Showing 111001 words to 114000 words out of 299981 words
don tsoro nake ji sosai saboda ni kadai ce a gida, duk suna,asibiti gaba dayan su gidan,
Ya,shigo gidan inda shima tun a,waje yaga gidan yai mai wani fadi fayau,
Ya shigo da yar mashin din shi daga ciki ya kaita kofan mama inda yake ajewa ya kulle,
Sannan ya juyo zuwa dakin mu cikin takon shi na, natsuwa,
Zaune nake saman kujera na idanuwa na,a kan kofan shigowa,
Yana shigowa na gyara zama na mike sosai ina cewa sannu da zuwa Yaya ?
Ya dan rugumoni daga gefe tare da shafan dan kumci na yana cewa cikin harshen turanci ni ban son kiran yayan nan da ake min fa,,
Murmushi nayi nace anfitar dani a cikin kannen ke nan ko kuwa,
Kafin ya kai ga bani amsa sai nace ya kabaro jikin Umma din da sauki yanzu ko?
Ya ce da sauki don tana ta barci ne har yanzu sai ruwan ake kara mata nace shine lafiyan ta,
Abinci na gabatar mai tare da mikewa nake cewa ga ruwan wanka, zan kai ma bayi,
Har na kai ruwan wankan bayi na dawo yana zaune inda na barshi yayi tagumi da hannayen shi, dukka biyu,
Lafiya dai yaya ? Natambaya cikin son jin may yasaka shi tagumi haka,
Ya sauke yar ajiyar zuciya yace Humaira dole ne ki ganni haka don ban da kudi a hannuna duk na zubasu a gona gashi dan kudin mama da ta ban na saya mata kangon gida dashi,
Ga kuma lalurar asibitin nan yataso komai na kudi ne yanzu asibitocin mu ba tausayi a cikin su,
Kudin zasu kai nawa, ? Natambaya cikin son jin yawan abinda zai bukata na kudin,
Sai daya dan sa hannun shi a bakin shi ya busar da wata iska mai nuna bak8n ciki
Yace na, dai rike koda goma ne don test test din da ake yawan yi mata, su ne ke cin kudin,
Nace akwai kudin da mama ta bani na bawa Ummi na daga ciki sai na,sana,ata dana tara a asusuna zan fasa naga may ke a ciki,
Yace kinga kuma ga abinci don duk da,asibiti gurin jinya ne amma yan sa ido na gurin suna kallon kalar abincin da ake kawo wa mutum daga gidan shi,
Wanan matsalar su ce don wani ma idan ka rabu da shi har abada,bazaku kara haduwa dashi ba,
Yace hakane Hummaira amma ya kamata na samo dan shinkafa da,sauran abubuwan da,za,ayi amfani da,su,
Nace dare yana yi ruwan wankan ka yana a cikin bayi kada yai sanyi ko wani shedani ya taba ma,
Yana fita na dauko a susu na nafasa nazauna kasa dirsha nafara kidaya kudin dake ciki na,samu shauku da dari takwas, cif,
Yana shigowa da ruwa a jikin shi yana daure da zani na da ya daura da zai shiga wanka,
Na ce mai ga kudin na fasa asusu sha uku ne da dari takwas na samu a cikin sa,
Yakai zaune bakin gado yana mamaki yace duk da wanan sana,an kika tara wanan kudin haka?
Gaskiya sana,a tana da amfani sosai shiyasa akace zaman banza baida amfani a rayuwa,
Yanzu gashi zamu ci albarkacin sana,ar cikin gida a gurin ki,
Yakarbi kudin yana cewa Allah ya bani ikon biyan ki su a cik8n dadin rai kamar yadda ya dace duk wani wanda ya dauki bashi ya fadi,
Ranan ba wani abinda ya shiga tsakani na da Hamza don ya kwana ya na juyi saboda damuwan ciwon mahaifiyar shi,dake a rayuwan shi,
Washegari tun da asuba na tashi na,dora ruwan kunu da sauran aiyu ka don nasan bawanda zai taimaka min da aiyukan, tunda mama bata gidan tana asibiti a can ta kwana tana jinyar yar uwar ta,
Ranan bani na samu kaina ba sai kusan karfe daya alokacin komai da ya kamata nayi nayi nagama na gyara gidan fes ta ko ina,
Nai wanka na sa wasu atamfana wax masu ruwan blue color,
Shigowan shi gida don daukan abinci ya samu na shirya nima sai dai ban yarda mun fita ba sai da na zaunar dashi a cikin dubara ya danci wani abin sannan muka rufo kofan gidan zuwa asibiti,
Kofan gida zamu hau mashi muka hadu da Baba Mudu wanda ya fito daga cikin gari,
Hamza ya sauka ya nufe shi acikin alkunyar sarakuta kamar kullun suke gaisawa,
Nan Hamza ke fada mashi Umma ce aka kwantar a sibiti ba lafiya,
Ba ya dago kai gurin da nake a tsaye da kullan abincin dana kulle ga wani dan kwalina, yake cewa,
Kin aika cikin gida a fadawa iyayyen ki kuwa Aisha ?
