Murucin Kan Dutse

Chapter 77 of 146

ma inda halin hakan don duk wanda ya baka kadan akwai ranan da zai baka babba ai.
Yana gamawa ya hawo gadon yana cewa kin fadawa anty ki zancen ginan da akewa baba ne nace ban fada mata ba tukun.
Yace wani amsa kika shirya bata don kin san zataji ko tagani ranan da duk mama Altine tazo garin nan.
Shiru nayi don nasan maganan shi gaskiya ne yace sai ki ce da ita kudin kine tun tuni kike tarawa kikai aikin dashi.
Nace dashi nagode na lumshe idanuwana don sai godiya nakewa Allah da ban fada mata komai ba tun farko tunda nagane bai son asan shine ya gyara muna ko may yasa oho.
Kamar ya karanci zuciyana sai naji yace bana son abinda zai kawo bacin ran wani daga cikin ku ne.
Kuma ya kamata a taimaka masu duk da nasan ina da amsa ga kowan su don ba wanda banyiwa shigen hakan ba daga cikin su.
Gori da habaici irin naku na mata ne ban so ga alheri idan nayi shiyasa ban son yawan surutu haka.
Daga haka ya rungumoni nan wasa ya canza sallon shi ranan daddy ba karamin jirkita ni yayi ba don kamar ya zauce min ya koma a ranan da kyar na samu ya barni na huta.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA DON CIN AMANAN ALKAWARI DON KIN SAN ONLINE NOVEL NE, , , ,
56
Washegari nafito shar dani cikin dogon rigar material kayan sun matukar karban jikina sosai.
Nayi kyau dani kaina na sani don na bata lokaci wurin shiryawa na samu an hada breakfast dan fruit na hada mai da ferfesu.
Nakai mai har lokacin daddy yana kwance bai tashi ba na shiga na hada mai riwan wanka a bathroom.
Inda yake kwance saman gado yana barci na nufa na zauna a bakin gado nafara ja mashi dan yatsun kafan shi a hankali.
Da kyat ya bude idanuwan shi ya sauke su a kaina nace daddy ka tashi kaje ka duba yadda baba ya kwana don naga ko jiya yana dan jin jikin nan nashi.
Ya gyara kwanciya gami da mika yace dani da safe haka Rama ?
Daddy tara fa ya kusa yanzu ai gara kaje ka duba shi don hakane kawai yanzu tsakanin mu dasu.
Murmushi yayi ya jawo ni zuwa jikin shi yace kwalliyan nan naki ya burgine sosai Rama.
Nace nagode daddy Rama ban san godiyan da zan maki ba a daren jiya kin mantar dani duk wani tarin matsalolin dake a cikin rayuwana.
Kunya naji na noke kaina kasa yace Iam telling you the true kina sani a farinciki ko yaushe wanda ni ban san dalilin shi ba Rama ?
Na dan yi kokarin raba jikina da nashi sai naji ya kara matse ni yace da ace zan san wake gyara min babby na haka ko yaushe zan iya yi mata kyauta a rayuwana.
Nagane so yake ya gane may ye sirin nawa sai nace cikkin dariya daddy ka godewa Allah don shine yai min hallitta na hawainiya kila mai canza kama ko wani lokaci.
Rama ya fadi a kasalance na amsa a hankali yace bana so kina fushi dani kina min rowan farin cikina a kan ki.
Baki san irin halin da kika jefa daddy naki ba yan kwanakin da suka shige ko kin saka ziciya a cikin garari a gidan nan ?
Bana so kina daukan zafi haka dani bake ba duk wanda ke a karkashi bana son ya bata ran shi a kaina ko kadan.
Wanan dalilin yasa nabarki kije gida har tsawon kwana hudu don ki samu ki huce ko zan samu kwanciyan hankali.
Bana so ina fadi mutum yana fadi nakan ji zafin hakan a raina sosai gashi harkin hasalani nakai ga taba lafiya jikin ki wanda ko yaushe nakan kalli hannuna dana daga na mare ki da shi a matsayin bai min adalci ba ko kadan.
Kara lafewa nayi a jikin shi nace daddy ni yar kace daka raina da hannun ka kuma yanzu ina a matsayin matarka don haka kana da ikon daukan ko wani irin hukunci ai a kaina don ka cancanci yin hakan a gareni.
Idan babba bai nuna matsayin shi na babba a na kasa dashi ai ko yauahe karami baya sanin yai laifi don haka nima ina mai baka hakkuri da kayafe min duk abinda nai maka a lokacin.
