Murucin Kan Dutse

Chapter 44 of 146

falon abina.
Dayan mutumin yace amma idan baku amince ba zan iya cewa kunyi sakaci ga hakan don ba kowane ke samun irin wanan saan ba yai sakaci dashi.
Dakata Alhaji ina an kashe wanan magana anan kun dai ji daga bakin yarinya bata ma san da yaron nan ba ko kana gani zamuyi amfani da kudi ko wani abune mu rude ta dashi.
Idan da kudi na gaban ta ga bayanin ka kawai ya isa a samu kan ta ta bada goyan baya ga maganan.
Sun fahinci ba zasu samu hafin kai gurin daddy ba haka yasa sukai mai sallama suka tafi sunajin kunan rai a zukatan su.
Suna gani duk inda suka tafi nema wa dan su aure sukan yi amfani da karfin arzikin su suci galaba dashi.
Amma nan gashi babu alaman samun nasara ga hakan sun gwada arzikin sun gwada mulki amma babu alaman nasara akai.
Mahaifin nashi yasan idan ya koma gida akwai rigima don yasan halin dan nashi ba yarda zaiyi ba ga hakan .

Ina shiga dakin mu na wuce kai tsaye na koma na kwanta ban ko cire hijjab din dake jikina ba haka na dunkule a cikin shi.
Bayan tafiyan su daddy ya nufo part din anty a dakin ta ya samay ta zaune tana amfani da wayan ta tana ganin shi tace ina Raman bakin har sun wuce ne ?
Yace sun tafi ina wanan yarinyar Rahama take ne kinga abinda take kokarin jawo muna agidan nan ko yanzu fa iyayyen wanan mara hankalin da sukai fada a kan ta jiya gurin buki wai shi soja sune sukazo wai sun zo nemawa dan su auren ta.
Da karfi anty tace What iyayyen shi fa kace suna da hankali kuwa har yaushe aka hadu da zasuce sunzo neman aure haka kimkau.
Yace koma may ye ai laifinki ne da kike bari tana fita irin wanan gurin da maza masu jin karfin iskanci a jiki ke taruwa.
Harda fitowa tsakiyan fili gata uwar turawa wai tana magana harda rawa tsakiyan maza haka for god sake ?
Yanzu laina zaka gani idan batafita ba jikata zanyi insha a gida ko haka kake so taita zama tunda kai bakajin shawara.
Shawaran may kuma ana maganan gaskiya zaki dauko wani magana can ki saka ciki.
Nan dai ya kwashe yadda akayi ya fada mata komai, tai murmushi tace suna ganin zasu iya rudin Rama da kudin su ne ko may ?
Yanzu dai ai kafara gani garin kallon kitse dai, , ,
Tsaki yayi ya mike yana cewa tana ina ne yanzu tace dashi tana daki tun jiya na kasa gane kanta sai fushi takeyi don nai mata fada.
Yanzun haka ma ta hada kayan ta tun jiya wai gida zata koma ita bazata zauna nan ba kuma.
May akai mata kuma da zata tafi idan ta tafu karatun nata fa kuma tafasa ke nan ko may ?
Wa yasanar ma haukan ta kyale ta ai babu inda zata tafi gaskiya batason a fada mata amma ina amfanin rawa a gaban mutane.
Koda yake Farida tace wannan kawar tasu mai rawan kaine tajata zuwa gurin rawan nima naga lokacin da ta jawota ai zuwa saman fada dai nai mata don gaba kawai.

