Murucin Kan Dutse

Chapter 63 of 146

ga kowa dake son nakasa ki a gidan nan acikin hikima da basira basai kinyi fada a fili ba.
Akwai hikimomi na mata kala daban daban wanda zaki iya don kinga bazan tsaya akan ko yaushe nace sai na tsaya a bayan ki ina fada kinga sai a dauka nice nake saka ki yin wani abin.
Yau ayi va dadi a gidan nan tsakanin besty da hindatu har sai da mahaifan ta suka zo wai akan may zai fita dake bayan ita ce da girki.
Don haka ina son ki natsu ki kiyaye duk abinda zai kawo shiga hakkin wani don ki samu bakin magana idan hakan ya taso a kan ki.
Sai lokacin na daure nai magana ina cewa anty ban san may na tsarewa wanan matar ba nan dai na fada mata irin abubuwan da take yawan yi min tun shigowa na cikin su.
Rama nasan komai bani dai magana ne kawai don naga kina da fahinta irin wanda ake son mace na gari ta dinga yi.
Ba ko yaushe zaka tsaya kana maida martani ba akan abinda ake maka sai idan ka tara rana guda ka tsiyaye shi yafi zafi ga kishi.
Yadda kika rufe ido kika bata amsa daya dayace da maganar data fada maki magana daya yasa ta haukacewa bayan itace ta fara fada maki shi.
Idan ma tayi ne don neman fitina da son musgunawa yanzu tayiwa kanta ai don taja wa kanta saboda ansaka doka a gidan babu mai fita nan da can bada izinin miji ba kuma.
Kamar yadda suka saba a baya sai dai mace ta kada kai tafita duk inda taga dama babu mai magana bayan sun saba da hakan .
Gashi yanzu an saka dokan tabaci a gidan kinga sun jawa kan su ba wani ba don sune masu fita ba wani ba.
Kiyi hakkuri don Allah kinji Rama kada ki sawa kanki damuwa akan komai a gidan nan.
Ki sake jikin ki kamar kowa a gidan kiyi yadda ko wace mace keyi a matsayinta na mata a gurin mai gida bawai ina zuga ki bane kiyi rashin mutunci ga mutane a,a ki dai nuna kema fa mace ce shine zai kwato ki ga wa yan nan don ba fasawa zasu yi ba don halinsu ne.
Amma idan kin faso kema zaki samu saukin cin fuska irin nasu zasu rage maki shakiyancin su sosai zasu san kin iya kema.
Nai ajiyan zuciya don na gamsu da bayanin ta kuma na gane may take nufi da maganan ta.
Nan dai naita tunane ina dan juya spoon din dake hannuna a cikin plate din a hankali naji abincin ya fita raina.
Hiran mama Altine ta dauko min shi ya dan kawar min da damuwan da nake ciki.
Nake fada mata naso Fatima yar wurin maigari ta danzo min zama na kwana biyu sai dai ban fada mata bane kawai.
Tace ai hakan yana da kyau Rama don zama da naka akwai dadi sosai wallahi gashi yanzu naga wata yar kunya da shakku ya shiga tsakani na dake sosai.
Na dago nace kai anty ni kuma tace ke mana Rama in ba haka may zai sa ki boye min abinda hajiya tai maki da wanda matan gidan nan ke maki yanzu.
Nace ba hakana bane anty bana son kina fama da lalurar ki na kuma kara maki wani akai.
Nidai da Allah ya nufa da fanin hakan sai naji dashi tace haba Rama, ya kamata fa ki gode min gaki ga daddy ki lafiya lau bako yadda na tsanmanin kiyi ba ?
Kunya ya kamani sosai na dukar da kaina a jikina nace hai anty idan kuma banyi bakice ban maki mutunci ba fa ?
Tace cikin dariya to aini dai bance komai ba da kina gida kikaga yadda yau dadi ya haukace da fada gidan nan da kin sha mamaki wallahi.
Nace anty ba dai a kaina ba kan sai dai in wani abin can dama ya hada su.
Wanan matar tashi da yake ji da ita ko fa tana abu a gaban shi daddy baya daukan mataki sai dai yai kamar baiji ba ko bai gani ba.
Tace lalai da sauran ki Rama Allah ya taimakeki, baki da rawan kai dakin gane kuren ki ai.
Baki san yadda take taka masu burki bane bai dau yiwa wata wani abin ne a gaban wata hakana sai in kuna ku biyu zaki gane kuren ki ai idan kiyi mai ba dadai ba.
