Murucin Kan Dutse

Chapter 38 of 146

za, a gani ace wai matar shi ce.
A lokacin sai nake dauka don tana yar uwarsu ce take jin haushin abin da ake mashi ashe ita abin ba haka yake ba a gurin ta.
Nafito na shiga da yaran na kara yi masu wanka bamu fito ba sai dana gyara su tsab muka fito na samu ita anty bata ma shirya ba tana kwance da taimakona ta samu ta shirya ina shirya jinior take cewa daddy yace shi zai kai mu ai.
Ban ji dadin haka ba naso mu fita da ita kawai don mu dan yi yawo saboda mu ga gari da bukin sallah da akeyi.
Na fito da kayan dana hada tana gani tace ikon Allah Rahama ashe yau zaki saka Abba cikin farin ciki dama yana min korafin nabar kawo mai abinda nake mashi a da can baya.
Muna fitowa dauke da basket biyu ni na dauki dayan Gajiye ta dauko dayan yana cikin mota mu yake jira ya bude buth din motan na saka kayan a ciki.
Na koma na karbo jinior dake hannun anty suna fitowa kamar kullun motar shi bakajin komai sai sautin tashin kira, a a cikin sa ta tsaya ta rufe kofan shiga part din mu ta miko min keys din na kada a handbag dina.
Tana gaba nida gajiye da yaran muna baya nan muka gaida shi ya amsa muna kamar dole.
Yaja mota muka fara tafiya suna hira shi da matar shi nima a baya yaran sun matsa min sai da nai magana dasu har nabiye masu muna hira muma da gajiye.
Uguwar su anty tsohon gari ne don gidajen dake unguwar zaka fahinci haka dagani suma gidan nasu daga baya akai mai kwaskwarima na zamani .
Sai gidan ya haska uguwar sosai dashi da wasu gidaje daga cikin unguwar.
Nan dai muka fito muka shiga ciki a falo muka samu Abban yana tare da wasu dattawa a zaune yan uwan shi.
Muka zube kasa har daddy muna gaida shi yake cewa Alhaji Yusuf ka dawo ne kuma Allah dai yai maka albarka kin gane shi nan idan har yana garin nan sai yazo ya gaidani wallahi jiya nan yake da yaran nan sun zo gaidani da sallah.
Yafi min sauran mazan yan uwan ki sau dubu wallahi shiyasa nake jin shi kamar ni na haifi abina Saade don yanzu ma kusan ya karbe maki nine ai .
Tace kai haba Abba akwai wanda ya isa ya karbe min kai kuwa yace to tsaya kiyi wasa nan dai yaja yan jikokin shi yana wasa dasu wasan jika da kaka.
Nan yake fada masu cewa kwana biyu ba, a karasa azumi dashi ba ai don jikin nashi ya motsa mai.
Anty tace dashi ai Abba nima haka nake tun jiya wallahi tafiyan nan ma dai na karfin hali nayi don nasan yanzu ne ake samun ka a gida.
Daddy yace amma Abba da ka daure idan zamu fita atafi dakai kaga likita kaima a can yace kai haba wani likita zan je gani har waje Allah dai ya yayye kawai za, ace yanzu.
Rama baki ba Abba tsara ban ki ba mana sai lokacin na dan motsa shima Abban ya kallo inda yaji an ambaci sunana yace au itace yarinyar da kuke rikicin akan ta ke nan ko ?
Rikici kuma nace a raina sai kuma nake cewa killa zan cen fitinan su hindatu ne a kaina yakawo ga kunnen Abba din.
Abba itace fa kagan ta nan amma shine wai yake daukan magana a shirmay nakeyi yin shi daddy ne yace damu ku dan bamu guri Gajiye mu gana da Abba haka yasa nafi kowa saurin mikewa na bar gurin muka shiga daga ciki don dama nasan gidan muna zuwa da anty wani lokaci.
Dakin wacce nake ganin ita ce uwar gida a gidan muka fara shiga muka gaida ita sai dayan dakin don su biyu ne a gidan.
Kamar sauran gidaje su ma da alama ba wani zaman hadin kai kamar sauran gidajen da ake tsara akidar kishi a ciki.
Muna barin gurin daddy yace ban san abinda ke damun saade ba ta matsa min akan maganan yarinyar nan har tana kokarin ganin mun samu sabani a tsakanin mu.
Murmushin manya Abba yayi tare da jawo basket din abincin da mu kazo dashi a gaban shi yana dan budewa.
Yace in ban da abinka Alhaji Yusuf yo tunda kaji har mace ta bude baki da kanta tace ka aura mata kishiya ai tana da hujjan yin hakan.
