Murucin Kan Dutse
Chapter 36 of 146
a hankali.
Haka yasa na dan kai kwance daga inda nake zaune har barci ya dauke ni a haka ban sani ba sai muryan anty naji tana tambaya ko lafiya na kwanta lokacin la,asar.
Firgigit na falka ina salati sai dai jikina ya dauki zafi a lokacin haka na mike naje nai sallah da karfin hali nazo gurin hada abin buda baki ranan adadafe na taimakawa Gajiye muka hada komai nakoma daki na dunkule saman gado sanyi nake ji a lokacin sosai.
Nasir ne yaje yake fadawa maman su wai banda lafiya sai gata a rude tana shigowa ta tsugun na gabana tana cewa Rama baki da lafiya inji danki.
Nace kaina ke ciwo anty ta dora hannun ta a kaina jikina radau yake a lokacin .
A hankali na runtse idona don sanyin hannun ta da naji a jikina huci na fitar daga bakina ina mika ta mike da sauri tana fadin baki da lafiya shine koka kumshe a daki haka.
Maza ki tashi muje asibiti cikin karfin hali nake ce mata bari dai nasha magani basai mun tafi asibiti ba anty.
Kin faye gardama wallahi sai ta fice daga dakin zuwa wani lokaci sai muryan daddy naji a dakin yana cewa .
Ke Rahama mike muje asibiti dama tun dazun nai tunanen a dubaki ke ma tun a asibitin.
Karasowa yayi bakin gadon tare da dan kai hannun shi saman wuya na a hankali.
Wani irin yanayi naji a lokacin tundags kaina hae yatsan kafana sai da naji yar ajikina gaba daya.
Na rutse idanuwa na sai ga hawaye na zubo min a hankali a idanuwa yace ku fito da ita mutafi ina waje ina jiran ku.
Da tai makon gajiye na fito dakin jiki sai kaduwa yake kamar ana shocking dina a lokacin.
Tare dashi da anty muka tafi asibitin nan muka karbi kati aka shiga dani ganin likita nan ya rubuta min allurai da maganunuwa da zan sha.
Bayan an gama muka juyo zuwa gida a hanya daddy ya tsaya wani shago ya sayo muna kayan sanyi da nama gassasa mai zafi sosai na mikawa anty yace kila bazata iya cin abinci ba sai ki bata wanan taci.
Tunda muka dawo gida na kwanta ban fito ba koda asuba tea din da gajiye ta hada min ban wani sha sosai ba .
Washegari ba laifi na samu zazzabin ya dan sauka min yanzu na dan samu sauki na dawo falo na zauna da sauran mutane.
Anty ce tafito daga daki ta samay ni zaune a gurin tace kin falka Rama yaya jikin yanzu daddy yazo ai har sau biyu kina barci ya tafi asibiti don ance jikin hanifa ba dadi tun daren jiya basuyi barci da dadi ba da ita.
Farida tace da suwa suka kwana acan anty tace uwar ta da mahaifiyarta sai mama Laraba.
Kai shine bata barsu su kwana da yarinyar ba Anty Zulfau bata da kirki wallahi sai lokacin nai magana nace ba rashin kirki bane tana son yarta ne shiyasa.
Dubi yadda taci wa Rahama mutunci ranan sai gashi jiya ta taimaki yarta ni wallahi naga karfin halinki Rahama da kika fada cikin ruwan nan haka na ni may zai kaini.
Nace nima wallahi ban san lokacin dana fada ba Farida yadda naga yarinyar a ciki kamar matatta hankalina ya daga sosai wallahi.
Har da ciwo naji saida nazo wanka nagani ban ma san naji ba wallahi.
Anty tace ai shine daddy ku ke magana tun a asibiti yake cewa bai masan irin godiyan da zai maki ba wallahi.
Wayan anty ne yai kara ta dauka daddy ne a layi muryan shi bai fita yake cewa da ita yana ganin hanifa ta rasu fa.
Da karfi anty tace hanifa ta rasu besty ?
Lokaci daya duk muka mike tsaye muna fadin innalillahi wa, inna alaihin raji,u.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE , , ,
IDAN KON BIYA KIKA TUWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YANA KANKI YAR UWA
28
Hankali a tashe gaba dayan mu muka mike sai muka nufi hanyar waje cikin tashin hankali.
Babu kowa a haraban gidan a lokacin sai mai gadi dake kokarin kunna redion shi na hannu.
Anty ke cewa maigadi ba a shigo da gawan yarinyar bane gida ko kuwa yace hajiya shin wani gawa badai Allah yaiwa yarinya rasuwa ba.
Take cewa yanzu maigida ya bugo waya yake fada min abinda ya faru akan yarinyar.
