Murucin Kan Dutse

Chapter 43 of 146

ta gyada min kai tana fadin kece zaki taimaka muna sister please .
Da stly ta miko min takardan da zan karan ta na karba kowa ya tsura ido yana son ganin wacece Rahama din.
Nafito a hankali nake takawa karan takalmana na bada sauti kwas kwas sai gurin ya hau tafi.
Na fara da gaisuwa tare da yiwa mutane barka da zuwa da fatan Allah ya maida kowa gida lafiya.
Nafara da dan bayani kan nice zan gabatar da tarihin amarya nan na fara gabatar da takaittacen tarihin Amarya har zuwa haduwan ta da miji ta cikin harshen turanci wanda mutane da dama ke ganin kamar a waje nake karatu ba a kasan nan ba.
Ina gamawa gurin ya dauki tafi da fito na sauko saman tsage din da na hau sai hasken waya da ake daukana ke tashi gurin yab mata na koma na tsaya.
Muna nan ana ta gudanar da shagalin buki wayana yai tsuwa na dan duba anty ce kece min yayi ina raba ido naga ko zan ganta tace ki duba kujeran dake dama dake na hudu.
Gaba dayan su ne a gurin lokacin daddy ya fita kiran Ibrahim ya shigo daidai na kashe wayan.
Yake cewa nazo mu gaisa da friends din shi pleplease don Allah kada na bashi kunya.
Ban fita da wuri ba sai da na dan ja ajin mu na mata na sulale zuwa waje.
Su uku ne da abokan nashi ina zuwa ake tambayan na wai dama wanan zukekiyar ce taka amma gaskiya ka taka babban saa Ibrahim nan muka shiga gaisawa dasu suna dan jana da hira a hankali muna dan dariya.
Jikina ya bani ana kallona daga dayan gefen don duk gurin a cike yake da motocin mutane fal.
Daddy na hango tsakan kanin wasu motoci yana waya ne amma idon shi yana akan mu gaba daya.
Wani faduwan gaba naji don hango tsana karara a kwayan idon shi lokaci guda naji tsayuwan nason ya gagare ni.
Allah ya taimake ni maryam ta kirani a wayan ta wai ina nake ana nemana nace gani zuwa.
Nai masu sallama nace zan shiga ciki ana son ganina da sauri na juya ibrahim na magana ban tsaya sauraren shi ba na shige.
Ina shiga take cewa wai ana nemana wasu ke son nafito nai rawa zasu yi min mannin kudi.
Cikin mamaki nace ni ga muryan MC na ta cigiya na a fagen fili maryam taja hannuna muka haura zuwa sama.
Wakan gwanja aka saka muna wai rawan shi zamuyi ni ta ina ma zan fara ne wai ?
A hankali na fara takawa sai naga wani guy ya fito an taka mai baya da gani boss ne ga wasu.
Yan dubu yafara manna min a hankali yana wani sake shu, umin murmushi kaina na dukar a kasa naji Mc na fadin da kyau major mustapha Sabo .
Guri ya dauki ihu da tafe a lokaci daya sai ga Ibrahim ya fito yana lika min yan dubu dubu sai shima guy din naga ya murmusa ya fara manna wasu kudi masu kore shar take guri ya rude da sowa da ihu stage din take ya cika da mutane suna min manni yan uwan su na masu manni suma.
Ganin abin nasu nason zama rikici daya a bayana daya a gabana a hankali na juya na nufi hanyan sauka basu barni ba ina tafiya zuwa kujeran dana barsu Gajiye da yara suna bina suna min manni har na zauna mutane sai sowa da ihu sukeyi.
Mc yana ta kara zuga su a gurin kaina na dukar a kasa duk kunya ya rufe ni a gurin a hankali gajiye ta mike taja hannuna muka kama yaran zuwa wajen holl din aka bini da idanuwa kowa da abinda yake fadi.
Gurin motar mu muka nufa nan ina kokarin shiga bayan na bude wanda aka kira da mustapha ya iso gurin da mutanen shi.
Daganin shi kaka dan duniya na kwarai sai dai fuskan shi a daure yake tamau.
Muryan shi kamar amon sarewa yake cewa hi beauty ba dai mun hanaki zama ba nida abokin hamaiyyan nawa dan naga kamar kishi ya rufe mai ido ko.
Ban yi magana ba sai kallon shi da nakeyi na fada mota na zauna ina kokarin sa key ya sa hannu ya karbe key din a hannuna.
Yace ina zaki tafi ban san komai ba a kan ki ni dai ba sai na tsaya fadar sunana ba don Mc ya fada kinji haka ma ya fadi naki kowa yaji.