Mahifin mustapha ya fada masu duk yadda akayi a gidan daddy yana zaune yana sauraren mahaufin nashi ya mike yana fadin waye shi a garin nan da zaice ba zai bani yarsa ba mai ya taka shi din da zai ki bada goyon baya akai.
Dakata boy wanan mutumin da kake gani duk abinda muke takama dashi yana dashi koma ince yafi mu wallahi.
Mugun yarone don yana boyon kurwan shi ne ba a ganewa kawai amma shima don ne a garin nan ba karami ba.
Ai tunda kaga na kyaleshi kaima kasan akwai dalili hakan don bazamu iya nuna mashi kudi ba sai dai mu fito mai ta wani hanya muci galabar shi a hakan .
Jin sunan uguwan su mustapha yasa anty ta kira layin wata kawar ta don tayi bincike a kan shi.
Bayan sun gaisa ne suka dan taba hira kwana biyu yaushe rabo anty take cewa don Allah dama ina son tambayan ki karima ko kin san wani mustapha sojane dan gida haruna hadeja ?
Tace kai wanan yaron mara mutunci kin san ai yaran gidan ba mutunci ne dasu ba ko kadan.
Wayan anty yana a hands free kowa dake falon yanaji abin da take fadi tace kin san shine saade?
Indai mustaphane dan iska ne auren shi uku yana saki sai kinga irin matan da yake aure amma kwana biyu kiji ance ya rabu dasu ai.
Baida kirki yaron banza ne wallahi ni laifin ma masu bashi diyan su nake gani don shi ko ganin shi kayi kasan tantiri ne ai.
Tace injin ba wata naki yake so ba dai saade tace a, a diyar wata kawatace wai yake so amma basu bashi ba ai.
Tace sun kuru wallahi da nan da wata uku suna ta bazawara kawai don bai shekara da mace shi a gidan shi.
Gaba na ya fadi a raina nace anyi kyaun dan maciji ke nan ga mutum.har mutum a fuska amma babu halin ko kadan.
Bayan anty ta kashe wayan tace dan iska shine yazo muma ya yaudare mu ko wai harda son su gwada wa mutane gudi da mulki a fili don sun saba harka da makwadaita.
Ai shine daddy ku ke cewa kin burgeshi da baki tsaya karban kudin uban shi ba da haka suke yaudaran mutane ai.
Nace balle ni wallahi bai mun ba ko banza ko ba, a fada ba ai da ganin shi dan iskane yana magana yana son taba mutum.
Gajiye tace Allah dai ya tsare ai maza na cutan mata yanzu akan abin duniya sai asan halin mutum amma saboda kwadai a dauki diya a bashi.
Anty tace kin san mutane son abin duniya yai masu yawa yanzu ko an sani sai a take sanin a cutar da yarinya ga banza.
May aka gane ga aure wata uku ko hudu a halaka ma yarinya a maidata karamar bazawara an cuce ta an gama.
Nidai haushi da takaicin wanan abin bai barima nayi magana ba don haka kawai sunja min barnan suna ina zaman zamana hankali a kwance.
Mai gadine yai sallama a kofan anty yana fadin wai ana sallama da Rahama a kofan gida.
Anty tace maigadi waye kuma baida lamban tane da zai turoka kana bakin aikin ka ?
Yace wani sojane da soji a waje cikin kakin su da motar su na soja sukazo nan kofa yace a sallamo mashi ita.
Nace kace ban nan yace sai dai kiyi hakkuri don Allah don na fada mashi kina gida ko.
To kace nace bazan fito ba kuma don Allah kada ya kara zuwa gidan nan da sunan gurina yazo .
Naga maigadi ya dan kalleni a dan tsorace kamar zaiyi magana sai kuma ya juya yafice da sauri.
Bai dade ba sai gashi ya dawo yana fadin wai yace don Allah ki fito akwai abinda zai fada maki yanzu ba dadewa zakiyi ba.
Nace bazan fito ba sai farida tai farat tace bari naje na bashi hakkuri ya tafi nace hakkuri may kuma zaki bashi yanzu.
Anty tace bari ta tafi kawai tamike ta fice gajiye tace kin san ta da rawan kai indai ba zuwa zatayi ta cusa mai mumunan ra, ayi ba dai.
Duk abinda zataje tayi ai taje tayi ni dai bazan fita ko ina ba wallahi .
Tajima sai gata tadawo da ledoji manya manya tanacewa kinga da ban fita ba da wanan damar ya wuce mu ai.
Ko baki son shi kici banza kawai kinci bulus nace kidai ci keda kika karbo mai kayan shi.
Ledan ta shiga budewa tana washe bakin ta kayane irin na mata a ciki turare agogo shadda earing da sarka da sauran tarkace sai dayan ledan kayan kwalama ne kala kala acikin shi.
Ta mayar da ledan tana turo min a gabana na mike na shige na barta da kayan a gaban ta.
Ashe ta bashi nomban wayana da ta fita ban sani ba bata kuma fadi cewa ai tabashi layina ba.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE IDAN KIN YI GANGANCIN KARANTAWA NA BARKI GA ALLAH, , ,


IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH YABI MIN HAKKINA A KANKI CIKIN GAGAWA YARWA ALLAH YA SAKA MIN AKAN WACCE TA FITAR MIN DA NOVEL DINA, , ,

