan magaifiyana.
Saboda may zakuyi muna wana mugun sakkaiyan hakan kuna amfani da mahaifa na don ganin an cutatawa yar mutane saboda hakkurin ta.
Kada kuyi tsanmani ban san abubuwan dake gudana a gidan nan ba na bar kowa tana abinda ta ga dama a gidana.
Akwai watarana yaba tafe ranan da zan dauki mataki daidai da laifin kowan ku amma dai ina mai kara ja maku kune ga abu biyu zuwa uku.
Na farko shine mai son zaman lafiya ya bar hadani da matata da iyayye na fada.
Sai kuma ina gargadin ku da ku daina shiga harkan Sa,ade ku barta taji da lalurar da Allah ya jarrabe ta da shi.
Don haka zance shiya da kuke cewa ta zaba ta bar maku wanda bakwa so zaku iya komawa can dakunan ku da kuka fito don yau idan Sa, ade tace min bata bukatan zama da kowacen ku a cikin gidan nan ya ya tabbata hakan a gare ni.
Aiko na hajiyan shi ta amshe da cewa tau issahe akan wanan figagan matar naka mutu kwakwai rai kwakwai kake wanan magana.
May yarinyar nan tai maka hakane har idon ka da zuciyar ka ya rufe yau a gabana kake wanan magana.
Lalai Sa,adatu kin gwada min ki kai kin kai matakin daba naki ba a gidan nan tunda har yau Alhaji karami ya rufe idon shi a gabana yake wanan magana haka.
Hajiya ya kamata ki sani yau idan haka ya kasance a gidajen auren yan uwan mu mata ba zaki ji dadi haka ba, muma ba zamuji dadi ba don may hajiya ba zaki daina wanan halin ba ko don kwanciyan hankalin diyan ki mata dake gidan mazajen su suna aure.
Au to lalai abin har yakai zakaiwa yan uwanka mata baki akan matar son ka duk ka haukace min yau don na taba ko.
Ai kafin kayi naka, naga wata fitsararar yarinyar da matar ka ta dauko ta aje a gidan don isa da mallaka ra fara nuna min fitsara don samun wuri.
Ta juya gurin antyna tana cewa ban son ganin wanan yarinyar a gidan nan ta gagawan barin gidan nan tun ban dauki mataki ba a kan ta ?
Hajiya wanan yarinyar yar uwar Saade ce nina bada bakin ta dauko ta nan don ta samu mai taimaka mata ga halin da take ciki tana bukatan taimako ?
Kafin suci gaba da magana sai ga maigidan ta ya kirata yana tambayan ta tana inane wai.?
Ta kasa bashi amsa don tasan ya hanata zuwa gidan dan nata saboda wanan halin da take zuwa tayi.
Kwata kwata bata kaunan zaman Sa,ade da danta don acewan ta kullun wai ta girmay wa mijin nata shi yasa take masu wayo.
Ta manta cewa itama tana da diya mata dake aure a wanu gidan har su uku bata tunanen cewa abinda take wa yar mutane zai iya faruwa akan diyan ta.
Mata bamu tunanen cewa mu uwaye ne masu diya duk abinda ka shuka shine kake girma a rayuwan ka.
Muryan mijin nata ne ke fada mata cewa tazo gida ga Aisha, yar su ta dawo gida da matsala.
Wanan maganan da taji ne yasa ta dafe kirjin ta tana cewa zata tafi amma zata dawo don bata karasa maganan da ya kawo ta ba.

****** ********* ******
******
Tun da farar safiya muryan Jatau ne ya tayar da mutanen gidan da balain da yazo masu.
Yake cewa mama tafito bazai yarda ba tasan yarta honko ne ta dauka takai mashi gidan shi don an raina shi.
Shi za, aiwa wullakanci ko may da za, a dauko honkon akawo maigida don an mai dashi tsoho.
Gaban mama ne yai mugun faduwa haka ta daure tafito zani na faduwa mata gashi har mutane sun fara taruwa don gulma.
Tace a ranta bari ta rufe ido tai mai na mahaukaci kawai a wuce gurin gaba daya.
Ta na lekowa take cewa kai Jatau kada ka dauka ko tsoron ka ake ji duk haukan da kakeyi kyaleka na keyi.
Mata kace kana so mata kuma na baka banga dalilin da zaka taso tsofai tsofai dakai ba kazo muna kana wanan magana abin kunya.
Tace ankai maka honko din sai ka turo min yata yau din nan na fasa auren bazata zauna ba a gidan ka.
Da Jatau yaga mama ta fishi iskanci da hauka dole ya kwantar da nashi haukan yace baki da hurimin daukan min mata, don mata zamana take yanzu.
Matar ka da kace honko ce ai daga yau ta gama zama dakai a gidan ka don dama kudin bazawara ka biya bana budurwa ba.
Yace a shekeke yo ina budurwan take anan kin kai min hinkon diyar ki aiko sai ga su Rukaiyya sun fito daga cikin gida.
Mama ta juya garesu tana cewa maza kuje kuzo min da Lawisa gidan nan yanzun nan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANI NA BARKI DA NAUYIN AMANA A KAN KI YAR UWA

