Showing 3001 words to 6000 words out of 299981 words

Chapter 2 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17614

Mai so za ta iya shiga group dina domin register akan shi,
Ina fatan zaku fahinceni da kyakyawan fahinta akan wanan sabon yanayin novel din mu mai suna sarautar mata,
Inda zamu yadda uwayen gida suke shan kwaram da maigida kishiya uwayen maza, dangin miji makwabta, da sauran su,,,,
Allah ya nufe da, yin darasi mai amfani a cikin wanan novel din namu watau sarautar mata labarin Hamza da Aisha,,,,
Kubiyoni mu kasance a tare yan uwa kada ai fushi da zee don wanan sauyin yanayi ne yakawo hakan yan uwa don,ci gaba marubuta,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
SEENABUšŸ‘‘SARAUTAR MATAšŸ‘‘
0⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

SUBBAHANALLAHI WABBI HAMMDI SUBBAHANALLAHI AZEEMUN,,,,


Yau kimani sati uku ke nan da fara karatun Hamza inda ya,mayar da hankali sosai ga karatun shi don dama shi mutum ne mai sha,awan karatu, sosai,
Idan yadawo da yamma yakan sayar da yan abubuwan da kobo zai shigo mai kamar su,
Rake, mazzakwaila, alawa, gyada soyayya da ayya har da madaran gullusuwa,,
Da zaran lokacin zuwa daukan darasin addini yayi zai bar gurin zuwa gurin daukan karatu sai dare ya,dawo yakara kasa yan kayan nashi, wanda yaran uguwa har ma da,wasu matasan shiya suke saya,
A irin wanan yanayin Allah ya rufawa wanan zuria asiri suke samu suna ci suna sha daga ciki,
Abin da yafara jawo hankalin mutane a gare su ke nan ganin yanzu sun rage yawan wahalan da,suke a da can baya,
Saboda tasowan wanan yaron da Allah yaba Umma, Rabi mai hazaka da kwazo,
Take yan surutu suka fara kewaye shiya cewa yanzu Rabi ta,samu saukin wahala,don danta da ya taso,
Wanan dalilin yasa yan uwan mahaifin suka saka idanuwan su a gare su sosai,
Wanda hakan yasu hango cewa hakan zai iya sa su cigaba,
Don haka babu kunya wan mahaifin nasu yazo har inda Hamza yake sana,ar shi suka ya karbe duk dan kudin da yake a hannun shi yana juyawa da,sunan zai biya tsohon bashin da,aka,saura bin mahaifin su hamza din,
Ba musu Hamza wanda dama ya,sayar zai koma zuwa,saro wasu ne ya mika,mai kudin,
Baba Ado yana barin gurin, kasuwa ya wuce kai tsaye zuwa gurin yan namq ya sayo kan rago da sauran kayan hadi ya,sayo shinkafa ya nufi gida dasu ran shi fal da wanan ranan,
Matar shi kunne har a,baka don ganin yadda yau mijin ta ya kawo masu kayan ciko mai hadi irin hakan,
Ba bata lokaci tamike ta shiga gyara ta waka wa sauran matan gida cewa ita mijin ta gwaninne wajan ciyar da gidan shi,,
kafin wani lokaci har dahuwa yai nisa sosai gida ya dauki kamshi ko,,

