Showing 33001 words to 36000 words out of 299981 words
gaban yaron amma gashi maigirma babban bako ya zo gurin yaron,
Shima,shugaban na wanan kasar diban wanke yayi yana dan juyawa yayin da,sauran yan tawagan suka shiga diba suna kallon
Kowa sai yabawa da kyau da,girman waken sukeyi gwanin ban sha,awa,,,
Nan ya jawo irin dawan da Hamza ya shigo dashi filin shima yana dubawa a hanakali,
U
Idanuwan jamaa yoyyy a kasu don su azaton su laifi hamza din yayi,
Sun dauki lokaci a tare da,Hamza suna,mashi yan tambayoyi ya ba basu amsa sai cewa,suke interested,
Daga karshe dai aka,rubuta sunan hamza din daga,cikin wa yan da za,a bawa kyauta a gurin,
Nan aka karbi sunan shi aka juye wanan kayan a cikin wasu robobi na gwajin kayan agric din da aka zaba,
Hamza ya koma gefe guda ya na sauraren su kamar yadda suka umurce shi da yayi,
An dauki lokaci mai tsawo kafina agama wanan gasar gwajin kayan amfanin gonan da,akeyi,
Nan aka soma kiran sunayen mutane ana fadin iri abinda mutum ya,burge bakin dashi daga fanin abinci dabbobi da kuma kayan ruwa,
Can kamar a mafarki Hamza yaji ana kiran sunan shi inda ya,fara ratsa taro don zuwa inda ake kiran sunan shi,
Nan wanan baturen ya daga hannun hamza yana fadin cewa Hamza matashin da yazo na,daya gurin nuna dogaro da kai har ya kawo amfanin gonan shi da,full confidence,
Ga kuma waken da yakawo gwaunati tanq bukayar wanqn irin don wani gwaji da zatayi a kan shi don haka gwauti ta,sayi wanan waken akan gudu naira,,,,,,,
Haba guri ya rude da,sowa da ihu da kuma tafe daga yan kallon da,sukazo na,sassa daban daban na kashen Africa,,
Inda wanan bature ya nemi hamza da ya bashi full address din shi da in da yake da zama,
Haba aikuwa hamza yana karba,sai kawai ya,saka kabbaraza fili da cikin zuciyar shi,
****** ********* ******
Ina zaune gurin dana idar da sallah na daga hannaye na biyu sama ina rokan Allahya rufa muna asiri duniya da lahira,
Ina gab da zan sauke hannaye na ji murya Umma a cikin murna tana cewa o, o Allah nagode ma,Allah mun godema bisa wanan baiwar da kai muna ,
Ina kuke yaran nan kufito kuji abin arzikin da ya,samay mu a gidan,
Jin abinda ta fada yasani saurin mikewa zuwa kofan daki do ganin may Umma kewa farinci haka,
Babu kowa agurin na dai fito sai naji tana cewa yau kan Allah ya nufa Hamza ya samu yar ga Allah yasa shi cikin zabbabu,
Yar fara wace ina ga ban taba yinta ba tun zuwa na gidan nasake ina cewa masha Allah ashe yaya Hamza Allah ya karba addun mu,,
Uguwa baki daya zance ya karade ko ina kowa da abinda yake fadi a bakin shi,
Wasu har dakari sukeyi wai har da mota aka bashi wasu suce ai mashin ne aka,bashi,
Ga yan murna sun fara shigo muna gida gashi shi mai abin arzikin bai dawo gida ba har wanan lokacin,
Saboda farin ciki Umma taje ta,auno muna shimkafa a,makwabta mudu daya tace nayi tuwo da,miyar sobarodo da busashen kifi,
Ina aiki ina Allah Allah kafin na gama kafin yashi nayi wanka na dan kimtsa irin da naga mata sunayiwa maza jen su idan sun fita gurin neman kudi,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