Cikin karfin hali nace anty bari kawai muje asibitin mu samay su a can asibitin gaba daya .
Asibitin na kudi ne mai tsari daki ne harda kayan kallo da naura sanyi akwai a dakin mun samay su jugun jugun a tsaye daga kofan dakin hankalin su a tashe a lokacin.
Daga inda muke tsaye muna kallon likita na kokarin ceto rayuwan yarinyar a lokacin.
Hawaye ne yake sauka a idanuwana a hankali na dafe bakina da hannu kada sautin kuka na ya fito a lokacin.
Na dafa kaina a bango yadda nake kuka shi ya kara tayar wa mutanen dake gurin da hankali sai cewa suke haba Rahama ku daina kuka haka mana.
Daddy dake fitowa daga dakin tare da likita ya dago kai ya dan kalli gurin da nake manne da bango ina kuka cikin tashin hankali.
Tambayan daddy da likita da suka fito daga dakin su mama ke tambaya da cewa ta tafi ko .
Daddy ne ya juyo inda suke yake cewa sai hakkuri mama , Allah ya karbi abinshi ko.
Nan gaba daya a lokaci guda guri ya rude da ihu shi kanshi daddy gani daya zakai mai ka fahinci karfin hali yakeyi kawai alokacin.
Gaba daya muka kwaso muka nufi gida kowa hankalin shi a tashe gidan mahaifan daddy aka wuce da kayan yarinyar a can akai mata sutura aka kaita makwancin ta Allah ya karbi bakunci musulmi Allah ya gafartawa hanifa.
Gidan ya koma shiru baka jin motsin komai sai dan hayaniya jefi jefi daga sauran bangaren gida ita ko Zulfa abin yaso ya mayar da ita kamar wata zautata don mutuwan ya bugeta sosai a zuciyar ta .
Ba uwarta ba ko mu da muka dan saba da ita rashin ta yai muna zafi balle uwarta mahaifiyar ta ita ke nan mata a duniya ana neman haihuwan ido rufe don sun saka lamarin haihuwa a cikin kishin su.
Bamu shiga gurin ta ba sai da dare lokacin mutane sun rage yawa a part din nata ni da gajiye da farida da Amira da Nasir muka shiga part din mata wani tsami ne ya daki hancin mu kace kamar ba dakin yar kwalisa bace irin Zulfa ashe namane ya rube a fridge yake wanan warin haka.
Da sallama muka shiga dakin tana zaune da mahaifiyarta da mama laraba a dakin ta ga kaya a saman gadon an tara ko ina kwamatse a part din kamar dakin tsohuwa .
Sallama muka fara yi sai muka fara gaida su muna masu yaya hakkuri Allah yasa ta huta.
Mama Laraba tace Amira Amira Allah sarki kaunar ki abokiyar wasan ki yau Allah ya karbi abin shi .
Shiru mukayi kowa da yadda yake jin zafi a ranshi sai Zulfa ne da tun ahigowan mu ta fara kuka sosai nasan ganin yaran da tayi ne na anty ya tayar mata da mikin rashin diyar ta datayi.
Mun dan dauki lokaci zaune a falon munyi shiru nice nafara mikewa tsaye sai sauran suka mike mama ke cewa sannun ku da kokari kunje.
Rahma Allah baiyi hanifa rayayya bace dan ba don ke ba ma ai da bata kara kwana ba kila don zuwan ki ne kika shige ciki aka dauko ta .
Mama Zulai tace da ace tazo da wuri kila da bata sha ruwa hakana ba sosai.
Nace wallahi muma muna cikin barci ne a cikin barci ne muka dinga jin ihu jin mu ke nan muka fito a lokacin ta dade ina gani a ruwan.
Sai Zulfa dake kuka take cewa ai na dauka maigadi zai iya fitar da ita don nace a fada maku Hindatu tace wai a, a a bari mai gadi ya gwada a gani ko zai iya fitar da ita lokacin.
Nan uwar ta ta hau fada tana cewa da ita ai idan baki daina bin wanan hindatun ba sai ta kaiki ta baro sosai.
Farida tace ni haushi ma tabani data kama kirawa yarinya mutuwa tun bata mutu ba nan dai Farida ta basu labarin komai kaf ai kamar an tunzura Zulfa da Uwarta mama Zulai ne a lokacin.
Mu dai muka fice muka barsu nan suna ta maida magana kuwa bayan yaki don mai faruwa ya riga da ya faru ko a lokacin.
Haka na farko azumin yazo gidan ba dadin rai rasuwan yarinyar ya hana uban komawa Abuja gurin aikin shi a lokaci sai dai yakan je ya dawo amma ba ya irin dade bai gida din nan ba.
