Murucin Kan Dutse

Chapter 95 of 146

in dane.
Yarinya kamar hatsabibiya ba duk abinda nayi mata tankar taki nake zubawa akan ta shigiya ko gezau sai naga kamar aiki zaici amma kwana biyu sai abu ya koma fiye da farko.
Tace da ita su bata kwana biyu su dawo idan ta gama mata hadi duk da kudin da ta tsala masu amma haka hindatu ta lale ta biyata kudin ta kai tsaye.
Suna fita wayana dake gefe na yai kara na daga da kyat don a kwance nake tun safe da yake yau ban fita aikin sai da dare.
Ina dauka muka gaisa tace Rahama kin san may nace a, a tace wallahi yanzu wanan kishiyar taki tazo guna yau.
Nan dai take fada min yadda sukayi da irin zagin da ta dinga min sai dariya nake nace kai Allah na gode ma wallahi Allah ka kara rufa min asiri dama nan suna yawan jifana duk kan su Allah ne dai ke kareni wallahi don ba imani ne dasu ba akan mijin su.
Tace ni dai yanzu na bata kwana biyu ta dawo idan kuma ta dawo zan mayar mata da kudin ta ne don ba zan iya mata komai ba.
Nace a, a hajiya kadai ki haka don Allah kefa akasuwa kike don haka na rokeki da duk abinda kika san na amfanine tsakanin miji da mata ki bata ni a gareni babu komai wallahi ai zaman lafiya zai sa a tsakanin su Allah kuma yasa ta gane gaskiya.
Waiko kina da hankali kuwa Rahama kishiya har kike fadin nabawa abin amfani taji dadi da miji ko may ?
Nace yo hajiya sai may jikinta daban nawa daban ai bashine zaisa tafini ba kema ai zakiji tsoron Allah ya tambaye ki akan yi mata kissa da kikayi idan baki bata mai kyau ba.
Tace kai lalai ma Rahama halinki daban ne wallahi da zasu gane natabbatar ba karamin zaman lafiya zakuyi dasu ba amma kishi ya rufe masu idanuwan su.
Mun dan kai wani lokaci da ita muna hira daga karshe mukai sallama da ita tabarni ina tunanen irin hakin na kushiyoyina naga maganan maigyaran harka gaskiya ne datace na kar mikewa na nemi tsarin jikina da na yarona.
Haka na wuni da zancen lafazin hindatu akaina nasan Allah ne ke tsare ni bawai iyawa na ko wani abin ba da na keyi.
Sai dare na shirya nai masu sallama nafice zuwa asibiti inda zanyi night duty dina tun shigana na shiga na shiga aiyukana na manta da zancen wata hindatu can a raina don aiki da yai muna yawa a gany don matsalan mata da yai yawa yanzu.
Sosai nake kula da kaina ban wasa da duk abinda zai kawo min kuzari ajikina na masu ciki tunda na sani ba sai wani ya fada min ba.
Ranan na shiga wurin aikin mu nan nasamu sauran likitoci mata yan uwa na suna hiran aka rayuwan duniya kowa tana fadin nata matsalolin.
Ina sauraren su banyi magana ba sai da sukaji ni bance kala ba sai wata hadiza ke cewa dani ke kan doctor Rahama kin huta ke kadai ce a gun mijin ki kin huta da matsalan rayuwa.
Murmushi kawai nai mata nace a ganin ki ke nan doctor hadiza ni jinku kawai nake don nafi ku matsala idan da zakuji sai kice ashe ke naki dan mali ne.
Tace kajiki da wani zance matar dake zaune daga ita sai mijinta ke har may kika sani akan halin wani zaman takewa haka ?
Nace doctor hadiza nice ta hudu a gun mijin mu ba yadda kike tunane bane din a lokaci daya suke hada baki wurin cewa what nace hakane namike ina tattara takatdin dana gama dubawa na wata mace da aka kawo a cikin dare ciki ne idan ta samu sai yaki zama a jikin ta har sai yafita asamu lafiya.
Nafice duk suka bini da kallon mamaki dayar tace kai ina ban yarda ba wallahi ta dai fadi ne kawai don muce itama din ai tana da nata matsalan.
Amma mai kishiyoyi ne zata zauna haka ko yaushe hankali a kwance bata cikin wani damuwa ko kadan.
Basu yarda ba nima ban kara masu bayani komai ba muka bar zancen a haka a tsakanin mu bandai masu bayani ba.
Sai kuma kamar sati uku na shigo na samu abokiyar aikina tana waya cikin tashin hankali sai na fahinci da mahaifiyar ta take wayan.
