Sarautar Mata
Chapter 39 of 94
san saboda jinin hailar da mukeyi bai bari asiri yayi wani tasiri mai tsawo sosai akan mace sai dai idan asirin yayi muni da yawa,
Mama tace yanzu ni shawaran da na yanke a raina basai yaya ta sani ba a gidan nan
Zan shiga in futa inga nayi wani abu akan zancen nan don ita uwar taku bata da kwanciyan hankalin fahintar halin da yake ciki,
Naji dadi sosai ga yadda mama ta nuna min so da kauna kuma tabani shawara kan na dage da,addu,a don mukai karshen matsalan ,
Nace cikin dan share hawaye, na mama nagode insha Allahu zanyi yadda kikace min,
Tace nagode Aisha ki kwantar da hankalinki kinji kada ki tayarda hankalinki ko kadan
Naima mama godiya na ci gaba da aiyukana sai dai jikina ba karfi atare dani,
Saboda zuciyata tana min tunane kala kala akan ko wacece zai aura din,
Sai yama lis yashigo gida tare da wani mutum makulin dakin hatsin shi ya karba a hannun Umma suka shiga tare da mutumin inda sunkai yan mintina acikin dakin tare da mutumin,
Sun fito dakin inda suka fita tare da wanan mutumin, jimawa kadan yadawo dauke da wani leda wanda hakan ke nuna kudine a cikin ledan,
Sai wasu katai maza su uku suka shigo suka fara jidan buhu hunan abincin zuwa waje suna lodawa a cikin wani mota mai budaden baya,
Ban san lokacin dana fada daki ba ina kuka kuka mi tsuma zuciya wanda ni kadai nasan may nakeji araina,
Can natuna da wani abu sai nafito waje da sauri gurin masu daukan buhun na nufa nace ku aje min buhun wake biyu ku fada min kudin shi naji,
Yadda suka ganni kamar a,hargitse yasa suka dakata dayan su yadaga wayan yakira wani layi yadan fita waje na wasu mintina ya shigo,
Ina nan gurin yadawo yake ce min yace nabada dubu hudu hudu nashiga na kirga dubu takwas nakawo masu nace su dauko min zuwa dakina,
Sukaci gaba da kwasan abinsu suka fita duk su Umma suna tsaye suna kallo na a cikin yar damuwa,
Da dare bayan yashigo sun dauki lokaci da Umma a dakin ta sai daga baya akakira mama hafsi tashiga ta,sasan ta su,
A cikin dare maimakon Hamza ya tsaya muyi magana ta fahinta sai wani dan sha min kamshi yakeyi,
Ko may ya tuna kuma zuwa can naji ya ce Humaira, jin ya ambaci sunana yasani dago kai na kalle shi,
Bana son kiji zancen nan a bakin wani ko wata don haka nake son fada, maki kiji shi a bakina,
Aure nake son karawa kuma bawai kin min wani abu bane zan kara aure a,a ra,ayine kawai nayin haka yazo,
Tunda ya fra zancen shi kaina yana duke a kasa ban daga na kalle shi ba,
Yaci gaba da cewa kuma wanan abin irin yadda nake ji idan har banyi auren nan ba a yanzu zan iya mutuwa Humaira,
Da sauri na dago kaina don jin may yafada min don na gaskanta zancen shi,
Gaba daya ya canza min ya koma kamar wani tababen ya ramay yayi wani baki, dashi sai dogon wuyan da ya kara,
Gabana,ne ya fadi don sai naga,gaba daya ya,canza min kamar ba Hamza na ba,
Ya dan sauke ajiyan zuciya tare da,furzu iska yake cewa idan ban yi auren nan ba wani babban matsala zai ita samu na don indan har banga Lima ba acikin yini ji nake tankar zanyi hauka, a rayuwana,
Duk abinda na kalla zanga wanan abin ya koma,min tankar fuskan Lima ban ganin komai a duk abinda nake sai ita nake gani ,
Innalillahi wa,inna alaihim raj,un,,,
Ya Allah ka ga bayinka suna,bukatan taimakon aka wanan matsalar da ya bullo muna a gidan Allah kai muna mafita mafi alheri akan wanan al,amari, ya Allah ka tausaya muna ba don halin mu ba,,