Sai dai ba yina bane don a lokacin wani irin yanayi nake ji a kan ka daddy ina jin zafin ka ina jin takaicin ka fiye da kima raina yana matukar baci sosai koda kuwa sunan ka naji an ambata min.
Sai naga ya dago ya kalleni kadan ya mayar da kaina a saman kirjin shi ya sauke ajiyan zuciya bai yi magana ba sai dai ina jin yadda kirjin nashi ke halbawa sosai can naji ya sauke ajiyan zuciya.
Yace, Rama akwai matsala a wani wuri don abinda kike ji nima din shi nake ji sosai a raina akan ki sai da nayi kokari na sa ai min rokon Allah don na dan samu sauki don gaskiya koda zamu zauna a hakan ba zan iya rabuwa dake ba a rayuwana.
Yace na kuma ji dadin fada min sirin zuciyar ki da kikayi don haka shine zama na tsakani da Allah halinku ne na mata shiyasa ko yaushe bani zama ban saka an min sauka ba akan iyalina dani kaina don neman kariya daga fititinu masu haddasa fita a tsakanin ko da yaushe.
Rama ina son ki nima nasani wanda hakan yakai ban iya boye hakan a gaban kowa duk yadda naso na boye irin yadda nake jinki a raina ba zan iya hakan ba a gareni.
Don haka ki kara hakkuri akan wanda kike dashi ki zama mai juriya akan komai ki kawar da idanuwan ki akan kowa a gidan nan.
Nidai ke zama daku nakuma san halin kowace daga cikin ku ance kowa da halin shi ake zama dashi ai.
Kin min abin da yasa raina jin dadi a daren jiya kin gwadawa duk wanda ke guri ke yarinya ce mai tarbiya da sanin yakamata.
Ba komai ba sai daraja min iyayyena da kikayi a gaban kowa wanda nasan ko a bayan mu zasuyi magana a kan hakan da kikayi nakin zama aaaman kujera suna sama su ma.
Don haka shine girmama iyayye da daraja su wanda matan yanzu basu san barin haka a gare su wani sakaci bane maigirma sun dauki yin hakan garesu a matsayin wayewa ne.
Kin ba Alhaji zuma wanda har yasa ba Alhajin ba har hajiya saida taji dadin hakan da kikai masu nagode Rama Saade ce kadai a cikin ku takewa mahaifana haka a baya yanzu kuma naga ta daina hakan itama.
Amma ance shi alheri ko sau daya kaiwa mutum bazai taba mantawa da shi ba a rayuwan shi.
Nai murmushi nace daddy kakanina ne fa kuma iyayye na don may nai masu alherin don su saka min albarka har zakai min godiyan yin hakan da nayi albarkan su fa nake nema nima ?
Murmushi yayi yace dani ai kin samu kuwa Rahama don Alhaji ya saka maki kwado kwado.
Daddy tashi kai wanka ruwa yana jiran ka a ciki tun dazun yace bakya so na kara shakan kamahin matana naji dadi ne bayan kwana biyu an hana ni jin dadi da abata.
Murmushi nayi na zare jikina daga nashi na mike ina cewa Allah ya kaican yana hanaka jin dadin abinda kake so ai.
Bayan yai wanka ne ya karya bai tsaya ba ya dauki key zuwa ganin Alhajin nashi har mota na raka shi saida ya fice gidan na juya zan shiga ciki.
Hindatu ce a tsaye ta dafa bangon gina tana min kallon harara ko ajikina nace a raina sai dai ruwan idon ki ya tsiyayye.
Ban bi ta nata ba na shige abina na barta a wurin ta bini harda zagi ni dai na shige abina.
A can part din anty na shige har lokacin bata fito ba na juya zuwa daki nawa part din.
Ban dade da shiga ba sai ga gajeye ra shigo wurina tana cewa dani hajiya Rahama dama ina jiran ki huta ne muyi magana dake.
Nace gajiye lafiya dai ko ?
Tace dani bakomai sai zance na da maigadi gashi ya matsa min yana ganin nice tare da ku yaji har yau ba wani zance akan maganan mu.
Na nisa nace hakane ai baki ma san wani abu ba wani sabon zance tsakanin Fatima da Hamza driver.
Tace ashe kin sani Hajiya nace wanan tafiyan da mukayi ne na fahinci akwai matsala a tsakanin su.
Nace ni yanzu Gajiye ba wai naki hakan bane kinga ga naki zancen ya shafe ni kin dai san halin matan gidan nan cewa zasuyi munga wuein ci munzo mun tare wa mutane haka a gida gaba dayan mu
Wanan kan zasu fada don fada don basu raina magana su nace ni indai haka bai zama matsala ga maigidan da uwar dakin mu ai suje suyi ta fada kawai.
