Showing 36001 words to 39000 words out of 299981 words
saude da,Atika,
Ba,wani amsan da ta samu sai dan tabar bakin da,suke suna cewa umma ta gaida Aissha yau kan zamu sha iskan rahama gida ba yar agola a cikin sa, yar gola kiwon Allah ya isa,
Sai suka tafa tare da,shewa suna masu rangada guda,
Akarata can inda talauci ya yanke cibi mugani,
Tafiya suke duk zukatan su a,cakushe saboda bacin rai don har Ummi din, yau ji take tankar tabar gidan malam Mudi din gaba daya,
Suna jin shewan mutanen gidan a lokacin da suka fita suba cewa yau yar agwai an tafi,
Atika tace yau kin muna maganin wanan shigiyar yarinyan mai kama da mayya kawai,
Duk Ummi tana jin su amma ta kyalesu kawai suka,sa kai zuwa gidan Mama Rahana yar uwar ta,
****** ********** ******
Anty Rahaba ta gama komai na yinin ranan ta na,zaune daki ita da,yaran gidan suna kallo Ummi ta,shigo da,sallama,
Mamakin ganin ta su keyi a lokacin saboda ba,al,adanta,bane fitowa uguwa da,dare, irin haka,
Daya bayan daya yaran suka watse daga don bawa yan uwan guri saboda su sirint a tsakanin su,
Bayan gaisuwar da,su kayi a tsakanin sai yar shiru ya biyo baya nan mama Rahana take tambayan ko may kuma ya faru,
Ummi Fatima tana kuka tana bawa yar uwar ta labarin abinda ke faruwa a gidan su yadda matan gidan yanzu suka dauki kahon zuka suka saka mata ita,da yar ta,a gidan da kuma hana mata abincin da akeyi a gidan,
Ummi ta karasa acikin wani irin kuka mai ban tausayi, atake rayuwan yar uwar nata zuciyar ta ya, baci sosai take, magana a hasale da cewa ni wanan al,amari nagidan ku yana,daure min kai wallahi,
Yanzu ace har a hana ma wani abinci a cikin gidan ka kuma shi maigidan bai dauki mataki ba a kai
Nan suka yanke shawaran cewa Aisha ta zauna a gurin Rahana har zuwa lokacin da za,a kaita gidan mijin ta,
****** ********** ******
Zancen duniya baya boyuwa don haka,barin gidan Aisha da,kwana biyu labari ya fara kewaye uguwa cewa saboda auren da malam Mudi ya daura da Aisha ,
Su mama Saude sunyi sanadin da yarinyar tabar gidan da zama zuwa wani gidan irin tsangwaman da ake mata a gidan,
Haka zancen yai ta,yawo abinda ba,ayi aka dinga fafin cewa shi akayi a gidan har maganan yazo kunne Umma Rabi,
Hakankinta ya tashi don ji irin wullakancin da akaiwa yar mutane saboda dan ta,da ta aura don ba,a bari yai kunya ba,
Umma Rabi tasa,a,fara gyara daya daga cikin dakunan gidan inda yaran zasu zauna,
Tsohon part din mahaifin Hamza din wanda yake ciki da falo ne sai dai ba masu girma bane sosai haka sune ake tawa dan gyara don su zauna a ciki,
Dakin ya tsufa sosai amma dole haka zasu zauna din a ciki ,tunda basu da wani,
Yanzu rayuwar Kubura ko ba,a fada wa mutum ba yasan cewa ta zama wata yar birni sosai saboda irin yadda idanuwan ta suka,bude,
Shigar ta kawai zai nuna,wa mutum cewa ta sake fiye da tsanmanin mutum,
Yau suna da wani dan liyafa da su yi wanda zai hada matasa masu yi da zamani da a gurin,
Tayi kitson attachment ya mayar da ita kamar diyar yare,
An mata gyara fuska wanda ya,sauya yanayin ta daga na diyan musulmai zuwa na diyan kabilu,
Wani dogon riga ta,saka a jikin ta ya dane mata jiki sharp din jikin ta y fito tsab,
Sai faman kiran ta ake a,waya cewa tazo an fara taruwa agurin sha,anin nasu,
Uwar ta,sai murna,da farin ciki take ganin irin yadda diyar ta yanzu ta koma one in town,
Sai washe baki take yayinda,Atika mishon batta da musulmi take faman koda yarinyar agaban uwar ta,
Wani daga cikin diyan Atika ne yashigo yake fada masu cewa ga Baba nan zai shigo gida,
Da sauri shige daki ta zuro wani katon hijjab a kanta, ta boye takalmanta a cikin jikin ta,
A,a yau sai ina haka tace Baba littafin da muke hadda dashine zan karbi a gurin wata yar uwar karatuna tunda Aisha bata,nan,
Tasako zance Aisha ne aciki don Baba din ya ya ji dadi ya barta ta fita, zuwa inda zata,