34
Haukan kiran da Soja ke min yafi karfin na ibrahim da nake ganin ya damay ni a baya da kira hakan yasa ba shiri na kashe wayan nawa gaba daya.
Dama waya ba damuna yayi ba don ban faye amfani dashi ba nazo nagane cewa Farida ce tabashi layi na haka yasa mukai fada sosai da ita.
Ta kwashi nata ya nata tabar gidan da yamma wai tayi fushi tana gani zan bata hakkuri ne ta tsaya.
Batasan yadda nakeji zan iya yin komai a lokacin ba gashi tsoron wanan bakin sojan ya fara kamani don abu yake kamar mara hankali.
Don har zuwa yayi ya samu daddy da maganan cewa ko daddy ya yarda ya aura mashi ni da girma da arziki ko kuma yasan hanyan da yabi ya aure ko ta karfin tsiya ne.
Daddy yazo ya samu anty da maganan yadda sukayi da Soja mai sona yace yanzu dole ta samu mafita don wanan mutumin mahaukacin gaske ne.
Wani mafita kake son na samu mafita guda ne shine ka yarda da bukata ayita ta kare ko ba shike nan ba.
Yafita daga dakin cikin fushi ya barta da tunane ita kadai a dakin ta na fito cikin shirina zani makaran ta nazo na sallamay ta dakin ta.
Nan na samay hankali a tashe tace anya Rama fitan nan naki kuwa yau zai yuyu .
Da sauri na juyu nace anty lafiya dai ko ?
Tace ina fa lafiya Rama wanan mahaukacin da ya like maki yazo ya samu daddy ku da hauka yace koda karfin tsiya sai ya aure ki.
Duk da naji tsoro a raina amma a fili cewa nayi Allah ya fishi mugu azzalumi kawai.
Nace mata sai na dawo tace fitan zakiyi ke nan Rama ?
Nace anty saboda shi na zauna gida karatuna ya tsaya kuma ?
Tace to Allah ya tsare nace amin anty sai na dawo ke nan tace Allah yasa nafice.
Tun barin layin uguwar mu na lura da wata bakar mota dake bina a baya a guje na kwasa Allah dai ya tsare ni na isa school lafiya.
Yinin ranan a firgice na wuni har Zarah ta fahinci hakan a gareni take tambayana ko lafiya nake haka yau ?
Ban boye mata ba tace badai boy kike nufi ba dan gidan haruna daura nace kamar haka naji sunan shi fa.
Tace aiko kin shiga uku wallahi wanan dan iskan mara mutunci may zakiyi dashi ke ?
Tace abu daya zan muyi shine idan mun tashi sai ki shiga motana ni na tafi da naki gida na ko yaya kika gani ?
Nace hakan yayi ba matsala ai yadsa muka tsara haka mukayi na samu na isa gida lafiya a firgice itakuma ashe sun bita sai da sukaga ta nufi gidan ta har can suke tafito sukaga bani bace sai suka juya.
Washe gari tsohuwar motar anty na shiga basu gane ba sai da naje school suka fahinci nice a cikin motar.
Aiko suka darkakeni saida na shige wani guri na samu na isa gida lafiya haka yasa na fadawa anty halin da nake ciki.
Tace na zauna babu inda zan kara zuwa sai komai ya lafa zan fita nayi hakkuri da karatun kwana biyu.
Shiryawa tayi sai gidan mama laraba tasamu babu kowa a gidan suka gaisa da ita take cewa lafiya dai ko Saade.
Nan anty take cewa mama magana nazo muyi dake da fatan zaki saurareni ki fahinci abinda nazo maki dashi.
Nasan baban su Amira a duniyan nan babu shawaran da zaki bashi bai dauka ba kuma ya zamo mai alheri a karshe.
Tace matsala kuka samu ne dashi tace mama ba matsala bane sai dai kuma matsalar ce.
Nan dai ta kwashe abinda ke tafe da ita na neman shawara akan auren da take son yakara ya bijera mata.
Mama laraba ra dubeta da kyau tace yanzu ke Saade da kanki koke son mijin ki ya karo maki kishiya bayan wa yan nan ma da kike dasu ba wani zaman dadi kukeyi dasu ba.
Nikan Saade da zaki bi shawara na da sai nace hakan ma da kuke ya isa don kishiya fa ba dadi gareta ba.
Mama nasan da hakan amma ina sin ki fahinci manufata a hakan don samun saukin mu nan gaba dani dashi da yaran baki daya.
Mama kinga da yaje gaba a kasa rike mai diyan diyan shi yace zai dauko wata don nasan halin shi akan yaran shi.
Gara ya dauko wacce na sani kuma na yarda da ita da ya dauki fitsarariya wace zata zo ta ganawa yara mugun hali.
Umm, umm Saade dadai ki kara tunane matan yanzun ko ince mutum yanzu ba dan goyo bane wallahi.
Mama garafa da wanan din nasan ta yasan ta musan halinta kin ga yafi komai sauki a gare mu.
To ke saade dakike wanan magana Allah fa shi yai ciwo yai magani ai ciwo ba mutuwa bane don sai mai lafiya ma ya tafi yabar maiciwon a duniya.
Tace hakanane mama nidai don Allah a duba min bukatana ko za, a dace ga hakan tunda ni yaki jin magana na.
Mama tace kin ga idan har wacce kike son ya aura din batai mashu ba ko kuma ita din butulu ce fa kinga kin zalunce shi ta zalunce ki ke kuma.
Jikin anty yai sanyi a lokaci guda hankalinta ya dan tashi take kuma wani natsuwa yazo mata tace cikin kuka mama ba wata bace can daban nake son ya aura sai Rahama dake gurina.
Kin dai gane ta kinga ko nasan halinta yasan nata ai banyi tsan manin irin hakan ba daga gareta.
Salati mama Laraba ta saka tare da tafa hannunuwan ta alaman mamaki ya kashe ta lokaci guda.
Tace Rahama dai Rahama dai Sa,ade dana sani ta gurin ki anya kuwa kanki daya Saade da zakice mijin ki ya auri yar uwar ki.
Mama Rahama yar uwata ce amma bata jini ba sai girma da arzikin daya hada mu ya koma yan uwan taka a tsakanin mu yanzu.
Jikin mama laraba yai sanyi yadda taga anty na zubar da hawaye tasan irin haka ita kadai tasan abinda take ji a zuciyar ta ai banza baikai zomo kasuwa.
Idan ya duba ga maganan ta gaskiya ne don dan nata ai yana son kulla amma Allah bai hada shi da matan arziki ba ita waban mai hankali lalura ya hana ta bashi lokacin ta.
Mama Laraba ta nisa tace yanzu tunda ke da bakin ki kika bukaci hakan ai Alhamdullahi da shine yazo da maganan kinga sai muce yayi rashin hankali duk da aure ya hallata a tsakanin shi da ita.
Don haka ki barni dashi insha Allahu zamu zauna dashi kan maganan kuma da yardan Allah zai fahince ni don ban taba bukatan wani abu dashi ba bai min ba don haka wanan din ma ai bazaki ba idan na fahintar dashi.
Anty tace nagode mama da kika fahince ni haka da wuri ba kowane zai gane hakan ba sai ma ai min daukan banda hankali ban san ciwon kaina ba.
Ai maganan aure babban magana ne Saade ba ko wace mace zata iya wanan sadaukar da ran da kikayi ba haka shiyasa za, a dauka ko baki da hankaline.
Tsananin son mijin ki da yaran ki yasa har kike masu gwadayin fatan alheri a rayuwa nan gaba.
Anty tace ni har ga Allah ina ma mijina kwadayin kasancewa da wanan yarinyar koda kuwa ina da raina na ne nidai bukatana naga ya samu kwanciyan hankalin aure kaman ko wani magidan ci a gidan shi.
Naji na kuma gane manufan ki don haka banda abinda zance sai nace Allah yai maki albarka a rayuwan ki yasa a gama da duniyan nan lafiya.
Tace amin a sanya tasan takawo maganan inda za ai mata maganin shi indai mama ce don Allah ya bata sa, an dan yar uwar ta sosai.
Tace yanzu mama ba sai na sake mai magana ba ke nan ko?
Ba sai kin shiga ba Saade ki barni dashi kawai zamu zauna da shi insha Allahu.
Tai sallama da mama Laraba ta barta tana mamakin ta da tausaya mata don tana gani don kawai rashin lafiyan dake damunta ne ya kawo mata wanan danyen yanke hukuncin da taiwa kan ta.

