Murucin Kan Dutse
Chapter 78 of 146
sallah daddy.
Wani kallo ya watso min na noke kaina a kasa sai naji ya jawoni zuwa jikin nashi ya rugumay ni yana sauke numfashi.
Daga tsaye ya shiga lugwigwita ni har muka kai saman gado duk tsoro da imani ya na cin zuciyana.
Sai da ya tabbatar da ya samu natsuwa a gareni ya sake ni yana mayar da numfashi a hankali.
Ya dan jima a zaune ya dafe kan shi da hannu daya, ina kwace na kura mai ido baiyi magana ba zuwa can naga ya mike yace dani thanks ya mike ya fice na dade kwance da kyat na mike na rufe kofan part di na ina tunanen ina matar shi don nasan mace yake bukata haka.
Har barci ya dauke ni ina tunane may ke faruwa tsakanin daddy da matan nashi ne yau haka a gidan.
Washe gari barci na nayi sosai ban fito ba sai shadaya na mike nai wanka na shirya na nufi wurin anty.
Ina shiga take cewa dani yau wani irin barci ne haka gida ya hargitse muna da rikici haka ba dadi .
May ke faruwa ne anty tace besty ne mana da matar shi suke rikici tun asuba ne ko daren jiya ban sani ba wai ya rufe kofa ya hanata shiga gun shi.
Yau kuma da wanan fitinan muka tashi kuma tace ke dai bari Rama na rasa may ya kawo masu wanan rikicin ne haka ?
Shiru nayi ina tunanen abinda ya faru a daren jiya tsakanin mu dashi daya zo min a bukace dashi.
Ban daice ma anty ga abinda ya faru ba tsakani na da daddy daren jiya don da kunya ma koda ace a wurin wanj ta samu wanan labarin.
Ban dade ba na koma wurina, sai gashi ya shigo yace ki shirya zamu bi jirgin yamma zuwa lagos yau din nan.
Na mike daga kwance na zauna ban kuma yi magana ba sai nai shiru don fuskan shi babu annuri a cikin sa.
Bayan ya fita na mike zuwa wurin anty na sheda mata zancen tafiyan sai take cewa yau zai tafi ke nan ashe ?
Nacd haka yace dani tace to sai ki shirya ke nan ko kafin yamma yayi jiki ba sukuni nafice na samu Fatima ina mata bayani tafiya na.
Ita ta shirya min kaya don dai ni ban so binshi ba bana son abinda zai taba min karatuna ko kadan.
Yadda yace haka akayi don magariba muka bar gida nai wa anty da yara sallama babu wacce na sallama a sauran matan don banga amfanin hakan ba gareni.
Don ka dawo basu taba zuwa su gaida kai da zuwa ko su fada ma zasu tafi don haka nima nasa a raina babu wacce zan kara sallama.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE, , , , , , ,
IDAN KON BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH DON ONLINE NOVEL NE KIN SANI, , ,
57
Zaman mu a lagos bazan iya cewa ga irin dadin da nasha ba a gurin daddy don ya nuna min karamci sosai a wanan tafiyan da mu kayi.
Banda wani damuwa sai idan ya fita tun shidda na safe baya dawowa sai shidda na yamma daga hakan muna tare bai fita kuma ko ina sai washe gari haka yasa shakuwa sosai ya kara shiga tsakanin mu sosai.
Don zamu zauna muyi hira inta zuba shagwaba gareshi abinda ban samu ba a gida yanzu na samu a nan wurin shi da muke mu kadai.
Ina ji tankar a ce haka zaman mu zai dore a haka har abada don bani da damuwar komai a hakan da muke anan.
Sai nake ji a raina macen da take daga ita sai mijin ta a gida ta more miji don dai ni sai nace ban san dadin aure ba a hakan.
Sai da mukai sati uku a lagos mukai haramar dawowa gida kano gurin yan uwa.
Matar abokin shi ne tazo har masaukin mu ta dauke ni muka shiga kasuwan lagos inda na narka kudi na na kwaso les da sauran abinda nasan zasuyi saurin shige min a gurin mutane.
Na sawo wa yara na kayan masu kyau da tsada da abubuwan da bamu dashi a nan na sayawa Atika kayan yara mata masu kyau a cikin rahusan kudi mai sauki har yaran su Zulfa da hindatu sai da suka samu tsaraba na duk da nasan akwai matsala a gurin karba.