Yashige part din shi inda ta,waigo tana,wa uwar ta dan bye bye din samun nasara ta fice abinta,
Gurin part din ya hadu sai kida ke tashi samaru da yan mata masu karamin kwakwalwa suna ta sha,anin su gungu gungu a gurin,
Kubura tana daga cikin masu gudanar party din haka zirga zirganta yai dan yawa a gurin,
Daga inda yake tsaye yana iya hango wanan yawan sintirin da take a guri,
Turawa yayi wani dan duniya yakira mashi ita kamar bazata zo ba can ta taso a cikin ragwada tana tako daidai har ta karaso gaban,
A dan tsiwace take cewa malam kai ke kirana tana wani taunar chewing gun
Yace a cikin kasaita da mu samu dan guri inda babu hayaniya da yawa,
Motar big show suka shiga wace ke daga gedaya a Parker wanan shine mafarin haduwan ta da Nura wanda yaxo mata da kudi irin wanda take bukata da mafarkin samu,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,
👑 SARAUTAR MATA 👑
0⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAHUMA AJINIR MINAL NARRR,,,
Wanan novel din kada ku manta amanace tsakani na daku Allah yasa muci gaba da rikewa Allah yasa mu dace yan uwa
Hakannan naci gaba da zama a gidan mama Rahana, inda nake zaune ba wani tsangwama komai,
Ina gudanar da,al,amurana cikin natsuwa da kwanciyar hankali,
Saboda gidan mama Rahana kowa yana nuna min so da kaunz a fili tare da yaba min hankali,
Sai nake ji a raina dama ace tun farko a nan din nake zaune ina rayuwana,
Matsalata guda shine kewar yan uwana da ke damuna tunda ban taba tafiya na barsu ba,
Yanzu duk wani mugun hali a,Ummi suke nuwa shi tare da hattaran ta da yan diyan ta,
A wani yanmaci lokacin ina da sati uku a gidan mama Rahana sai ga mahaifiyata tashigo da zancen wai zan tare a gidan mijina,
Zance da yadaga min hankali kenan gabadaya wanda itama mahaifiyar tawa hankalin ta duk a tashe yake, ita,ma,
Ummi tazowa da yar uwar korafin cewa bata aje komai ba akan zancen aure na yanzu gashi zance ya tashi,
Mama Rahana ta kwantar wa da Ummi hankali da cewa shi aure ai alheri ne daga Allah dazaran ka dasashi sai kaga hanyoyin Allah suna budewa ta inda mutum bai tsan mana ba,
Da irin maganganun haka har Ummina ta kwantar da hankalinta ta zurawa sarautar Allah ido
Yan sayaya akai min duk da bangani ba amma inajin yadda su mama da Ummi ke shawara a,dakin akan zance na,
A can gidan baba Mudi matan gida sai gori da habaici suke sakewa wai rana bata karya saidai uwar diya tai kunya,
Yau gashi aure ya taso ummi bata aje komai da zatai min aure dashi ba ga shi malam Mudi ba dama ya taimaka min don sun kai karan shi a gurin yan uwan shi cewa yana maida hankalin shi ga yar agolan gidan shi fiye da,diyan su sosai,
A tsayar da magana cewa a gidan mama Rahana za a guda nar da duk wani abinda za,ayi sai a kaini daki na,
Raban da,za,a kaini a,ranan ne aka,sakani a lalai don ba wasu tarin kawaye ke gareni ba ni,
Ranan na yi kuka kuka irin mai tsuma zuciyar mai sauraren ta ,
Don za,a kaini aure ba gado da shimfida irin ta,al,ada sai tabarmi da yan sauran tarkace kawai,
Zokaga murna a gurin masu son gqnin bayan don sai shewa da raha suke suna yadda magana a gaban kowa,
Cikin ikon Allah sai ga dangin mahaifina tare da na mahaifiya suka iso tare da mota fam da yan kayan su sai dai irin na kauyawa ne,
Isowar su yasa guri yadan rude sai kama baki ake ana mamakin abinda,su kazo dashi, anan sabon gulma ya fara tashi kuma
Da yamman fari yan uwa suka tasani a gaba wai naje muyi sallama da mahaifiyata da kishiyoyinta da,suka tayar dani,
Mun shiga gidan da,sallama banyi tsanmanin sun karba muna ba,sai dai naji muryan Ummina,
Mun shiga dakin ta tana zaune tare da,wasu baki mata mutum biyu yan uguwar mune da,take shiri dasu,
Can daga kuryan dakinta kadan na,samu guri na,durkusa a kafana,