Yanzu ki bari idan daddy ya natsu zan fito mashi da maganan ai muji may zai fada akai don ayita ta kare .
Tace bari ta koma kada uwar dakin mu ta falka bata kusa tana fita na koma na kwanta don a gajiye nake a lokacin sosai.

********* ********* *********
Ya shiga gida da sallama ya samu daddy da hajiya zaune suna karyawa tana bashi abinci, a hankali ya shigo da sallaman shi duk suka bishi da kallo don bai saba shigo masu wanan lokacin ba hakan.
Sun zauna da shi suka gaisa yake tambayan yadda mahaifin nashi ya kwana da jikin shi hajiya tace da sauki sai dai cikin dare jikin ya dan motsa mai Allah ya taimake mu zumar da wanan yarinyar takawo muna yana nan shi muka samu mukai amfani dashi Alhamdullahi sai ya samu sauki yai barci sosai sai yanzu ya falka shine yake girkawa.
Alhaji ya dan gyara zama yana cewa da kyat wanan yarinyar Allah yai mata albarka na dade ina neman zuma na sahihi na kwarai ban samu ba ko wani aka kawo baida kyau yana da dan hadi acikin sa kuma sai mutum ya rantse ai mai kyaune nashi .
Yanzun da Alhaji ka gamsu da wanan din da Rahama ta kawo ma ke nan ko ?
Yace ana magana zuma ne mai kyau sosai wallahi, Allah dai yaiwa wanan yarinyar Albarka kaita hakkuri da abinka yarinyar nada kirki wallahi sosai.
Ga mamakin sai yaji hajiya tace tana da tarbiya kan gaskiya ji jiya su fitsararun ma zaman gwada sa,a mukayi dasu amma ita ina lura da ita tun bata aureka ba bata taba zama dakai a saman kujera in kuna tare.
Yace ko a kaina haka take bani zama ta zauna kamar sauran yanzun haka ma ina barci ita ta tayar dani da ga barci nazo naga lafiyan Alhaji yanzu don taga alaman mun barshi yana jin jiki.
Yace tagani ne don duk hiran da ake tun lokacin nake jin jikin na motsa min ban dai yi magana bane.
Daddy bai dawo gida ba sai da ya shawo kan Alhaji suka koma asibitin aka duba jikin shi sun fito suka hade da wani abokin daddy yake cewa ai idan daddy nason yayi lafiya to ya samu daddawa na ainihi wanda baida surki ya dinga cin miyan shi da kayan yaji sai kuma ya samu rake ya zauna yasha shi sosai insha Allahu jikin zai kara yi mai sauki.
Tun da suka dawo ake neman daddawa mai kyau da za aiwa Alhajin amfani dashi basu samu ba.
Muna zaune da anty muna hira nace anty na manta na fada maki ai na hada dan kudin dake a wurina na bayar anawa babana gyaran gida dashi.
Nan dai nai mata bayanin komai tace kai amma ko kin kyauta wallahi Rama shine baki fada min ba nace sai yanzu abin ya fado min a raina ai wallahi.
Mu kai ta hiran akan rashin lafiya ta nake ta bata karfin gwiwa tun tana murmushi har tana daukan magana ina dai yi ne amma dana matsa sai jikin ta yai sanyi ta gamsu da magana ya kara mata karfin gwiwa sosai a ranta.
Haka maigidan ya shigo part din ya samay mu tana zaune a three seat ni ina kwance a kasa daidai kafan ta sai hira muke zubawa da dariya a tsakanin mu.
Shigowan shi yasa na dan mike zaune, muna gaidashi ya zauna yana cewa may yai maku dadi kuke kwasan dariya haka tundaga waje anajin muryan ku haka ?
Kai daddy yara wanan dariyan ne har yakai waje inji anty ke fadin haka cikin dariya.
Hira dai muke ni da kaunata abin ya bamu dariya ne shine kaji muna kwasan dariya haka.
Yace to nima gani ai sai ayi hiran dani muyi ta dariyan ko dariya ya bamu anty tace gulma ka mukeyi ai ko.
Yace dama shine aikin ku ai da kun zauna sai a kirkiro min laifi a za akaina kuma ?
Dariya ne yazo muna a lokaci daya tace kila kayi laifin ne kake shakka ko yace bani rasawa fa ni fa kin san yanzu babba ne na wuce mijin mace biyu sai mijin mace hudu.
Ni dai ina jin su suna ta fafatawa sai dariya nake masu kawai suna ta faman musu a tsakanin su.
