Murucin Kan Dutse

Chapter 62 of 146

zama na gori ne yanzu wanan ai halin zama tare ne amma wanan ai ba zai sa na yarda da kishiya ba ko wacce ke tare da kishiyana a da can baya.
Allah ya kyauta yace Rahama shiga ki dauko min charger na bedside yana nan makale.
Tankar banji abinda suke fafatawa ba da Zulfa a kaina na mike tabini da kallo yadda jikina yake shocking duk takawan da nayi sai mutum ya dauka yanga nakeyi a hakan.
Bayan na shige ne taja wani uban tsaki tare da dawo da kanta gareshi tana cewa wai yaushe wanan kucakar yarinyar har ta koma hakane ban sani ba ?
Murmushi yayi tare da gyara zaman shi yace kuna dai zubar da mutuncin ku ga wanan yarinyar ranan da zata fara baku amsa zaku raina kan ku don na tabbatar na bakunta take maku kawai idan kunci gaba ba zata juri hakan ba gare ku.
Ko yanzu ma idan zata iya ai bissimillah Hindatu ce ta shigo sai maganan nasu ya tsaya anan.
Tana ganin Zulfa zaune suna magana ta dauka maganan girma da arzikine sai ta hade ranta tana cewa dashi.
Na dauka kai kadai ne dama magana nazo dashi zan tafi na dawo idan ba zan samu lokaci yanzu ba.
Zulfa tace kina nufin in tashi zakiyi magana dashi ke nan ko may kike nufi da wanan maganan taki ?
Nan kuma suka kaule da fada a tsakanin su shi dai yana zaune yana jin su sai dakilan wayan shi yake yi kawai.
Ina fitowa na samay su a hakan suna ta fitina a tsakanin su ganin na fito ina bin su da kallon mamakin abinda ya kawo masu fina yanzu yanzu don ban ma san shigowa Hindatu ba.
Na kara inda yake tare da rusunnawa nace daddy gashi ya dago daga abinda yakeyi yace min tnxs.
Maimakon na zauna sai na juya zan bar masu falon lokacin ya dago kai yana cewa dani ina kuma zaki ki bani abinci naci na kwanta.
Duk sai sukai tsit suka juyo kamar suna min kallon gareni komawa nayi na zauna daidai inda abinci yake na fara bude kulolin abincin .
Tuwon Alkama ne da miyan karkashi danye sai bussashen kifi da yaji da kayan yaji.
Ok idan kun gama sai ku bani guri zanci abinci yanzu .
Haba dai ai magana kowar mu tazo dashi sai dai mu yi mu fita kawai yace ba yau ba don banda time din hakan kuma .
Yana fadin haka ya mike ya sauko daga saman kujeran ya zauna akasa kusa da inda nake zaune yana gyara zaman shi tare da jawo roban ruwan wanke hannun dana aje a gaban shi.
Basu baya yayi yana fuskan ta na ina gamawa nima zama nayi a kusa dashi tare da gyara zaman gaf dashi muna fuskantar junan mu.
Bussimillah yayi ya soma cin abincin shi haka tasa Zulfa fara mikewa ta fice a hasale itama hindatu tabi bayan ta dama ba zaune take ba tana tsaye bayan kujera ta dafa ne don ganin Zulfa da ta sama a falon tare da shi.
Abinci yake ci hankalin shi a kwance ya miko min wayan shi yana fadin saka min cajin wayan nan.
Karba nayi da hannu biyu na mike zuwa jona cajin ya dan bini da kallon tausayi.
Bai san may yasa mata akan kishi basu da tausayi ba yasan ina dakon bacin ran abinda mahaifiyar shi tai min a raina da yamma.
Yanzu su kuma a kan hauka sunzo suna kara dada min wani sabon tention don baki kishi mai kama da hauka don ko kan su basu bari ba kuma wai suna kishin wata.
Na dawo na zauna a inda na tashi yake cewa dani ba zan so ace wata rana zaki kasance cikin irin wanan rayuwan ba.
Rayuwa irin wanan baida amfani da ace kamar yadda suke caza min kai irin haka Saade take da yanzu zaman garin nan ya gagareni.
Bana son rayuwa da fitina irin haka amma sai gashi yau Allah ya nufi rayuwa na da irin haka.
A da can baya idan naga mata suna caza kan gidajen su haka nakan ga sakacin kamar daga maigidan yake.
Ashe abin ba haka yake ba hakkuri ne da kawaici tare da dubaiyya irin na maza ke sa suna sakawa matayen su masu yawan fitina ido haka.
