Murucin Kan Dutse

Chapter 99 of 146

banfi kowa iko da gidan ba.
Yace wanan ne hujjan ki dama na sani sai dai kina da aiki idan kikace ke baki mantuwa da sabani idan anyi.
Ba rashin mantuwa bane sai tunatar dani wani matsayin da nake ciki wanda naso na manta shi a baya can.
Yace cikin kada kan shi ok yayi kyau tunda haka kikace ba matsala yasa kai ya fita na bishi da kallo har yabace min da gani na share kwallan fuskana tare da gyara kwanciya na.
Ina kwancen ban daga ba sai gashi ya sake shigowa dakin a karo na biyu wanan lokacin ya sauya kayan dake jikin shi zuwa rigar barci.
Take kuma ganin shi yasa gabana ya soma halbawa a hankali, da kyat na tatara natsuwa na wuri daya har ya karaso inda nake kwance.
Muryan shi naji yana fadin Rahama kin ban matukar mamaki da kalaman da kika fada min a yanzu kafin na fita.
Bayan aure na dake sai nake daukan zan samu natsuwa da kwanciyan hankali a gare ki ganin irin tarbiyan dake gare ki.
Sai kuma irin yadda rashin kwanciyan hankali ya yawaita a tsakanin ki da abokan zaman ki daya biyo baya musanman ma Saade da Allah kadai yasan sirin ku a baya sai ga sabani yazo yana yawan shiga a tsakanin ku kuma.
Wanan dalilin yasa naga gara na raba ku ko za, a samu zaman lafiya da kowan ku shine dalilin da nai dubaran dauko ki zuwa nan garin na kawo ki inda babu kowa naki ko nawa sai abokan arzikin da Allah ya hada mu dasu anan.
Duk da hakan da nayi Rahama ke nan na kasa sama muna farin ciki gayin haka don gashi har yakai a gaban iyayyen mu kina son su fahinci akwai wani matsala a tsakani dake a yadda kike yi din nan.
Kina nufin ko nuna masu ni na kasa sama maki farin ciki da kwanciyar hankalin da mutane suke hasashen kina a cikin sa a nan din.
Jin yayi shiru yasa nace dashi, daddy ni bakai min komai ba fa kuma ba wai nayi wani abu bane a sani kawai dai na kama kaina ne ga tunin da akai min a matsayina.
Yace tuni akan may yanzu ke kinga yadace a yadda zulfa ta gaya min anyi na tsaya nagoyi bayan ki batare da na dauki mataki ba ai sai ace dani gaskiya ne nafi karkata akan ki kamar yarda ake fadi din.
Nace aini da kai mun san fadi ne kawai amma may akai min wanda su ba ai masu shi ba sai dai suce ina nan garin a tare da kai ni kuma ban hana kowa zuwa ba ai tunda suma gidan mijin su ne nan din.
Murmushi yayi yace keda bakin ki don bacin rai kike fadin wai wata tazo ku zauna da ita anan din ?
Nace in Allah yayi akwai wacce zata zo mu zauna dani dakai ai duk bamu isa mu hana ba daddy .
Daddy Allah ne fa mai tsarawa bawan sa rayuwan da zai yi a duniya ba wai tsarin bawa bane duk mai zama tazo mu zauna mana.
Don ka ne nake ganin wa yan nan abubuwan daddy baka tsaya bincike ba ka rufe idanuwan ka ka sauke min masifa akaina yadda kake so don kawai ka gyarawa matar ka rai.
Dariya magana na ya bashi yace idan na san yadda ake tsayawa gyarawa mace rai ai kin fi kowa sanin hakan gare ni ke dai kice matsalana daukan mataki batare da na tsaya bincike ba kawai.
Nace ni ko may ye yanzu ai ya wuce sai dai ka sani Allah ya na tare da mai gaskiya ko yaushe banga dalilin da da hannun ka ka rufe kofan ka ba da zata zo ita tace na bude mata dakin dan na kowa ne.
Yace yanzu dai komai ya wuce ai Allah ya wanke ki banga abin tsayawa bata rai ba anan tunda zancen ya wuce.
Nace ai kaine duk wani sanadin fitina na dasu ina son in tabbatar ma daddy zan jure ko wani irin hali da zan shiga dasu akan ka nakuma jure hakan na zama jaruma a wurin su, don na tabbatar masu da kai kan ka cewa ni zama nake da kowan ku tsakani da Allah.
Insha Allahu daddy bazaka taba danasanin aure na da kayi ba indai ta wurina matsala zai fito har mu saba maka.