Ai sai ka bari mu saurari hujjan ta muji yanzu ko anty ta nisa tace hujja na akan haka daddy ba wani dalili bane sai ganin da nayi rayuwan yarinyar ya cancan ci hakan a gare mu.
Kamar yaya Saade inji Abban ya tambaye ta sai hawaye ya fara zubo mata a idon ta a hankali tace dashi.
Abba idan kai la, akari da yadda yanayi yake yau ciwo gobe lafiya yarana suna bukatan taimako suna bukatan kasancewa tare da mai son su tsakani da Allah.
Shi kan shi ai yana bukatan kwanciyan hankali tare dashi wanda kwata kwata tunda na fara ciwon nan babu shi a tare dashi.
Amma idan ya auri Rahama ko bayan bani ina da yakinin yarana dashi suna da mai rike min su a tsakani da Allah kuma ai Abba wanan abin da nake son yayi kamar taimakon kan mu da kan mu ne za, a yi shi.
Ni dai take jiyewa nikuma wallahi harga Allah na yafe ma ya auri yarinyar nan ta zauna damu babu komai a raina na burbushin kishin ta a tare dani sai kuka ya kubce mata a take a gurin .
A, a a haba Saade may yakawo kuka kuma ana magana na fahinta anan magana zaki tsaya ayi a fahinci juna ko ?
Abba ya kasa fahintar manufata akan yin wanan shawaran danayi ni kuma ina jiyewa makomar bayana ne a gidan.
Haba Saade ai ciwo bashine mutuwa ba ga yadda wa yancan likitocin naku masu jajjayen kunnuwa sukace a baya wa ya dauka zaki kai wanan lokacin.
Bagashi Allah da hikimar shi ba har da rabon haihuwa kin samu a hakan kuma aikwai may yine bayan Allah.
Ki kwantar da hankalinki kiyi nazarin abin da kike kokarin shiryawa kada daga baya kuma kizo abin ya damay ki .
Aure ne fa shi sha, ani na aure ana son kwanciyan hankali da natsuwa a cikin sa kada kuma ayi garaje abu yazo ya koma maki ciki daga baya.
Abba na riga nai nazari sosai akan halaiyar yarinyar babu wani matsalan da za, a samu a ciki da yardan ubangiji.
To maji ita yarinyar tasan da wanan magana ne a yanzu haka ga abin da kike shirin yi a kan ta ?
Tace cikin girgiza kan ta bata sani ba Abba don ina son ne shi mu daidaita dashi kafin na tun kare ta da zancen tukun.
Don insha Allahu Rahma mai kaunata ce bazata ki abin da nake so da ita ba tunda taimako na zatayi ga hakan.
Murmushi Abban ya dan karayi yace kai Saade ban taba ganin mace maitaushi kamar ki ba don taushin ki har yafi na mahaifiyar ki baki rageta da komai ba a duniyan nan.
Yanzu kai Alhaji Yusuf kaji hujjan ta dabara ta rage naka tun da ita ke bukatan yin hakan gareta.
Daddy ya numfasa da karfi yace Abba kaji abinda take fadi wai hujjata ke nan a koda yaushe.
Ita burin ta ke nan shiyasa take kokarin hasasa muna rashin zaman lafiya akan wanan magana da ta a ranta don nata manufan kawai.
Tace eh shine burina don ni abinda zai fishe mu nan gaba nakewa bawai son zuciya ba.
Hakan ne naga yafi dacewa ayi don samun mafita a rayuwan mu shiya kaji na matsa da maganan.
Abba yace wanan shine abin da ake fadi idan kana son kama uwa to kaso dan ta da zuciya daya shine nan.
Ita wanan yarinyar na lura ta yi amfani da imanin ki ne gurin gwadawa diyan ki son da take masu da zuciya daya amma baki ganin idan ta shiga ta samu nata watarana zata iya watsar da naki yaran ta kama nata.
Daddy yace hakane Abba ba wani abu takewa wanan ba nikuma ban dauke shi a hujjju da zata sani abin da ban da niyya ba akan shi.
Yanzun dai da ita da kai kuje ku kara sasanta kan ku a kan zancen amma ni Alhaji yusuf ai naga wanan kamar kai aka taimakawa.
Don hujjan Saade gaskiya abin dubawa ne kaje kai nazari zanji daga gareka yadda kuka kaya daga baya.
Allah ya tabbatar da Alherin sa Allah kuma yau maku albarka yasa wa zuria albarka dayyaba.
Suka karba da amin Abba daddy yace amma ni Abba naso ne ai mata magana ta fita wanan zancen don Allah kada mu samu matsala akan shi nan gaba.
