Murucin Kan Dutse

Chapter 82 of 146

may nai maki don ni ban san laifina ba gareki.
Ta dago kai ta kalleni tace o bakima sani ba ko dama haka duniya ya gada ai kaga mutum a rana ka dauko shi ka sa a innuwa yace kai zai cuta kuma.
Ikon Allah nace a fili anty cuta kuma kada Allah ya kawo ranan da zan cuta maki a rayuwana bake ba ma anty koda wani naki ne a duniya.
Yaushe kuma ai sai dai kada a kara dama tun farko saida aka jiye min haka amma ban san may ya hau kaina ba a lokacin na nace ni sai kin shigo gidan nan ina gani kamar mafita ne hakan gareni ashe guba na daukowa kaina ban sani ba.
Hawaye kasu dumi suka kara zubo min har nakai kofa tace daga yau ma gajiye ban yarda da ita ba don haka idan zata koma wajen ki da zama ne wala,ba,asa ni dai badani ba kuma.
Juyowa nayi nace don Allah anty kiyi hakkuri kada ki bari matsalar nan ya fita waje har wani yaji mu yai muna dariya akai.
Tace ji na nawa kuma tunda yanzun na fahinci komai an dade ana cutana ni ban fahinta ba sai da masu sona suka wayar min da kai nagane.
Anty suka dai cuce mu amma ai wanan ba wayar da kai bane ki dai kara tunane akai kafin ki zurma ciki.
Kada fa kiyi min rashin kunya Rama inma mijin ki ya turoki don kizo ki min maganan banza ki koma ki fada mai ko shi yayi kadan wallahi.
Ni ban ma san kunyi magana dashi ba akai ni zuwan kaina nayi don naji laifina tace to yanzu ai kinji ko ?
Na fice ina kuka daga dakin ita ko ko ajikin ta shedan ya riga yai mata huduba ko ra hau ban tsaya ba dakina na koma na samu su fatima na kallon su hankalin su kwance.
Wayana na dauko na kira innata don ita kadai zan iya fara fadawa wanan matsalan dake batun kunno min kai kuma.
Bayan inna ta gama saurare na tai salati tace kai amma dai mutum abin tsoro ne wallahi idan tana ganin kinci amanan ta ne ga haka ta manta ita ta hada ki da mijin ta ki bar mata gidan mana sai ki bar mata mijin ta.
Nace to inna idan dai naga abin yaci gaba zan bar masu gidan su tunda dama itace ta sakani yin haka dana bata mata gara na barta kowa ya huta.
Washe gari tun sa safe sai ga gajiye ta shigo min da kukan ta wai anty tace ta bar mata part din ta dawo gurina da zama ita an samo mata mai aiki sabuwa don yanzu bata yarda da ita ba kada mu hada mata kai mu cuta mata.
Hankalina ya tashi sosai naso zuwa wurin ta nai mata magana amma kuma sai na tuna yadda mukayi da ita jiya da dare.
Dole na hakkura wanan zance sai daddy dole nan muka zauna da Gajiye da Fatima muna magana akan matsalar.
Gajiye ce ke fadin nifa sai ina ganin wanan matar mai yawan zuwa suna shigewa daki ne ta juyawa hajiya kai a lokaci daya haka ?
Nace zato mukeyi gajiye tun da bamu san may ya kawo wanan matsalar ba haka sai dai biri yai kama da mutum irin yadda matar tun ganina na farko da ita take dauka na da zafi ko kishiyana ce ita ya tsaya hakanan wallahi.
Sai da na tabbatar daddy ya fito zuwa lokacin na saka zullubeben hijabina na nufi gurin shi na samay shi shida hindatu a falon suna karyawa don da alama ma sun gama ko.
Gaidasu mayi da kwana sai shan mur hindatu keyi nasan ba komai bane fushi take may kuma ya kawo ni gurin shi don tasan ni bani shiga idan bani ce da girki ba tunda muka taba samun matsala da ita a baya kan hakan.
Yau baki shiga school din ne yace dani yana goge bakin shi da tisue daya dauka saman table din.
Nace zan shiga dama kai nake jira ka tashi magana nake son muyi da kai yace ok ai gani ko sai na dan kalli inda hindatu take zaune gefen shi.
Yace ko maganan ta siri ne ko kai na kada mai alaman eh sai yai murmushi yace hindatu bamu guri don Allah muyi magana yan mintina.
Take ta canza fuskan ta har yafi na farko tafara kanan magana ciki ciki yace nace ki bamu guri muyi magana tunda har kikaga ta shigo wanan lokacin ai kin san magana ya kawo ta ko ?
