Murucin Kan Dutse

Chapter 35 of 146

gurin ki takoma baya tana ci miki mijin ku ta baya.
Haba mama wallahi haka ba halin Rahama bane ni wanan yarinyar banga abindata tsare masu ba a gidan nan haushinta kawai suke ji don zaman ta a guri ai ba Rahama ce kawai a gidan zaune da mu ba.
Ni may yasa ban taba damuwa da duk wani dake karkashin su ba sai sune zasu damu da yarinyar mutane .
Ai haka ma zakice tunda ta riga ta asirce ku a gidan tana yadda take so yarinya haka fikiu fikiu da ido kamar ita ta tsara kan ta har zaki jawo wa kan ku wahala da ita.
Mama wanan maganan da kuke yi fa yana kara tunzura ni ne wallahi mota dai ni naga dama na saya mata ban damu da duk wanin abinda wani mutun zai fada akan haka.
Zargin kuma da suke min na barsu da Allah shi zai saka min ni da wanan yarinyar.
Salati mama Zulai ta saka tana cewa yanzu akan shedaniyar yarinyar nan kake jawa matan ka Allah ya isa Alhaji ?
Yace ai cewa nayi idan sheri sukai min idan kuma ni neman ta nakeyi ai kinga a kaina abin zai dawo min ko ?
Haka dai suka zauna basu fahinci komai ba don sun rasa gane kan shi ga baki daya nan zulfa ta shiga surfa min zagi ni da anty tana ja muna bakar Allah ya isa karshe ficewa yayi ranshi na mashi kuna ranan dai haka akai buda baki rai ba dadi a gidan.
Yana zaune yayi buda baki a falon shi wanda ba wani abin buda baki aka shirya mai ba saka makon mai girkin na cikin fushi tana son jan ajin ta a matayin ta na mace gareshi.
A kasa yake zaune saman kafet din dake tsakiyan falon nashi goran ruwa da fruis din daya sayo a gefen shi.
Kan shi ya dafe da hannu daya saboda kan nashi ya dau zafi a lokacin ji yake kawai ya saki matan nashi ya huta da wanan tashin hankalin nasu dayaki ci yaki karewa garesu.
Wata zuciya daga ban gare zuciyar shi ke bashi shawara ya sallami Rahama kawai daga gidan ya huta da zargin dake damun matan shi akan ta.
Na yau daban nagobe daban duk akan yarinya daya abin ke faru idan kaji fitina akan wani dake gidan.
Bayan duk halatcin da yarinyan ke masu agidan akan diyan su zuwanta yasa ta yiwa diyan shi tarbiyan da iyayyen su suka kasa basu a baya sai bakin kishi da suka sa agaban su.
Yanzu yaro daya gan shi zai gaidashi suna karatu na addini komai tare da yaran takeyi bata daukan kan ta wai ta girmay wa yaran don kawai ta saka su a hanya madaidaiciya.
Yace a hankali shi kadai zaune a mamakeken falon shi Ya Allah ka agajeni kai min mafita akan wanan matsalan a gidana.
Idan nace kai tsaye Rahama ta barmin gida ban kyautawa Saade data dauko taba a gidan kuma tana taimaka mata nima nasan da hakan.
Matsala dai dayace rikicin su da matana ko yaushe wanda kuma idan an bibiya sune ko yaushe basu da gaskiya akan fitinan.
Fitinan da sukeyi ga Sa,ade yanzu ya koma gun yarinya mutane wanda ba komai ke kawo shi ba sai cin fuskan da suke kokarin yiwa wacce ta kawo ta gidan a gaban ta.
Wanda koma waye ba zai lamunci hakan ba a gaban shi don ba kowane keda hakkuri irin na ita sa,aden ba yanzu.
Kawai barin su zanyi suci haukan su ai dawowa zasuyi a hanya su fahinci gaskiya da kan su.
Haka dai ya kare zancen zuci da mika al, amarin shi ga ubangiji tun da shine ya kaddari zaman su haka a gidan.
Sallaman Saade da iyalin ta sunzo gaida shi da shan ruwa ya katse mai tunanen shi.
Kusan nice tafe a baya dauke da Jinior a hannuna nan muka zube kasan kafet muna mashi barka da shan ruwa daddy.
Ya amsa cikin dan sakin fuska yana cewa kun sha ruwa lafiya kowa yace lafiya lau daddy har dasu Amira da basuyi azumin ba cikin mu.
Ganin babu komai na shan ruwa a gaban shi yasa anty cewa yau baka samu abin buda baki ba ke nan an dau fushi dakai ?
Inajin haka namike inacewa yaran suzo mu tafi sai naji yace miko min jinior nan na dan taba shi na karasa inda yake na mika mai yaron ya karbe shi yana cewa dat is my boy.