****** ********* ******
Hamza ya shigo gida hankali a tashe saboda ya,rasa inda zai nufa don ya samo dan kudin da,zai ci gaba da sana,ar shi,
Wanda haka ne yasa shi samun guri yazauna yai tagumi da hannu biyu ya,shiga tunane mafita,
Umma wace ta fito daga bandaki taiwanka don gudun kada magariba ya risketa babu wanka
A,a Babana lafiya dai ko nagan ka a nan a,daidai lokacin da ya kamata ace kana lambu gurin sarin rake,
Gyara zaman shi yayi yana kokarin ganin cewa ya danne damuwar shi kada mahaifiyar shi ta gane bacin rashi
Amma abin da da mahaifi sai Umma ta nufo shi hankali a tashe tana cewa,may akayi may yafaru ne wai,
Cikin dan marairaice murya yake cewa ba komai Umma kawai dai dama ina tunanen ida yanzu zan samu kudin sayen wasu kayan ne,
Cikin kaguwa taje cewa kudin da kake juyawa din fa, da farko,?
Murya kasa kasa duk da baiso fada mata ba yake cewa Baba Ado yazo ya karba dazun nan zai biya wasu bashi da ake bin Abban mu da dadewa,
Salati Umma Rabi ta,sa tare da tafa hannayen ta tana mai cewa amma ko yaya Ado baida tausayi a duniyan nan,
Yanzu don rashin imani da rashin tausayi yazo saboda mugin hali ya karbe dan kudin dake a hannun ka,
Aikuwa yau bazan kyale shi ba don cin fuskan ya isa hakana ban san may suke so damu ba a duniyan nan,
Duk dan abinda bawan Allah nan ya bar muna sun kwace sun barmu da wahala da talauci,
Yanzu kuma don yaga Allah ya rufa muna asiri shine yazo ya tona muna,
Umma da kin kyaleshi don sauke nauyin bashin da ke bin mahaufin mune ai saboda bashi baida amfani ga mamaci,,
Daki ta fada tana shiri ta bambami ita kadai yana daga waje a zaune yana bata hakkuri,
Cewa take yau hakkurin ya isa don idan har bata je ta tsayar da zancen ba abin zaici gabane ba zai tsaya ba,
Hamza sai baki yake bata yana cewa ba komai Umma kada ki bari ku samu sabani dasu wanan ba abin damuwa bane tunda sun muna wanda yafi wanan a baya,
Umma Rabi rai a bace tace yau dolene ta tafi gidan idan ma kashe ta zasuyi sai dai suyi, sai da ta daidaici kowani magidanci na gidan ya shigo gida ta shiga gidan
Ba bata lokaci ta isa gidan tun a kofa take jin kamshi yana tashi ga katon tabarma an shimfida ansakawa yara abinci suna ta kwasan gara,,
Da sallama a dauke ga bakinta tafada part din Baba Ado inda sauran matan gidan sai binta da kallo suke suna kyashin ta da hassadanta duk da mijinta baida rai har yanzu,
Sama sama suke gaisawa da matan Baba Ado wanda suke zaune zasu soma cin abinci,
Idonta ya sauka a saman abincin dake a gaban su cike cikin wani kwanon tasa mai fadi a kwanon miya ga kashin kan ragon da aka,dafa yana tashi da kamshin kayan yaji,
Daidao lokacin Baba Ado ya fito daga dakin amaryan shi yana kokarin zama saman shimfidar da akai mai na cin abinci,
Ina wuni tai mashi a,tsatsaye ya amsa mata kamar yadda ya ganta don yasan zancen da ya kawo ta,
Zata fara magana yace cikin daga hannuwan shi da muryq da ke dakata don nasan abinda ya kawo ki gidzn nan,
To dakata kiji indon kudin da na karba a hannun dn ki ne ina nima dana ne hamza din don karbi kudi a,gurin shi zaki wanko kafan ki ba kunya zaki zo min gida tambayan ba,asi,
Shi yaron bai maki bayani bane a kan a binda zanyi da kudin da na karba a gurin shi,
Wasu irin hawayen bakin ciki ne suka tokaro mata tace a cikin kuka Yaya Ado aika kashe mu ka huta kawai da wanan irin musugunawan da ku ke muna ni da diyan dan uwaku,
Baba Ado yace oho sherin da zaki yi min ke nan lalai ba laifin kowa bane laifina,na ne da,tun farko ban sayar da gidan nan ba kinbar garin nan Hamza din da yan uwan shi su zauna a guri na,