ZAINAB IDRIS MAKAWA👑SARAUTAR MATA👑
0⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
RABBI LA TADHARNI FARDAN WA ANTA KHAYR AL-WARITHIN,,,
YA UBANGINA KADA KA BARNI MAKADAICIN ALHALIN KUWA KAINE MAFI ALHERIN MASU ALHERI,,,
Ranan haka muka wuni zugun zugun a gidan ba wani dadi rai alhalin tun bayan daurin aure bamu ga baba a gidan,
Ba wani bukin da akeyi kamar yadda mutane sukayi zaton yi don uwar mai buki bata da shirin buki,
Sai dai yan uwan baba sun dan taka rawa gurin ganin cewa, sun hada dan kudi sunyiwa mutanen dake nan dahuwar dafa dukar shikafa,
Ummi suna daki da yar uwar ta acikin jimamay abinda zai fito daga gurin mutanen da,suka kira da yan uwa na wai iyayyena,
Mutanen da,sam basu damu dani ba a matsayin yar su,
Don ni da farko ma nayi zaton cewa ko banda ubane don ganin irin yadda ake tsangwama min a,gidan Baba Mudi mijin uwata,
Alhalin gashi shine uban yayena da kuma kanne na
Ni kadai ce Allah bai nufa nafito daga tsatson shi ba,
Sanadiyar fitar da mama tayi a gidan bayan haihuwan yaya Audi,
Na fara fahintar hakan ne don ganin irin tarin damuwar da mahaifiyata take shiga a kaina a gidan,
Nayi zaton cewa Baba shine mahaifina amma saboda irin bakin cikinnda yake yawan cusa wa mahaifiyata dani agidan yasa na soma fahinta cewa bashine mahaifina ba tun ina karama,
Abu na biyu shine irin yadda Baba ya dauki son duniya ya,dora a kan yan dakin su Kubura duk da dai namu diyan daki maza ne,
Gashi da azahiri zaka zaci duk diyan gudan bugu daya yake masu a kan so,
Amma idan ka tsaya sosai ka natsu sai kagano tarin kin jini da yakewa diyan mahaifiya na,
Dan abu kadan zasu yi kaga kyara da hanttara daga gare shi, kodan kuskure kadan ne yanzu za,a jishi dasu har ya hada da uwar mu,
Sai da idan ka shiga gidan zaka ga matan gidan suna normal life din su a tare ne tankar babu k8shi a tsakanin su ,
Hakan ma diyan su komai a tare sukeyi komai babu wari a tsakani nice kawai suke nunawa wari a gidan babu boyo ko shayi,
Fitar mahaifiya ta agidan yadda mama Rahana ke fada min tace ya faru ne ga hadin kan ds matan gidan sukai mata wanda matsi yai yawa har takai yan uwan Ummi sun bukaci da yasauwaka mata a lokacin ,
Bayan komawan Ummi garin su sokoto ne tana cika idda ta,auri wani dan uwansu saidai shi bafillacen daji ne yana zaune a gari yana yar sanaan dabbobi,
Sai kuma zaman ba,a kai ko ina ba ya,watse saboda rayuwan ta yana gurin "ya"yan ta da ta bari a gidan Baba Mudi,
Wata uku ta kashe auren tafito ashe da akwai rabon ciki a jikinta gashi har ta cika idda ana batun komawa gidan malam Mudi sai ciki ya,baiyyana don haka aka dakata dole sai da ta haihu da yar jaririyar ta ta tare a gidan wanda tun a lokacin take ta samun wani kalubalen rayuwa daga maigidan dama abokan zaman ta dakeyi a boye,
Suma abokan zaman sun gwanmace dawowan Fatima gidan ne akan sabon auren da yaso ya kara a lokacin,
Don haka zaman nasu ya kara zama na kwarai babu mai tsangwama,wa wani daga cikin su a,fili sai dai kishin boye wanda baa rasa ba can,
