Murucin Kan Dutse

Chapter 40 of 146

ya kamata take cewa to may ye kuma don taba dan uwan ka layin wayan ta shiba na miji bane ?
Yai mata wani irin kallo yace eh lalai kuwa namiji ne kuwa tace to kagani yashigo layin da maza ke nuna bajintan su ne shima ayi dashi.
Yace ai sai suyi din amma dai kin san ko waye Ibrahim tun farko da kike wanan magana balle yanzu da yazo turai idon shi ya kara budewa haka .
Tace ni yanzu may kake son nace a nan tunda yana son ya gwada saan shi ne a kan ta kuma.
Yace baki da hankali Saade har ke da kanki ke wanan magana haka akan yar uwarki kuma kan Ibrahim.
Tace Ibrahim fa dan uwanka ne besty yaya kake son na hana shi hurda da yarinyar dake gidan ka ai Rama na da hankali bazata yarda tai wani abinda bai dace ba ai.
Yace ok yayi kyau matsalan ki ne ai hakan banawa ba don haka dabara yarage akan ki yanzu ni ba ruwana.
Tunda kin san yaron nan uwar shi ta fada muna an mashi mata a dangin su tun bayan tafiyan shi.
Tace aiba aure aka daura mashi da waccan dib ba don haka yana da right din canzawa yanzu.
Ya shiga sake sutura a jikin shi ba tare da ya kara mata wani magana ba ita ko sai dariyan mumuke take mashi a ran ta.
Washe gari da yamma after five sai ga Ibrahim yazo gidan Allah ya taimakeni ina ban daki ina wanke unders di yaran da nawa nan ya samay su a falo suka shi hira da yaran.
Gajiye ce tazo ta kyankyasa min zuwan Ibrahim din a lokacin don haka ma sai na turo kofan bayin na rufe kaina aciki ban fito ba.
Sai da yagaji da zamane yake tambayan yaran ina anty sukecewa tana ciki tana aiki ne yace suce Uncle Ibrahim yazo yana gaishe ta .
Nasir yazo yana kwankwasa ban dakin daga ciki nake tambayan waye yake cewa shine wai uncle yazo yana gaisheki a falo nace je kace ina amsawa ina abune .
Nan ya karaci zaman shi da shirmay da yaran da zai tafi ya basu wani farin leda da yazo dashi a hannun shi.
Ya tafi baiji dadin rashin fitowan da banyi ya ganni ba a lokacin ina fitowa kiran wayan shi ya shigo min na dauka naji yana sakin ajiyan zuciya yana fadin nagode.
Nazo don na ganki amma kika boye kikaki fitowa nagan ki ko zanji sauki a zuciya na.
Amma kika ki fitowa nagan ki Rahama why da kike min rowan ganin ki ne hakawai ?
Ya kamata ki tausayawa wanan dan bawan Allah naki da ya susuce da son ganin ki kamat zan yi hauka.
Dariya ya bani yadda ya ma rairaice murya kamar da gaske bayan nasan da yaudara yazo min already yana da wace zai aura ko a gida cikin dangin shi.
Nace gashi ko fuskan nawa koda ka gani a lokaci ba zakaji dadin ganin shi ba don a hautsane yake yanzun haka saboda aiki kan fuskan dan kauye yadda yake ai dai.
Yace babu ruwan ki ni dai ai ko yaya yake ni nace naji nagani zan gani a hakan .
Nace next time if you are among the lucky one's.
Yace insha Allahuma ina ciki don ba a taba Ibrahim raggo ba a duniya ai.
Yace ki karbi sako a gurin dana nabashi sako ya baki da fatan zakiyi farin ciki da wanan sakon da zaki gani.
Nace na gode koda banga sakon ba nasan sakone daidai da na yan kauye ai .
Murmushi yayi yace ina jinn dadin sunan yar kauyen nan da kike kiran kanki dashi don alamane na sauki kai gareki.
Nace to nagode da harka fara fahintar halayena don haka ka kula da sauran nan gaba.
Yace indan dai har za, a bani dama na fabinta a hankali ai nafi kowa farin ciki nace yayi nagode sai anjima.
A daidai wanan lokacin daddy ya shigo tsararen gidan su da suke can zaune shida iyalinshi idan sunje kasan.
Ya samu anty a kwance da danta suna barci a hankali ya dauki wayan tare da kwashe lanban wayan da yake ta muradin samu daga gareta kuma girman kai ya hana ya tambayi matar tashi.
Bayan ya yi nasaran kwashewa batare da matar shi ta sani ba ya sauke shu, umin murmushi a fili cikin sanda yafice daga dakin.