Ba karamin alheri na samu ba a wannan tafiya da mukayi da daddy haka yasa na kara fahintar dalilin da yasa matan shi ke son yin tafiya dashi don daddy yana sakarwa mace hannu idan yai tafiya da ita sosai.
Kayan mu sun riga mu shigowa arewa don sai bayan kwana biyu muka dawo mu da karfe uku na rana muka sauka garin kano.
Duk kyau da tsarin da gidan dadi ke dashi sai dana raina hakan don abinda nagono a tafiyan mu din.
Na samu taro sosai a gurin anty babu wani canjin fuska dana samu a gurin ta da murnan ta, ta tare ni.
Nai wanka nai sallah ta turo gajiye har part dina ta gabatar min da abinci na kaiwa maigidan.
Shima na samu yai wanka a lokacin tare muka ci abincin rana dashi sai kuma wanan lokacin da muke tsaka da cin abincine matan gidan ke shigowa yi mai sannu da zuwa.
Babu wacce tai min an dawo lafiya nima ban damu ba da hakan don na riga dana saba da wanan halin wurin su haka ake tafiya.
Yar wurin zulfa ce ma take mika min hannu na dan mata wasa daga hannun uwarta ina cewa babby mun samay ku lafiya ?
Sai uwar tace kalau muke ba ta kuma tsaya ba tai mashi a huta gajiya tabar falon inda muke zaune muna cin abinci.
Kai ya girgiza kawai yace a fili kukan kuna da matsala wallahi ban ga ranan da zaku daina wanan halin kishin tsiyan ba haka ?
Kamar nai magana sai dai na daure ban taka shi ba kada na ja zancen da nisa na hade komai a raina muna gamawa dama a gajiye nake na kwashe kayan zuwa ciki sallah nayi tun wurin ina addua barci yake sata na.
Barci nayi sosai a kasa saman carpet din sallah har sai gab da magariba ne fatima ta shigo ta tayar dani sai dana tashi take fada min daddy ya shigo ya samu ina barci amma ga kaya nan an shigo min dasu part dina.
Ina alwala naji shigowan yaran da murnan su sunzo taro na ina fitowa duk sukayo kaina suna murnan gani na.
Sai da na sallamay sallah na sa Fatima jawo jakar dana zuba tsaraban su na ba kowa nashi haka suka koma fun uwarsu da kaya masu yawa a hannayen su.
Kusan tare muka shigo da jinior na dauko mai kayan wasan shi ina jin anty na fadin wai ita Rama bata gajiya da lodo maku tsaraba haka ne duk tafiya kamar don ku takeyin shi.
Na karaso ina cewa haba anty indan ban masu tsaraba nayo mawa balle kudin uban su ne ai anty.
Tace ke kika san wanan Rama idan bake koni mukai tafiyan ba dashi ina zasu samu kaya haka wani magani na miko mata nake mata bayani yadda akace tayi dashi.
Bataki ba ko ta zargi wani abu daga gareni tun a gabana naga tace gajiye ta bata ruwan dumi ta fara sha tasha shi sosai muna hira ta soma cewa zatai fitsari kamar yarda mai maganin tace zatayi da kuma barci.
Hakan kuwa akayi na ce gajiye ta zauna a dakin da ita na kwashe yaran muka nufi part dina acan muka kwana tare dasu.
Da safe ina idar da sallah na fito, zuwa dubata na samu gajiye na kokaein azawa yara abin zuwa school muka gaisa da ita nake tambayan ta yadda suka kwana ?
Tace kai ai hajiya jiya batai barci ba ta kwana kewayawa fitasri ne harda gudawa ma tayi.
Koda na shiga na samu ta dan samu barci nafito na taya gajiye aiki na koma na shirya yaran don kada su makara zuwa school.
A gurguje na shirya suna ficewa nima na shirya na bar gidan zuwa nawa karatu.
Na sha fada sosai a gurin course mate dina don suna ta fadin wai ni da nake serious a da can baya yanzu ina wasa da karatuna sosai kuma.
Haka na dage da karatu na mayar da hankali na sosai don kada a barni baya ga karatuna sosai.
Ban dawo ba sai yamma lis na shigo gidan a gajiye dani part din anty na yada zango na samay ta kwance saman three seat tana jin sallama na ta dago kai tana min sannu da dawowa na zauna ina fadin wassh tace ai dole ne.
Nake fada mata sati biyun da nayi na samu an wuce ni sosai a karatuna, take cewa dole ne Rama nima sai da nai magana a kan hakan abune dai da baka da ikon kan ka amma zanyi magana da maigidan insha Allahu ya dinga sanin abinda ya kamata ayi.
