Sarautar Mata

Chapter 3 of 94

mutane sun shagala basu iya tallafawa maraya ko kadan,
Abinda mutane basu sani ba shine taimakon maraya guda daya yafi mutum, ya kai miliyan masalaci yace a rabawa mutane,
Haka da zaki rike kan maraya kiyi addua ki roki Allah bukatan ki ki bashi wani alhreri wanda zai sa yaji dadi har a cikin zuciyar shi insha Allahu ke kuma bukatar ki zata biya bi,izzinillahi,
Zaki iya daukan sati guda kina ciyar da maraya don samun biyan bukatan ki na duniya da lahira, yar uwa,
Don haka mu taimaki maraya duk inda yake mu bar sakaci da falalar da ubangiji yai muna ta hanyayoyi masu saukin aiwatar wa,
Marayun wanan zamanin namu suna matukar bukatan taimakon mu ta hanyoyi da dama, Allah ubangiji ya bamu ikon kyautatawa Allahuma Ameen,

****** ********* ******
Kubura tana zaune a tsakiyan sauran yan uwanta dalibai suna daukan darasi, inda sannu a hankali yara ke ta kara taruwa a makarata,
A daidai lokacin ne wata yarinya tashigo saye da wani farin hijabi tsoho kudadde yasha gyara, tasamu gefe guda dan nisa kadan da inda kubura take zaune ta zauna,
Daga inda take zaune sai kokarin su hada ido da wanan yariyar da tashigo take don ta muzanta mata, amma sam yarinyar taki yarda ko ta juya inda,suke zaune ta kalle su,
Sai karatunta take sannu a hankali batare da ta tsaya wasa irin na sauran yaran gurin ba,
Wani yaro ne ya jefawa kubura wani abu ga hijab din ta anan fa fitina ya kaure har gurin malam din inda malam yake mata fada akan, cewa ita duk safiya sai anyi fitina da ita,ne wai,
Tafe suke kowana yar wasan shi irin ta yara idan an taso daga makaranta amma banda Kubura wace hankalin ta yana gurin Rake da ta hango Hamza ya na sarawa a kofan gidan su,
Idan ya,sara ya yarda kasan sai ta dauka tana sha, hakan yasa shi mata fada akan ta,daina ta wuce zuwa gida,
Amma fir Kubura taki tafiya dole ya dan datsa masu kasan ya mika mata ita da dayan yarinyar da suke wasoson nakasan a tare,
Har zai mayar da kai ga abinda yakeyi sai yahango wanan yariyar a tafe cikin natsuwa ba tare da ta duba inda suke ba hakan ya sashi datsa mata rake azaton shi itama tagani lokacin dayabawa sauran,
Yana mika mata amma sai ta girgiza mai kai ta furta a hankali da fadar nagode, tasa kai zuwa hanyar gidan su wanda zan iya cewa ba,wani nisa a tsakani zamu iya kiran su da makwabtan juna,,,
Binta yayi da kallon saboda tarbiyan yarinyar tayi mai matsala guda ce bata da gata agidan kullun ka ganta a takure take ba kamar sauran yara ba,
Ihu su Kubura ne yadawo da hankalin Hamza gare su inda ya bisu da gudu suka watse kowa ya shige gidan su,
Nan yaci gaba da aikin shi tare da kasa yan sauran kayayakin sanar shi wanda Umma ce ke soyawa daga cikin gida,
Duk yamma yan matasan shiya da ma wasu manya na aguwa suna saye a gurin shi,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA YELWA SEENABU👑SARAUTAR MATA👑
0⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


Godiya gare ku makaranta wana novel din na,sarautar mata tare da fatan kara samun goyon bayan ku gurin bani hadin kai don ci gaban mu