Tace nifa ban shiga hakkin mace ba don may za,a shiga min hakkina haka a hana mutum sakewa da mijin shi don Allah dai.
Nace kiyi hakkuri anty ba dadewa zanyi ba nima dole ce takama na shigo maku yanzu din ai.
Ta wani bata rai tafice daga falon tare da rufo kofan ya dago ya kalleni ya sauke ajiyan zuciya yace ina jin ki may ke faruwa ne wai ?
Kuka na fara ina mashi bayani nake cewa ni zan bar gidan tunda na fahinci akaina har wasu zasu shiga matsala irin haka ba zan so na toshewa kowa hanyar samun shi ba ni.
Yake cewa dani amma baki da hankali ko bazaki barni na aiwatar da binciken da nakeyi bane zakizo min da wani zance kuma can na daban.
Nace daddy anty fa cewa tayi wai na cuce ta da yn uwana da sani na na shigo don na yaudare ta ni may nai mata haka har take wanan hasashen haka a kaina.
Koma may ye nace ki barni da ita zamu fahinci juna keda ki ta hakkuri dama haka zama ya gada ai zo mu zauna zo mu saba nace dashi na gode sai na mike tsaye da zumar na fita.
Wani irin jiri ne ya kwashe ni sai naga kamar zan kife a wuri da sauri na dafa kujeran shima ashe yagani ya yo kaina ya rike ni yana fadin subbahanallahi kin gani ko zaki jawa kan ki wani matsala kuma can.
Hindatu ce ta shigo ta samay mu a hakan da sauri ya sake ni yana fadin ki lalaba kije ki kwanta ki dan huta.
Wani kallon banza ta watso muna batai magana ba na samu na mike da kyat na bar falon daki na koma na kwanta sai barci kai nauyi ya dauke ni.
Ranan ban shiga school ba koda na tashi na samu miscalled din Zarah yakai shidda a wayana nan dai na kirata muka gaisa take tambaya na ko may ya hanani shigowa yau.
Nace dan matsala ne ya ke faruwa sai kuma banjin dadin jikin nawa shine na dan kwanta ashe barci ya dauke ni ban sani ba.
Mun kai wani lokaci muna waya tana fada min abinda akayi a ranan muka kuma shiga wani hiran da ita sai da muka gaji na kashe wayan .
Wanka na mike na shiga nafito na gyara jikina na nufi inda su Gajiye suke muka zauna muna hiran mu dasu.

********* ********* *********
Yashigo part din daidai lokacin da bakuwar yar aikin anty take dauko mata abincin ta a falon.
Gaidashi tayi kallo daya yai mata ya kawar da kai gareta matar ta fice daga falin ya juya gare ta yana kallon ta yace wanan kuma fa daga ina take haka ?
Tace sabuwar yar aikina ce yar aiki kuma ya tambaya tace dashi eh yace ina ita gajiye din kuma tace na sallamata na dauko wace na yarda da ita.
Rai bace yace kamar yaya kin sallamata ita wanan din kin san ta ne ko kin san halinta ne ?
Tace ko ban san ta ba tafi min zama da mai cuta na yace gajiye din ce take cutan ki kuma Saade ?
Don Allah mu bar zancen tunda na fada ma komai ba shike nan ba yace bashi ke nan ba kan don ba zan zauna da wanan matar a gida na ba na fada maki.
Tunda abuyazo kaina yadda baka so ba yanzu ai dole ka fadi hakana babu inda zata ita nake son zama da ita ba wata bacan.
Yace bako a gidan nan ba na fada maki wai may kike nufi danine haka Saade na dai biki da lalama amma naga abin naki sai gaba yakeyi.
Sai kayi abinda zakayi dama ai kaji dani zaman dole kake dani tunda ba komai nake tsinanama ba ko ka samu yarinya karama yanzu kana murza.
Koma may ye naji don haka sai ki san dabara tun ban shiga rigan arzikin ki ba rayuka sun baci mara tunane kawai.
Yafice rai a bace ya barta tabishi da harara tana cewa ni za aiwa burgan maza ko may ?
Bai tsaya ba ya fice yaje ya samu mahaifin anty ya labarta mai komai dake faruwa a gidan shi tsakanin mu da anty din.
Mahaifin nata ya murmusa yace kaji halin mata ko kamar ba ita bace nan da kukan ta akan a bari ka auri yarinyar nan.
Yace ai Abba cewa tayi yanzu kuma wai asiri ne su kai mata abba yace kai mata sai a barsu kawai in bashi ba keda kikai aikin lada dan kankanin lokaci kuma kizo ki zoje ladan naki haka ta hanyar shimay irin nasu na mata.