********* ********* *********
Ance labarin gari a tambayi dan gari ashe komai nawa dadin hira yaja Gajiye har sunyi hiran da Farida.
Wanan labarin ne da sunan kauyen mu da sunan iyayyena yadda za, a samay su idan sunje garin mu kaf Farida ta fadawa soja komai.
Haka yasa yafita batun daddy a nan birni suka zagaya shi da iyayyen suka tafi har kauyen mu gurin iyayyena.
Kan sunzo nemawa dan su aure na Allah ne ya taimaka babana da maigari yakira shi kan zancen basira yazo mai yace.
A gaskiya sunan na haifi Rahama ne kawai yanzu amma uwar rikon ta da maigidan ta sunfi ni iko da ita don ko a gurin su take kun ga idan nace nai masu haka ba kyautawa zama tare ba.
Basu so jin haka ba sai cewa Alhaji haruna yayi amma kai ka haifi abinka kana da iko da ita har yanzu .
Kayi tunane akai ko nawa kada kaji komai zan zube maku shi yanzu anan basai mun tashi ba.
Babana yace adaiyi hakkuri don Allah Alhaji a bari zan ga shi marikin nata don idan nai masu haka kamar naci amanan zamane.
Don dai a rayuwa banda abinda zancewa wa yan nan mutane sai godiya ga irin alherin da suke min.

Download complete TXT · Novel page