Shi besty mutum ne mai baudadden ra, ayi abu mai girma bai faye bata mashi rai ba sai dan kalin abu don haka kiyi taka tsantsan da halin shi don watan watarana.
Nace ashe haka daddy yake bari na kara shiga karatun na natsu dashi kada na fada watarana.
Kagin tai magana kamshin turaren shi ne ya ziyarci hancin mu sai muryan shi da mukaji yana fadin .
Besty yau kuma gulmana kike yi da kaunar ki haka da kanki besty kike gulmana ?
Tace rufa min asiri don Allah mu ba gulma mukeyi ba hira dai na duniya mukeyi da yar uwata.
Yace in baki hankali ba wanan mai kukan banzan yanzu tana jike ki da hawayen ta don bata da aikin yi ita sai saurin hawaye kan dan magana kadan.
Tace Rama ai ba dai shagwaba ba anan ita kuka Jinior kuka shiko Nasir din ta zuciya.
Nace hai anty har da ke ma gurin min wanan shedan haka ni kan ina nai kukan jinior mai kukan banza yace see you ni wanan kukan ai na kusa maganin shi don ma tsani inga ana kuka hakana.
Dan dago kai nayi cikin kallon mai kama da shauki da ban san ma nayi mai ba nace ni dai ansani gaba cikin shagwaba.
Muka hada ido dashi yana tsaye ya saka hannayen shi ga aljihun wandon shi, wa yasaki gaba yace min yanamin wani irin kallo da baima san yanayi ba cikin so.
Zauna nake dama irin zaman dirsha, na mike kafana ina dan kadawa a hankali banyi magana ba sai yun kurawa nayi zan mike na fice na basu guri.
Sai ya dan jawoni na fada jikin shi wani iri mukaji dukkan mu anty da wani abu ya dan tsikari zuciyar ta don tun shigowan shi ta.
Da sauri ta kawar da kanta daga ganin rugumar da daddy yai min don ba zata iya jure kallon hakan ba ga idon ta gashi ya rike daidai kirjina ya matse ni a gaban shi yana fadin ina zaki sai kin fada min suwa suka saki a gaba nace ?
Cikin tsigar kauna yake rike dani wanda ina ganin ya ma manta da tana gaban shi a lokacin ne.
Muryan anty ke fadin nikan bari na baku guri kada idona ya gano min abinda bashi ba a nan.
Da sauri ya sake ni ya juya gareta yana fadin kiba mu guri don may ke kuma don na rike kaunar ki a gaban ki ko may ?
Tace kai kaji besty kuma da wani fassara dai ni dai bance ba bari na barku kawai nace ma ko ?
Hankalin shi na gurin Anty na samu na sulale falon na nufi part dina, da sauri nima banji dadin kamani da yayi ba a gaban ta don ya barni da nauyi da kunya.
Sai da ya dan juyo ne yaga har nafice daga falon bai sani ba lokacin .
Tace naga kamar ka manta ina gurin ne ai zaka sake layi ba matarka bace ina hanaka rugumar abinka ne ?
Murmushi yayi cikin dan jin nauyi da kunyan ta yasan shima ya dan sake layi a hakan da yayi.
Yace kuna dai da matsala ku mata wallahi, dan rike tan danayi yanzu kuma har kinji zafin hakan bayan ke kika halasta min ita ga hakan.
Maganan dai kake son yai nisa kawai naga alama amma ni na isa na hanaka rugumar Rama ne ?
Kan shi ya girgiza kawai ya juya ya fita daga falon nata itama binshi tayi da kallo don tasan ya kamu da tarkon Rama sosai inbashi ba bai taba rike ko hannun wata mace ba a gaban ta haka balle runguma kuma.
Yana fita falon ta har zai wuce sai wata zuciya tace ya lekani part dina kafin ya bar gidan.
Ina zaune tun shigana part din saman dogon kujera na dan rufe idanuwana ina kallon yanayin fuskan anty na cikin rashin jin dadin abinda daddy yai min a gaban ta.
Banji shigowan shi ba sai jin da nayi ya riko kirjina nai saurin bude idanuwana da sauri nagan shi duke a gabana.
May yasa kika gudu muna magana kuma shine zaki barmu ki taho nan ki zauna kuma ?
Nace daddy agaban anty fa ka rike ni haka kasan ranta ba zaiyi dadi ba ai yadda ka rike ni.
Yace and so what ?
Harda rikeki kuma ba zanyi ba a gaban wani don ina tsoron a kirani mr lover, lover ko may ?
Nace hakan ba dadi ne ai daddy bazata ji dadi ba kaifa mijin ta ne na aure itama kuma matar kace fa ?