Can ya koma waje kasa ya sauko gurin motar shi tare da samun kan shi da kiran layin wayan.
Ina zaune ina sawa Nasir kayan barci muna shirin kwanciya a lokacin naga kira da lambar kasar waje sai dai ba anty bace to waye nace a fili.
Na dauki wayan daidai lokacin da yake shirin tsinkewa tare da sallama cikin murya mai taushi.
Daga inda yake a tsaye ya runtse idanuwan shi a hankali don jin wanan muryan da yayi.
Ya daure ya amsa min da muryan nan nashi mai gadara sai lokacin nagane dawa nake magana.
Yace yakuke nan na amsa cikin ladabi da lafiya kalau muke daddy yaya anty da jinior yace gasu suna barci ne.
Sai nai shiru ina sauraren shi yace Rahama kina jini ko nace eh daddy.
Yace dama akan wanan yaron ne da naji kuna waya dashi watau Ibrahim nake nufi nace eh daddy .
Yace to ina son kiyi hankali dashi kada ki yarda ki fada tarkon yaudaran shi ki mayar da hankalinki ga karatun ki shi yafi maki alheri kinji ko ?
Na amsa a sanyaye da eh daddy yace nagode Allah yai maki albarka nace amin daddy kukala da kanku don Allah kafin mu dawo nace insha Allahu daddy.
Har zai kashe wayan sai naji yace dani anty ki batasan na kiraki ba don haka ba lalai bane tasan da hakan ?
Nace insha Allahu daddy nakuma gode nai massalama na kashe wayan ina mai bin wayan da kallon mamaki.
Mamaki nakeyi may zai sa daddy yace don yai min fada da kada na bari kuma anty taji hakan.
Ban fahinci komai ba a ciki na dai aje wayan tare da karasa yaron da yai barci ko a lokacin.
Sai lokacin ne naga ledan da Ibrahim ya bayar a bani na jawo ina budewa naga turare ne na mata masu tsada guds uku sai set din agogon hannun irin na mata shima ma igiyan daurawa a ciki kala kala duk kayan da ka saka akwai kalarshi da zaka iya sawa dashi a ciki.
Abinda daddy bai sani ba idon anty biyu koda ya shigo tunane ya hana ta barci ta tashi tana nazari a ranta har yagama abinda yake yafita idon ta biyu tana kallon shi sai dai batan lanban waya dauka ba a wayan ta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYABA HAKKIN AMANA YANA KANKI YAR UWA DON ALLAH NAGANIN KI, , , ,

31

Zaune yake a falo hankalinshi na saman system din shi da yake bincike a ciki.
Sai jinior dakebarci da ga gefen shi saman dogon kujera hankali kwance yaron daya gama rikici ya samu ya lalashe shi har yai barci a lokacin.
Ya mayar da hankalin shi sosai ga abinda yake yi a hankali take sauko zuwa inda yake zaune.
Sai da ta karaso gap dashi ne ta yaji motsinta amma hakan baisa shi ya daina abin da yakeyi ba.
Yau kwana biyu ke nan da ya dauki wayan ya ya dauki lanban da batasan ko na waye ba don haka take son ta tabbatar da zarginta a kan shi.
Sanin halin mijin nata da tayi koda ta tsaya tambayan shi ba wai zai fada mata bane don ko fuskan haka ma bata gani a gurin shi ai.
Inda watan shi ke aje saman desk din da system din shi yake takai hannu tana daukan wayan tare da fadin ara min wayan ka na danyi amfani dashi don Allah.
Har yace mata uhum yana maici gaba da abinda yakeyi ko may ya tuna sai yakai hannu alaman ta miko mai wayan tare da tambayan ta ina naki ke ?
Tace baida issashen kudine a ciki, yace da ita har yaushe na loda maki kudi a waya may kikayi dashi keda ba wani waye kikeyi ba.
Tace ara min kawai ido ya tsura mata kamar yana son gano wani abu a gareta babu zargi ko wasa a idon nata yasa ya mika mata wayan ta dauki nata tana kokarin saka layin mahaifinta data fi zargi sai ga sunan mahaifinta ya fito ta kawar tana dan tunane can Rahama ta fado mata a rai ta kai gurin nombba na tana kooarin sakawa sai taga an rubuta .
DHT mamakine ya kamata don haka cikin daurewa ta kira layin nawa sai kusan zai katse na daga da sallama batai magana ba don taji may zance , ina dauka nafara gaidashi tare da cewa daddy yaya anty da jinior muna gaida anty da jinior muna matukar kewan anty daddy adawo muna da anty mu please ?