Wana Falmantan takai shuuma babba wallahi ai dole muyi kokarin rabata da ita yace da daddy ya tafi zai zo har gidan da kan shi ya samay ta ai.
A ranan kuwa Abba yazo gidan inda yai masauki a falon maigidan a can aka kira yar tashi ta samay shi sun buga wuta sosai saida Abban ya nuna mata bacin ran shi akai ta dan sauko.
Sai dai taki yarda sam da zancen canza yar aikin da tayi dole aka hakkura aka barta da wacce take son zama din acewan ta.
Nan daddy yasa akirani nazo yake cewa dani don Allah nayi hakkuri da abinda ya faru ina kuka nake kara ba anty hakkuri idan na saba mata ne tace ita ban mata komai ba sai daddy yace babu inda Gajiye zata tafi ta zauna dani don auren ta ya kusa dama shi ke nan sai a wuce wurin.
Nan dai muka watse muka barshi da yar shi yana kara dan mata nasiha yake cewa kefa da bakin ki kikace yarinyar nan ta sama maki magani akan matsalan ki kuma yanzu alhamdullahi alama ya nuna kin samu lafiya shine zaki saka mata da wanan halin da kika tsiro da rana tsaka.
Ki sani fa da kanki kikai tabin yaron nan akan ya auri yarinyar nan yanzu kuma anyi auren kina samun lada zaki bata zancen ki a dan kan kanin lokaci haka har may akayi ko ga zaman ku in akwai rayuwa bazaki kwadayin kema kiga kin saka wa yarinyar nan ba kada fa ki matan da irin halarcin da kukaiwa junan ku abin gwanin ban sha, awa daku.
Jikin ta yai sanyi da kalamin mahaifinta sai dai gaskiya hudubar Falmata ya riga yayi tasiri a zuciyar ta sai dai zata rage wani abu don bin umurni kawai.
Da Abba ya fito sunyi mai rakiya hindatu nagani tasan da akwai magana don Abba baya zuwa gidan haka a banza kai tsaye.
Can ta samu Zulfa da zancen duk da ba dadine a tsakanin su ba take cewa da ita mutanen ki fa ina ganin zumunta ya watse a tsakanin su don akwai magana koma may ye ai ji zamuyi muna zaune don sai na gano komai ke faruwa din inji Zulfa take fafin hakan.
Ranan dana karbi girki har lokaxin bana jin dadin jikina daurewa kawai nakeyi gashi da dare jikina yai wani irin mugun gashewa da zafi amma daddy bai sani ba.
Hakana nake daurewa har na gama girki na gashi ba wani daddy tsakanina da anty sai dai dan saukin anin ina gaishe ta ta karba min harda tambayana ya school tanayi.
Sai dai ba wani dogon hura a tsakanin mu kamar da can baya bani dau gajiya da zuwa gurin ta gaida ita duk da na fahinci bata son hakan.
Matsala kuma yar aikin ta kazama ne ko girki bata iyaba gashi part din duk ya lalacemata kullun sai sunyi fada da daddy ya kasa cin abincin abin ya fara damunta sosai sai rikice ya fara samuwa a tsakanin su take cewa wai ya dai gaji da ita ne kawai yake kirkiro mata matsala a tsakanin su.
Ranan suyi rikici sosai har ya daga hannu ya mareta fada sukayi ba dadi a tsakanin su sosai harta jefo zancena a cikin maganan fada sukayi take fadin wallahi sai taga bayana a gidan nan.
Ranan kan makiya sun dara don tabar abin fada a garesu hankalina yai matukar dagawa sosai nake cewa da ita nikan anty zanbar gidan don dama kece sillar shiga na a ciki.
Nan na barsu nafice falon da aka taru masu ban tsaya ba su gajiye da fatima na bani hakkuri na dauki handbag dina na fice daga gidan ban masan inda zan nufa ba sai can dabara ya fado min na wuce zuwa gidan Amina course mate dina na kuma roketa kada tafadawa ko Zarah ina gurin ta zaune.



ZAINAB iDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE WANAN BA A YAFE BA, , ,

61
Gajiye ce tsaye a waje cikin tashin hankali tana jiran dawowan maigidan daga masalaci wurin sallah magriba daya fita.
Tana ganin shigowan shi ta tare da sauri tafara gaida shi a cikin tashin hankali take fadin Alhaji dama uwar dakin mu ce tun safe kuna wanan rikicin da hajiya ta fita bata dawo ba har yanzu.