Idanuwanta cike da hawaye sai zance zuci takeyi saboda tarin damuwar dake tare da ita,
Ganin yamma yayi tasan cewa yanzu yartan gidan zasu shigo gida saboda tasowan su daga islamiya,
Fitowan ta tsakar gidan yai daidai da,shigowan yaran gidan, yar tace a gaba, tashigo da sallama dauke a bakinta,
Sai kuma Kubura wace ta shigo a guje daga bayanta har tana bangaje yarinyar,
Ji kayi tim a kasa tafadi har bakinta ya fashe abinda yasa uwar yin magana ke nan cikin sanyin harshe take cewa haba
Kubura baki tafiya a hankali ji yadda kika buge yar uwaki har ta fasa baki,
Tana tafiya take cewa nikan ba yar uwata bace wallahi,,
Uwarta ce tafito daga dakinta, tana cewa wanan yarinya anyi ar nema yanzu kin ture yar uwar ki shine, baazaki tsaya ki dubata ba,
A hankali ta mike yar nata tare da,bata ruwa don ta wanke fuskan ta dashi,
Alokacin maigidan ya,shigo dauke da,butan roba a hannun shi yana son diiban ruwan alwala,
Ke, ke ke yaya haka kina barnan ruwa haka akan yar ki, kko don baki san yadda zafin sayen ruwan yake bane,
Daga kofan ta uwar gidan nashi ke cewa ayya malam wallahi wanan maraa,jin maganaan ce ta ture ta har bakinta ya fashe,
Maimakon ya tausaya wa yarinyar sai wani kallon rainin haankali da,ya,watsawa uwar da yar dake tsaye daga gefen shi tana goge mata fuska,
Karban mutan uwar tayi tana zuba mai ruwa a cikin buta,
A cikin yanayin bacin rai suka fada daki ita da yar nata suna mai kokarin kawar da zancen a,rasan duk da bawai yau bane farkon zancen, irin haka a gidan ,
Saukin abin shine Allah ya hore mata yarinya mai albarka gata dai karamace amma tana iya shanye duk wani bacin rai na gidan da ake mata,
Abinda yaciwa uwasr rai shine har da dan da ta haifa da cikin ta yana nuna ma yar uwan haihuwan shi tsana da kyamar jinsi, a tsakanin su,, kamar yadda sauran yan gidan ke gwada mata,
Sallah tayi don gudun kada lokaci ya,shige mata bata bar gurin ba yara maza na gidan suka shigo gida sun dawo cin abincin dare,
A lokacin ne ko wani yaro nagidan ya,nufi dakin mahaifiyar shi kamar yadda suka saba yi a kullun ,
Babban dan nata Abdul shine hankalinshi ya kai ga yar uwar shi wace ke kwance dunkule zazabi ya rufe ta a lokacin,,
Ita waccan may ya,samay ta haka take kwance a lokacin nan bazata ci abinci bane yau,
Yafada a daidai lokacin da yake kokarin jawo kwanon abincin shi a gaban shi, yana bude,
Jin may uwar ke fada ne yasa shi dakatawa daga abinda yakeyi tana cewa Kubura ce tashigo gida a guje ta,ture ta,sai da ta,fadi har hannun taya amsa bakin ta kuma ya fashi,
Shine zazabi ya buge ta haka tace bazata ci abinci ba sai anjimaa,
Dayan yaro dake daga tsaye a gefen su ne yake cewa ai maganin ta ke nan wallahi ,
Yarinya hakka kamar yar roka,ba,dadin gani wallahi da za a mayar da ita gidan su da zai mafi min dadi wallahi,
A har zuke uwar ke cewa ai, sai ka mayar da ita,din da hannuka tunda baka kaunar ganin ta a nan din,
Mama fita zance shi kawai baida hankali shiyasa atake fada kuma ya kaure a tsakanin yaran wasa wasa tun uwar tana fada har abin yafi karfinta,
Sai da abokan zamanta suka saka baki a zancen yaran ana cikkin hakane maigidan ya shigo gidan
Tun a kofa yake cewa kao kai wai yayane may kke faruwane haka a gidan tun a waje ake jin hayaniyar ku,
Nan ake mayar mai da ba,asin zancen komay yakawo hayaniyar haka,
Wani irin uban tsuki yaja tare da cewa kai kai gaskiya ni wanan al,amarin ya fara kai min ko ina a gidan nan,
Yarinyar nan zaman ta a gidan nan yana dagulamin lissafi a rayuwa na don dai gaskiya dole ne na dauki mataki kafin ta fara hada min kan zuria na anajin su,,
Uwar gidan shi Hurera dake tsaye daga kofa take cewa haba dai malam wanan irin maganan bai dace dakai ba a,gidan nan ina,dai yanzu an wuce wanan zance dadewa ,
Hakan baida dadi wallahi, kadaina don shi da ai na kowane ladan ka yana a gurin Allah fa,
Da kuka kamar kullun idan ana irin wanan hatsaniyan ta shige dakin ta tana mai kuka wiwi,
Abinda ya sa yarinyar farkawa daga dan barcin wahalan da ya kwashe ta ke nan, a lokacin,
Mamana kiyi hakkuri nice dai matsalar taki ko don Allah kiyi hakkuri kinji maman mu,
Tausayin yarinyar ne ya kara kama uwar a lokaci guda take ji a rayuwan ta kamar ta mutu ta huta da,wanan irin bakin cikin dake cin ta a rai,,