Na karawa Amira dake kusa dani wayan ina fadin Amira ga su anty da daddy sun kira mu.
Tai murmushi dataji muryan Amira tana cewa hello Daddy tace amira mummy ce yarinyar tai ihu tace mummy please yau zaku dawo gidan ba dadi baku sai dai anty Rama kuma munajin dadin anty Rama tana bamu abin dadi da bakinan mummy tana kaimu yawo park mun je munga lion ni da Nasir da anty da Gajiye.
Saida naji yarinyar nakiran mummy yasa na fahinci anty ne a layin to kuma shine batai magana ba tabarni ina zuba hakana may ke faruwa da ita ne wai ko kuma jikin ne ?
Na karbe wayan a hannun yarinya na fara zuba mata shagwaba ina cewa haba anty na dauka daddy ne ai a layin don shekaran jiya yakira mu da wanan layin sai kuma nai shiru na tuna da warning dina da daddy yayi ranan.
Murmushi tayi tace Rama ke nan waike yaushe ne zaki girma kidaina wanan shagwaban haka ?
Jin suna wacce anty takira yasa shi saurin dago kai da sauri yana kallon ta batare da yai magana ba yana kallon fuskan ta sai murmushi takeyi tana sauraren abinda nake fada mata.
Niko cewa nake anty shagwaba kan ai sai ranan da kika yaye ni kila zan bari wallahi anty na matsuki dawo kullun saina bude dakin ki na shiga na dinga shakan kamshin ki watarana har kuka nake don missing din ki da mukayi.
Dariya na bata tace aiko sai dai kiyi ta shiga daki shakan kamshi na don ba ranan dawowa gare mu sainan da tsawon wani lokaci.
Nace cikin kuka shagwaba wayyo antyna don Allah ki dawo kada na mutu jiya fa har zazzabi nayi na rashin ki a gidan nan.
Tace ki mutu kuma Rama rufa min asiri please inkin mutu ai na shiga uku.
Nace to anty yaushe ne zaku dawo wallahi muna son ganin jinior sosai munyi kewan shi munyi missing din ku anty.
Tace ina ganin likitane Rama kuma daddy kin san aikin shi bana hutu bane shima aiki yai mai yawa sosai anan.
Nace to anty injin daddy bai saka ki wanan bacin rai din don fa ni ina tsoro kada yai ta maki fada ban kusa balle nayi kuka ?
Kai kedai Rama mashirirciya ne wallahi yanzu don daddy na sani bacin rai sai kiyi ta kuka nace eh mana anty ji nake kamar na shake shi anty don wallahi idan yana bata maki rai nakan ji kamar na make shi shima ran shi ya baci.
Ban sani ba ashe tunda tace daddy kike jin haushi anty ya wauce wayan a hannun ta yana sauraren abinda nake fadi gamay dashi.
Sai ji nayi yace ai sai ki kasheni ki huta ko stupid idiot na kike jin haushi Rama dip na kashe wayan da sauri tare da dafe kaina a fili ina fadin ma shiga uku.
Gajiye da take zaune sai kalloni tayi tana fadin may ya faru nace cikin kwalalo idona waje ashe daddy yaji abinda nake fadi shine ya zage ni.
Gajiye tace dani ai maganin ki ke nan ba bakiji ba shiga tsakanin miji da mata basai Allah ba.
Nan shiga damuwa ranan ina fadin aiko na gata kaina wallahi yanzu ni daddy yaji irin hsushin shi da nakeji tafaru ta kare min nasan zamana a gidan ya kare ke nan.
Tun mutumin da nake zaune a gurin shi yaji ban kaunan shi ai shike nan nawa ya samay ni sai komawa kauye ke nan.
Nace idan na koma kauye karatuna fa nace na bashi hakkuri ya yafe min to amma kuma ai abinda kunya gaskiya.
Can kuma yana kashe wayan anty ta kalleshi tana murmshi take cewa hmm Rama ta ke nan boyar Allah.
Wani kallo ya watso mata mai kama da harara yace wanan yarinyar ko zanyi maganin ta wallahi ni take fadan magana haka a kaina.
Anty ta murmusa tare da zama dan gefen shi kadan tana cewa akaina Rama na iya komai besty shi yasa nake son ta wallahi.
Yace ai ban taba sanin rashin kunyan ta ya kai haka ba sai yau din nan ni zatace wai zata shake ko ta make ni ?
Ita har yaushe ta sanki ta san dadinki haka anty tai dariya tana cewa bar min yarinya na please kada ka damay ta.
Ya dan dago kai yana hararan ta yace cikin kutawa zata gane bata da wayo wallahi.