A hankali ya karasa takowa inda nake yakai zaune tare da min kiss a goshina yace nagode da kika kara tabbatar min da hakan da bakin ki Rahama.
Na dade da sanin kina gujewa bacin zuciyan wasu ki hade shi a ran ki ni kaina nazo nayi nadaman yadda nai maki gama yadda Allah yai saurin nuna min kuskuren abinda nayi da wuri.
Wani sanyi naji ya lulubeni a lokaci daya atake kuma hawayen nadama suka soma zubo min don nasan nayi kuskuren daukan zafin da nayi da kowa bayan Allah ya wanke ni ga maganan ko.
Yace ina son daga yau ki saki ranki da kowa ki koma normal batare da su mama sun fahinci akwai matsala a tsakanin mu ba.
Nace in sha Allahu ya wuce zanyi yadda kace tunda haka kake so amma ni kawai dama dan hutawa nake kafin na koma bakin aikina.
Yace ai ban ki hutun ba nima ina son hakan amma a rika dan kula mutane aba kowa hakkin shi don Allah.
Ya fice daga dakin bayan mun samu fahintar junan mu nace a raina dama ance matan yanzu a dakin su suke yaji ba sai wani yaji ba.
Gashi mun samu matsala kuma mun shirya a tsakanin mu batare da tsofin dake gidan sun fahince mu ba.
Tun washe gari na dan fara shiga mutane in dan zauna sai dai ban jin dadi sosai saboda dana zauna zan fara barci a gurin.
Har sai nake tunanen ko dai wani ciwo ne ya shigeni haka na barci na san dai dana haihu duk wani treatment din daya dace aimin a asibiti Faiza tai min shi a gida.
Ashe ba haka bane gajiya ne kawai yake sani barcin bayan kwana biyu sai na murmure har na fara zuwa gun aikina yadda ya dace don saura wata daya da kwanaki mu gama bautar kasan namu ko .
Haka yasa na dage sosai ga aiyukana na gidan mijina dana wurin bauta ma kasa don kada na samu matsala a ko wani ban gare.
Daddy yakan yi kwana goma zuwa sha daya ko sha biyu sai ya leka kano yai kusan kwanakin da yayi muna ya dawo.
Har nai arbain wanda yazo daidai kuma da gama bautan kasa na a asibitin da nakewa aiki din.
Sun karbi takatdun mu mu hudu sunce zasu iya neman mu anty time idan bukatan hakan ya taso garesu.
An bamu kyaututuka na yabo kamar kada a rabu muka barsu suna jin kewar mu sai kuma gida gasu mama na shirin komawa gida don yanzu hankalin su ya koma gida sosai sun gaji da zama wuri daya.
Daddy yaban kudi masu yawa mukaje dasu sukai sayayya saura kwana uku su tafi sai shirin tafiyan su akeyi don shi zai mayar dasu gida da kan shi.
Naso zuwa amma daddy ya hana yace na bari idan sallah yazo sai mu tafi can muyi sallah tunda ya gabato su ma don azumi suke son komawa dakunan su.
Ranan da zasu tafi kusan duk mun nuna damuwan mu don bamu son su tafi saboda suna da dadin zama sosai.
Bayan tafiyan su sai gidan ya koma muna shiru kamar ba kowa dama ance bako Rahama ne ga wuri.
Shirun da gidan yayi yasa muna shirin kwanciya ranan saiga Ihisan cikin kayan barcin ta take cewa wai ita bazata iya kwana dakin ta ba tsoro take ji.
Nace a, a Ihisan in banda abinki ai ba yau kika fara kwana dakin ba kuma kefa kika matsa da abaki wanan dakin ke shi kike so.
Don haka kiyi hakkuri ki koma dakin ki ki kwanta kiyi addua Allah zai tsare ki tace itafa atabau sai dai in Atika zata zo su dinga kwana a tare.
Atika tace wa ni wallahi bazan tafi ba keda kike fada a school din mu cewa ba baban mu daya mu yan aikin gidan ku ne anty mu ta karbewa mamakin miji shine mukewa mutane sallon banza kika sa akai min dariya.
Wani iri naji ba dadi a raina amma na daure nace haba Atika don kawai tace ki tayata kwana shine zaki mata sheri haka ?
Tace wallahi anty ba sheri bane ai mama Laraba ce tai muna sharia da muka dawo gida tace kuma nayi hakkuri kada na fada maki.
To ai yanzu gashi duk da anbaki hakkuri kin fada naji tace ai haushi naji wallahi ni ba zan tafi ba na juya inda Ihisan take da alama dai tsoro take ji din nakoma lalashin Atika din tace muje amma kinci arzikin anty wallahi nace nagode.