Nace anty ga daddy wai yaya zancen Gajiye ne da maigadi ake ciki gashi har yanzu ba a ce komai ba shima ya samu ya kai ga ko daya ne.
Anty tace gaskiyan ki Rama tunda gashi shi har yana ikirarin shi kai mata hudu ne sai a taimaka wa mai son yi daya ya samu shima.
Daddy yace wai tsaya zancen dama gaskiya ne tace yanzu ba gashi kaji ba sun dade ai su da sasanta kan su ko.
Daddy yace to aini ba wanda ya fada min wanan zance tun wancan lokacin da may zai hana ayi tunda raya sunna ne kuma hakan ai taimako ne garesu.
Shima Hamza baba yai min magana akan shi wai wanan yarinyar dake wurin ki Rahama yake so.
Nace kamar ban san zancen ba wa ke nan ko Fatima dai yace ita mana ita ya ce sun shirya wai a tsakanin su ko.
Ko ke baki san da zancen bane dama ?
Nace to ni dai naso nagane da mukaje gida amma sai na dauka mutunci ne kawai a tsakanin su hakan.
Anty tace ai Fatima mutum ce ya koyi saan mata gata da tsabta kamar Ramana itama gashi bata da yawan surutu.
Yanzu zan samu lokaci na gansu sai muyi maganan da ya dace akai ina ga zaifi.
Naji dadin jin mincewa daddy sosai a raina don ba wani muhawara ya yarda da zancen.
Hajiya ke son daddawa mai kyau Alhaji ake son yiwa amfani dashi an rasa mai kyau na kwarai duk wanda ake samu wai bai masu ba.
Nace nako dawo da daddawa daga gida ban sani ba ko zaiyi mashi gardin sai dai a gwada a gani.
Na mike ina fadin bari na dauko a gani, nafita na barsu nan ban jima ba sai gani dashi a leda na bashi.
Bai jima ya mike ya fice daga wurin mu nima nace da anty zan je na leko su Fatima.
Koda na shiga na samu Fatima na sancewa Atika kan ta nace a, a yau kitso za, a sha ke nan tace naga kan nata yayi wani iri ne.
Nace gama sai na kwashe mata kafin mu je a wanke muna wani sati nima kan nawa ya fara damuna ai.
Muna kitso nace wai Fatima kin tabbatar da zancen ki da Hamza don yanzu daddy yai min magana akan zancen.
Tace cikin dan razana don Allah da gaske anty daddy yasan da zancen nan ashe.
Nace in dai kin tabbatar da gaskiya kina so to ki fada min sai a san abinda ake ciki.
Shiru tayi naci gaba da kitso na har muka gama nace taje tai wanka tazo ta shirya kafin aje islamiya.
Daga nan na shige na barsu tunda ba girki muke dashi ba a part din mu don haka na kwanta abina.
Barci na samu nayi sosai don ina fashin sallah a lokacin haka yasa na samu nai barci yadda nake so.
Ko da nafito yamma yayi sosai a lokacin ban shiga gurin anty ba sai da mukai sallah .
Na samu suna kwasan hira da yaran suna ganina sukayo kaina nan muka zube tare da su har wani lokaci.
Ina ganin sun fara jin barci na mike na kaisu daki na kwantar dasu tare da masu addu,a.
Na dan jima wurin su nafito anty ke cewa dani ai na dauka kin tafi kin kwanta ne ko ?
Nace a, a ina can da mutanena ne na samu sunyi barci yanzu da kyat ai.
Na ce zanje na kwanta nai mata sai da safe ina shiga wayana yana kuka alaman kira yana shigo min.
Na duba daddy ne ke kira na na daga yace kinyi barci ne ko ?
Nace a,a yanzu dai nake shirin kwanciyan yace ok gani nan zuwa kada ki rufe kofan ki.
Mamaki nake a raina may kuma ya faru daddy zai shigo yanzu sai gashi yazo yana saye cikin kayan barci nasu na maza.
Ina tsaye ina son saka riga sai gashi ya shigo dakin na juyo ina kallon shi fuskan shi babu annuri ko kadan yace dani.
Ki shirya muje dakina ki kwana a can yau nace daddy dakin ka kuma yace eh haka nace ko baki fahinta bane ?
Nace daddy naga banice da girki ba yau din nan yace zaki shirya mu tafi ko zaki tsaya min gardama ne kuma ?
Daddy ba hakana bane, naga haka ba kyau ne shiya ni zaki fadawa abin da na sani akai.
Nace kayi hakkuri daddy ina ma up ne yanzu haka bana

Download complete TXT · Novel page