Yace ba mai hanani yadda nake so a gidana yana magana yana kokarin kara cusa hanayen shi cikin kirjina a lokacin.
Saukan hannun shi ya sani lunshe idanuwa na tare da fadin washhh, don Allah daddy ka bari bafa a guna kake ba yau.
Yace shine akace don bana gunki kada nayi yadda raina ke so da gidana ko ?
Bai daina abinda yakeyi ba sai cigabama da ya kara na lumshe idanuwa na sosai da kyat na bude baki nace dashi please daddy ka bari mana don Allah haka ba kyau fa ?
Da kyau ya jawoni ya matse ni gam a jikin shi yace haka ba kyau sai may ke da kyau akace.
Rama iam in need of you ina bukatan ki ina son shan wanan abin sosai a jikin ki ina jin dadin hakan kina da matukar dadin al, amari Rama.
Ganin yana kokarin kauce hanya yasa na saurin dan dukawa na zille daga jikin shi nai kasa ya dan kalle ni a kasalance yace rowan su zaki yi min nace inda kake ma yau akwai irin shi a can daddy kada kasa muyi sabon Allah please.
Ajiyan zucita ya sauke tare da kada kanshi yace banzaci zaki hanani abinda zuciya na ke muradi ba.
Saboda ke na kasa tafiya aikina ina jiran dawowan girki na dana na wuce abinda ka fisheni Rama.
Nace daddy kaji ranan ai ba yawa yafi mu fada ga sabon Allah haka ba kyau ai kasani.
Baiyi magana ba sai gyara kwalar rigan shi yayi yadan kalleni ya juya ya fice daga dakin nawa kawai.
Nabishi da kallo ina jin wani abu a raina shin dadin abinda yai min ne ko tausayin halinda yake cikine a lokacin bandai sani ba..
Daga haka na mike na shiga ban daki na dauro alwala har nai sallah ban daga ba ina wurin a zaunr kunya da nauyin yadda zan fuskanci anty nake ji lokacin.
Babu yadda zanyi dole na mike ina saye da hijjabi mai hannu a jikina na nufi part din yara na samu sin dawo.
Na shiga suna ganina sukayo kaina kallo daya naiwa jinior na fahinci baijin dadi da sauri na karasa gun su na dan riko shi ina tambayan shi may ke damun shi ne ?
Sai ga uwar tafito daga daki itama bata kwabe bijjab din jikin ta ba da tai sallah take cewa ni koro shi ina sallah yazo yana damuna.
Nace anty jinior fa baida lafiya ne, tace lafiyan shi lau kalau yake fushi yake na koro shi kawai.
Najawo yaton zuwa jikina inda nake tsugune nace ga jikin shi da zafi sosai tana kokarin gardama nace maike damun ka jinior yace goshi na ke ciwo nace da ina kuma ?
Ya bude baki zai min magana sai amai yazo mai shar ya amaye min duk jikina da amai ban damu ba duk na rude na da sauri itama ta karaso tana cewa ikon Allah.
Har ina gardama ashe ko baijin dadin jikin shi ne haka banyi ta kaina ba sai da na tube yaron na goge mai jikin shi nace gajiye don Allah dauko min rigan shi da sauri daki.
Ta fice ta dauko rigan na saka mai na kwantar dashi namike na cire hijjab dina daya baci da aman yaron.
Dagani sai dan karamin riga daidai cibina sai dogon wandon dake jikina surar jikina ya fito gwanin ban sha,awa dashi.
Na dan duka gurin yaron dake kwance ya dunkule a guri daya ina dan tausa mai cikin shi a hankali.
Daddy ne kaman an jefoshi falon a lokacin ya shigo yadda ya samay mu mu uku akan yaron ne yake tambaya tun bai karaso ba mai ke faruwa ne kuma.
Juta mukayi inda yake tsaye yanan shigan shi ya nuna ya dawo ke nan ba zai fita ba kuma indai kagan shi a cikin jallabiya a jikin shi.
Anty ce take cewa baida lafiya ne sai amai yake ta faman kwararawa tun dazun.
Ya nufo inda yaron yake ya dan duka gareshi tare da kura mai ido kamar yana nazarin shi.
Inda nake ya jiwo yana may ya samay shi yanzu yanzun fa na dauko su daga islamiya lafiyan shi lau.
Fever ne ya kama shi ina ganin sanyin da akayine ya dake shi hakanan.
Yace sai da nai magana da na ganshi da dan riga karami haka a jikin shi wanan wani haline irin sanyin da akayi yau za, a sawa yaro wanan dan riga haka ?