Na juya wurin Ihisan nace da ita haba ihisan ai ba sai kin tozarta dan uwan ki ba zakiji dadi kowa ma ai yasan cin arziki mukazo gidan ku shi mutum rana gare shi da kike ganin shi don akwai ranan da zai taimaka maka.
Tace Iam sorry mummy bazan sake ba ai mamanace tace dama idan sun min tsiya na fada masu hakana amma na bari tun ranan da grandma tai min fadan hakan.
Nace good girl haka ake son yaro ya dauki fadan manya dama ki bari kinji a zauna lafiya da mai kudi da tallaka ai duk Allah yayi shi ko.
Suka wuce zuwa dakin nace kada a manta ayi addua dai idan za a kwanta suka insha Allahu.
Bayan tafiyan su mamakine fal a zuciyana yadda mace zata zaunar da karamar yarinya haka tana koya mata kissa da kisisina Allah kadai yasan irin hudubar da taiwa yarinya da zatazo ko idan sunyi waya.
Don haka zan bi yarinyar sannu a hankali na fahinci komai da take kullawa agidan don idan nai sakaci zata iya min wani kulli da ba zan iya fitar da kaina a ciki ba wata rana.
Sai da na samu kebewa da Atika nai mata fada mai kama da jan kunne akan ta sani ba daya suke ba da Ihisan don kada wata rana taga tayi abu tace ita ma zatayi sosai naja mata kunne Alhamdullahi kuma yarinyar ta fahinci maface ni sosai.

********* ********* *********
Bayan daddy ya isa gida ya kai su mama Laraba gidan ta inda anan Attu zata kwana sai washegari yasa akaita gida.
Ya isa gidan shi ya samu iyalin shi lafiya anty ce da girki bayan sun gaisa ne take tambayan shi su mama yace da ita ai tare suka dawo ya sauke su gida ne.
Tace a a na dauka ai tare da Rahaman zasu dawo gaba daya tunda ta gama abinda ya kaita can din ko ?
Yace cikin mamaki ta dawo ina kuma tace ban gane ta dawo ina ba, ba anan take ba dama ko a can zatai ta zama kuma ?
Yace dama kunyi da ita cewa idan ta gama zata dawo nan ne ?
Tace da kai dai mukayi haka da zata tafi yace to a can zata zauna don aiki zata fara badadewa ba da zaran danta yayi kwari.
Nan ta bishi da kallon mamaki tace au Rahaman aiki zatayi ita ke nan yace eh ba shine burinta ba ko haka zatai tsawon shekaru bakwai ya tafi a banza bata more mai ba wa alumma ?
Abin mamaki baya karewa kullun a gidan nan tace daga karshe yayi ashe nike wautana anan ina murnan zasu dawo gida.
Yace ai da nan da can duk daya ne a garesu ko may ake a can wanda ba ayi anan din waya ne kullun kuna gaisawa idan kun ga dama to sai may kuma ?
Bata iya magana ba don mamakin daya bata yawani zare a lokaci daya kamar bashi kamar wani bako ya koma mata sam yanzu ba kamar wanda ta sani ba a baya.
Mai dubaiyya da son jin bukatunta amma yanzu shi da kan shi ma ke kirkiro mata matsala.
Don tunda ya tafi da yara karatu can ta fara kawo wutan gane cewa akwai magana gaba don haka ta mike tsam ta bar falon ta barshi yana cin abinci.
Ya bita da kallo sai dai yana jiran ta tunda duk itace ta jawo mai yin haka ai ta dauko fitina ta saka a ranta bata zaman lafiya dashi kwata kwata yanzu haka ma abokan zamar ta kamar wacce asiri ke aiki a kanta har yanzu.
Shiru shiru yana jiran ta sake maganan ya bata amsa daidai da maganan ta amma sai yaji shiru bata kara yin maganan ba again.
Abinda bai sani ba ranan ta kwana tana tunane kan maganan sai daga karshe ne ta dai yanke shawaran ta hakkura tasawa kanta saida kawai akan zancen Rahama.
Don dai koma may ye dai ai itace silarshi tana ta bada kai ana mata dariya a tsakanin su ga yaranta can har biyu gunta amma bata ji wani korafi ko kadan ba daga yaran har yanzu ko sunyi waya dasu lafiya lau take jin su.
Hakkuri da nadaman abubuwa yazo mata a rai a lokaci daya ta mike ta roki Allah da ya sanyaya mata zafin Rama da take yawan ji a zuciyar ta koda yaushe.
Tasan yarinyar bazata iya cewa ga wani abinda ta taba mata ba na cutar wa amma yakai yanzu saboda halin da take gwada mata har ta fara mayar mata da amsan magana mai zafi.