Tana fada mata rikicin da suke da mijin ta da kushiyar ta har takai gayin kuka nasan uwar tace ta nemi tsarin jikin ta ne sai naji tace mama nida ke nan a ina zan samu wanan ?
Sai dai ke ki sama min don Allah dai mama daga ni har yaran da zaran Nafisa ta shigo garin nan bamu da sauran kwamciyan hankali har sai ta bar garin nan zamu zauna lafiya dashi.
Har ta karasa wayan bata daina kukan da takeyi ba nai ajiyan zuciya nace da ita kiyi hakkuri hakana don Allah.
Shi alamarin namiji sai idan kana sakawa a ranka ne zai damay ka tunda har kin san inda matsalar take maku da zaran matar shi ta shigo gari ki rungumi yaran ki kifita zancen su har lokacin da ta tafi ya dawo maku.
Idan yaga kina damuwa da alamarin maimakon kiga sauki sai dai kiga ma yana kara tula maki haushe ga hakan yadda ranki zai kara baci ga banza.
Mafita dai daya ke nan mama ta fada maki shine kidai tsare jikin ki dana yaran ki don kariya daga duk wani manufa nata akanki.
Don idan kin fahinta sai kiga bayin kan shi bane hakan shuumanci ne irin namu na mata take kara ingiza shi akai don ranki ya dinga baci kawai idan tazo garin.
Tace doctor Rahama don baki da kishiya ce yasa kike fadin haka wallahi a yanzu nayi dana sanin auren Abdul a rayuwa na.
Haba dai don Allah kice astangafurullah mutun da kuka haihu har biyu dashi zaki tsaya fadin haka kuma akan shi.
Tace doctor kishiya fa ba abin yarda bace walkahi nasani nace mata don ma sai nace ni nafiki sani don ni nan da kike ganina kishiya tai sanadiyar aure da mijin mu na zama ta hudu amma kuma yanzu nice babban makiyiyyarta a duniya don halin kishi kawai.
Da sauri ta dago kai tana kallona a cikin mamaki nace kwarai kuwa nan nafara bata labarina har zuwa wanda hajiyan harka ta jiyo min din ga hindatu.
Nisawa tayi bayan tagama saurare na tace amma kan matsalar ki yafi nawa gaskiya ni ina zan iya zama cikin mata uku na zama ta hudu ai sai su caza min kaina dayan ma yaya na gama da ita balle har na zama ta hudu.
Nan dai muka yanke shawara tare zamu tura wa mahaifiyanta kudi ta taimaka muna yadda tace daga kasan bargu na kayanji.

********* ********* *********
Ranan dai nace bari na kira anty mu gaisa don kwana biyu ban kira ba bata kirani ba kuma dama dai nice mai kira din ba ita ba.
Ga mamakina sai bata dade ba ta dauki wayan na fara gaida ita tare da tambayanta lafiyan yaranta.
Mun dauki lokaci muna dan hira wanda duk akan yaran ta ne mukayi shi normal ba wani matsala a ranan haka yasa bayan mun gama wayan naiwa Allah godiya kan hakan.
Tun wanan lokacin nakan dan kira wayan ta mu gaisa tunda ta rage yawan daure min da takeyi a baya gashi har zata tambayi lafiyan baba wani lokacin abinda a baya batayi.
Abinda ban sani ba yanzu ta fahinci zama dani ba karamin rana ne gareta ba don barina yasa ta fahinci cewa ni ba kishi nake da ita ba sai taimako amma ta biyewa son zuciya tana musguna min haka.
Gashi tsakanin su duk da miji baigida kullun da irin matsalan da zai bullo a tsakanin su sai iyayye sunzo sun shiga ga maganan.
Don raini dama sun riga da sun raina tako tun baya wanda ba komai yaja mata haka ba sai son kai da suka fahinci tun farko tana dashi ashe ?
Ga gori dan abu kadan zasu rufe idon su suyi mata gori akaina kuma su zageta fes shikuma mijin dake goya mata baya yanzu yafita zancen ta .
Shiyasa taga ta shirya da Rahama kila zai kawo mata saukin zaman doya da manjan da ke tsakanin su tunda dama shine matsalan nasu.
Haka yasa take kokatin ganin ta taushi zuciyar ta akan kishina da take ji a zuciyar ta ko za,ta samu sauki a rayunta.
Ban dai yarda na sake sosai da ita ba kamar baya don bana fada mata komai na sirin daya shafe ni yadda muke da ita a baya can.
Koda yaran ne suka bulstiye mata zata kirani ta fada min nai masu magana kuma suji tundai ma Amira dake yawan dauko mata magana a gidan yanzu.