****** ********* ******
A yanayin shigar ta,duk wanda ya,ganta zaiyi tuunanen cewa tana cikin nagartaccen jin dadi,
Sai dai da zaran idanuwan mutum ya yi tozali da fuskanta mutum zai iya gano tarin damuwa a tare da ita , saboda yanayinta da ya dan canza a lokacin, guda,
Tafe take tafiya hankalin ta a tashe sai jefi jefi take dan gaisawa da mutanen da suka santa,
Wani gida ta shiga da sallama inda kai tsaye ta tun kari wani daki mai labule a,dage zaka iya hango kujerun da ke a cikin dakin daga waje kadan,
Tana shiga dakin ta zube a,saman daya daga cikin kushin din dake falon yayin da matan gidan dake waje zaune a tsakar gida suka biyo bayan ta,
Ganin irin yanayin da tashigo dashi dakin tasa su gaba daya yin cirko cirko a kanta,
Karamar daga ciki wace itace amaryan gidan tai mata gaisuwan karfin hali ta juya inda tafito,
A hankali mai dakin ta tako har zuwa saman dayan kujeran ta,zauna idanuwan ta kyam a kan yar uwar ta,
Sai da tayi nazarinta na dan tsayin lokaci sannan ta dan nisa tana cewa
Yau ma kunyi halin naku ko duk da,bata fada mata dalili ba tasan dai zancen daya,biyu ne,
Ta nisa tare da cewa nasan dai ba da abokan zaman naki bane wanan karon ko, ?
Kai ta dan girgiza kadan a cikin kukan ta tana cewa a,a sai da taci kukan ta mai isarta batare da yar uwar nata ta dakatar da ita ba, ta yi shiru don kanta
Can ta sauke sanyayar ajiyar zuciya tare da dago jajayen idanuwanta tana fuskantar yar uwar haihuwan nata, wace itace silar zuwanta garin,
Cikin bacin rai ta soma magana da dakusheshen murya irin ta wanda yasha kuka,
gaskiya Anty ni wanan abin ya isheni tun yarinyar nan batai wayo ba har yanzu ta,soma wayo ta soma fahintar tsanar da,ake mata a gidan nan,
Dago kai yar uwar nata tayi tana kallonta a cikin damuwa itama sai a cikin dakiyar zuciyar irin wanda zai karama kaunar nata kwarin gwiwa take cewa
Ki natsu Fatima kiji abinda zan fada maki kisani cewa yanzu yaran ki girma,sukeyi suna ganin irin halin rayuwar da kuke ciki ke da mahaifin su,
Don may bazaki karawa kanki hakkuri ba akan irin al,amarin rayuwan mijin naku,
Gashi dai dake da yan uwan zama lafiya lau kuke mutum bazai ce akwai wani abuma kishi ba a tsakanin ku,
Don yanzu samun abokan zama irin naki sai an tona amma ke kin kasa hakkuri akan zancen yarinya guda,
Iyakar matsalar ki da kowa a gidan akan Aisha ce, Aisha kuma yarinya ce bata san komai ba,
Da sauri ta,dago rananun idanuwan ta ta,saukesu ga yar uwar nata, a hankali ta,sauke ajiyan zuciya irin ta,wanda yasha kuka yagaji,
Tana cewa wallahi anty yanzu yakai har yarinyar nan ta fahinci irin rayuwan da take a ciki ko,
To sai may inji yar uwar nata ai sai ke ki dinga kwantar mata da hankali tare da koya mata hakkuri a cikin al,umma,
Baku da rashin ci ba rashin sha balle sutura a gidan naku to may zai sa ki dauki magana guda ki saka,a zuciyar ki har ya batun maki illa a,rayuwa,
Don haka ki natsu Fatima ki bawa yar ki kulawa yadda ya dace don kwana biyu diya mace ce girma zatayi idan har ta taso tagan ki a cikin irin wanan yanayin zaki jefata a wani haline,,
Ta kara dago idanuwanta,a karo na,barkatai tana cewa, ni dai kawai gara na,tura wanan yarinyar can gida na huta yafi min,
Wani irin dan gajeren murmushi yaruwar na ta,ta,sauke a lokaci guda tana cewa ai da kin gwanmace zaman ta a hakan da zuwa ta can din dakike tunane,
Ni dai har kullun shawaran da,zanbaki shine kiyi hakkuri don idan da rayuwa,komai na,duniya mai wucewa ne ,
Sannu a hankali tafara kokarin tsayar da kukan da takeyi tana mai sauraren yar uwar nata
Cikin daurewa takara cewa wallahi Anty na,rasa irin wanan mugun kiyayyan da,ake gwada,wa yarinyar nan ace har da diyan cikin ka,suna kyamar yar uwar su,
Tau ni dai hakkuri zan baki tun da bai iya bude baki yace yarinyar tabar mashi gida ba iyakar shi dai nuna mata halin ba yar shi bace ita,,
Don haka da zaki bi shawarana kawai dashi da yaran duk ki basar da fitinan su gareta, ki koya wa yar ki hakkuri shi ke nan,
Kada ki kara,sanya zancen a ranki ki rungumi addua ki tayi Allah zai kawo saukin al,amarin insha Allahu,
Daga haka su ka,dan yi shiru na,wani lokaci kowa da irin abjnda yake tunane a ransa,
Anty tamike tafita can sai gata dauke da goran kunun ayya sai wani kula mai rikon zafi mai nuna abincine acikin sa,
Dago kai Fatima tayi tana cewa da kibar abincin nan don bazan iya cin komai ba,
Batace uffan ba ta aje kulan da,goran a gaban ta ta juya zuwa waje ta bar mata dakin,
Fitar yar uwar nata a,dakin shi yayi daidai da kwanciyan Fatima saman doguwar kujeran dake dakin,
Tana dan sauke ajiyan zuciya a kai akai daga haka barci ya sace ta mai dan nauyi don ta kwana da bacin rai batai barci ba,
Zuwa wani lokacin Anty tana daga waje jin shirun Fatima yasa ta fahintar cewa tayi barci ke nan a lokacin,
Daga waje abokiyar zaman Anty Saude ke tambayan ta da cewa halan Fatima barci takeyi naji shiru,
Anty tace kyale yar rigima ta dauki damuwar duniya ta saka a rayuwanta kan zancen Aisha,
Bayan idan tai hakkuri watarana zancen mai wuce wa ne ga rayuwan kowa, gashi mijin ga naki bai kasa da komai naku ba bare kuma kishiyoyin ki da kuke zaman ku na,arziki da su,
May zai sa ki kasa hakkuri da abinda ake gwada mata din ai m,sunyi hakkuri da suka rike ta hakan a cikin su,
Duk tabi ta ramay tasawa kan ta damuwa da tunanen banza tankar wace bata da ci da sha a tare da ita,