May zakai mata besty ?
Anty ta tambaya cikin son sanin abinda zai aiwatar a kaina yace ina ruwan ki amma ai naga ni ba ruwana da shiga harkan ta balle ta min wanan mumunan shedan haka.
Idan baka shiga harkan ta ba ai kashiga na anty ta ko itako nice bata so taga kana batawa din.
Bata makin may nayi ni din, tace bukatana a kan ta mana gareka ?
Shine ta fahinci kana sani bacin rai a dan lokacin nan wanda da tasan dalili nasan da ta fi fushi dani bisa gareka.
Ai idan baki barima sani zatazo tayi tunda harkin jawo karamar yarinya tana fadin bakaken magana na batanci haka akaina.
Maynene maganan bataci data fada a nan kuma daga tana fadin ra, ayin ta kawai kuma.
Oh wanan ba bakar magana bane a gurin ki ko har kina dariya haka don bake ta bata ba ke nan.
Haukan Ramane baka sani ba kuma besty ai Rama tunda ta watse mama lauratu a kaina tun tana yar ficiciyar ta nasan bata wasa bace akaina.
Yayi kyau yace tare da mayar da hankalin shi ga abinda yakeyi bai kara magana ba.
Ashe ma kana da layinta a wayan ka ban sani ba ai na dauka baka dashi.
Kallon ta yayi yace kamar yaya ina da layinta bake kika bani ba a baya.
Tace ni kuwa kadai tuna amma bani ba dai kan Rama dake tsoron ka kamar may zanbaka layin ta kuma?
Yace a, a bata tsoro na da batace zata makeni ba ai wanda kake tsoro ai baka ko gigin furta kalami mai sauki a kan shi balle wanan.
Gaskiya ni dai ban san kana da layin ta ba sai yau din nan danagani a wayan ka yanzu.
Cikin basarwa yace to wai samay idan ina da layinta ba, a gida na take zaune ba don na samu layin ta kuma wani matsalane kece dai baki san ina dashi ba dai.
Wani kallon zargi tai mashi tare da kawar da kanta tana mamakin shi ita zaiwa muna funci don ya saci wayan Rama a wayan ta ko may ?
Bayan gashi Rama ta fada da bakinta da layin ya kirata shekaran jiya kenan lanba ya dauka daya dauki wayan ta ranan.
Shine girman kai ba zai iya bari ya tambayeta ba sai ya dauki wayan ta don muna funcin maza ya kwasa.
Baibada kafan ta sake mai maganan ba ita ma bata sake bi takan maganan ba ido tasa mai taga gudun shi kawai.
Amma abinda mamaki fa ji yadda take binshi akan zancen yarinyar nan yake wani basar yau kuma don yana son nombata shine zai munafunce ta damay yake son taji a rayuwan tane.
A yadda ra san shi miskili bata taba zaton zai iya yin haka ba amma sai gashi ita da idon ta ta gan shi kuma ya basar to may yake nufi da hakan ne wai ?
Amma kuma ko ma may ye ai ai yarinyar dai ta fada min in ma har wani magana ne yai mata ai da Rama ta fada mata.
Kawai don kana son jin lafiyan iyalinka shine kuma sai ka munafunce ni don girman kai irin na besty nasan dai ba wani abu a tsakanin su sai tambayan lafiyan su kawai da zai yi, amma yana jin girman kan fada min hakan.

********* ********* *********
Abu kamar wasa sai gashi irin matsin da Ibrahim ke yawan kirana dashi a waya yasa har na fara dan sake jiki dashi a lokacin.
Don zai kira waya yace na bawa kowa su gaisa har gajiye da muke tare sai sunyi waya da ita idan ya kira.
Sai dai a waya kawai nake bari yaji ni bana yarda mu hadu a fili dashi don warning din anty da daddy da sukai min a kan shi.
Hakan bai damun shi bai kuma hana shi kirana bayan dan wani lokaci shi dai kokari yake ya samu ya kafa gwaunatin shi gareni kawai.
A haka har muka sharare kwanaki kwanki ya koma makwanni makwani ya share watan ni muna shakuwa tawaya dashi kawai.
Sai faman shiri muke na dawowan mutanen gidan komai mun wanke mun goge munyiwa shiyan kwalla ni da gajiye gwanin ban sha, awa dashi.
Dawowan nasu a lokacin ya samu nasaba ne da aiken da Alhajin shi ke mai na aurar da yaran yan uwasu da za, ayi.
Ciki harda sisters din Ibrahim su biyu da zaa auran a lokacin dinkin duk event din da za, ayi Ibrahim yai muna

Download complete TXT · Novel page