Abinda nake son sani yanzu shine a ina kike da zama kuma ki ban phone nomba dinki don naga wasa ya fita ranki ko.
Amma naso ki tsaya don ban gama nunawa mutane shedata ba a kan ki kika fito.
Ban iya yin magana ba don yadda nake ji zan iya yin duk abin da yazo min cikin dakewa na mika mai hannu ina fadin bani key dina please ?
Murmushi yayi yace mai kyau komai naki na da kyau har fushin ki da zaki daure ki bari na dan daukeki photo a hakan dana gode.
Wautan key din nayi daga hannun shi sai yai murmushi kawai yace Daniel execute my lady please.
Ban tsaya bin ta nasa ba na tayar da mota muka bar gurin sai da na hau titi dakyau na hango bakar motar su suna bina a baya har biyu.
Nace na shiga uku da wanan mutumin gajiye biyan mu fa sukeyi a baya a tsorace gajiye tace suna ina ne nace gasu nan a bayan mu tafe dabara nayi na kauce hanya nabi shorcut.
Muna hawa titin da zai sadamu da gida sai ganin su nayi sun sha gaban mu ban tsaya ba sai get din gida nai horn maigadi ya bude muka shige da sauri muka fito zuwa ciki.
Ina shiga Farida na kirana wai ina inane nake cewa gida tace what shine kika barni a furin maryam nace yi hakkuri please raina ne ya baci wallahi ban gan ki ba na wuce zuwa gida.
Ba, a dade ba sai gasu anty sun dawo fuskan ta a daure yake sosai a lokacin.
Ganin yanayin ta yasa na sha jinin jikina batai min magana akan komai ba sai shigewa dakin ta tayi.
Nima dai dakin mu na shige na fara rage kayan jikina don duk sun isheni a lokacin dau nauyin su nake ji .
Har bayan sallah kowan mu na daki yaran suka damay ni na fiti na basu abinci suci shine fitowa na lokacin.
Farida ce ta shigo da kaya niki niki duk muka bita da kallo har anty dake fitowa falon a lokacin.
Ta zauna tana fadin wash Allah ke kina nan ina can an tsare ni a kan ki ni yau naga fadan maza a kan mace wallahi.
Ke kingani kuwa yadda wuri ya yamutse da fita sojoji sun tayar da hankalin guri haka akan ki.
Anty dake zama tace ni san haka za, ayi ai tunda naji besty yace mu tashi muje gida tun ba, a tashi ba nasan da magana gurin.
Nan farida ta shiga bamu labarin yadda fada ya kaule a tsakanin Ibrahim da soja.
Idanuwana na rintse don takaici tace ai da gudu mutane sukai ta fita gurin wai an taba babban soja.
Nace ni ina ruwana da zama babban shi daga shi har mustaphan duk basu cikin tsari na gaskiya.
Anty dake sauraren labarin Farida tana kuma kokarin canza chenel din tv take cewa amma gaskiya ni ban ga laifin su ba ga mai babban laifi nan Rahama.
Da sauri na dago ina kallon ta tace kin san yadda kike da farin jinin ga jama don babu namijin da zai ganki bai kyasa ba may yasa kika fita tsakar fili yin rawa.
Banda na cewa don haka shiru nayi don ba sama nace da ita maryam ce tajani ai.
Farida ce ta cece ni take cewa aiko Rahama bataso ba wallahi maryam din nan ce ta fita da ita nasan don kada taji kunya yasa ta fita itama.
Koma may ye ai dai yanzu kin ja wanan kuma ni shiyasa ma tun farko ban so zuwan ku gurin nan ba wallahi.
Nikan shiru nayi na makure a saman kujera cikin damuwa don naga rayuwan anty yai matukar baci a lokacin.
Wanan kayan fa naji anty na tambayan Farida din tace bakin ga na manta ba na Rahamane abinda suka rabane a gurin maryam tace a kawo mata wanan kuma naku ne inji maryam din nasan don Rahama ta bayar dasu.
Mika mata kayan inji anty ta fadi cikin basarwa nace ni may zanyi dasu kuma anty ?
Ba naki bane ki bude mu gani mana ko haka za, a barsu a leda kuma na dago nace bude mata Farida don Allah na koma na kwanta tare da kawar da kaina daga kallon su ma balle nasan may ke cikin ledan.
Tana cikin bude kayan ne sai ga daddy ya shigo da jinior a hannun shi nan aka shiga gaida shi na mike zaaune ina gaida shi ya amsa min kasalance.
Yaron da ke barci ya samu kujera ya shimfide shi akai yana cewa sarkin kiriniya yayi barci yanzu .