Shine dalilin da taja bakinta tai shiru ta dai san halin mijin su fiye da kowa hutsune bai jin mutunci idan idon shi ya rufe.
Kowa kuma haka yakewa don may karamar yarinyar da ta raina zata fita sanin maganin zama da mijin su lafiya aiko wacce mace na kishin mijinta ta san kuma Rama na da kishin ita ma tunda mace ce amma ta iya dannewa ta boye sai itace bazata iya boye nata ba.

Aike da kira ya ishe shi a gidan su Hindatu har takai ranan an datse a gidan mahaifan shi nan Alhaji shi ya sa baki yace sai yaje ya duba matar nashi tunda yanzu ta gane kuren ta.
Baiso ba haka ya daure ya tafi da yamma shi da Bashir daya dauka don ya raka shi gidan ya ganta amma ran shi baiso haka ba.
Sun isa gidan suka aika a sanar da zuwan su hindatu naji ta fada daki tafara dauko kwallin da aka bata ta shafa tare da wani powder da turare duk tayi yadda aka umurce tayi ta yafa taiwa uwarta sallama ta fita uwar nacewa kinyi yadda akace kiyi ko kin dai san irin kudin da muka kashe a gurin nan.
Tace kada ki damu mama nayi komai yin fatan dai mu dace kawai idan ya ganni din.
A lokacin saura wata daya ta gama idda da takeyi tana fita ta samay su zaune a falo ta gaidasu a cikin wani irin ladabin shagu.
Ya dago kai da kyat yana amsa mata yana kallonta yaji wani irin shock a ilahirin jikin shi gaba daya yaga ta sauya mashi ta koma kamar wata hawai niya mai rikida ako wani lokaci.
Tai mashi kyau ta koma kamar wata yar shila a ganin shi, wani irin sonta da kaunarta yana fisgan shi.
Cikin washe baki yace da ita idon ki ke nan daga magana kadan sai ki fushi ki dawo gida.
Take ta gane cewa tarkon ta ya kama kurciyar da take hako nan ta shiga juya shi yadda take so har sukai mata sallama suka tafi Bashir dai yana kallon ikon Allah.
Sai da suka kama hanya yaji daddy ya sauke ajiyan zuciya da karfi yace yaya akayi ne mutumina ?
Yace kaina ne naji yai min wani irin sarawa wallahi muna barin wurin nan kamar kar hindatu tafito gaba daya sai na nemi natsuwana na rasa.
Yanzu kuma mun bar wurin naji kaina yana sara min ba dadi wallahi nan dai Bashir ya nisa yace dashi nifa kada nai magana nayi laifi kuma ?
Yace kamar ya kayi laifi kawai kafadi maganan ka mana kai tsaye ?
Yace abinda zan fada ne da nauyi akwai kuma kamshin gaskiya a cikin sa yace kafadi maganan ka mana kai tsaye ka tsaya kana wani kwanaye kwanaye haka dakai ?
Bashir ya nisa yace anya Hindatu bata gama da kaiba yadda naga ka zabura daka gantaka kuma sukurkuce a lokaci daya ga wani kamshi wani irin mugun turaren gargajita danaji tanayi.
Daddy yace kai amma akwai ka da wani magana yanzu nine hindatu zataiwa magani kake gani ya kamani ?
Bashir yace kai kafi karfin sherin mace ne ko may wallahi ka fada tarkon mata kace nace da kai wata rana bai yi magana ba sai murmushin da yayi yace kai akwai da wani zance wallahi hindatu fa matatace ka sani.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,

77
Idan daddy ya tafi baya wuce kwanakin da na fada a baya sai gashi wanan tafiya har ya gwauta kwana ashirin da biyu a kano.
Baya kiran mu kamar yadda ya saba kiran mu a baya idan yana can sai jefi jefi zai dan kira sama sama yaji lafiyan mu.
Sai dai abinda na dan kula dashi shine yawan kiran Ihisan da takanyi musanman ma da dare naso na dan gane wani abu amma sai kuma nai tunanen kila rashin uwar ta a gidan yanzu yasa yake yawan kula ta din.
Ranan sai gashi ya dawo sai dai ya fada ya dan yi baki kadan mun tare shi da murnan ganin shi sai dai ba wani walwala sosai a tare dashi sai na dauka duk gajiya ne hakan kawai ya kama shi.
Sai da yai wanka ya huta bai dade ba yafito ya fita daga gidan ina mai tayin abinci yace dani barshi kawai bana jin cin abinci yanzu.
Ga

Download complete TXT · Novel page