Sai wajajen yamma bayan la,asar kadan Anty ta tayar da ita daga barcin da takeyi don ta,taahi tayi sallah,
Tana cewa,ki tashi hakana kiyi sallah ki tafi gida don nasan yanzu mijin ki nace yana sintirin tambayan baki dawo ba,
Ta mike tare da yar tatausan salati a nakin ta tana mai kallon yar uwar nata, sai a lokacin ta dan saki gajeran murmushi tana cewa, ashe nai barci ne haka ban shina ba,
Dan haratan wasa yar ta,jefa mata tana cewa ai duk kika kwaso fitinan ki idan kinyi barcin kina,samun sauki nagani,
Ta mike zaune tana murmushi ta nufi bandaki ta gabatar da alwala ta sallaci sallah a take,
Bayan idar da,sallah tana zaune tana,addua Anty Saude ta kara shigowa dakin karo na barkatai don daukan abu ,
Sai tajuya inda Fatima take a zaune ta addua take cewa abinci fa ?
Girgiza kai Fatiman tayi alaman ba zata ci ba a koshe take ,
Fatima ki ci abinci awanki nawa da,shigowa gidan nan zaki ce wai a koshe kike hakan ya kara bata daman samun kujera ta zauna tana cewa
Wallahi Fatima ki cire damuwa akan wanan zancen a rayuwan ki ke ko fada bakiyi wa kanki dubi irin yadda uwargidan ku take kokari a kula da zancen Aisha a gidan ,
Gaba dayan Su sai kiban su suke narkawa hankalinsu a kwance basu saka komai a ran su ba,
Dan dariyan yake Fatima ta,sake tare da dan gyara zaman ta tana cewa akwai bambanci sosai Anty tsakanin ni dasu a gidan nan,
Cikin mamaki Anty ke kallonta tana cewa may kike ganin sun fiki dashi a gidan
Tamike daga inda take zaune tana cewa adai bar zancen kawai don tone tone baida amfani,
Lokacin da take kokarin gyara hijjab din take cewa ita yaya watau uwargidan su take nufi ban da ma raina a kan ta don gaskiya duk yadda,babba ke daukan girman shi tana dauka don abinta duk bai wuce mu da yaran mu,
Amma ita kan Hannatu na ciki ai yanq ciki ne tsakanin ni da ita kawai ana dai wayyayya ne kawai,
Ganin tana shirin tafiya yasa yar uwar nata cewa bari na zuba maki kunun a leda ki kaiwa yara ko tace ai da ki barshi kawai zai fi nake gani,
Har kofa fita gidan yar uwar nata tare da,abokiyar zamanta,suka kaita suna kokarin bata baki akan tayi hakkuri ta kawar da idon ta a kan komai tankar bata gani ba ko ji akan duk abinda wani zaiwa Aisha agidan babba ko yaro,
Tana dan share kwallah fuskan ta habar hijjab din ta tare da yi masu godiya sosai ta fita zuwa gida,,