An sa an kwashe ruwan tank din da Hanifa ta fada ciki an kara mai tsayi sama sosai ko babba sai yayi da gaske zai iya ganin iyakar shi amma akwai kan fanfo daga kasa inda ruwa ke fita.
Mutuwar yarinyan yadan rage yawan fitina a gidan don yanzu ba wani hadin kai na gulma da suka saba hadewa ayi don a kullawa anty sheri da mu ma damuke a karkashin ta a gidan.
Da alama Zulfa ta ja baya da hindatu sun samu matsala a tsakanin su a gida don yanzu ko azumine basu yawan zama guri daya da junan su kowa harkan gaban ta takeyi a lokacin.
Ranan da maigidan ya kirasu kan abin kayan sallah da za, a saya a gidan nan rikci ya kaure a tsakanin su.
Ko wacce na fadin irin abinda za, a sayawa yara a lokacin, Zulfa na daga gefe daya tana sauraren su abinda suke fadi.
Har aka kawo kan zancen kayan sallah yaran gidan nan Hindatu ta zake itace mai bayanin abinda za, a dinkawa yara na sallah.
Idan kaji yadda take bayani kasan da gaiyya take magana adole sune masu yaya a gidan yanzu don haka magana ya zama nasu bada Zulfa ba da bata da ko dunge a gidan.
Sai da ta gama bayanin ta kaf Anty Saade da maigidan suna sauraren ta can anty ta nisa tana cewa ni dai hakan bai min ba ni da Yaran zamu shiga boutiqu mu diba abindaya dace har yan matan dake gurina.
But sukaga Zulfa ta mike ta fice daga falon inda suke zaune tana sharare hawayen a fuskanta.
Tausayin ta ya kama daddy da Anty shine ya mike yabi bayan ta yana bata hakkuri akan tayi tawakkali tabarwa Allah.
Anty ma da yamma ta shiga part din na Zulfa ta samay ta a har lokacin a ya mutse ta zauna taci kuka har tagaji.
Jin shigowan Anty Saade dakin yasa ta dago kanta daga inda take zaune a kasa duk ta kode da ita take cewa wa, alaikis salam.
Ansha ruwa lafiya maman Hanifa sai kawai ta fashe da kuka jin an kirata da maman hanifa don anty ce kawai mai kiranta da wanan sunnan.
Don ita Anty duk kan su da sinan diyan su take kiran su dashi sabanin su dake kiranta da sa,ade kai tsaye haka.
Guri anty ta samu ta zauna a kusa da ita tashiga bata magana tana bata hakkuri tace da anty nagode maman Nasir.
Yaune rana na farko da ta kirata da hakan anty tace ki dinga kai kukan gi Ubangiji don shi daya baki kuma ya karbeta a inda akeson ta yafi sanin hikiman yin haka dayayi.
Idan kin dage da addua dakai kukan ki garshi sai ya baki abinda ma baki zata ba daga garshi ki dage da yawaita karanta Innalillahi waina alaihin rajiu, Allahuma ajirni fi masibati wa, akalif, lil hairan min ha, , ,
Sai kiga Allah yai maki sakayya da mafi alherin sa amma wanan kukan dakike bashi ne mafita ba a gareki don zaki iya jawa kanki wani ciwo kuma again.
Bafa ke kadai ba mutuwan yarinyar nan ya shafa ba kowan mu yataba wallahi Rahma sai da na tashi tsaye sosai akanta take cin abu yanzu don ta saka abin a ranta sosai wallahi.
Zulfa tai murmushi tace dole ne maman Nasir don ba karamin shakuwa ne a tsakanin su ba ban kara gaskantawa ba saida naga yarinyar nan tai kundunbala kan Hanifa ta fada ruwan nan don ceto ranta amma kuma Allah bai bar muna ita ba wallahi.
Har taji sauki cikin dare saiga ciwo yataso kamar conbultion tana fisge fisge shine bai sake taba har ta tafi da shi.
Anty ta sauke ajiyan zuciya tace Allah yai mata rahama yasa ta huta tamike tanace kiyi hakkuri ki fitar da damuwa a ranki kibita da addua shine tafi bukata yanzu a garemu.
Tana fita Zulfa ta sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwan ta a hankali tace rayuwa ke nan koba komai dai yau Saade tai min rana don duk abinda ta fada min yanzu gaskiya ne.
Ita Hondatu ma na fahinci kamar dadi abin yai mata babu wani damuwa akan mutuwan yarinyar nan a kanta ji yadda take magana a falo don kawai ni da ban da kowa yanzu a gidan maji haushi.
Yanzu ai nasan zamana da ita a gidan nan dama can dai ai ba wai wani son tsakani da Allah muke wa juna mu ba don kawai mu hade kaine muci karfin Saade kwai yanzu ko tunda babu mutunci ta iya min haka ai kowa ya kama kan shi kuma.
