Kanin Ajali

Chapter 15 of 34

wurina ya kyale ni ba yadda zaiyi yayi fushin shi ya gaji har ya sake don yasan na fishi gaskiya a kan zancen zanin.
Iskanci ko yanzu baijin kunya a gabana zai dinga waya da yan mata suna hira da farko naso in sa mashi ido sai naga zanja wa kaina damuwa gurin kyale hakan.
Ranan ina zaune wata ta kirashi ya dauka sun fara fira ke nan na wauce wayan daga hannun shi na fara dura mata ashar cikin dakiyar fuska ya dauka zanji tsoron shi dana saba ji ne ya fara daka min tsawa akan in bashi wayan har yana fadin you very stupid ki ban wayana nace.
Nima tsawa ba daka mai take na birkice mashi a dakin yana gudun iyayyen shi suji ko daya daga cikin yan hayan mu suji.
Girman shi ya zube a gurin su don idan zai shigo gida sai ya daure fuska kamar hadarin marance fuska ba annuri ko kadan.
Zakace shine maigidan da muke cikin sa yadda yake basu doka da iko a gidan nasan badon baba yasa yan hayan ba da zai iya koran su ma.
Ganin da gaske ina shirin tona mai asiri yasa ya sauko yana fadi amma ke baki da wayau dafa budurwan yayana sa,idu nake waya kin dauka ko budurwa tace.
Da yake wawiya nake sai na yarda da maganan shi na miko mai wayan yayi saurin kashewa ya kuta ya fita daga dakin bai dawo gida ba sai da dare ya raba sosai ya dawo.






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: ZIM




Ina zaune ina kare mai kallo yana shirin fita da yamma don duk yamma haka yake wanan al,adan ya tsala ado a jikin shi ga kamshin turare mai tsada yana tashi.
Sai daya gama shirin shi yana batun fita nace gida nake son zuwa in duba su yau kamar baiji abinda na fada ba ya kara dauko kwalban turaren shi ya kara fesa ma jikin shi yadda yake so.
Bakajini bane na fadi daga inda nake zaune ina kallon shi cikin tagumi yace najiki mana sai dai ban san abinda zaki je yi gidan bane.
Zuwa zanyi in gaida su kawai don nasan in ka fita ba lalai ne ka dawo da wuri ba yace ni na rasa ma may zance maki hadiza .
Wai da kike dadin zaki ki duba su ina ko dazun naga shigowan Baffa gidan nan shekaran jiya kuma summaiya sun zo nan gurin ki.
Nace su kadai ne a gidan halan yace ke kika damu dasu su basu damu dake ba ni dai da zaki bi shawarana ki hade kan uan uwanki kuzama tsintsiya daya madaurin ku daya ku hudu da zai fi maki alheri.
Nace ban gane may kake nufi ba har yanzu yace eh bazaki gane ba muddin baki kwantar da hankalin ki yanzu kin fahinci magana na ba.
Don yawan zuwa gidan nan da kike yi ko wani lokaci yana daya daga cikin daman da zasu samu su cinye maku kudin ku idan ya fito nan gaba.
Wani kallo na watsa mashi tare da fadin kudin ina baba kabiru ne mai muna fafutukan fito dashi yace ko yanayi ai da wata manufa yake yin su don shima ya debi rabon shi daga ciki.
Kara mai kallon mamaki nayi don jin furucin shi akan baba kabiru din yace yes waye bai san da dukiyan ku yake tunkaho ba a garin nan.
Sai ku da har gobe baku wayau da zaku gane hakan sai idan sun gama maku barna zaki dawo kina fadin dama na fada maki kinki ji a baya.
Ni fa ban fahinci inda maganan nan naka ya dosa ba har yanzu zama yayi a kusa dani don ya fahinci banda saurin zurmawa idan ya tsarani da magana.
Yace ni abinda naga yafi maku shine kiyi kokari ku hade kai da yan uwan ki tun yanzu ta inda bakin ku zaizo daya a kasa gane tsakanin ku.
Nace ai muna hakan ko yanzu wani shu,umin kallo yayi min tare da fadin ke har yanzu dai yarinya ce hadiza ana gabas kina yamma ni zan fita idan na samu lokaci zan maki bayani a tsanake.
Daga haka yasa takalman shi ya fita kallon inda yaci abinci nayi naga ledan kazan daya shigo dashi da rana yaci yashe saman dan table din da muke cin abinci a falon namu.