Wani ikon Allah gaba daya gidan malam mudi babu yaro mai hazaka irin Aisha din,
Duk wani karatun da zatayi, zaka,ga tazo na daya a gurin amma duk da hakan babu yabon da take samu, daga gurin maigidan sai ma ya gune cewa andai batane kawai ba,wani ilimi da tafi su dashi,
Haka rayuwan Aisha ya kasance a gidan da dadi ba dadi, har zuwa wanan ranan da Aisha ta taimakawa Baba tafitar dashi daga kunya,
****** ********** ******
Gidan su Hamzs babu wani abinda suka gudanar akan zancen don basu ji komai daga gurin Baba ba,
Suna sauraren dawowan shi don anzo ance baya gida tun da safe,
Ashe shi baba tanufi sokoto ne gidan iyayyen Aisha din ya,sanar dasu irin yadda abu ya kaya,,
Da,farko kanin mahaifiyar Aisha ya dauka suka tafi can garin gurin yan uwan mahaifin yariyar don shi uban yanzu bai kusa ya kara gaba ko,,
Bayan an fito, daga massalaci suka zauna dasu inda a cikin girmamawa da mutuntawa suka karbe shi don ya rike masu jinin su a gurin shi,
Nan Baba ya,fara koro masu da bayani abinda yake tafe dashi tare da sheda masu cewa yazo ya basu hakkuri a bissa kuskuren da yayi na rashi sanar da,su
Har ya shige gaba ya,daura wa yarsu aure ba tare da sanin su ba,
Sunnuna rashin jin dadin sanar dasu da ba,ayi ba amma kuma sunyi mashi godiya da nuna cewa yana da hakki a kan yarinyar ai tunda shine ya tayar da ita, a gurin shi,
Nan suka cecmai idan lokacin da yarinya zata tare a gidan mijin ta yayi ya sanar dasu zasu shigo gurin bukin , tare da abinda Allah ya hore masu,
Wani irin sanyi malam Mudi yaji na samu mutane masu saukin kai, ya kara,masu godiya yabar su suna mai godiya, sumq din, akan rikon yar su da yayi har da aurar da ita,
Sun hado shi da dan tsaraban kauye cewa yakaiwa iyalin shi agida ai masu godiya,
Ba karamin farin ciki Baba ya,dawo dashi da ruggan mu gurin iyayyena,
Sai da dare ne ya samu iyayyen Hamza suka dan tattauna dasu yana mai basu hakuri akan sauyin da suka gani ,
Inda yake cewa yai hakane don ya gwadawa Saude da yar ta cewa idan har bai da iko da isa akan yar cikin shi,
To ga diyan bayin Allah sunyi mashi biyayya yadda ya kamata,
Sun yake zancen cewa zasu ba uwar Aisha dan lokaci yadda zasu yi dan shiri a tsakanin su,
Hamza wanda abin duniya ya kaiwa,ko ina, a rayuwan shi yarasa yadda zai yi da,rashi,
Aisha yar karamar yarinya kuma kazama dabata ko san yadda mata,suke gyara,ba,ahine wai yau take a matsayin matar shi,
Ya dan gyara juyawa daga saman yar mokaddan katifar da yake a,kwance sama yana mai nazarin siffan Aishan yarinyar da koda yaushe a cikin hijjab take a dunkule baka taba gane kalar surar ta,
Washe gari yan abokan shi da suke zama a,shago suka,dasa mashi sheri da,wasa irin ta angwanne,
Umma Rabi ce sukai ta tausan shi har ya hakkura da zancen auren Aishan don gudun kada ya budawa malam Mudi kasa a ido,
Bayan sati, guda da,daurin auren su ya na zaune a bakin shagon shi suke jin ana yekuwar cewa mai gari yana neman duk wani wanda yasan cewa shi manomi ne don akwai bayani akan gagarumin wasan gwajin amfanin gona da za,ayi, a garin,