Take cewa dani dazun kin fita kin barni na dan samu barci wanan maganin dana sha jiya bai barni nayi barci ba sai fitsarin da nake yi.
Nace dama haka mutumin mai magani yace min idan maganin ya karbi mutum zai dinga fitsare cutar dake a jikin shi.
Tace jiya kan nasha bauli ba kakatawa a gareni Rama har sai da naji tsoro sosai.
Amma wanan maganan da ki kayi yanzu ya sa hankalina ya kwanta sosai da jin bayanin hakan.
Take cewa ni masu fitinan nan na kullun suka tayar dani daga barci na da na keyi.
Cikin mamaki na juyo gareta nake tambaya nace fitina kuma akayi a gidan ne anty ?
Tace akan ki ba ai kema kin san cewa da duk ku kai tafiya sai anyi fitina saboda ke a gidan nan.
Nace a sanyaye ni kuma anty ?
Tace ke mana Rama kin san su zasu iya saka ido akan mutum amma shi mutum bai damuwa da abin da suke ciki da miji ko yaushe.
Tai tsuki tana cewa sunce idan kunyi tafiya sai ya kashe maki makuddan kudi masu yawa da baya kashewa mata shi.
Tace bari Rama yau naji abin mamaki sosai a gidan nan gurin mutanen nan ashe ba karamin kudi matan nan suke karba gun mutumin nan ba haka.
Yau da Allah ya kama su kinji yadda yake masu fallasa ai sai da sukayi dana sani yace daga yau idan ba gaba daya zai ba da abuba ba zai sake ba ko wace mace kudi ba komai lalurar da tazo mai dashi a gurin shi.
Ajiyan zuciya na sauke nace anty zato zunubi su a ganin su gun daddy na samu wanan kudin haka nai sayayya dasu ko may ?
Tace in ma a gunshi kika karba Rama ina ruwan su da hakan ne wai su udan sun fita dashi wayan san abinda sukeyi a can din.
Yanzu ai ya basu amsa don yace kin mai daidai don haka yake son gani idan yabawa mace kudi yasan inda suka shiga ba gobe sai anzo tambayan shi ba alhalin bai san may ake da makudan kudi hakan ba masu yawa .
Wai Rama kiji matan nan fa, da kuma namiji munafuki wai ashe har wani kudi yake basu na sayan kayan need din su da bai ba mu anan.
Nace cikin mamaki kamar ya anty tace wai na sayan pad da kayan makeup ko da may ye ma don ni takaici ya hana na tsaya na saurare su ma na dawo nan abina don dashi dasu duk haushi suka bani.
Tace ni dama nasan karya ne in bashi ba a ina suke samun wanan kudin da sukewa mutane karya haka dashi ?
Anty kiyi hakkuri akan wanda kike dashi mai hakkuri yana tare da Allah ai da baki da amanan su ai gashi yau kowa yaji may suke ciki kuma ai sun wa kan su in sheri ne don kowa yaji may suke ciki yanzu ai.
Wai ma don ya mayar dani van san ciwon kaina ba Rama sai gashi wai yazo min da maganan su nai banza dashi ya karaci zamqn shi ya ban guri don ni banga abinda zai fada min ba kuma na yarda dashi.
Na mike na cewa anty bari na shiga naga mutane na nadan watsa ruwa na fito sherin su dai a kansu zai kare ai.
Ina fita na shiga part dina na samu su Fatima zaune suna kallo suna ganina sukai min oyoyo da gani na.
Tambayan su nake ko sunci abinci suke cewa dani sun dafa sunci don yanzu suna girki abinda suke so a waje na.
Ban tsaya ba na shige dakina na shiga wanka na fito sallah aka fara na shiga yi.
Ban daga daga wurin ba har sai da na idar da sallah nai shafa,i da wutiri na mike fatima na kira nace ta fitar da kayan na gani nan muka baje komai na kwashi tsaraba na da anty da sauran na yaran na shiga wurin anty da su.
Tana daki anan na zube kayan falo na samay ta a cikin daki ta idar tana addua na shiga gun ta.
Ta shafa take cewa har kin fito ne Rama nace eh anty dama tsaraban da na sayo ne na kawo maki ki gani idan sunyi maki.
Ban da na yara har da kuma ni Rama abin ai yayi yawa dai ko nace haba anty yawa kuma fa akan ki abu zai min yawa anty ?