Naja tsuki tare da mikewa ina duba ledan kazan na samu ya rage dan guntu a ciki zama nayi na karasa cinye sauran tare da sude kasusuwan da bai karasa cinye tsokan su ba na gama na kwashe kayan na fita dasu.
Gyaran daki nayi na fita gurin girki na don kada yamma yayi min don nasa a raina yau zan shiga gidan mu da dare.
Da sallama na na shiga gidan namu inda na samu yan gidan mu a dakunan su suna kallo da murnan ganina kowa ya tare ni muka shiga gaisawa dasu.
Sai da nabi da kunan matan baba na gaidasu na dawo dakin yan matan gidan mu na zauna muna hira sai tsokanana sukeyi wai ciki yasani muni.
Anty ne ta shigo dakin ta zauna don ganina a cikin dakin tana fadin wai ke haka zaki haihu daki ba komai a cikin sa har yanzu hadiza.
Ko kun gyara dakin naku ne yanzu muzo musha kallo mu kan tana fadi a cikin zolayata don takanyi wasa damu wani lokaci.
Fadin haka yasa kanwata fadin wanan shegen macuci ai itace ya samu har ta yarda da hakan idan da nice wallahi sai ya fito min da kudin kayana wallahi.
Take na daure fuska don jin ashar din data dura ma Jamil dina alhalin yanzu ya gama maganan alheri a kan mu.
Sai anty ne tace kuna zagar mata miji a gaban ta yanzu kuna samun sabani a gidan nan bandai sake fuska ba har lokacin har ta gama dan hiran da mukeyi sama sama da ita a dakin ta fita.
Can takira yarta dake dakin tare damu tayi mata wani abu lokacin na samu fadin yanzun ke da kanki kikewa Jamil haka idan wani yai min ashe ba zakiji haushin sa ba summaiya.
Tace wallahi halin mijin nan naki yana ban haushi anty dubi yarda kika koma don Allah kamar wata bakauya dake don babu mai kallon ki ya dauka wai kin yi karatun boko.
Nace to ki matsa kowa bada yadda Allah ke masa tsarin rayuwan sa ba ko kin naso ne in dawo wanan gidan ne kuma mu kama ganin laifin juna daku.
Nan dai na nuna mata bacin raina akan abinda tayi min din har sai da ta bani hakkuri na sauka nace da ita ta samu lokaci ina son ganin ta ita kadai idan zata zo kuma ta zare jiki tazo ita kadai tace min taji.
Ina shirin komawa baba ya dawo do yayi tafi ashe kwana biyu bai gidan yana dawowa muka fita muka gaida shi yake fadin a,a hadiza kin shigo ne ?
To ya kuke ya mijin naki na amsa da suna lafiya suna gaida ku baba yace lafiya dai ko nace lafiya baba na daizo gaida ku ne kwana biyu ban shigo ba na duba ku.
Yace cikin nuna jin dadin shi ga hakan mun ko gode naji dadin hakan sosai adaita hakkuri don Allah komai na duniya sai da hakkuri ake cin riba nace na gode baba daga inda nake tsugune.
Har na mike ya sake fadin ina ganin kwanan nan zancen kudin ku zai tashi don munyi magana da wanan mutumin dake muna hanya kudin su fito a cikin jin dadi nace Allah ya nufa baba na kara mai godiya.
Na fito ban dade kwarai ba don daren da yayi na yi masu sallama na nufi gida sai da yan gidan mu suka rakani har gida muna hira suka juya suka dawo gida.
Har lokacin na sami Jamil bai dawo gida ba nima ban sa rai da zai dawo haka da wuri ba don sai dare yayi sosai yake shigowa gidan.
Washe gari ya gama barcin shi karfe goma da wasu mintina ya bukaci ruwan wanka na kai mashi bandaki kafin ya fito na aje mai abin karyawan shi ko a inda na saba aje mai ina gyaran gida ne ya kwala min kira.
Nazo yake fadin wa zai sha maki kunu haka babu sugar ko kosai nace yau baba bai sawo muna kosai bane kuma sugar ya kare tun jiya na fada maka.
Ya ja tsaki tare da rufe kwanon kunun ya dan mayar da kan shi saman kujera fuska a daure nace jiya naje gida baba yana gaida kai ya mace wai kudin mu ya kusa fitowa.
Wani irun dagowa yayi daga yadda yake kwance yana fadin saboda Allah nace wallahi ko jiya baba yake fada mi hakan da naje yace ashe mun kusa warkewa ke nan nace insha Allahu.
Nan ya fara sake min hira a ciki sakin fuska inda yake shiga ba nan yake fita ba jin dadin hira yau yasa na sako mai zancen da anty tayi min.