Kaina ya,sade a kasa yayin da take gaisawa da matan da muka shigo tare, dasu,
Daya daga cikin matance take cewa tau fadima ga Aisha nan mun kawo ta tayi maku sallama keda abokan zaman ki,
Nan da nan naji idanuwana sun ciko min da hawaye kaina yana sadde a kasa nace cikin kuka Ummi ki yafe min don Allah,
Shiru kamar ba zatai magana ba,sai can naji tace nikan Aisha may kikai min a,duniyan nan,
Kece dai zance ki yafe min nida a,sanadina rayuwanki ya zamto irin haka,
Wani kukane yazo min maiban tausayi da ni da ummi dama sauran wanda ke dakin
Dayar matar tace ai shi mutum duk bai wuce kaddaran ubangijin shi don haka sai muyi mata fatan alheri ga sabuwan rayuwan da zata,shiga a yanzu,
Ki tashi kije ki roki sauran matan gidan gafaran zama muyi haraman kaiki tun dare baiyi ba,,
Dakin mama Saude muka fara shiga kamar bazata amsa muna ba sai can tace ku iso mana,
Muka shiga da sallama a,bakunan mu muna gaisheta tare da mata yaya,gida,
Daya,daga cikin gwagwanina ta ce mata tau uwargida ga yar ki nan mun kawo maki ita kunyi sallama yau zata tafi dakin ta insha Allahu,
Mama Saude tace "Ya ta kikace fa aida yata ce da bazata wanan gidan fakiran ba,
To kiyi hakkuri don Allah duk abinda tai maki ki yafe mata akwai kurciya a tare da ita,
Mama Saude tace ai mu gamu gani shine namu kawai,
To Allah ya kyauta inji gwago na dake kokarin tashi tsaye,,
Sai da na dan yi jin nace mama don Allah ki yafe mi duk laifin da naii maki,
Allah dai yakai lafiya aini baki min komai ba yar Agwai,, kanki kikaiwa,
Mubar dakinta muka nufi dakin Atika amm sai muka samay ta a waje take cewa mu tsaya daga wajen ma yayi ai,
Tace yar Agwai sai ayi hakkuri daduk irin yanayin da za,a gani a gidan Hamza don ko sai rarita yasan da zatayi yoyo,
An nufi dani gurin malam Mudi wanda shigowan shi gidan ke nan a lokacin,
Mun shiga turakar shi yana zaune yana kokarin cin abinci Atika tana tsaye daga kan shi tana kokarin mika mai ruwa,
Baba yai muna sannu da zuwa tare da,bamu guri don mu zauna daga dan nesa kadan,
Baba yace Aisha yau Allah yayi aure zai raba mu dake, zai rabaki da uwar ki da yan uwan ki ko ?
Baba yace aure kenan sha kan yaro duk da,ba nesa zakiyi damu ba amma shi al,amarin aure yana da matukar yawa da a,rayuwa,
Baba yace Aisha yau Allah yayi rayuwar ki zata koma a cikin wasu jama,an dabaki saba zama dasu ba, a baya,
Aisha kamar yadda na fada maki a baya aure sunna ne maikarfi,
Wanda yatara wajibai masu yawa a gare shi sosai ,
Nan Baba ya kara nanata min yadda mukayi ranan da na umurci yai fitar kunya dani akan Kubura,
Baba yace Aisha dake da mijin ki ku kasance masu matsakaiciyar rayuwa kamar yadda nasan halin kowanin ku,
Halaiyar ku danasan ku dashi indan har kunci gaba dashi zaku kasance acikin jin dadin rayuwan zaman takewa,
Yace yau Aisha abinda kikai min yasa na tuna da wani Hadisi na na mazon Allah inda yake cewa,
1 Mutane zasu so abin halitta su manta da,wanda yayi su,
2 mutane zasu rayuwan su har su manta da makomar su,
3zasu mallakar manya manyan gidaje su mance da kabarin su,
4mutane zasu zabi aikata zunubi su manta da yawan tuba (gafara)
5 mutane zaso dukiya su manta da hissabi,,
Baba yace yau Aisha kin gwada min cewa kedin diiyace a duniya kin nuna min cewa mahaifan ki sunyi sa,an haihuwan ki a,duniya,
Yadda kika iya fitar da mutumin da kikewa ksllon uba a gare ki alhalin wanan mutumin yai sakaci da damar da Allah ya,bashi na kasancewa uba agare ki tun farko,
Sai kawai baba yasa kuka yana cewa Aisha yadda kika fitarni kunyan duniya Ubangiji Allah ya albarkaci auren ki yabaki zuri,aa masu albarka duniiya da lahira,
Itama Aishan kukane ya kubce mata inda ,suka bar gidan a cikin hawaye,
Yan uwanane kawai suka rakani gidan miji sai yan tsiraru daga matan uguwa masu son ganin kwam,