Na durkusa nace daddy nagode Allah ya kara rufa asiri yace amin sai a dinga tuki a hankali don kin san garin akwai cunkoson motoci da yawa banda tukin ganganci don Allah.
Kuma ki mayar da hankalinki ga kararun ki don ki cin ma burin ki na zama likita dakike so ki taimakawa wasu kema nan gaba.
Na sake tausa muryana kasa nace nagode daddy yace ba matsala sai ki yi ta hakkuri da kowa agidan don a zauna lafiya insha Allahu nace muka fice daga falin nashi nan muka bar anty tare dashi.
Muna fita tace Allah dai ya kawo saukin wanan fitina haka mutane basu son azauna lafiya agida kullun da sabon fitinan da suke fitowa dashi idan gari yawaye.
Na kuma fahinci duk sheri da makirci yana gurin Zulfa da tana boye halinta amma zuwan yanzu tafitar a fili da halin ta sai wani hafin kan sheri da sukeyi a tsakanin su don ganin sun cutata min a gidan nan.
Yace hadin kan banza tunda ko kan su basu bari ba ina hadin kan yake anan ?
Besty nabaka shawara kaki dauka ne suluntion daya ne shine ka auri Rahama shike nan amma kaki nifa ni na san hikimar dake cikin ha, , ,
Don Allah Saade ki rabani da wanan shirmay naki naji da abindake agabana please ?
Kai ke ganin rashin dacewan haka amma ni nasan da zaka zauna kai naziri dakyau ka hango abindana hanga baza ka ki shawara na ba ai.
Nan dai ta mike tana mashi sai da safe ta fice daga part din yayin da yabi bayan ta da hararan jin haushin ta a lokacin.
Na yakai kan shi saman kujeran da ya jingina bayan shi tare da lumshe idanuwan shi yana tunanen wai ita sa,ade wata irin mace shin a duniya ?

********* ********* *********
Wanan satin haka azumin ya kasance muna agidan farkon shi babu dadin rai ga matan gidan da maigidan duka.
Sai ranan da anty ta karbi girki ne yasan ya samu taron watan azumi da biyan bukata don mun hada mai kayan buda baki kala kala an jera mai.
Ita kuma tayi kwaliya irin daya kamata na taron maigidan a gurin ta yadda ya kamata haka ya man ta da damuwan shi.
Koba komai Saadatun shi, na son farin cikin shi akoda yau she da itace suke da matsala bazata barshi haka kamar mara galihu ba a gidan shi.
Tana zaune a gefen shi inda ya zauna daga gefen ta yana saye da jallabiyan maza daya sauya daya shigo gidan daga gurin sallah asham.
Ya kalli irin kayan buda bakin da aka girka mashi inganttaciyar cima ne na zamani aka hada mai mai warawarw jinin dan adam don wanan watan mai alfarma.
A haka muka shigo gaida shi wanda duk yamma idan yana garin da watan azumi kowani part zasu shigo yi mashi barka da shan ruwa.
Namiji ke nan gashi da karamin shekaru amma Allah ya bashi wanan girman haka mata har uku mai a gida kowace tana ji da kanta kuma duk zaman shi sukeyi.
Zaune yake kamar kullun idan zai sha ruwa a kasa da alama ya gama buda baki koda muka shigo falon don yana dan kishingide ne yakara bayan shi ga kujera.
Ita kuma anty tana zaune daidai saitin kafan shi suna fuskan tar junan su taba kofan shigowa falon baya.
Yaran nasu ne agaba sai gajiye da Farida dake bin su kamar kullun nice a baya koda kuwa da anty zamu shigo gurin.
Daga can dan nesa kadan nida gajiye da Farida muka tsugunna muna gaida shi ina dauke da jiniyo a hannuna .
Idanuwan shi na akan mu lokacin da muka tsugunna muna mashi barka da shan ruwa ya amsa yana kokarin kawar da idanuwan shi garemu.
Anty ce ta juyo garemu tana cewa aa shi wanan ai na dauka ko yayi barci ne fa ?
Gajiye tace idon shi biyu yanzun dai suka gama kwasa da uwar dakin shi wai sai ta bar sallah ta dauke shi.
Miko min shi nan inji anty na nufo ta da yaron ta mika hannu ta dauke shi daga gurina tana fadin kaji ba dan gatan maman shi harta sauya ma kaya kuma kana mata rikici.
Gajiye ke fadin hajiya a rage kayan ne a shiga dasu ta juya tana kallon shi ya lumshe ido yana kada kafa dayan daya daga a hankali.
Tace dashi a kwashe kayan ne yace tare da bude idanuwan shi No abarshi in an jima zan dan kara ci ne.