Nakan wa yarinyar magans maikama da Nasiha a cikin hikima kuma ta fahinci magana na ta bar abinda takeyi din.
Cikin jikina ya girma yanzu sosai don har ya fito watan shi bakwai da kwanaki haka nake ta fama dashi ni kadai nake kunshe da abina ba wanda ya san da shi bani ma fatan wani yazo daga fannin daddy har ya fahici hakan.
Shima muna waya dashi amma ban taba sanar dashi komai ba akancikin don haka baisan dashi ba tare dani sai dai nasan ranan da zai gani da akwai rikici kan gaskiya ban damu ba an dai riga da anyi din ko.
Ya bugo waya zai dawo cikin wani sati don watan shi uku acan da kwanaki kenan baya kasan sai da yaga komai da suke so ya kammalu masu shine zai dawo gida.
Naso bashi sakon kayan baby amma kuma may zance dashi ga hakan sai kawai nashiru sai yazo ya ganewa idon shi zai san yadda yayi ai da hakan.
Anty da kanta ke kokarin sanar dashi shiryawan mu da ni da ita sai dai idan tai magana a waya yayi murmushi don yasan tuban mata na mazuru ne dan abu kadan zai sa ta koma wa halinta tunda ya fahinci abin a jini yake muna.
Sai dai ya fahinci tunda muke ni baitaba jin nai mai wani korafi mara dadi akan kowacen su ba bani kuma sukan su gaban shi koda kuwa sun bata min rai na.

********* ********* *********
Da yamma ya dawo ya iso gida da biyar da wani abu lokacin ina daki ina kara shirya duk da dogon riga ne a jikina light blue na daura dan kwalin shi a kaina sai cikin daya turo a jikin rigan yai tsiri dashi.
Nafito da fara, a na don na manta da baisan da zancen cikin ba ni da murna na samu yaran gidan suna taron shi nace daga kofan da nake fitowa din da daddy oyoyo.
Ido ya zuba min bai iya karba oyoyon danai mashi ba a lokacin sai idon da ya zuba min har na karso inda yake tsaye sagale da corth din rigan shi a kafadan shi.
Da hannu ya daga yace dani dakata Rahama da sauri naja wuri daya na tsaya kamar yadda yace min din.
Kallona yake cikin mamaki idon shi akan cikin nawa, yace Rahama ciki ne dake komay nake gani haka ajukin ki ne wai ?
Murmushi nayi nace kai wallahi har naji tsoro na dauka wani abune wallahi, ina karsowa inda yake a tsaye sai su Aisha suka fara sulalewa falon.
Ya kara kallo na yace yaushe har kikai ciki a gidan nan har ya girma haka ban sani ba Rahama ?
Nace daddy wani ciki kuma kai mutum bai kiba sai kace ciki kuma humm naji yace kawai tare da kara bina da kallon mamaki ?
Boye min kuma kikeyi ko may Rahama da har ciki zai zauna a jikin ki yakai haka ni uban cikin ban sani ba saboda may zaki boye min wanan irin maganan da ba karami ba haka.
Na rugumay shi ina sauke ajiyan zuciyan ganin shi ya dan dafa bayana tare da kai hannun shi ga cikin take kuwa dan cikin yai wani bul bul daga cikin riga.
Yace tabbas kuwa cikine dake Rahama, don gashi naji motsin shi yanzu ai.
Na sake shi ina fadin daddy sannu da hanya yaya aiki yaya jama, a kuma da sanyi ?
Yana dai tsaye yana kallona daga inda yake bai motsa ba yace abin ya daure min kai wallahi yadda har mace zatai ciki yai girma haka ace wai ban sani ba don may zakiyi min hakane wai ?
Zama nayi don banda jimirin tsayuwa mai yawa yanzu da kyat na kai zaune ya kara kallona a cikin mamaki.
Ganin baida niyar zama nace ka zauna mana daddy ka huta tukun kafin muyi wani magana dakai ko.
Yace dani barni a nan tunda banda wani amfani a gunki har zaki iya boye min alherin da ubangiji yai min haka banyi mai godiya ba.
Nace afuwa yallabai tuba nake nayi kuskure amma may zan fada ma tunda lokacin da zaka gani yayi ko .
Kallon mamaki ya sake min daga haka bai sake magana ba sai ya fara tafiya zuwa part din shi ran shi a bace mai.
Bin bayan shi nayi da kallo daga gurin da nake zaune na sauke ajiyan zuciya bayan naga shigewan shi ciki.
Ban iya tashi ba don tashi wuya yake min sai da na dauki lokaci mai tsawo na mike nabi bayan shi zuwa dakin.