Take ya bata rai ya fara fada yana fadin ina ruwan ta da rayuwan mu ne nifa kwata kwata wanan matar batai min ba a rayuwana nasan duk wani cin amana da baba keyi da zuginta ne yakeyin shi.
Nace niko banga hakan ba gaskiya don bata saka kanta a cikin maganan mu yace ke may kika sani so take kowa ya koma yadda take wai ita ta waye din nan .
Ranan kan hirane zamzam dashi ba wani nuna bacin rai a tare dashi fitan da baiyi ba ke nan har mahaifin shi yana tambaya ko lafiya yake gida har yanzu.
Yace lafiya yana dai hutawa ne a gida yau tun wanan ranan muke zamzam dashi kanwata tazo na danyi mata nasiha kamar yadda Jamil din ya lurar da mu muyi din.
Bata ki ba sai dai cewan da tayi amma kada mu nuna yadda har za a fahince mu a gida tun daga wanan ranan muka dinke tam dani da yan uwana da muka fito ciki daya.
Babu mai gane jan mu komai namu a hade mukeyin sa a gidan ga summaiya Allah ya dora ma anty sonta a rayuwan ta komai ta samu ko zatayi sai tace summaiya dai har yan uwanta suna sata gaba akan hakan da take nuna ma diyan cikin ta bata damu dasu ba sam.
Bayan kamar sati uku dayaji shiru shi da kansa yace mu shirya muje mu gaida mutanen gidan namu nayi mamakin haka sai dai naja bakina nayi shiru tunda gidan mu zamu tafi.
Mun samu baba a gidan ya tare mu a cikin fara,an nan nasa suka dan taba hira da Jamil din ina gefe ina jin su sai dan zungura na Jamil keyi akan inyi maganan kudin mu mana a gurin baba don ya gama kitsa min abinda zance tun a gida gamay da kudin da mukaji shiru.
Can nace baba har yanzu dai wanan mutumin bai kira ba ko cikin mamakin wani mutumi nake nufi baba ya tambaye ni nace wanan mutumin da zancen kudin mu ke gurin shi baba.
Baba yace wallahi har yanzu banji wani abu a guri sa ba amma dai barin kira shi muji yanzu komay ake ciki akan zancen nan ya daga waya tana ringing gab da ta katse ya dauka.
Suka gaisa a cikin harshen turanci suke magana baba yace yaji shiru yace eh kasan abin da wuya amma dai insha Allahu ana sa ran fitowan shi a cikin wanan shekara din sai dai kasan ba duka yake fitowa ba za a kasa shi kamar kashi uku ne haka.
Baba yace haka abin yake yace yadda tsarin namu yake ke nan ai dama sukayi sallama bayan baba yayi mashi godiya ya katse layin tare da dubo mu yace kunji ko.
Abin sai kaman za a kama sai kuma aji shiru duk dai wani abinda suka bukata na riga dana gabatar masu dashi ko akan takardan nashi.
Ya kare da fadin Allah dai ya jikan wani yai masa rahama muka ce amin don ni nama manta rabon da inwa mahaifina addua irin haka yanzu idan ba raina ne ya baci zan tuna dasu ba.
Nan dai mukai wa baba sallama muka fito tare da yiwa sauran mutanen gida sallama ganin tare da shi muke yasa yau ban samu rakiyan yan gidan namu ba har gida.
Tsuki yai ta ja har muka kawo gida yana dura ma wanda bai sani ba zagi wai sallon suci kudine yasa suka rike kudin har wanan lokacin ace mutum ya mutu har kusan shekara biyar kudin shi bai fito ba.
Ni dai ina jin sa sai jefi jefi nake saka mai baki a zancen nasa sai kawai kwana biyu angulu ta koma gidan ta na tsamiya ya tayar da halin shi na yawon dare da yakeyi sosai.
Nan dai nayi ta zaman hakkuri ban faye damuwa da halinsa ba sosai a cikin haka maganan kanwata da wanan mai nemanta usman magana tayi karfi sosai akai masu baiko a tsakanin su.
Don yafi jamil dina hali ta ko ina bama za a hadasu ba kuma ya dan girmay ma Jamil din ga shekaru shi karatun shi yasa ma gaba sosai don gidan su suna karatu har nisa .
Ba irin Jamil ba da yasa karyan duniya a gaba kuma a haka nake son abina kamar in hade shi ba dama wani dan gidan mu ya fadi maganan shi a gaba na koda kuwa mahaifan mu ne.