Dakafa muka taka don ba nisa sosai da gidan Mama Rahana da mu,
Ina rike da hannub kaunar mahaifna da mahaifiyana, muna kai kofan shiga gidan su Hanza sukace min dakata daga nan sai mukaja mukai tsaye,
Yayin da gwago na,tadan rankafo daidai kunnena ta rada min da cewa nac bissimillahi A,uzu bikkalamatillahi tamat min sherin mahallak, 3,
Takara cewa kiyi bissimillah kija suratul Iklas kafa uku hagu da daman ki sai ki shiga da kafan dama Allah ya sa albarka a rayuwar auren ki,
Kamar yadda gwagona ta umurce ni da nayi hakan nayi don ita din malamar addinice a kauyen mu,
Inda ina tafiya bakina yana lailaha,illah hasbunallahi wani,imal wakil,,
Kofar shiga dakin da aka gyara a matsayin nawa muka dan ja runga muka tsaya gwagona ta kara furta nin kiyi bissimillah ki kara jan Iklas kafa uku ki shiga da kafar dama,
Hakan na kara karantawa tace shiga da kafar dama da,addu,an da duk kika iya domin Allah maji rokon bayin sa ne,
Duk abinda yazo min daga fannin addu,a haka nauta jero su har asma,u husna saida na jero su,
Nai mamaki kwarai yadda naga an gyara min daki a tallakance dai dan ban zaci haka ba sam,
Aka zaunar dani a saman gado shima,da,addua abakina yayin da nadanyi kamar minti goma a zaune sai suke cewa na mike zuwa dakin uwar miji,
Mun samu Umma Rabi da dan taron jama,an ta a dakinta tana zaune a saman katifan dake a cikin dakin ta,
Duk da bata da miji amma kafanta yasha kumshi yana sheki, ta dan yi kwalliya itama,
Yaranta duk suna a cikin dakin azaune suma tare da mahaifiyar su,
Daya daga cikin iyayyena take cewa tau yadai ga yar ki mun kawo maki Allah ya baku hakkurin zama a tsakanin ku,
Dayar gwagona tace sai anyi hakkuri da yaran yanzu don Allah aita tsawata mata akan abinda tayi ba,daidai ba,
Umma Rabi tace ai da na kowa balle Aisha ai dama diyatace, Allah ya bamu hakkurin zama da su,
Mijinta yaron kirkine baida matsalar rayuwa duk inda na ajeshi anan yake tsawa inaa fataan zaki bamu hadin kai muyi zaman lafiiya a gidan nan ,
Kina da kannen miji don haka sai kinyi hakkurin zama dasu don a zaunna lafiya,
Bamu jima adakin ba suka ce na taso mukoma dakina,
Muna shiga naji kauna mahaifiyana tace tau Aisha tun yanzu na,fara hango hakkuri a gare ki,
Din wanan sarrakuwar taki da alamar irin matan nan ne masu goyon bayan diyan su akan komai,
Don kiji tun a gaban mu tana yabon danta da kanta bata bari hallinsa ya nuna ba,
Don haka nasan kina da kirki kiyi hakkuri kinji gaduk irin abinda kika gani daga gare ta ki kawar da idon ki akan abinda take da diyan ta a gidan nan don ku zauna lafiya kinji,
Hawaye ne masu zafi suka zubo min ina kokarin dan share su da habar hijjab din dake a fuska na,
Na ji mama Rahana tana cewa nasan tunda baki da nisa da Fatima yan gidan su ma zasu dinga shigowa don yin lecture ki don haka ki zama mai boye sirin ki ga kowa, kadaa naji wani zance a waje akan zaman ki gidan nan,
Tsabta, yinayi bari na bari shine zaman aure harki ji daga baya ana fadar ai wance ta samu miji ko ta samu gida,
Daga karshe wanan gwagon tawa tace masu salli, allanabiyull karem suka karba da sallallahu alaihim wasallam,
Nataita jero adduoin nemamin zaman lafiya da kariya daga duk wani sheri na kalubalin rayuwa,
Sukai min sallama sukace su zasu tafi sai da,safe kafin su tafi zasu shigo mu kara sallama,
Har,sun tafii mamana,Rahana tadan dawo daga baya tana ce min ki yi duk abubuwan dana koya maki a gida
Na,amsa a hankali dacewa tau mama sai na saka kuka haka inaji ina gani suka tafi suka barni a,sabuwar rayuwa a wani gidan,
****** ********** ******
Kubura yanzi ita da,sabon saurayin da tayi mai suna Alhaji Nura dinke suke cif da shi don akan shi duk ta kore mane manta na farko shike masu ruwan kudi suna bushashan su ita da mahaifiyar ta,
Yan uguwa suna kallon ikon Allah don har kofan gida zai