Abba ya daga mai hannu yace na fahinci manufar hikiman saadatu ga hakan kaje kai nazarin maganan ta da basira ko zaka fahinci manufarta anan.
Sukai sallama ta mike tashiga gida gaida gaida mutanen gidan kamar kullun babu wani kyakyawan taro da ta samu garesu sun dai gaisa da ita kadaran kada ham tai masu barka da sallah tare da fatan Allah ya maimaita muna takawo kudi ta basu barka da sallah sukakarba da godiya babu addua a kai mata kin shi sai su don kishi harda matatta.
Muna dakin sister din ta murja don school din mu daya da ita muna dan mutnci a school da ita.
Haka yas in nazo gidan sai nanemay ta mun gaisa da ita duk saurin damukeyi.
Su ma yan uwanta tai masu alheri muka fito bayan daddy ya bugo mata waya yana waje a lokacin.
Tun shigowan aanty gurin mu na fahinci tayi kuka sai naji ba dadi a raina don kusan haka take yanzu kawai sI naji ba daddy a raina.
Wani irin hattenes din daddy naji ya tsirgu min a zuciya na ban san rikicin da ke hada su da anty ba yanzu yake yawan bata mata rai haka ko wani lokaci.
Hakan ya haifar min da kuncin zuciya a lokaci daya wanda ya sa naji sam bani ma kaunan ganin shi a lokacin.
Don idan abin sa naki ji ni a yanzu shine a taba anty da yaran take mutum zaiga bacin raina lokaci guda.
Tunda muka shiga motan har muka kai gida babu wanda yai magana a cikin mu ana tayawa ni na fara fita ban tsaya jiran kowa ba na wuce ciki fuuu dani ina jin Amira na kirana amm ban tsaya ba na shige dauke da jinior a hannu na.
Ina daki naji shigowan su suma na fara kokarin cire kwaliyan dake jikinana sarka da awarwaro hannu na sai dai ban cire tufafin ba .
Nan sauran yaran suka samay ni muka baje dasu kilishin da Abba ya bamu ne suke ci don duk mukaje gidan sau ya bamu kumshin kolishi mai yawa mu zo gida dashi.
Gajiye ta shigo dakin tana cewa wai may kuma ya samay ki ne Rahama naga tun a gidan su hajiya yanayin ki ya sake lokaci daya.
Babu komai gajiye haka kawai najini ahakakilagajiyan aikin danayi ne ya ja min jin hakan.
Gajiyan aiki kan nasakihaka akwai dai koma may ye kiyiwa kanki fada ki daina saka damuwa a ranki don Allah, kin yi karama da tunane balle ma ban ga abinda akai maki ba da zaki saka damuwa a ranki.
Nace gajiye bana son ganin bacin ran anty na ko kadan wallahi baki lura da yanayin anty na ba da tashigo cikin gidan su kiduba irin yadda matan gidan ma suka karbe ta kamar ba yar gidan ba gajiye ai wanan dole mutum ya kamu da ciwo.
Zama tayi kusa da ni tare da kura min ido tace a hankali kamar may rada tace Rahama ki rufawa kan ki asiri kada ki jefa rayuwan ki ga matsalan da bai shafe ki ba don kin ga wanan mtsalace da ta shafi rayuwan auren su da gidan ba abinda ya shafe ki bane.
Lalai Rahama ke yarinya ce karama har yanzu baki san mayye duniya ba amma ina ke ina saka damuwan wani a ranki har ya damay ki haka.
Yau na tabtar da cewa yadda hajiya take kaunan ki haka ne kema kike kaunan ta da zuciya daya a ran ki.
Altine ta fada min dama irin kaunan da kukewa junan ku a baya ban tabatar da hakan ba sai zuwana gidan nan na fahinci cewa abinda ma altine ta fada min a kan ku yafi karfin hakan.
Don haka dai don Allah kibi a sannun kada yazo ya zama maki matsala daga baya.
Ina sauraren ta har ta kai karshen maganan ta na saukar da ajiyan zuciya a hankali nace nagode Gajiye tace dole ne na fada maki gaskiya don ke tawa ce Rahama.
Mikewa nayi zuwa dakin anty na samay ta ta idar da sallah tana zaune ishishire da kafafuwan ta tana dan murzan su a hankali.
Ina shiga nake cewa antu kafan ne ke tauna kuma take cewa wallahi yanzu nake son kiran ki dama ki dan shafa min magani ga kafan.
Maganin na dauko nafara murza mata kafanta a hankali tana dan lumshe idanuwan ta da alaman tana jin dadin yadda nake mata din.