Sai dadin hira yasa na kwashe na fada mashi abinda kace mai wani fa mai miji don a yadda mukai alkawari a tsakanin mu sai nake ganin ni kadai zai zauna dani har tsufa mutu ka raba takalmin kaza.
Sai ya dibi kwanaki baya garin yana gurin yawon shi na banza zai dawo ga matsin daga wurun iyayyen shi dana fara fuskanta yanzu daga gare su tunda suka lura komai ya kare min danazo dashi daga gidan mu sai dan kamay kamay da nakeyi.
Ina ganin yadda mata sa,anni na suke kwaliya gwanin ban sha,awa dasu niko babu hali sai kamay kamay idan buki ya kamani dole in tafi.
Wani lokaci ina ji ina gani zanki zuwa bukin dangi daya dace ace na tafi don nasan yarda zan fito tsumai tsumai a gurin ina labe labe .
Kowa tausayina yake ji ga abin magana ba halin a fada min gaskiya in kwashe in fada mashi ya tsiri yin gaba da mutum take zai nuna masu hakan.
Shiya kowa ya kawo ido ya sa min dashi ana kallona don karya fure take bata yaya ni duk wanan bai damuna tunda dai muna zaune lafiya da mijina komai yayi.
Idan yan uwana sun zo suna ban sha,awa yadda suke fita tsab dasu har ana kwatance dasu a gari saboda iya kwaliyan su da fita niko ganinan kullun a rabe a gida.
Sai wani hali da yazo min yanzu dashi na ganin ya rabani da kowa daga cikin kawayena da mukayi makaranta a tare muna dan hurda dasu.
Sai ya nuna min shifa bai son suna zuwa min gida duk yadda zanyi in kore su dole inyi don dai kawai a zauna lafiya dashi.
A kwai wata kawata da tazo min muna zaune muna hira ya shigo suka gaisa dashi bayan ya shige ne take fadin hadiza dama mijin ki ke nan nace ina dariya kin san shi ne ?
Tace uhumm gani nayi dai kamar na sanshi a wani guri ashe a unguwar su yana neman wata yarinya anan ta sanshi sai dai bata fada min ba sai bayan ta wuce ne ya hau fada dani.
Wai shi bai son kwashe kwashen irin kawayen ga yan iska ya fa santa ba yarinyar kwarai bane sosai don haka kada ya kara ganin mu a tare kiri kiri ya hana wanan hurdan sai daga baya nake jin labari a gurin kawayen mu a inda ya santa yana gudun ta fada min komai inji.
Sai dai abinda na kula dashi yana matukar son yaga kawaye yan karya sun zo min nan zai fara rawan jiki ya fita ya sayo kayan sha ya kawo muna.
A zauna dashi ana hira da wasa da dariya har su wuce sai hakan ya fara kulle min kai don na rasa gane gabas din shi shida yace bai son kawaye sai inga idan wasu sunzo min yana rawan jiki wanan ke nan.
Ina ji ina gani banda halin shan abu mai sayi a dakina sai na saya ga cikin dake gare ni yana sani shan abu mai sanyi sosai.
Sai dai ban samu wani lokaci kuma banda canjin da zan saye a tare dani ga fridge dina Jamil ya hada dashi ya fitar yace wai karamine aka saya min.
Haka yasa yanzun nake kama kama da wahalan sayen abin sanyi in jika makoshina dashi ko tausayin halin da nake ciki baiji ko kadan.
A cikin haka har watan haihuwana ya kama inda na koma gida don haka aladan gidan mu yake haihuwan fari a koma gida a haihu a can.
Shi da kanshi ya matsa min tun watan bai tsaya ba yake damuna wai yaushe ne zan koma gida ne har mahaifin shi ya kama mashi shima yana fafin haka kamar sun gaji dani a gidan ni da gidana.
Haka dai na koma gida wurin haihuwa inda na dauki wasu satituka ban haihu ba ina zaune a gidan mu sai ya ga dama yake zuwa dubani a cikin sati sau daya.
A cewan shi wa kada ace yayi rashin kunya idan yana zuwa nan ko yana sheke ayyan shine a gari kawai da yab mata tunda shi dan karyane.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: IZ


Jamil zai dan zo ya dubani kacal yake zuwa a cikin sati a haka har haihuwa yazo min Allah ya sauke ni lafiya na haifi yar diya mace mai kama da mahaifinta sak.
Murna wurin yan gidan mu ba,a cewa komai haka ma yan gidan su Jamil gwargwado sunzo sunyi barkan haihuwa su tare da farin ciki.
Ba wani abinda suka kawo

Download complete TXT · Novel page