Ya juyo da sauri yana cewa da ita wa kenan Rahama ko wa tace dashe ita Alhaji yace ina ta tafi har wanan lokacin tace wallahi ban sani ba don bata kai war haka a waje.
Yace da ita yaji ya shige ciki kawai ya barta tsaye a gurin dama duk yinin wanan ranan rayuwan shi a bace yake sanadiyar fadan da sukayi da anty din.
Yana shiga ya furzu iska daga bakin shi yana fadin a fili ina wsnan yarinyar zata shiga kuma har wanan lokacin haka?
Wayan shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi ya shiga kiran layina duk iya kokarin shi bai samu layin ba gaba daya.
A Lokacin ne hankalin shi yai mugun tashi azaton shi ko ina gidan Abba ko na mahaifan shi ne sai yai dabaran kiran su da sunan gaisawa dasu amma har ya gama gaisawa da kowan su baiji an sako mai zancen Rahama ba.
Haka yasa ya dan shiga cikin damuwa sosai don shi baiga dalilin da zai sa na saka kafa nabar gidan ba don badani akai fitina ba ai suna na ne kawai ta shigo cikin zancen su.
Har dare sosai bani ba labarina a gidan dole ya hakkura ya kwanta cike da damuwa gashi anty ce da girki bata shigo gidan ba.
Ita ko uwar gaiyyan bata ma san cewa bani gidan ba har lokacin tana can ta dauki fushi da kowa a gidan don tana ganin an mata tozarci a bainan jamaa.
Tun da safe ya buga kofan part dina Gajiye ta bude kofan tambayan ta yayi da ta dawo kuwa ?
Cikin damuwa tace dashi wallahi bata dawo ba Alhaji ko gida ta tafine dai yace an ya ban tsan manin zata tafi gida don da sun bugo waya ai.
Cikin ikon Allah yana komawa part din shi sai ga maigari yakirashi suka gaisa yaji yana tambayan shi muna dai lafiya ko ?
Wanan yasa ya kara tabbatarwa da ina cikin garin dai na samu inda na boye je kawai amma ai duk inda nake zai gane.
Anty suna gaisawa da Falmata take fada mata abinda ya faru Falmata tace bana fada maki ba wanan yarinyar annobace a gare ki .
Don ta riga da ta asirce ki ta ko ina ba ki da sauran motsawa dole ne asama maki makarun abinda tai maki tun kan ki cutu da yawa.
Sunyi da ita zata shigo gidan su kara tataunawa zuwa rana don su san abinyi akai a cewar ita falmata din.
Sai dai suna gama wayan a bangaren Falma sai ta sauke wani shu,umin murmushi kawai tana magana a zuciyar ta ita kadai.
Daddy ya kira Bashir yazo nab yake labarta mai abinda ke faruwa a gidan shi har da barina gidan danayi bai san inda na nufa ba.
Nisawa Bashir yayi bayan ya gama sauraren abokin nashi yace watau su dai mata haka halin su yake basu da tabas akan halaiyan su ?
Yanzu ita Saade harta manta da irin halarcin alherin data shuka da Allah ya baku rabo tsakanin ka da Rahama aida ankai ga diya biyu a gidan nan da ita.
Nan dai suka yanke shawara akan su shiga school tunda sun san a wanan lokacin da nake ga ganiyar gama karatuna babu inda zan tafi na bar karatun nawa ai.
Sun shiga school din da tambaya suka isa department din mu inda suka rasa wa zasu tambaya sai ga wata daga cikin dalibai tafito da ganin ta yarece ita don tai kama da kabila suka gaida ita.
Nan Bashir yake tambayan ta ko tasan wata Rahama anan department din tace da hausa gaskiya da wuya da nan san abinda take karantawa ne sai lokacin daddy yai magana yace matar aure ne tana yawan shiga CRV assh color tana shekara na shidda ne yanzu.
Tace ok nagane ta wata fara kyakyawa mai kamun kai bata da yawan hayaniya sosai kawar Zarah Ko ?
Yace ita,
Tace nadai ga shigowan Zarah din dazun amma ban san ko ita tana ciki ba don ko tana nan baka ganin ta sai idan sun fito zuwa sallah.
Tace dasu tana zuwa ta juya zuwa ciki daddy yai tsuki yace wasu akwaisu da surutun tsiya wallahi wanan dogon bayanin waya tambaye ta ne wai ?
Bashir yai dariya yace ai ta taimaka muna koba komai munji wani abu gamay da Rahama din anan suna cikin magana suka

Download complete TXT · Novel page