Yau sai gashi na wayi gari a cikin irin wannan rayuwan da ban taba tsan mani zan yi hakkuri irin haka ba.
Ya jawo roban ruwan wanke hannu ya fara wankewa yana fadin nasan komai daren dadewa idan ba su daina ba hakkurina zai iya koma min ciwon zuciya.
Da sauri na dago kai ina kallon shi don jin abinda ya fada yace kina mamakin hakane ko.
Haka din ne zakiji yanzu an kwanta da mutum sai dai a wayi gari ace babu shi bakomai bane zuciya ta gaji da magana nauyi yai mai yawa ya buga.
Yanzu dai yan kinji abinda hajiya tace a gaban ki duk da tasan irin rayuwan hakkurin da nake da yaran nan a gidan nan amma ita bayan su take goyo ni nata nine mai laifi .
A sanyaye nace daddy kayi hakkuri Allah zai kawo ma mafita dayar dan shi insha Allahu.
Allah yasa su gane gaskiya su daina a koma daidai a gidan don ni banga abinda akewa wanan fitinan ba haka.
Jan jikin shi yayi ya jingina da kujera tare da zaman dirsha a kasa zo nan Rama yace na dago kai na kalleshi.
Yadda yace hakan nayi na dan yunkuro zuwa inda yake din yace naji kince baki san may yasa suke haka ba ko ?
Ina a durkushe na gyada mashi kai alaman eh yake cewa dani har yanzu Rahama baki fara so na bane a ranki balle ki faran kishin nawa ke ma ?
Kunya maganan shi ya bani sai na koma na zauna zama irin na mai shin cin abinci tare da dafe dayan hannuna a kasa daga gefena.
Yace tell me har yanzu da alaman ban samu gurbi ko kadan ba daga zuciyar ki wanda ke ma zai sa kiji abinda suke jin din don ance kishi a jinin ku mata take ?
Da zan iya fada danace dashi nafi kowa jin zafin kinshin shi a dan zaman kwana kadan da nayi dashi ya lasa min zuman da ban san akwai shi ba aduniya haka ?
Amma na daure na cije bani fatan ko rana daya na nuna wanan irin haukan kishin haka.
Bazaki bani amsa ba ina tambayan ki shiru nayi sai can nace dashi na hada ma ruwan wanka ko .
Yace kin matsu mu kwanta ke nan ko kunya da mamakin yadda in muna tare mu biyu yake sake jiki yana min magana irin haka.
Yace dauko min cajin da kika saka tunda baki bari na kalli news sai mu shige ko ?
Nace bari dai na kwashe kayan nan na shiga dasu ciki na dawo ban wa yara adduan kwanciya ba kuma ban sallami anty ba.
Yace you can go amma kada ki shanyani anan please kan yaran nan naki masu shagwaba.
Na danyi murmushi kawai na mike na fara tattara kayan na fice zuwa cikin gida ban dawo ba sai da nakai ga yin wanka na gyara jikina tsab naiwa anty sallama na koma part din shi.
Sai dai ina shiga naji muryan shi sama sama kamar yana fada yana cewa ban son rashin hankali may zai kawo ki nan wanan lokacin.
Ki fice min daga falo bani son fitina.
Dana fita da ita ina ranan girkin tane na fita da ita din ko kece da girki da zaki zo min da maganan banza ai da kika isa sai kije ki tambaye ta may nasayo mata a ledan da kikaga na shiga dashi.
Daidai lokacin na shigo falon don a zatona ma da waya yake magana amma sai naga Hindatu a zaune tana cika tana batsewa.
Kamshin turarena yasa ta dago kai tana kallon na ban yi magana ba na kama hanyan bedroom kawai na shige na barsu nan.
Bai jima ba naga ya shigo dakin wanka ta shiga ya fito ya tsaya ya gyara ko ina najikin shi ya hawo gado ya kwanta.
Rugumoni yayi zuwa jikin shi yana sauke numfashi tausayin shi naji ya kamani na lumshe idanuwa na ina tunane.
Nasan cewa tunda har ya iya bude baki ya furta min damuwan shi yau abin yakai mai inda yakai don na fahinci hakkuri yakeyi kawai.
Barci mu kayi ranan ba wani abinda ya wakana a tsakanin mu sai dai ina rungumay a jikin shi har safe .
Da safe zan shiga school don haka ban bata lokaci ba na abinda zanyi a gagauce na shirya nafito cikin shirina na bayan nayi sallama da duk wanda ya dace na sallama na bargidan.
Sai daya tashi ya shirya yazo part din anty nan ya dab zauna tare suke hira da ita tace dashi jita sai hajita ta ganka da amaryan ka ko ?