****** ********* ******
Alhamdullahi iyanzu Hamza harkan kasuwan shi ya budu mashi don yana yan sana,o,in shi sai sambarka,
Yanzu yana dan kimani
shekara goma sha tara
zuwa da ashirin ne, amma gashi ya iya,sana,oi kala kala, na rufin asiri,
Don Allah ya,tarfawa garinsa nono saboda yabzu yana daga cikin matasan da ake kwatance dasu musanman a uguwar nasu,
Don indai harka ce ta neman kudi yana daga cikin masu zafin neman tashi suyi aikin karfi don su samu na kan su,
Hakan ce tasa iyanzu sun rage yawan talaucin da,sukayi a,baya don yanzu koda yaushe suna dan girka,abinci sabanin da can baya, da zasu kwana su wuni ba,a girka ba,
Har takai yanzu yadan kafa yar rumfa mai rufi a kofar gidan su inda yake sana,ar tashi,
Matasan Uguwa suna,dan taruw,a,bakin shagon Hamza yaro ga irin sunan da,suke mai lakani dashi,
Tsakanin shi da Kubura yanzu soyayya ta kullu inda gidajen biyu zumutar su ya kara kullun duk da dai dama ana hurda a tsakanin su,

****** ********* ******
KUBURA iyanzu ta girma don ta zama babban budurwa kyawon ta yana haskawa a gari ga shi taa iya gyara, da kwalliya irin na yan matan zamani
Sai dai duk irin wayewanta bata da lokacin tsayawa ta taimakawa iyayyen ta,
Sai dai akwaita,da,kokarin zuwa buki ko yawon gidan abokai

Download complete TXT · Novel page