Shi yasa har kike ganin yanzu wuyar ki ya isa yanka zaki zo min har gida da cin mutunci haka,
To ki jira ki gani abinda zai faru dan yadda kike ganin kina da hakki ga yaran nima ina da hakki a kanku gaba,dayan ku don haka ki jira kigani irin matakin da zan dauka bada dewanan ba,
Kin ga sai kiji dadin zuwa min gida da cin mutunci da tushe don samun guri,
Aikuwa sai Umma ta fusato tace cikin daga murya wallahi Yaya Ado ta Allah ba taku ba duk abinda kuke nufi damu da dan uwanku da baida rai har yanzu kuna bakin ciki da shi,
Duk abinda zakuyi ya tsaya iya ni da abin dan uwan ku,
Don kun sayar da komai kun ce zaku biya bashin dan uwan ku dashi, yanzu kuma dan abinda yaron nan yake samu yana dan daukan rayuwan shi dashi ka karbe da,sunan biyan bashin da bai karewa ga dan uwan naku,
Cikin harzuka yace mata ke Rabi ki shiga hankaliki da ni don wallahi zanbata maki rai,
Yau duk abinda zakai min Yaya,sai dai kaimin don wanan abin ya isa haka, don ban yarda abin har ya kai ga yara ba,
Kudi kudi fa kamar naji kina cewa ya karba a hannun dakin ki ?
Gaba daya,suka juya daga gurin da suke jin muryan baba Awal daga bayan su wanda shine marigayi mijin ta mahaifin su Hamza ke bi mawa sai mata,
Ki fice min daga gida kafin na bata maki rai don baki da kunya zaki zo ki na fada,na karbi kudi hannun dan ki har nawa danki yake dashi, da zaki zo min gida,
Malam kudi dai ka karba ko yace eh saboda ya,san halin dan uwan nashi Alwalu wurin rashin mutunci,
Umma Rabi tace, ni dai abar cewa wai yaro shi zai biya bashin mahaifinsu wanda ya rasu tun suna kanani sosai,
Yanzu kuma dan abinda yake juyawa ka karbe a hannun shi, gaba daya,
Na karbe sai kije ke da danki kuyi karata shi nake jira tunda har yai kudi da zaki zo har nan ki yi min cin mutunci a kai,
Ba yau ba,duk lokacin da naga wani abu a,gurin shi sai na kwace naga yadda zakiyi,
Umma tace ai arziki na Allah ne mutuwa kuma tana a kan kowa, in har Allah ya nufe su da aje abu a hannun su ko kullun kake kwacewa sai sun aje,
Inda mahaufinsu kuma ya tafi hanyar kowa ne kulba dade kulba jima kowa zai tafi can din ma,
Jinan malam kudi dai anci su don kingan su a telle don haka sai ki koma inda kika,fito don baki da kunya har zaki shigo fadan an karbi kudi a hannun dan ki,
Ta share hawaye tace eh dole nazo babu jin kunya tunda tun ranan da mahaufinsu ya kwanta dama har iya babu wanda ya taba tallafa min daga cikin ku,
Don haka 'ya'ya na nasani don komai wuya su basu guduna kuko gashi duk.irin halarci da mutunci da dan uwan ku yai maku da yake da,rai duk kun manta,
Wahala ai yanzu kika fara don sai kinga na dauki mataki a kanki zaki gane,
Ta juya fuuu tabar gidan acikin mita da jinini tana Allah waddai da irin halin su,
Tana barin gurin Awal ya juya gurin dan uwan nashi ya na mai mika hannun shi gare shi yake cewa miko min kaso na da ka,karbo a gurin yaron,
Wani wawan kallo ya,aika mai yayin da yake kokarin bude kwanon miyan dake a gaban shi wanda kamshi ya daki hancin dan uwan nashi Awal,
Sai da ya hade wasu miyau masu zaki yake cewa ai baka isa ka karbo abu ba ka cinye kai kadai dole ne mu rabashi tare,
Ganin zai fara kai loma yasa shi azamar dauke kwanon miya anan gaddama ta gaure a tsakanin su suka fara sa,insa akan zance,
Haruna wanda shine karamin su yashigo gidan ya shiga tsakanin su inda yake tir da wanan irin halin zaluncin iri nasu,,
A,ranan haka Umma ta kwana da bacin rai rayuwan ta,saboda i,yanzu dangin mijin nata sun kai mata ko ina,
Don haka hattakai ga fara basu martani akan irin zaluncin da suke masu,,,