Mikewa nayi zan shige yace ku zauna abinku fita zanyi sai wayan shi tai kara ya dauka anan inda yake tsaye bayan sallama yai shiru yana saurare.
Can ya kashe yana fadin ganinan zuwa anty ke tambayan shi yadda yanayin shi ya koma yace da ita gwagoce ta bugo min waya yanzui bari naje naji ko lafiya.
Nikan yana fita na sulale na shige daki kayana na fara hadawa gaba daya gidan da garin ma sun fita min a raina a lokacin.
Tsab na gama hada kayana duk wani abin amfani na saida na dauka, nabar na bari, jira nake safiya yayi kawai na bar garin.
Anty ce ta shigo dakin ganin ta dakin wanan lokaci yasa na daga kai ina kallon agogon dakin idon ba idona ke gezau ba sha daya da rabi na dare wanda nasan a irin wanan lokacin ta kwanta ko ?
Idon ta a kan jakkan kayan dana dora saman gadona sai kuma ta juya tana kallon yaran dana shimfide a saman gado na rufe su yadda ya kamata ai masu.
Murmushi tayi tare da kara karasowa bakin gafon tace cikin nuna kayan da bakin ta wanan fa kayan may ye kuma ?
A sanyaye nace nawa ne,
May za, ayi dasu kuma shiru nayi tace bakiji bane may zakiyi dasu a nan nace gida zan koma gobe.
Gida zaki koma gobe akan may fa zaki gida da umurmin wa maimqkon na bata amsa sai kawai na zauna na dafe kaina da hannu daya.
Ba dake nake bane Rama ko baki jini bane wai ?
Anty ina son in koma gida ne gurin su Inna kawai, tace da akai maki may anan din da zaki koma can ?
Ni ba ai min komai ba zan dai koma ne can ne kawai.
Karatun naki fa idan kin koma gida ?
Sai nayi shiru,
Tace akan baki son maganan gaskiya zaki zabi komawa kauye ki zauna ki watsar da karatun ki ko may ?
Shiru nayi mata batare nai magana ba sai kukan dana farayi kawai inaga bata iya jure sauraren kuka nane sai naga ta mike tabar dakin.
Shiko daddy da yaje kiran gwagon shi cikin daren nan ya samu ta cika fam tana jiran shi yana shiga ta tare da zance na da Ibrahim inda take shiga banan take fita ba wai dan ta daya ina son in salwanta mata shi.
Daddy yace amma a gabana akai mai kashedi akan Rahama ai itama yarinyar da kunne na ji tana fada mashi ya fita harkan ta ai.
Don haka gwago ba sai nayiwa Saade ko yar uwar ta magana ba shi dai za, aiwa kashedi akan ta don Rahama ko banza ba saar auren shi bane ita don haka yanemi wata can.
Yai mata sallama yafito ya barta da takaicin cewan da yayi nafi karfin auren dan ta idan tana daukan dan ta wata tsiyace dama.
Yana tafe a han ran shi bace shi kadai ke fada komay ma za, ayi da danta da har take son ganin laifin Saade ga banza.
Bayan tayi sakaci tun farko ta bari ya lalace shi kan shi wanan mahaukacin sojan ba zai yarda yazo mai gida da hauka ba don yaga kalar shi baida mutunci a ido.

********* ********* *********
Asalin mustapha mutanen katsina ne a garin daura zama ya kawo kakan shi kano nan aka haifi iyayyen shi a kano har su din.
Su uku kacal iyayyen shi suka haifa shine na farko a gurin su duk kan su maza ne.
Sai dai ya taso cikin rashin ji haka yasa mahaifin shi ya kaishi aikin kakin soja ko zai daina halaiyar shi.
Rayuwan gidan su mustapha rayuwa ne irin na incin kai kowa abinda yakeso yakeyi a rayuwan shi ba wani kwabo sosai ga iyayyen su.
Auren shi uku yana rabuwa da matan batare da wani kwakaran hujja ba don acewan shi bai isa haihuwa ba a yanzu.
Da zaran mace ta samu ciki zai dauki tsanar duniya yasa mata bazata kara jin dadin shi ba, sai kuma yayi sanadin da ya zubar da cikin ajikin ta karshe kuma ya sake ta.
Kudin kan akwaisu don sun gada ta kaka da iyayye amma babu halin kai gida gareshi.
Baidade da rabuwa da matar shi ba ta uku da ya auro a maiduguri shine nan kuma ya kyalla ido yagan ni a gurin buki ya zo bukin ne ta dalilin mahaifin ango don suna business dashi sosai.