Wanda manya mayan baki zasu shigo daga sassan kasan nan ta ko ina don kallon wanan amfanin gonan na manoman kasar,,
Jin wanan shelan yasa mutane tururuwan zuwa kofan gida sarki don jin karin bayani daga bakin shi,
Abinda yai sanadin jefa zukatan mutane da dama a cikin nazarin shiga wanan gasar ,
Daga ciki harda Hamza cikin masu nazari yadda zasu kokarta,su kawo nasu amfanin gonan a,wajen gwajin mai taken suna AGRIC SHOW,
Daga dangin Hatsi, kayan labbu, dabbobi kayan ruwa da,sauran su,
A lokaci guda duk gari ya rude kowani gida zance a buguda akeyi kawai,
A wanan lokacin kuma uwa da diya a gidan malam Mudi suna a cikin matsi da,tsangwaman matan gidan,
Duk da,su suka nuna,basu son auren Hamza din da kansu amma,suna ta,sake magana a tsakar gida,
Har da,atika wace take bayan Saude da,yar ta,don muna funci kawai don son halin kishi,
Hakan yasa,a koda yaushe mutum ya shigo gidan zai samu Fatima daki da,yaran ta,suna yar hiran su ,
Aisha wace zuwa yanzu abin duniya ya kaiwa ko ina tana,mamakin irin yadda tai wanan subul da,baka har tace wa Baba ayi wanan hadin auren da ita,
Alokacin tausayin Baba ya,raja,a a kan ta har yakaita ga furta,wanan zancen a gaban shi,
Umma Rabi ta,umarci Hamza da ya hada yan abubuwan bukatan rayuwa,a,kaiwa, Aisha a gidan su,
Hamza wanda har yanzu ganin zancen yake kaman a mafarki don har yanzu ya kasa gaskanta al,amarin cewa wai Aisha a matsayin matar shi take,
Sabulun wanka Sabulun wanki omo manshafawa dasauran
Sune aka hada a cikin wani leda akabawa Halima sister din Hamza din takaiwa Ummi Fatima, kayan ace inji Hamza din,
Tun shigowar yarinya gidan da kaya su Atika da mama Saude suka shiga ya da,magana a tsakar gida, da cewa,
Iyakar ke nan tsiya tsiya ankawo wa Amarya kayan tausa, ,
Wanan gayar tsiyar akai shi can gurin mubukata irin sa,amma ba nan ba dai,
Atika tace ai adaiyi mugani uwa,kwance diya zaune, duk a kare a tagumay,
Daga cikin daki Kubura ta,dago labule don taga abinda ake zance akai yayin da,tai arba da kaunar Hamza na kokarin shiga,dakin Ummi Fatima da dan leda yellow mai layi layin baki, dan kayan da baikai rabin leda ba a cikin sa,
Tace tsiyatsiya ke nan dama a can ya,dace da akai ba nan ba,
Ni kan ai nagodewa Allah da ya raba ni da gayar tsiya,
Fatima ta tari yarinyar da mutunci tare da godiya,akai akai da haba haba da ganin ta a cikin mutunci inda tabawa yarinyar naira,Ashirin tace tukwaici ne,
Kaf zance abin da ya,faru a gidan malam Mudi ba abinda Halima ta rage a bakin ta,
Gaba daya ta tsiyayewa Umma Rabi shi a kunnuwan ta kaf,
Abinda yai matukar bata mata rai sosai yadda ake cewa wai suna yi,
Saukin ta,guda,shine yadda, Ummi Fatima ya karbi yarinyar a,cikin mutuntawa,
Hamza yana,tsaye daga bayan Umma har yarinyar ta,gama bada labarin irin cin fuskan da akai masu a gidan,,
Muryan shi Umma taji daga bayan ta ya fadin Umma kada ki damu da zancen su don su sai kiji fiye da haka daga gare su, ma, ai,