Kamar yadda na bata fuska haka ya bata nashi yace da ita eh sai dai ai kin san halin hajiya.
Ban taba tsanmanin zata iyawa wanan yarinyar cin fuska haka ba sai gashi tai mata abinda bai dace ba har tana kiranta diyan matsiyata mai farar kafa for god sake.
Subbahanallahi Rama ce kuma mai farar ka mai tayi kuma na farar kafa har yaushe ta shigo gidan ma ?
Yace halin hajiya ne baki sani ba kuma haushin ki akan ta ya koma tunda tace kece kikai hadin.
Amma kuma kaga Rama bata fada min komai ba wallahi.
Asalima dana tambaye ta suna lafiya tace lafiya suke suna gaishe mu ai.
Yace bazata fada ba aiko can ta bani mamaki don bata nuna komai ba har muka dawo dama nai mata magana sai cewa tayi dani ai hajiya uwace a gareta.
Ji yayi anty tace Alhamdullahi Allah mun gode ma ka fara ganin hasashen da nai maka ke nan akan son auren yarinyar nan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, IDAN KUMA KIN KARANTA DAKE DA ALLAH, , , , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH SHI ZAI BI MUNA HAKKIN MU A KANKI , , ,

45
Ruwan sama aka tashi dashi agarin tun da asuba ake tsula ruwa ba kakautawa.
Hakan ne ya jawo rashin yawan firan wasu daga gidajen su har da mutanen gidan mu don ranan ko yara basu samu hanyan fita zuwa school ba don ruwan yai yawa ga sanyi.
Sai zuwa goma da rabi na safe aka dan rage yawan ruwan sai dai still ana dan yayafi mai karfi.
Na shirya don dole sai na fita zuwa school din part din anty na shiga wacce yanayin yasa ta dunkulewa a cikin abin rufa.
Na gaida da ita muka amsa take cewa dani fita zakiyi ne haka cikin ruwan nan Rama , ?
Nace anty dole na fita don kin san rashin fitana ba zai hana aiyi muna karatu ba sai dai wanda bai fita ba yai hasara kawai.
Nace ba zan dade ba zan dawo ai har nakai kofa tace kada ki fita baki sallami besty ba fa ko kun gaisa ne dashi da safen nan.
Naja na tsaya tare da ce mata a, a bamu gaisa ba da shi yau.
Jeki ku gaisa dashi, ai yanzu killa yana falo shi ya fito har ga raina ban so haka ba don idan ban da girki bani zuwa part din nashi hakana.
Da sallama na shiga falon suna zaune da Hindatu ta wani dan kwanta da gefen jikin ta a saman jikin shi kamar suna wani maganan arziki ne idan ka gansu.
Jin sallama na yasa shi dago kai daga bin computer din shi dake a hannun shi da yakeyi.
Wani harara Hindatu ta watso min sai da naji yan hajin cikina sun kada min lokaci guda.
Cikin dakewa da gyara natsuwa na nake ce wa ina kwana daddy anty ina kwana ?
Tace malama lafiya kika shigo mina muna hutawa ko jarabar taki kuma ya kai ki kasa hakkuri kijirashi yazo gareki.
Ke kan tir da halin jaraba wallahi irin naki bazan daukar maki wanan rainin ba don ni ba saar ki bace.
Allah ya baki hakkuri anty dama nazo gaida daddy ne na sallamay shi zan tafi school ne yanzu.
Ke dan Allah rufe wa mutane baki jarababban banza kawai mara tunane.
Hindatu zan saba maki yanzu akan wanan haukan naki keda kike shigowa idan tana da girki ashe kin fita jaraba ke nan.
Jaraba kuma ai isa ne a gun miji tayi jaraban sai may tunda har kin fahinci jarababba ce ita.
Ya juya inda nake yake cewa ina ga ai ba a tsayar da ruwan saman ba har yanzu ki bari na sauke ki.
Ka sauke ta ina ranan girkin nawa zakace zaka fita da waban kwailar mai kama da mage.
Ke fice ki bani guri ana mazuru ana shaho ace wai ana fita karatu kullun.
Maganan yai min zafi don haka na kasa danne zuciya na na juya na dan kalleta nai murmushi nace ai ko gara dani.
Don ni har ina da inda na fake ga fita na kowa yasan inda nake zuwa ashe fitan ma da ake fiye da sau goma a wuni mazuru da sha akeyi sai yau na gane hakan.
Dama abinda kakeyi shi kake tsamanin kowa ma haka yake ni banda lokacin haukan ki don ban dauke ki cikin masu hankali ba tun farko.