Tunda ya kyalla ido ya ganni ya haukace a kaina ya hana kowa nashi shakat a gidan su kan lalai sai anzo nema mai aurena don yaga Ibrahim ma da gaske yakeyi akaina.
Haka yasa mahaifin shi baiyi sanyi a gwiwa ba da yake dan so ne dan gata da safe sai gasu gida gurin daddy wai sunzo nemawa dan su aure na.
Daddy jin maganan yayi a ban barakwai don jiyane ma fa ya hadu dani shine yau da safe haka har mahaifin shi yazo neman aure.
Wanan wani irin rayuwa ne haka da gani babbu kai a cikin ala, amarin ko ga mahaifin don daga maganan su ya fahinci suna matukar tunkaho da kudi da mukami ga mutane.
Daddy yace da mahaifin nashi shi a sanin shi bai san ina da wani saurayi ba amma zai kirani a gaban su suji ta bakina.
Ina dunkule a daki sai shawara nake ni kadai a zuciyana na gudu ko na tsaya don anty ido ta saka min kawai.
Daddy ya kirata a waya yake cewa ta turo ni inzo falon shi ina da baki a nan da kan ta ta shiga dakina ina kwance na dunkule a guri daya kamar may jin sanyi.
Ta tsaya daidai kofa tana cewa Rama nasan ba barci kike yi ba kije falo yanzu daddy ya bugo waya wai kina da baki a falon shi.
Gabana ne ya fadi ras nace baki anty wasu baki gareni da zasu zo gurin daddy kuma tace kitafi koma su waye ai zakiji ko ?
Hijjab dina na dauka na sa har kasa na nufi falon da sallama a bakina na shiga falon suna zaune su uku na samu a falon suka amsa min sallama na.
Nakoma gefe na tsugunna tare da fara gaida su na dukar da kaina kasa ina sauren may ya kawo su gurina.
Daya daga cikin mutanen naji yana fadin tubarakallah masha Allahu lailai wanan katon boy baiyi zaben banza ba ga ladabi ga addini da mutunci karara mun gani ba sai an fada uwa uba ga kyau kuma.
Ikon Allah nacee araina waye kuma boye da suke magana akan shi dan shiru ne ya biyo falon na dan lokaci bayan mutumin ya gama maganan shi.
Muryan daddy ya katse dan shiru yace Rahama ga iyayyen mustapha nan sunzo nemawa dansu auren ki ne .
Shiyasa nace bari a kiraki muji daga bakin ki idan kin amince da maganan su ba matsala sai mu tsayar da magana tun basu tafi ba.
Sai lokacin na dago kaina dake a duke nace mustapha ?
Daddy ni ban san wani mustapha ba gaskiya ima ganin watakila dai bani bace ake zance akaina don ni ban san shi ba.
Wani ajiyan zuciya naji daddy ya sauke yace to a gaskiya inaga ba gidan nan bane don banda labarin hakan a gidan nan.
Eh haka din ne dayan mutumin da baiyi magana ba tun shigowana bayan gaisuwan da nai masu.
Yace zaki iya fadin hakan don jiya jiyan nan ne ai kuka hadu a gurin dinner da akayi ko shine ya koma muna gida a rude shii yaga matar da yake so a gidan nan.
Nace gaskiya bani bace baba sai dai idan watace yagani amma banice ba gaskiya.
Hmm ki kwantar da hankalinki yarinya kece kada kiji komai don ba wani matsala ga hakan zaki huta a gurin boy ga abinda yake so zakiji dadin rayuwan ki sosai idan kin amince da bukatan shi.
Nace baba don Allah kuyi hakkuri shima abashi hakkuri nagode da kaunan daya nuna min anan ma yadda nake a cikin jin dadin rayuwana nake.
Don Allah yayi hakkuri ya samu wata asalima yanzu ni karatu nake yi babu zancen aure nan kusa a gabana.
Nai shiru na dukar da kaina daddy yace to Alhaji kaji daga bakin yarinyar ina ga magana ya kare ke nan yanzu don Allah abashi hakkuri ya samu wata don ita wanan din yanzu haka karatu takeyi na likita kaga ke nan babu zancen aure nan kusa a gaban ta mun kuma gode da karamcin da kukai muna .
Rahama tashi ki shige abinki mutumin dake da alama shine mahaifin shi yace dani dakata ki karbi wanan duk da ba yawa ban san zamu gannki a yanzu din ba ne.
Na dago kai tare da dan sake murmushi a fuskana ina cewa baba na gode baba ka barshi kawai daga haka ban ko kalli kudin ba na fice daga

Download complete TXT · Novel page