Tun wanan ranan gaiyyan hadin kai a tsakanin su ya watse ba ruwan wata da wata agidan kowa tashi ta fitar dashi kawai sai zaman ma yafi dadi a haka don an rage yawan tsegumi da gulman anyi an ce.
********* *********
*********
Mun shirya kamar yadda anty ta bukaci na shirya na rakata unguwa ni da Farida sai yaran da muka fita dasu ranan Gajiye kawai muka bari a gida.
Wani katon shago takaimu kayane na redmaid na kasan waje nan muka zabawa yaran kaya masu kyau kala biyar biyar sai ni da Farida dake da kala hudu hudu nan itama ta zaba masu kyau da tsada nata takalma handbag da sauran kayayyaki haka muka dawo gida a gajiye .
Ban zauna ba tare muka karasa aikin girki da Gajiye sai baya mun idar da sallah mun sha ruwa aka baje kayan da aka sayo muna kallo.
Na kwashe na anty na kai mata dakin ta na samayta a kwance tace tagaji bata jin dadi don azumi ma ba kullun takeyi ba don yanayin jikin nata.
Nace bayan na gaida ita, ga kayan ki nan na shigo dasu tace Rama don ki fa na sayo su saboda ba zan iya saya maki su ba a gaban Farida .
Don bai yuyuwa na saya maku komai iri daya da ita tunda ba wai wani abu take muna ba banda hira da kwanciya.
Nace a sanyayye ma gode Anty Allah ya kara rufa asiri tace amin zaki iya ki barsu a nan sai idan ta tafi ki fitar da abinki.
Sallah saura kwana biyu mun samu hutu ta kwashe mu zuwa gyaran kai da jiki a saloon din da take zuwa gyara wanda ko ni daya yanzu tana turawa can.
Ba karamin gyara akai muna ba mun dawo muka samu an kawo muna dinkunan da ta bayar ai muna nan kan ta fitar da banbanci a fili don nawa sunfi na Farida sosai.
Take naga Faridan ta hade rai naji anty na fadin kai tella dai ho dinkin nan kusa wata uku fa a hannun shi sai yanzu ya hado da wanda na bashi na sallah yai maku.
Sai dataji haka ta dan sake ranta nace kai dan adam ho gashi ita ba, a more mata sai aukin hira da barci idan kuma za, a sha ruwa itace ta farko gurin fitowa aci abinci bata jin nauyi da kunyan hakan.
Ranan Sallah tun safe muke aikin girki a lokacin har Farida tai wanka ta shirya cikin daya daga cikin atamfan da aka dinka muna.
Ban samu kaina ba nida GaJiye sai zuwa shadaya saura na rana don anty ce mai girkin sallah din.
Wanka mukayi bayan mun kara tsabtace falo da dakunan gidan muna atamfa muka saka dogon riga ne wanda akaiwa dinkin manyan hannuwa mai dagwari biyu daga hip din rigan ya kamani sosai kasn shi ya wani bajewa sosai ina tafiya yana bajewa a kasa.
Kicibis mukayi da daddy dake shigowa part din wanda ina ganin dawowan su ke nan a gidan tun fitan su zuwa sallah.
Yana saye da manyan kaya a jikin shi farare kal dasu da hullan shi da ya dace da aikin da akaiwa kayan dake jikin shi.
Kayan sun matukar karban jikin shi sosai yadine mai matukar tsada sajen fuskanshi ya kwanta qa fuskan shi lun lub ya kara mai kyau da kwarjini sosai.
Gefe na dan rakube ina cewa sannu da dawowa daddy barka da sallah ?
Yace an sha ruwa lafiya Allah ya maimaita muna nan naji gajiye tana gaida shi kamar yadda na gaida shi.
Ya saka hannu a aljihun shi ya ciro bandir din yan dubu daya daya ya kirga ya fara mikawa Gajiye ya tana godiya ya kirgo ya miko min na rusunna nakarba ina godiya.
Saiga Farida itama tana gaida shi itama ya bata nata ta karba tana kallon hannuwana.
Ya shige dakin anty yajima sai gashi yafito yanayin shi ya sauya ga yadda ya shiga dakin don gajiye na mashi a huta lafiya bai amsa mata ba yafita da zafin rai.
Kusan hakan ne ke faruwa dasu yanzu ba kamar yadda suke ba a baya a tsakanin su da zai fito da fara,a.
Lokacin ina cirewa nasir fararen kayan dake jikin shi zaici abinci don nayi mai mutumin shi watau masa da miya yaji kayan hadi yayi laudi sosai.
Saida yaron ya fara cin abinci ina gyara mai zama naji anty na kwala min kira da sauri na mike zuwa amsa kiran nata.
Zaune take ta caba kwaliya