Sai dai wanan abincin a tafi dashi nagama dashi ke nan yanzu tace wa gajiye a kwashe gajiye ku tafi dashi idan bazakuci ba a mikawa maigadi kada ya lalace a banza.
Rama kin ko ci abincin kuwa don ke idan kina ciwo bakya son cin komai, da sauri ya bude idanuwan shi yana kallon mu tare da tambaya may ya samay ta kuma ?
Tace dashi kanta ke ciwo tunda rana take kwance kasan ta da karfin hali haka ta tashi tai girkin nan da ciwon kan.
Ki dauko mata panadol a daki tasha ko zai bari ya bata amsa tace don Allah dan jirani Rama wanan mai zukan ya kama nono ko.
Shi da kan shi ya mike zuwa dakin shi sai gashi da magani a hannun shi ya miko min tace ga ruwa nan kisha don nasan ba sha zakiyi ba idan kin fita.
Ko haka kikeson zama likita kina gudun magani sai son yiwa wasu allura kikeyi ke.
Na bare maganin a gaban su ina hadewa Zulfa tashigo da yarta wani kallo ta watso min daga inda nake duke ina shan magani Hanifa tayo kaina ta rugumay ni tana cewa anty zan kwana a gurin ki kimin story.
Da wani karfi uwar ta jaye hannun yarinyar a gurina tana fadin mara zuciya kawai zonan na rabaki da irin tsiya bakya ji ke.
Wai ke zulfa may ye matsalarki ne yarinya baki bari tayi yadda take so ne wai may ye a cikin haka kuma tace ansha ruwa lafiya?
Tana rike da hannun yarta gam ajikin ta ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna.
A hasale ya karba mata na juya zan fita jinior dake shan nono ya saka kuka anty take cewa dawo dauki abinki kada ya damay ni.
Dole na juya na karbe shi muka fita ashe bayan fitana sunyi kaca kaca kan abinda zulfa din tayi a gidan.
Take cewa babu ruwan shi abarta da yarta ita ta haifi abinta tasan zafin abinta don haka ya kyaleta lumshe idon shi yayi yana mai jin kunan abinda suke mai a ranshi.
Ya kyaleta ne wanan lokacin don idan ya tsanan ta magana za, a ce akan Rahama ne yakawo fadan ga zargin da ke tsakanin shi da yarinyar.
Washe gari tun asuba na taya gajiye gyaran part din mu bamu kwanta ba sai da muka gyara komai muka wanke kayan abinci fariida kan bata saba da irin aiki haka ba ta koma ta kwanta kafin ai sallah.
Bayan mun yi sallah gari ya dan haska muma muka kwanta don mu rage lokaci muyi barci.
Barci sosai nakeyi hankalina a kwance can cikin barci nake jin ihu na tashin hankali a gidan da kyat na bude idanuwana dake da nauyin barci ihun a cikin gidan akeyin shi kuma ba mutun daya ba kamar ma harda namiji nake jin ihun.
Cikin matsanacin tsoro da firguci namike zaune farida ma dake gefe na tamike ai muka kwasa mukayi waje da gudun mu cikin firgici.
Nan mukaci karo da anty da tafito daga dakin ta sabale da danta suma barcin sukeyi a lokacin sukaji ihun suka fito.
Da gudu muka kwasa muka fita inda ake ihun mutanen gidan kaf suna waje gurin katon rizabuwan ruwan dake a gefen da mai wanki ke wanki da muma mukanyi sauran aiyuka a gurin wani lokaci can ta bayan dakin Hindatu.
Mun isa gurin ganin yadda suke ihu muna tambayan ko may ke faruwa sai nuna muna katon rizabuwan ruwan sukeyi suna kiran Hanifa hanifa ta fada cikin tankin ruwa.
Innalillahi nace shine kuke tsaye kuna kallon ta hindatu dake kusa da uwarta dake ta ihun neman taimako tace yaya kike son muyi mu yanzu ?
Lekawa nayi naga yarinyar tasha ruwa har ta taso sama da sauri na gyara na tsunduma ciki na dago yarinyar tare da dabara na mikota maigadi da shima ihun yakeyi kamar mace yana neman taimako ya cabe ta shida gajiye hakana fito a galabaice don na dade rabona da ruwa haka.
Babu alaman motsi ko kadan ga yarinyar nan uwar ta sai faman yanka kuwa tana fadin ta mutu tamutu ko na shiga uku na lalace shike nan hanifa shike nan na rasa yar guda daya da Allah yabani na shiga uku ku taimaka min kudawo min da farinciki na don Allah.
Sun kewaye ta sai faman kuka sukeyi ina fitowa nace don Allah ku daina kuka nan, ba kyau aiwa wanda ya fada ruwa saurin kuka haka please.