Yafita zuciyar shi na mai kuna yadda yake jin zafin irin wanan gorin da Saude da,yar ta,har ma,da,abokiyar zaman ta dayan,
****** ********** ******
Duk abinda Aisha ke yi hankali ta yanzu ya koma ga zancen Baba, da yake mata a ranan daurin auren ta,
Ta dan gyara kwanciyar ta a hankali tare da dan lumshe idanuwan ta tana mai dan hade miyau masu daci,
Ta dan kara gyara lumshe idanuwan ta tana mai sauke ajiyar zuciya a hankali,
Ki kwantar da hankalinki Aisha wanan aure naki Allah yai mashi albarka Allah yasa muce gwamma da akayi,
Saudayawa alheri kancin ma,bawan shi ta hanyar da bai zata ba, arayuwan shi,
In har Umma Rabi da danta zasu rike min ke amna Aisha sai ince zaman ki a,gidan su yafi min zama a gidan nan,
Zaman da kike a gidan nan a cikin wahala, tsangwama da shagube,
Sun manta da cewa Allah ne bai nufi ki fito daga cikin tsatson su ba kika fito a can wani gurin na daban,
Wanan hattaran da tsangwaman da suke maki a gidan nan kiris ya rage hawan jini ya kamani a kan hakan,
A hankali Aisha tafara dan kuka a hankali don kada mutanen gida suji muryan ta,
Washe gari sun tashi da,safe ba fashi daga duk wani aikin da Aisha din ta,saba yi a gidan da,safe,
Da ita akai komai amma sai Umma saude taki saka,wa Aisha dan kunun kokon da take saka ma ko wani yaro a gidan da,dan kosai din su kwara biyu a matsayin abin karyawan su,
Yau Saude ta hana wa Aisha wanan kosai din haka abincin rana ma again,
Malam Ummi ta sama da zancen take tambayan shi ko shine ya hana a sakawa Aisha abin karyawa a gidan shi,
Kafin ya ba da amsa buty suka ga mama Saude wace take kamar a jirace a bayan su ta,shigo tana cewa,
Nice nan na hana mata ba wai wani yasani yin hakan ba,
Ai aure take yanzu don haka sai taje can gidan mijin nata a saka mata shida keda alhakin ciyar da ita yanzu, don duk wani nauyi nata ya rataya a kanshi yanzu,
Malam Mudi wanda kr reacting kamar wani shanyaye sai cewa yayi ai zata tafi gidan mijin nata kowa ma ya huta ,
Ummi bata samu bakin magana ba,sai kallon yadda Mama Saude ke faman budan baki tana vin mutunci wa mijin nasu,
Ummi ce ta katse su da cewa Aisha zata koma gurin mamanta Rahana har zuwa lokacin da zata tare a gidan mijin ta tunda abinci da ake bani ni kaina ba isa na yakeyi ba balle nace zan dinga ci da ita,
Daga fadar haka tabar daki inda ta samu yar ta Aisha take fada mata cewa ta,shirya zuwa gidan maman ta Rahans,
Da sauri Aisha ta dago kai tana kallon mahaifiyar nata don son tagano ko anyi wani abu a tsakani,
Amma sai bata iya hango komai ba a fuskan uwar nata,don haka ta dan mike daga zaune ga yunwa,da ya damay ta a,rayuwanta,,
Yan tsunmakaranta ta hada a cikin wani bakin leda bag mai giwa,
Ta,dawo daga kofan daki ta zauna a rakube tana kallon yadda yau zata tafi tabar Ummin ta, a cikin wanan yanayin zaman hakuri da tsangwama da take gani daga kishiyoyin ta ga,goyon tagwaye a,tare da ita ga,wahalhalun duniya iri iri a gidan,
Bayan Ummi ta goya hassan ta umurci Aisha da tagoya hussai din taku ma umurce ta da ta je suyi sallama da su mama