Nace Baba ban samu yaro ba yau duk su Aina basu shigo guri na ba,
Yace kin san yau ana zuwa boko babu kowa duk sun tafi makaranta ku isa insha Allahu yanzu zan karaso nima insha Allahu,
Mun samu ba laifi Umma ta samu lafiya don tana zaune saman gadon ta tana magana da kishiyoyin Anty Zarau,
Mun gaisa da,su nai masu yaya maijiki suka karba min da,Alhamdullahi,
Na aje kwanonin abincin daga can inda naga kayan abin karin safe dana aiko masu dasu,
Na lura Umma sai da kyat take amsa min gaisuwa na ina zaune ruwan dake manne a,jikinta ya kare sai ake kira nurse on duty ta cire mata take cewa tana aiki gata tafe,
Ganin ruwan ya kare zai iya fara dan sinking din blood din ta yasa na mike daga gurin da nake na nufi inda cotton yake na debo na wuce direct gurin ruwan na cire na mayar da canular din na,rufe mata
Ke Aisha kada kije rigima ki ja min matsala a ce sai an sake yi min allura, ko wani abu don walle duk na gaji da soke soken nan,
Umma ce ke fadin haka cikin maganan ta na yanayin mara lafiya, take maganan da kyat,
Lokacin ne nurse din ta iso gurin don cirewa Umma ruwan bayan mintinoni da na cire mata ganin ancire anyi komai yadda ya dace yasa ta dan fara waige waige tana cewa wacece ta cire maki ruwan, ?
Cikin sauri Umma take cewa dama ai na fadi rigimar yarinyar nan kada ya jawo min matsala,
Gata nan waje sallonta, ta cire min shi, ina cewa tabari amma sai da tacire, saboda iyayi,
To ai tayi daidai don ni ban zaci ruwan ya kare haka ba gaba daya ina ce kadan ya saura suka kirani, kin kuru da yaja jinin ki badon tana gurin ba,,,
Inda nake nurse din ta juya tana cewa, amma kina karatune ko,?
Nadan bata amsa cikin gyada kai tare da cewa eh ,
Wani school kike karatu nace mata health, good, good, yana da kyau hakan
Muna so mata suyi karatu sosai don taimakawa sauran matan mu nagida da basu son fitowa asibiti,
Kamar wanan maman taki sai da jiki ya kashe ta agida akazo muna da ita nan
Ai wallahi ta kuru don da sai dai wani ba ita ba a yadda akazo muna da ita ,
Mama Hafsi daga inda take zaune tace malama ai ita wanan yarinyar taba da shawaran mu wuto da ita asibiti
Don duba mai ke damun ta, saboda yadda jikin nata yai tsanani sosai,
Tace shine amfani karatun at list a dan samu wanda ya dan san wani abu zai iya taimakawa, ko, yaya ne, yafi a zauna dip gaba daya, a gida,
A daidai wanan lokacin da take bayani su Yaya Hamza suka iso gurin sukai tsatsaye cirko cirko suna sauraren bayanin da matar ke yi,
Tai setting din wani ruwa bayan taima Umma din allurai sai ta saka mata,
Ta juya inda nake tana cewa idan kinga yana rushing zaki iya rage mata don kada ya sakar mata da reaction,
Ta juya ta wuce sai mama hafsi tai magana bayan wucewan nurse din take cewa
Aikuwa munga alamar hakan don dai yarinyar nan ta taimake mu sosai kan wanan rashin lafiyan na yaya,
Ibrahim yake tambaya may yafarune wai,
Sai mama take mai bayanin yadda akayi da nurse har cire ruwan da nayi,
Ya juya gurin Umma yana cewa wallahi Umma Aisha babbace don dazu na hadu da abokina dake karatu a makarantar su yake cewa tana cikin dal8ban da ake ji dasu a school din nasu don first class ce ita,
Umma tai wani mayde baki tana cewa ai sai ka bari har takare karatun sai ka yabeta ko,
Hamza daga inda yake sai murmushi yake don yasan Umma bazata taba yabo na ba idai da bakn ta ne,
Muna gurin na hangi wasu mata tafe sunyi kwalliya sunyi kyau dasu hannun dayar, matar, dauke da basket din abinci,