Gurin na nufa da sauri na duka na fara jaye mata ruwan ta hancin ta da ta bakin ta ina zubarwa ba motsi ko kadan gareta, sai cewa hindatu keyi aikubar wahala ta mutu kawai wanan bazata tashi ba ai.
Nan Zulfa ta zube kasa somama a kasa don kalamin hindatu ya kara firgita ta su kayi kan ta da ihu suna kiran sunan ta da karfi tare da firgici suke girgizata da karfi.
Dukawa nayi dakyau na kuma naja ruwan hancin da karfi tai wani irin tarawa ta bude ido sai kuma ta rufe nace Farida dauko min key din motana da sauri please bata dauki lokaci ba sai gata dashi muka kwasa ni da Farida da mai aikin uwarta dake rugumay da ita sai gajiye sai asibiti.
A guje muka shiga asibitin muna zuwa aka karbi yarinyar suka wuce da ita emargyncy da sauri.
Babu mai waya a cikin mu balle a kira mu sai da Zulfa ta farfado ne maigadi ke fada masu aina wuce da yarinyar asibiti.
Nan anty takira uba su lokacin yana gonan shi yana kallon dawa kan shi a can yaga kiran ta nan take fada mai yadawo gida ba lafiya fa take tai mai bayanin abinda ke faruwa agidan nasa.
Cikin razana yake tambayan yarinyar ta mutu ko, take Rahama ta wuce da it's asibiti dai, wani asibiti suka kai yarinyar tace mun dai fice da ita a hannu.
Mun kai awa daya da rabi sai gasu daddy da anty dasu mama laraba sun samay mu.
A gigice yake tambayan mu ta mutu ko na girgiza kai a hankali nace bata mutu ba suna ciki da ita dai tun dazun.
A lokacin likitan ya bude kofa yafito nan ya shiga mai bayani bayani sun gaisa da daddy yake tambayan shi yace ai an auna arziki an rage mata ruwan tun gida shine saukin ta gaskiya an ceci rayuwan ta da kafin Azo nan ruwan zai iya Mata I,lla ya kasheta, amma yanzu da sauki sosai gaskiya sai dai za, a bata gado don ta jirgita da yawa mu gani har wani lokaci.
Bayan an bada gado muka zauna a tare da ita dagani sai rigar barci dake a jikina lokacin nake zaune saboda yadda muka fito gidan a firgice damu.
Daddy ya shigo dakin da ledan magani a hannun shi kallo daya yaima inda nake zaune ya kawar da kan shi gefe yake tambayan tana numfashi kuwa ?
Tanayi daddy naba shi amsa a takaice batare da na dago kana ba hannu na yana rike dana yarinyar ina murzawa a hankali, sai ga gayyan mutanen gidan mu, Zulfa na gaba hankali a tashe ina ganin ta na mike a kujeran da nake zaune akai don in bata guri don nasan tana iya cewa may yakawo ni gurin yarta.
Mama Laraba dake tsaye gefe tun shigowan su sun tsura muna ido suna kallon abinda nakewa yarinyar tace ina zauna Rahama ake jaruma ce kinyi kokari wallahi koke ya kamata kiga likita yadda ake fadin kin yi din gurin ceto yarinyar.
Zulfa ta zauna a bikin gado tana cewa dani sannu Rahama nagode nagode kinji nan kowa ya shiga fadin albarkacin bakin shi akai.
Ni dai na mike nafice daga dakin na samu su Farida nake ce wa dasu muje gida na canza kayan jikinan nawa please.
A haraban asibitin muka hade da daddy naji kunyan yarda nake a yamutse dagani sai yar rigan barcin dake jikina sai rigan da aka cirewa hanifa ne ma na dora akaina madadin dan kwali ko hulla.
Yake cewa cikin son ji yaya akayi kuma Farida ce tai katfin halin bashi amsa tace zamu je gida ne ta cire kayan jikin ta yace yafi.
Muka fice daga haraban asibitin mun fara tafiya na sauke ajiyan zuciya a hankali farida tace ke Rahama ashe kin iya ruwa ne haka.
Murmushi nai mata nace kin manta ni yar kauye ce Farida sai dai na manta yaushe rabona da ruwa wallahi.
Ai kinyi kokari ji yadda anty zulfa ta gigice tana sambatu da mutuwa tayi killa ita ma mutuwan zatayi.
Nace bari maganan Farida insha Allahu zata tashi da yardan ubangiji ban son yarinyar nan ta mutu wallahi.
Sai da nake wankan ne naga inda naji ciwo a jikina duk firgici bai bari na sani ba sai yanzu da hankalina yadan kwanta.
Nafito na shirya cikin wani wando da riga falo na koma na zauna nan yaran suka rufe ni da tambaya dana shiga ruwa yaya nayi tun ina basu amsa inajin kaina yana dan sara min

Download complete TXT · Novel page