Yanzu gashi anja mai ciwon haka ga banza saboda rashin sanin zafin kai don may baza, a kula da yaro ba irin wanan ?
Gajiye dake daga gefe itace ta saka mai kayan a jiki da zai fita tace cikin sanyin murya wallahi shi ya matsa sai su yake so.
Yace don ya matsa shine dole sai su za, a saka mai baida wasu masu nauyi ne da za, a biye mai son ran shi haka ?
Ranan munga fadan daddy cikin bacin rai yace a shirya shi su kai shi asibiti a gani .
Ni dai ina gefe na makure guri daya don ya bani tsoro yadda yake faman fada haka ido rufe kamar yaron ne kawai dan shi kwaya daya a rayuwan shi.
Tare da anty suka fita sai bayan fitan su na sauke ajiyan zuciya.
Sai wani lokaci suka dawo gidan yaron ma yayi barci yasha allura da magani.
Naso na kwana gurin shi amma anty ta hana tace naje na huta ba ga gajiye nan ba gobe akwai makaranta kada na wahala.
Washegari tunda safe na shigo duba yaron yana barci har lokacin na dan dade tsaye anty tace kada fa ki makara Rama.
Koda naje school sai da na bugo wa anty waya ina tambayan ta ko ya tashi yaci abinci tace gsshima zaune yana shan tea zamu koma dashi asibiti idan baban su ya fito.
Haka yasa hankalina ya dan kwanta naci gaba da karatuna don Allah ya gani har cikin raina ina matukar jin yaran anty a raina.
Ba dole na so su ba so kuma na tsakani da Allah ni da uwarsu taiwa hanyan alheri a duniya iri iri wani ma ban iya tuna shi.
Sai shidda saura na shigo get din gidan na kai motana inda ake aje mota na aje na fito tare da dan tsayawa ina kwaso takardun dana dawo dasu daga school din.
Sam ban kula da suna gurin ba sai dariyan su da naji a lokacin yasa na dan dago kaina su biyu ne a tsaye da gani rakiya tayowa kawar ta wacce na sha ganin ta tana zuwa gidan gurin ta sosai.
Daga inda nake ina iya jiyo hiran su bawai a, asirce suke magana ba yadda zanji suke maganan.
Kai maza ho shi wai farin fatan ne yaha shi a nan ko may wai ?
Hindatu tace kin san yan kauye kamar dabbobi suke basu san makwancin da ya dace da su ba ko ina sai su dauka matsayin su yakai su shiga.
Wani za ai wa bRkado kila haka taga anayi a gidan ubanta zama da cin amana don rainin wayo ni da girki ki sa min miji gaba ki fice dashi wai ita karamar yar iska.
Wallahi jira nake ta kara gigin fita dashi taga yadda zan mata a gidan nan sai ta raina kan ta yar jakar uba kawai.
Ni duk iskancin da rawan kan da yake a kanta kar nake kallon su bawai na kyale bane a banza shiri nake kafin na fara aiwatar da nufi na yar abu kazan uba.
Zuciya ne yazo min na karasa fitowa daga cikin motan kawar nata tace ashe ba matar so bace tunda ya barta tana shiga wanan motar da ya sha jiki.
A zuciye na karasa fitowa na aje takarduna a cikin mota tare da gyara saitin hijjab dina na ce hindu kike ne ko wa ?
Idan baki aiwatar da nufinki a kaina ba ashe ba Adamu kwangila ya haife ki ba.
Yar kauye nake kuma Allah yai min zaben makwanci daidai dani don ban raina da kyautan Allah ba akaina.
Ni kika zaga lalai yau akwai balai gidan nan nace bala,i a kan ki keda kika kirashi mahaukayiciyar banza da wofi ke wakika fi kishi da hauka.
Shiru shiru ba tsoro bane wallahi ke kuma tsohuwar kilakiya na fahinci aure ta gagare ki sai yawon bin gidaje kina kashe aure mota kika ce ba, a canza min ba ko may ?
Nace na baki sati biyu ki dawo zaki sha mamaki a gidan nan don kin sara a kan gaba ko .
Nace dibeku don Allah idan ni farine ya rude shi a kaina ke may ya rudeshi a kanki shafafen baya ko shafafen gaba mace haka kamar an daurawa kara zani dake.
In ba halin aure ba ko auren ma na cinne ai ko a kafa daddy ba zai jaki ba nai tsuki na kwashe su na watsar na juya zan shige naji motsinta tanufoni a zuciye .
Shiryawa nayi da nufin

Download complete TXT · Novel page