Aiko da na zama butulu gare ki anty aduniya akwai abinda zan maki wanda zan iya rama abinda ki kai min a duniyan nan ?
Kai haba dai ki daina saka wanan a ran ki mana, Rama ai hakan hukuncin Allah ne ba yina bane.
Ni fata na yanzu shine Allah yabaki naki rabon a gidan nan nima naga jinin ki a cikin gidan nan kamar kowa.
A cikin raina na karba mata da amin amma a fili murmushi kawai nai mata nace kai haba anty muje kiga kayan a falo kada mu bata maki guri nan.
Tana fitowa taga kayan take cewa kai kai kai Rama wanan kayan haka duk a lagos kika samo su haka waya na daga na kira Fatima nake cewa duk su kwaso sauran kayan su kawowa anty ta gani.
Nai mamaki danaga tana jidan kayan kitchen din da nazo dasu sai bayan ta gama zabe tana ta yabawa da kyaun kayan haka .
Take cewa kin san ina da amare har biyu shiyasa na zaba masu ba sai munje saya waje ba daga baya.
Amare a ina kuma anty tace gajiye da Fatima mana Rama ai dole nice uwar amaren dai ina ce.
Shiru nayi mamaki ya rufe ni na hali irin na anty ko ni da Fatima take guna banyi wanan tunanen ba haka.
Amma saboda salihanci irin na anty sai gashi ta ita tayi wanan dabara ganin nayi shiru naji tana fadin Rama kin fasa abinda kaiwa wani a duniya shine rabonka a lahira walau sheran ko hairan don haka don Allah ki barni na samu wanan ladan na alheri dana sawa raina.
Wanan shine kadai abinda mutum zaiyiwa wani mai bukata na kasa dashi ya tsira ga ubangijin shi.
Don haka gobe zan baki kudin kayan ki sauran list din abinda nake bukata garesu kuma akan su duk kece zaki sawo Rama na saya a gurin ki wanan alkawari ne naiwa raina hakan.
Shiru nayi duk imani da tausayin ta ya kamani sosai sai tunane nake wai ita wata irin mutum ce a duniyan nan cikin mata ?
Bata fita ko ina tana gida anty time tana bautan Allah da auren ta haka kuma abinta ban taba ganin ya rufe mata ido ba ita a rayuwan ta.
Sai naji tana ta faman yaba kyawon les din da na sayo muna tace kuma kayan yara sun matukar burge ta a rayuwan ta.
Muna cikin fira sai ga maigidan ya shigo fuskan shi a daure murtuk dashi dagani har wanan lokacin ranshi a bace yake mai.
Gaishe shi muke yi daya bayan daya yana amsawa kamar baya son amsawan a lokacin.
Tambayan ko kayan may ye wanqn haka yayi take cewa kayan da Rama ta saro a lagos ne mana.
Inda nake ya juya yana cewa ke har yaushe kika samu sayan wa yan nan kayan haka cikin mamaki ?
Nake cewa dashi da muka tafi da matar Adebayo ne ta kaini na sayo su a can.
Yana tafiya yake cewa kada fa ki ce zaki fara shiga Dubai wanan abin dana gani haka fa ?
Dariya duk wanda ke falon yasa saboda maganan shi sai anty ke cewa aiko bataje ba sai tai oda kuma su shigo mata yanzu akwai hanyar bussines ai a cikin sauki masu yawa.
Ya har falon mukaci gaba da harkokin mu sai dare na koma ni da su Fatima part dina gan kwanta ba karatu na shiga yi ina nazari saukina abinda na koyo da muka tafi chaina dashi ne akayi bana garin.
Washe gari ban tsaya ba na loda kaya a mota na fice gidan Allah ya taimakeni tun a mosque da mukaje sallah nai ciniki sosai an kwashe lace din dana fito dasu ranan gaba daya har ana nema don kyaun su.
Na dawo gida nagaji mukai kicibis da Zulfa yarta na wasa a haraban filin gidan ina ganin ta na ja burki sai da aka dauke yarinyar na karasa inda nake aje mota na.
Na fito ganin Zulfa duk da nine na fito unguwa ya kamata tai min sannu da zuwa a lokacin amma na san bazan samu hakan ba a gareta na daure na gaida ita da gida.
Maimakon ta amsa min sai cewa tayi amma tukin naki Rahama ya zama na ganganci zaki shigo kin san akwai yara a gidan zaki kwaso haka a guje nikan ki rufa min asiri kada ki mayar dani baya please ?
Mu