18
Anty na barin falon ta dawo part din ta samay mu zaune inda ta bar mu ganin yanayin mu kawai zai sa kagane rayukan mu a bace yake dagani har mama Altine a lokacin.
A kasa nake zaune kusa da dima diman kujerun dake a falon ta samu kujeran dake daf dani ta zauna .
Sai bayan ta zaunane ta dafa ni a hankali tare da ambatan sunana ta riko min hannuwa na ta hade da nata guri daya.
Jin ta ambaci sunana da irin rikon da taimin yasa na mayar da hankalina gare ta tare da kura mata ido ina sauraren ta.
Rama ina son ki kwantar da hankalinki ki dinga nazarin kowa na gidan da idon basira.
Kamar yadda kiia san duk wani gida mai iyali akwai irin kalubalin da gidan ke fuskan ta hakane ma ko a wanan gidan namu.
Don gaba daya matan gidan da iyayyen gidan kalubalin su akaina yake wanda ba komai ne yakawo haka ba sai ganin Allah ya dorani kan mijina da kuma su baki daya a gidan.
Wanda ba komai ya kawo min shi ba sai hakkurina da kuma halaiyana na gari yasa na cin ma wanan falalan haka.
Rama ina so daga yau ki kasance mai hakkuri ga al, amarin gidan nan don zaki ji ko kiga abubuwa da dama na cin fuska a gamay dani amma dole sai kin daure ki kawar da kan ki ga hakan.
Babu inda zaki muna nan tare da ke har lokacin da Allah zai nufa ki kara yin wani aure idan Allah ya yarda.
Don haka kada ki jefa kanki cikin fitina da rigigimun gidan nan a kaina.
Nasan dazu ranki ya baci yadda hajiya bata ji nauyi idon ku ba a matsayin ku na yan uwana tana tozarta ni a gaban ku yadda taso ta saba da yi min hakan ne tun farkon aurena da danta.
Amma duk wanan ni bai taba damuna don dai nasan Allah kadai yakai ya rabani da heart beat ba wai wani mahaluki ba.
Nan dai taita min nasiha mai tsuma zuciya akan rayuwa har naji gaba daya ma zaman duniya ba dadi a cikin sa.
Washe gari kafin wani lokaci na gama gyaran ko ina inda ya dace a gyara sai na dora girki guri ya kaure da kamshi.
Ina gamawa na shiga nai wanka na saka daya daga cikin dogayen rigunan da aka sayo min na gyara na fito tsab dani.
Na dade a gaban mirro ina kallon yadda halintan jikina ya nuna min sura na a wanan lokacin.
Gaba daya dan lokaci guda na sauya nayi matukar kyawo na zama wata young fresh dani .
Dakin Anty na nufa don na tambaye ta ko zata ci abinci dana gama dafawa a lokacin.
Zaune na samay ta a saman sallaya da alama ta idar da sallah ne a lokacin .
Jin shigowana da yasa ta dan mayar da hankalinta ga kofan ido ta tsura min har na karaso inda take zaune durkusawa nayi daidai inda take zaune ina gaida da ita.
A daidai lokacin da ta shafa ta dago kai tana min murmushi take cewa dani dama yanzu nake son kiranki don zamu dan fita zuwa unguwa sai dai ba mai nisa bane .
Na sharada zamu tafi gidan sister din maigidan ta haihu yau kwana hudu ke nan.
Sai da na tabbatar da ta gama magana nake cewa Allah ya raya tare da cewa dama nazo na fada maki na gama abinci ko zakici yanzu ?
Tace da hakan nayi zaifi min don ina dan jin yunwa dama kin ga sai na fita da nauyi.
Dama fitan nawa kamar fitan dole zanyi shi kin san alamarin dangin miji yadda yake rashin zuwa zai iya jawo min matsala.
Kallon ta nayi ta bani tausayi ga cikin ta ya girma kwarai a lokacin gashi tana matukar karfin hali sosai a lokacin.
Abincin na kawo mata ta zauna nan inda take zaune a kasa taci sai dai ba sosai ba don yanayin ta ba dadi gare ta.
Na tace mu fasa fita sai zuwa gobe idan ta dan kara jin sauki amma sai gashi ina idar da Sallah ta shigo inda muke tana ce min na zo mu tafi mu samu mu dawo in time.
Da sauri na mike tare da dan gyara fuskana na saka hijjab a jikina sai naga anty taja ta tsaya tana kallona wani irin.
Nima dai din kallonn ta nake don ban san wanan kallon da take min ba sai na ga tayi murmushi ta nufo ni tare da daukan gyalen rigan dake jikina tana mika min take cewa haba ko dai ni macen aure ai kinga shigan dake jikina ko.
Dole ba don naso ba na cire hijjab din na yafa gyalen kayan a kaina na fito kamar wata yar birni dani don ni kaina nasan na canza sosai.
Tana gaba ina biye da ita a bayan ta rike da hand bag din ta muna fitowa haraban gidan ne mukai kicibis da maigidan wanda da alama dawowan shi ke nan daga wani guri

Download complete TXT · Novel page