Na samu har ya fito daga wanka ya saka dogon riga mai laushi a jukin shi ko jin nashigo bai sa shi ya juyo inda nake tsaye ba.
Daga inda nake tsaye nake cewa dashi abinci na falo yana jiran ka ya dan juyo tare da zuba min idanuwan shi a kan cikina.
Yace ba yanzu zanci ba sai nayi sallah zan zauna naci abincin nace daddy ko ruwa baka sha ba fa tunda ka dawo yace No ki barshi a koshe nake ai.
Sai banji dadin yadda ya daure din ba na juya don barin dakin cikin jan kafa na da kyat don bani da wani lakkan kwarai yanzu.
Muryan daddy naji yace Rahama may ye dalilin ki na boye min cikin dake a jikin ki, kika ki fada min kina da ciki tsawon lokaci haka ?
May kuma kike nufi da hakan da kikai min kika hana na godewa ubangijina da ya azurta ni da samun karuwa a gidana ?
Shiru nayi ba amsa ya dago yana kallo na ido da ido da sauri na dukar da kaina a kasa cikin jin nauyin shi na rasa may zance dashi din.
Ya sake cewa ba dake nake bane baki jini bane ki may tambayan ki nayi akan wani dalili kikai min hakan ?
A sanyaye nace daddy ni bana nufin komai ga yin hakan da nayi a gare ka na dau yi shiru ne don ban san yadda zan fada ma ba a lokacin ganin ina shayar da yaro dan wata goma bai isa yaye ba.
Amma ni bayan wanan bani da wani manufa akan hakan kuma nayi haka ne don gujewa maganganun mutane akan hakan.
Nace amma don Allah kayi hakkuri tunda ranka ya baci ga yin hakan da nayi din ba da wani manufa naki fadawa kowa ba ni.
Yace ashe baki da hankali ban sani ba Rahama cikine zaki boye har yakai tsawon wanan lokacin kina nukurkusa dashi a jikin ki batare da wani naki ya sani ba ?
Ko kuma kin dauke ni ban san abinda nakeyi bane saboda wani hujja can naki na banza mara dalili,
Ko waye baisan hikimar ubangiji ba idan ya tashi yin ikon shi akan mutum zaki dauki ciki har yakai wanan matsayin kina fama dashi a tare dake kin yi gum idan kika cutu ga hakan da kikayi laifin wa kike tsanmanin za, a gani ga yin hakan.
Shiru nayi mai har ya gama fadan shi nace don Allah daddu kayi hakkuri nasan nayi kuskure babba nima.
Bai min magana ba sai saka kai yayi ya fita daga dakin kawai na dade a wurin da nake a tsaye a cikin damuwa daga baya nabi bayan shi na fito daga dakin nima.
A falo na samay shi zaune yana waya na samu wuri na zauna sai faman wayan shi yake ya nuna baima san ina wurin ba sai baba ne da yazo yana dan jana da hira nake bashi amsa kawai cikin gwalancin shi na yara.
Sai da akai kiran sallah na mike na shiga dakina nai sallah ban fito ba don a gida yai sallah shima na idar da isha,i da shafa,i da wuturi na kara dan gyara jikina na fito falon na zauna.
Tun kan na kai zaune yace dani mikon min abinci nan naci a nan na mike zuwa wurin da abincin yake a table na dauko zuwa inda yake na jera su a gaban shi.
Sai da nagama har ya fara ci na samu wuri a gefen shi na zauna ban dai yi magana ba har lokacin don nasan nayi laifi babba.
Cin abincin shi yake hankali a kwance da gani abincin yai mai dadinci don ya dade yane kewan abincin gida irin haka.
Nan dai na zauna ina amfani da waya na ban bi ta kan shi ba sai can batare da ya kalle ni ba yace dani wata nawa ne cikin naki yanzu yake ?
Shiru nayi tare da dakatar da abinda nakeyi da wayan na dago kai ina kallon shi sai kuma nai saurin dukar da kan nawa a sanyaye nace dashi takwas da kwana ki ke nan yanzu.
Amma gaskiya rashin hankalin ki yai yawa wallahi ashe da sai dai kawai naji haihuwan ki idan na dawo ke nan da ban dawo ba a yanzu ?
Shiru nayi shima ci gaba yayi da cin abinci shi har ya gama ya jawo roban da na aje mai ruwan wanke hannuwan shi yafara wanke wa sai naji ya ce dani.
Amma ki sani wallahi, idan kin sake maimata min irin haka bazaki ji dadin matakin da zan dauka akan ki ba nan gaba.

Download complete TXT · Novel page