Daga haka na juta na fara tako takalmina yana ba da sauti kwas kwas kwas na fice daga falon ko ba komai dai yau na bata amsa ai.
Ina jinta tana hargowa wai fada ban tsaya sauraren ta ba nabar falon na mike hanyan fita zuwa inda kowa ke aje motan shi a gidan.
Ina kokarin bude mota naji muryan shi a bayana yana cewa ba nace ki bari na sauke ki ba.
Tsayawa nayi har ya karso ya jawo motar da zai fita dashi muka shiga tana tsaye daga coridor tana ta zabga masifa wai ita anci mata girkin ta.
Tana kallo ya ja mota muka bar gidan muna fita daga haraban gidan mun dan yi nisa naji wani hawayen bakin ciki ya silalo min a fuskana.
Jin sheshekar kuka na yasa yadan juyo ya kalleni baiyi magana ba sai mika min hankicin da yayi.
Ban karba ba naji yayi murmushi kawai yaci gaba da tukin shi har muka kai school din nai godiya zan fita yace karfe nawa zan dawo daukan ki ?
Nace hudu a takaice na fice daga motar banji ya tayar da motar ba ni ma ban juya ba na shige ciki don ruwan da ya dawo da dan karfi.
Ranan haka na wuni a cikin bacin rai har four yayi sai hamza driver ne yazo daukana yace maigida ne ya turo shi ya dauke ni.
Na dawo na fara shiga gurin anty na gaida ita ban tsaya ba na wuce part dina ina cire kaya gajiye ta shigo take cewa dani ashe kin dawo ?
Na dan kakaro murmushi a fuskana nace nadawo na duba kitchen baki ciki.
Tace abinci fa bari na kawo maki nan nace a, a dakin barshi idan nai sallah zan fito sai naci.
Har ta juya kamar zata fita sai kuma taja ta tsaya tace Rahama kiyi hakkuri akan sherin matan gidan nan dama hakan shine kishi ai.
Dazu bayan fitan ki anyi fada sosai kaca kaca da maigidan da hindatu har sai da mahaifanta suka zo gidan nan.
Murmushin takaici na kakaro nace da ita na gode kawai a raina kuma nace ashe shiyasa daddy bai zo daukana ba da kan shi ke nan ?
Bayan na fito na shiga gurin anty tana zaune falo na gaishe ta na samu kujera na zauna na dan daga kaina sama ina tunane.
Muryan gajiye naji tana cewa ga abincin ki Rahama na karba tare saukowa kasa na zauna saman carpet din tsakiyan falon.
Cibi biyu naci sai naji abincin ya fita min a rai ina ta dan juya spoon din na kasa cin abincin alaman ina a cikin damuwa.
Rama naji muryan anty na kirana tace kada halin matan nan ya tayar maki da hankali a gidan nan haka halinsu yake ko yaushe.
Hawaye ne masu zafi suka fara zubo min shar a idanuwana tace nasan zakici gaba da cin karo da abubuwan bacin rai masu zafi ko yaushe a cikin wanan gidan.
Amma idan kin fahinci halin kowa zaki iya zama da su da halinsu don su a kullun burin su ne su ga rayuka ya baci kawai.
Basu kaunar suga besty yana hurda da wata mace ko da a tsakanin su ne bayan su.
Naji abinda ya faru dake da kuka je gaida su hajiya wanda sam banji dadin jin hakan ba.
Sai dai na yaba da kaifin hankalin ki yadda kika nuna a gaban ita hajiyan da kuma shi kan shi maigidan.
Hakan da kikayi ya nuna cewa nan gaba ma zaki iya hadiyan duk wani fitinan da zai bullo a gidan nan ko a gare mu.
Rama sanin kanki ne ban da wani buri a duniya da ya wuce naga yaran nan, sun samu ingantattacen rayuwa da kulawa yadda ya dace wanda Alhamdullahi zan iya cewa mun samu ko yanzu.
Don ni dai banda ta inda zan raina maki akan irin kulawan da kike bawa yaran nan wanda tun yanzun ma sun dsuke ki tankar ni a gare su.
Aikin dake gaban ki shine na besty wanda ya kamata ki kara kaimai gurin kara fahintar halin da yake ciki a gida da waje wanda yana da matukar bukatar taimako da surport din mace a bangaren shi.
Rama zaki iya komai idan har kin saka hakan a ranki nasan cewa a yanzu nice ke maki shamaki akan komai da kikeyi don kina kawaici a kan hakan nasani.
Ina mai rokon ki da ki sake jikin ki kada kiyi amfani dani ki cutawa kan ki ki kwato hakkin ki

Download complete TXT · Novel page