Maigidan ne ya shigo ya samay mu a hakan yake cewa tun bai karaso ba kafan ne kuma ya fara tauna take cewa shine nace Rama ta tausa min tun bai damay ni ba.
Kamata dai yayi nai muna bukin wani sati mu fita zuwa ganin likita tun bai matsa maki ba shiyasa ban so kiyi azumin nan ba wallahi ke kina ganin kamar kin samu lafiya ne amma kika dage sai kinyi din.
Yai dan tsaki tare da dan dukawa daidai saitin kafan nata shi ma yana cewa gaba daya ne yake tauna ko iya nan ne kawai.
Ganin ya tsugun na gaf da mu yasa ni dan mikewa da nufin barin gurin sai yake cewa No zauna abinki zan fitane may kuke so a sayo maku ne zan dan fita .
Tace Rama akwai abinda muke bukata ne a nan ko nace sheltox ne kawai nake ganin ya kare muna tace sai may kuma nake cewa inaga madaran daya rage zai kai kwana uku kila.
Tace amma ki tuna kada kuma daga baya aza a tuna ya mike yana ce ta barshi dai zan fita kawai na sayo komai.
Ya mike tare da fice tace dashi sai kadawo ke nan baza mu rufe part ba sai ka dawo din yace yayi kyai.
Yana fita ina abinda nake ban bari ashe ta kura min ido ni ban sani ba sai naji tana cewa dani Rama may kuma daddy yai maki kike sha mai toka ne haka wai ?
Gabana ne ya fadi don ban yi zaton zata fahince ni ba zancen Gajiye ne ya fado min a rai da take cewa kada na shiga maganan miji da mata don ban san abinda ya hada su ba ai.
Nake cewa anty may kika gani ne halan tace barshi kawai amma naga daddy bai canci hakan ba ne na kara bata raina nace amma anty may kike mai da koyaushe yanzu yake yawan ganin laifinki haka bayan irin kokarin kyautata mashin da kikeyi ko yaushe a gidan nan.
Kai Rama dama nasan maganan ke nan don kinga nai kuka dazun komay ?
Magana ce kawai mukeyi dashi shine haushi ya kamani har nayi kukan amma ba wani abu bane da kike zargi.
Rama wai yaya zakiyi randa akace babu antyn nan taki ne wai a duniyan nan gabana nane naji ya wani mugun faduwa ras ras mai makon nai magana sai kawai hawaye shar yazo min mikewa nayi zuwa dakin mu can na kafa kai ga filo ina ta rusan kuka sai danayi mai isata nan na dunkule har barci ya dauke ni a gurin.
Gajiye ne ta rufe part a ranan bayan daddy ya dawo ya kawo muna sayyayan da yayo muna ko wani part ya kai masu nasu kayan bukatan .



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANI HAKKIN AMANA YA NA KAN KI DON ALLAH NA GANIN KI YAR UWA, , , , , , , , , ,

30
Wasa wasa jikin Anty yaki dadi kwanakin nan haka yasa na mayar da hankalina gurin jinyan ta a lokacin.
Mun godewa Allah bai wani tashi mata sosai irin da yake matukar kaita kwance ba sosai.
Haka yasa koda yaushe daddy yana , makale da ita koda yaje abuja ne zai dawo bayan kwana biyu sai shirin fita sukeyi waje.
Ranan da yai wani dawo ne yake sheda mata ranan jumma,a zasu wuce don haka ki shirya.
Nan aka shiga shirin tafiya wanda akasari nice akewa sayayyan abinda za, a bar muna na amfanin mu a gidan.
Komai da zamu bukata ba sai mun takura ba an saya muna a gidan an zube muna shi.
Ana gobe zasu tafi ina manne da anty ban son abinda zai daga ni kusa da ita ko kadan.
Take cewa taso ta yaye jinior amma daddy yace da saura nace anty aida kin yayye shi kibar min shi zan ji kewan shi sosai idan kun tafi.
Take cewa ai da zata barshi ne sai dai ta dauko mama Altine tazo ta zauna damu a gida kada ya bata min tsarin karatuna.
Tun da asuba sun shirya tafiya, idon mu biyu har yaran take cewa dani tare da miko min kudi masu yawa karbi wanan ki aje don bukata idan ya taso maku bana nan.
Nace da ita anty wani bukata zamuyi da kudi bayan komai kun tanadar muna a gidan akwai shi tace karbi dai ku aje indan an kwana biyu ki dinga kai yaran yawo kuna sayen abinda suke bukata kada ki bari su shige kewan komai nace insha Allahu anty.
Muka fito da kayan su waye nan tace damu zata ta sallami sauran

Download complete TXT · Novel page