Dayar kuma tana dauke dayaro karami a kafadar ta sai wani saurayi a bayan su dauke da flask din ruwan zafi da ledojin kayan tea a ciki sai na fruit,
Tsayawa sukayi inda gadon farko yake a dakin suna tambaya mutanen dake saman gadon,
Sai sukai masu nune da hannu a gurin da muke, direct gurin mu suka nufo,
Sai da suka zo gab damune na gane cewa su Hindatu ne ashe, tare da kannen ta suka shigo duba jikin Umma,
Nan aka shiga gaisawa da su ana tambayan ya jikin Umma din tare da mata fatan Allah ya bata lafiya,
Daga karshe suka gabatar muna da abincin da suka shigo dashi, a matsayin na dubiya,
Godiya muke masu tare da fatan Allah bar zumunci, tare,
Su waye Zarah take tambaya kasa kasa don son jin kosu waye su Hindatu din, don ganin su yan gayu da tayi,
Mama Hafsi ce ta cabe zancen da cewa mutanen arzikin Aisha ne suka zo ai kinga ita suka,sani,
Zancen yaiwa Umma zafi tana son cewa mutanen data ne, shi suka sani, bani ba ga kuma alluran da akai mata yana hawa mata kai,
Sai kuma ga yar yauri tashigo su ma har su uku suke cewa sunzo gidan mu ake fada mata shine tace bari su wuto direct asibitin,
Zarah take cewa yanzu ashe ita Aisha tasan mutanen arzikine haka take hurda dasu,
Hira,muke a tsakanin mu na,sake freely zakace bani bace ke yar hira har da dariya na a,cikin friends dina,
Bayan tafiyan yan gidan su,Zarah ta bude abincin da Anty Hindatu takawo muna,sai kamshi ke tashi cikin dakin duk ya,bure ko ina, a dakin
Mama hafsi ce ganin za ,a cinye abincin ni ina can tare da baki tai min tayi nazo naci abincin
Nace Mama sai da naci abinci na,fito daga gida a koshe na ke,
Ba wani kunya nan suka bude baki a gaban su hindu suka cinye abincin tas, akarshe ma suka bude wanda nazo dashi suna mai wani kallon wullakanci,
Sai mama ce ta shiga rigar arzikin su, take cewa su rufe mana anjima basai ankawo wani ba ai zai masu rana,
Ranan mama ta hana ni yin wani girkin dare tace aiki yai min yawa na huta hakanan,
Da dare dana dawo gida yaya ibrahim ya sayo kayan shayi yace na hada muna shi mu kasha muka kwanta, ni dasu,
Da dare bayan mun kwantane Yaya Hamza yake ce min,
Humaira zan so ace idan kin gama wanan karatun kici gaba da yin wani sai dai ina gudun fitanar Umma akan hakan,
Don ko wanan din da yaya aka samu ta yarda dashi balle a dauko wani,
Allah dai ya hore min nabar gidan nan kin ga alokacin duk abinda muka ga dama sai muyi abin mu a can babu sa idon kowa a kan mu,
Nace cikin gyara kwanciya na kadan Yaya aiko wanan din ma na gode don yai min rana,
Badon Allah ya hadani da gwarzon namiji irinka ba wanda yasan yakamata a rayuwa aida bankai ga haka ba, ma,
Da, har yanzu ina nan zaune ba wani karuwa a rayuwa na irin haka ni gaskiya ko a,wanan din ma nagode gaskiya,,
Ya rugumoni zuwa jikin shi yafara dan shafana hakan yasani gane cewa yau da dan karfin shi stress ya rage mai,
****** ********** ******
Kwanan Umma uku a asibiti aka samu sallama suka dawo gida take gida ya rude da yan shigowa gayar da Umma daga makwanta,
Yan uwan su baban su hamza maza biyu suka zo suna fadan ba,a fada masu ba,
Umma bayan sun wuce tace muna fukai afada maku kuzo kuga yadda nake ku karasa ni,
Cikin masu shigowa har da matan gidan mu, watau su Ummina,
Umma tana wani cika tana batsarwa wai ita tana da su a,rai tana jin haushin su a zuciyar ta,
Suma basu dade ba suka fito zasu tafi Atika tace su shiga mana su gayar da ni a dakina,
Duk da sun san cewa gulmace amma sun bi shawarata din sun shigo dakin nawa,
Wanda zance wanan ne karo na farko da su mamana suka shigo dakina