****** ********** ******
Zaune take a gaban mirror tana shafe shafe fuskan ta wanda ya zama mata al,ada yin hakan yar karama da ita,
Mahaifiyar ta ce ta daga labulen daga kofa tana cewa wanan kwalliya naki Kubura Allah ya,sauka dashi,
Yarinya baki da,aiki sai son yin kwaliya a,rayuwan ki irin haka kamar diyar bararo,,
Daga kofa taji muryan maigidan nasu yana cewa kibarta tayi ba mace bace,
Ai ban hanata ba malam amma dai kwalliyan Kubura ya baci ne malam,
Kai Allah yasa ga ki,
Kin taba ganin inda gyara ya zama barna a rayuwan dn Adam,
Hijabinta ta zura tare da dauko jakar islamiyar ta don zuwa makaranta ,
Sauri takeyi don gudun kar mahaifiyar nata tace sai ta tafi da wace bata kaunar jerawa da ita akoda yaushe,
Daga daya daga cikin dayan dakin gidan taji murya ana cewa ke Nana, ke nana bazaki zo ki shirya zuwa islamiyan ba ko?
Gani tafe mama zan kwashe shara ne na zubar da,saura a,waje,
Da,sauri Kubura ta fito ddaga dakin mahaifiyanta tana gyara hijab din wuyan ta tazo kusa da yarinyar da uwar ta ta kira da Nana tace cikin kashe murya,
Ke yar AGWAI indan kika fara kika bini zuwa makaranta sai nai maki mugun dukan da yafi na jiya zafi yau,
Cikin dan tausa murya yarinyar karama tace nima ai bance zan biki ba,sai in mamana tace lalai sai na biki din zan biki mu tafi,,
Ta juta taci gaba da kwasan tulin sharan da ke gban ta tana murza idanuwan ta,
Mahaifiyar nata wace ta dade tsaye a kofan daki ta,sake labulen dakin nata, ta juya zuwa cikin dakin tana mai jin bacin rai a zuciyar ta,
Fitan Kubara sai ta,wuce zuwa gurin Hamza mai rake don ta kashe yar biyar din ta da ake basu idan zasu tafi islamiya,
Amma sai yau aka samu akasi babu Hamza babu sanar sa a kofan gidan nasu gurin da ya,saba kasa kayan shi na sayarwa duk yamma,
A haka ta yanke shawaran shiga cikin gidan nasu don ta duba ko akwai a cikin gidan,
Sallama take tundaga kofa har takai tsakiyan gidan sai dan yatsune yatsune take tana karewa gidan kallo jin motsin fitowan Umma, daga dakinta cikin daga labule yasa ta,saurin juyawa gare ta,
Umma ina wuni rake za,a bani ta biyar ,
Allaj sarki Kubura yau ba rake sai dai zuwa gobe kila
Har ta juya,sai kuma tajuya tace to aban mazzakwaila, umma tace ke Kubara kina diya mace zaki saye mazzakwaila kisha ,
Kul na karajin ki sayi zaki da kudin ki sai na bata maki rai, tai wani iri da fuska har zata juya tace to aban gyada ko ayya ta biyar din,
Girgiza kai Umma Rabi tayi a cikin takaicin wanan irin sakaci na iyayye masu bawa diyan su kudi da sunan kashewa wai lalashi basu san cewa,suna bata tarbiyan yaran bane a haka,
Daki ta shiga ta dauko mata gyada soyayya ta biyar ta mika mata, tare da mata fatan adawo lafiya don ta lura da cewa islamiya zata tafi a lokacin,
Daidai zata fita a gidan ne sukayi kicibis da Hamza wanda yake dawowa daga guri da yake daukan rake ,
Cikin sakin fuska yake cewa a,a Hadizatul Kubura har anfito dai ke nan zuwa makarantar ko,
Ta amsa a tsiwace da cewa yau ba rake ba alawa sai gyada na,samu,
A daidai lokacin da ta,facce ledan gyada tafara sawa,a bakin ta tana ci,
Murmushi yayi batare da,ya bata amsa ba yadan jaye mata tasa kai ta fice daga gidan,
Umma Rabi wace take tsaye daga kofanta tana kallon duk abinda ke gudana a tsakanin su, ta girgiza kai tana cewa Allah ya kyauta a fili,
Tun kaan ya karasa karasowa gurin ta takecewa tau ya ina fatan dai da na sara,a tafiyan,
Hamza yadan bata fuska alamar ba dadi abin yake cewa Umma na,sayo na daidai dan kudin da suke a hannu naa don na kasa tambayan su cewa su bani bashi,
Au dama akwai wasu kudi ke nan a gurin ka baka bawa Baban naka,ba dukka,
Yace Umma,wanan din a cikin wanda a kullun nake dan tarawane don zancen karatuna idan ya taso,,
Shiru Umma Rabi tayi har zuwa wani dan lokaci daga karshen tunanen ta take cewa Allah Ubangiji yasa masu albarka Allah ya tsare min ku yakare min ku daga duk wani fitinan duniya da lahira,
Ameen Umma Hamza ya karba mata da sauri idan akwai abinda yake son ji a rayuwan shi shine jin kalman albarka daga bakin mahaifiyan shi,
Izuwa yanzu itace kawai ta rage masu aduniya wace ta san zafin da nuna masu kauna irin ta su ma diyan sone kamar kowani da a duniya,
Bazai iya mantawa ba da mutuwar mahaifinsu wanda a lokacin ba wani wayo ne dashi ba amma zai iya kawo zancen a ran shi har kullun na lokacin da mahaifin nasu ke da rayuwa,

****** ********* ******
Alhaji mohammed jega, dan asalin garin jega ne ta cikin jahar Kebbi na kasar Nigeria,
Mohammed yataso a cikin gidan su shi kadai ne a gurin uwar shi Allah yai mata rasuwa amma yana da yan uwan haihuwa maza hudu da ba uwar su daya ba har ma da mata hudu,
Sannu a hankali ya fara sana,ar sayar da dabbobi sai Allah yasawa abin nashi albarka, kafin wani lokaci sai harkan ta daga shi, sosai,
Don haka yaiwa yan uwan shi tazara a rayuwa don shi yana da rufin asiri, yafi sauran,
Wanan dalili yasa suka fara dora mai karar tsana a rayuwan shi irin ta yan uba duk da irin taimaka masun da yakeyi,
Duk da ya fahince su amma bai sa shi rabuwa da yan uwan nashi ba, don a duk lokacin da yakai dabbobi kurmi yadawo kowa da irin tsaraban da zai sayo mai daga cikin su,
Hakan bai hana su kawo mashi yan koken su na bukatoci kuma ya taimaka masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login