Don ko sun shigo iyakar su zauna awaje don haka shine karon su nabiyu da suka shigo gidan ina a cikin sa,
Sunyi, matukar mamaki kwarai dan ganin dakina a yadda basu zata ba don sun samu dakin acan acan duk da ba, wasu kayan zamani bane a cikin sa
Amma yadda yake a gyare yasa yana daukan ido, gwanin sha,awa
Don ga gadon yasha gyara ga kujera na tsab ga akwatina daga gefe na aza mai wani dan kyale fari sai fridge dina daga kofan shigowa dakin,
Ledan kasan dakin yana kyali sosai a lokaci don yasha guga kuma gashi babu yaran da zasu bata shi da dadti,
Mun gaisa dasu sukai min ya maijiki kamshin dakin yai masu dadi sosai,
Nace bari na basu sabon zobon danayi da rana yai sanyi sosai mama saude tace nabari idan sun tafi zasu aiko Aina ta karba masu,
Mama dai bata ce komai ba tun shigar su don kamar ma a takure take a dakin dole ce ma tasata shigowa dakin,
Hamza da yashigo ya tsaya rusunne daga kofa suka gaisa da su cikin girmamawa da mutunci,
Abinda yasa Atika cewa a lokacin da suka fito kai jama,a watau dai ana zaton wuta a makera sai a samay shi a masaka,
Gidan masu kudi babu tsabta ba tarbiya amma ga gidan tallakawa duk an samu abinda ake zaton samu gidan masu arziki,,
Wai ashe sunje gaida Kubura shine suka samu gidan da dakinta kaca kaca kuma mijin da yazo ya samay su shine ya wuce kamar bai gansu ba ita Atikar ce tai mashi magana cewa, baigane su bane yana tafiya yace nagane ku ma,na,
Suka fito ran su a bace kan irin yadda yai masu ita mama saude ce ma ta fara magana sai da Ummi tai mata magana cewa ba girman ki bane yaya,
Kowa da halinsa ake zama dashi tunda baiwa yar mu wullakanci ba kuma tana zaune lafiya da abinta banga abin bacin rai ga mutumin daba kai ka haife shi kai mai tarbiya ba,
Shine sukai shiru ba wanda ya kara tayar da zancen har suka dawo gida,
To shine fa ashe maganan na a cikin rayuwan Atika sai yau take sakewa mama saude habaici, akan shi,
Mama saude zatai magana Ummi take ce mata ai idan daji bai gama cin wuta ba yaya ba,aiwa kututure barka ko,?
Atika tagane inda zancen Ummi ya nufa kuma ita Ummi din tagane cewa badon Allah Atika ta yabi gidana ba don sheri ne kawai da kissa irin na kishiya,
Ai itama yaranta zasuyi aure aga inda suka dosa sai sukai shiru gaba daya,
Lokacin da Aina ta shigo karban zobon su Hamza na gurin don haka sai yafita waje shagon su ya shiga yadauko omo clean ya saka masu aleda da sabulun wanki,
Ranan kan habaici saida a kai fada da Mama Saude da Atika a gidan don ta kaita makura,
Da Baba yazo ya samu ana wanan jidalin yake tambayan ba,asi shine Atika tai tsagal tana cewa zance nake ina cewa ashe kwanciyan hankali da samun wadatan zuci yana ga auren tallakan da akai gudu shine yaya tace wai ita nake sakewa habaici,
Shi kuma Baba sai yace dama ai hakan gaskiyane ba karya bane,
Yau kin fara ganin gaskiyan maganata ke nan Saude,
Naso hada zuria da wanan yaron Hamza a rayuwata don gani da sanin halin yaron
Amma sai kikai min tutu arai keda yar ki kukayi kokarin watsa min kasa a idon jama,an da na gaiyato a gidan nan,
Allah ne ya rufa min asiri wanan yarinyar yar albarka ta share min hawaye na,
Yanzu don gaskiya tafara halinta shine zakice wai kada a fadi don may,
Ai dama kowa yasai rariya yasan dole zatayi yoyo indon wanan zaben tumun daren da kukayi ke da yar ki babu komai a cikin sa sai tarin bakin ciki da takaici don ko alhakina ya ishe ku,
Cikin kuka mama Saude tace lalai duniya malam yau kuma yar Agwaice abin yabo a bakin ka,
Ba hakana bane Saude dama ni yar Agwai ban dauketa komai ba sai "ya kamar kowa a gidan