Shiru mukayi gaba dayan mu ba mai iya yiwa wani magana har tsawon wani lokaci kowa da abinda ke mai yawo a zuciyar sa,
Yau ma kamar daren jiya ba,wani abinda ya wakana a tsakani dashi don tankar dutse ce a kusa dashi ba ma mace ba sai dan jayewa yake daga gare ni,
Tun da safe bayan ya shiga gurin su mama ya dan dauki dan lokaci tare da su can naga yafito rai a bace ina rakube ajikin bangon dakina daga waje, yafito fuu ya,shiga daki kafin ma nashiga sai gashi har ya fito daga dakin yana ce min yatafi,
Dakyat na iya bude bakina ina cewa Allah ya tsare hanya Allah ya rufa muna asiri duniya da lahira,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI KUSAKANI GA ADDU,AN KU,,,
IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WANI PLEASE,,,,
Ranan haka muka wuni a cikin wani irin yanayi babu mai wani kuzari daga cikin mu,
Kowa da irin abinda zuciyar shi yake raya masa dangane da zamcen abinda ya faru a gidan,
Wanan abin bai hanani yin aiyukana dana saba yi ba a baya,
Umma ma wace tun wucewan dan ta take daki a zaune bata fito ba,
Sai zuwa sha biyun rana ta dan fito ta kewaya bayi bayan tafito na ta shirya zuwa gidan mama sa,a gurin hiran ta,
Sai gidan ya koma tsit dagani sai mama wace kallo daya zakai mata ka hango tarin bakin ciki a fuskan ta,
Bayan nai wanka na shige daki nima ban fito ba har zuwa azahar, nafito nai sallah tare da cin dan abinci wanda sam ban jin test din shi a bakina,
Ina zaune a gurin naji muryan Umma wace dawowan ta ke nan daga gidan su mama sa,a,
Yan mintina naji tana kwada min kira hakan ya,sani tasowa daga gurin da nake zaune, cikin amsa ma kiran da take min din,
Kwanon abincin ranan danta jibrin shine a hannunta tana juyawa a hankali, acikin fada take cewa,
Yanzu Aisha wanan abinci ne, za,ace rabon yaron nan a gidan nan,
Ko mugun halin ki ya tashi ne zaki sauke a kan shi kuma,
Wasu irin yawun takaici na hade a bakina tare da dan karasowa inda take a zaune idanuwa na suna a kan kwanon abincin da take nuna min,
A hankali na bude baki da zuman nai magana sai sa,a de autar mama ta leko daga daki tana cewa,
Umma wani abinci nice fa na diba na zaci shine nawa ai, shiya sa na diba,
Nazaci duk bakin ciki karo kishiyan da za,ayi shine har ya shafi diyana za,ai masu horo da yunwa su ma,
Don dai ni bazan hana yaron jin dadin abinda yake so ba a ranshi,
Aure ne sai babana ya karashi a gidan nan dama kulba dade kulba jima,
Juyawa nayi simi simi zuwa dakina don zancen umma yana min daci a raina,
Taci gaba da cewa ban san alherin da ya gano ba don kawai ina Rabin mahaukata zan hana shi abinda yai niyar yi,
Idan baki hana shi ba ai, kika zama Rabin mahaukatan,
Yanzu danki zai auri kafura, wace bata tsarki bata wankan haila, balle na janaba shine har kike zancen kin ga alheri a ciki yaya, ?
Wanan abin bakin ciki da gori da ya samay mu yaya ke har kinga gurin saka yar ki sarakuwar ki karamar yarinya a gaba kina mata fade irin haka,?
Shiru Umma tayi don zancen mama yai bala,in shigan ta a rai,
Idan baba karami ya tashi karo mace a gidan nan Aisha ta isa hanashi ne ko maye nata aciki ita,
Yau yaya mu bakin ciki ya cika damu mu da dan mu zai auri kafira ba Humaura kishiyar kafira ba,
Mune duniya zatace dan mu yafi karfin mu ai ko,?
Sosai jikin Umma ya kara mutuwa tai wani kai zaune tana cewa,
Amma aikowa yasan halin dan yau hafsi sai wanda yaso ya zageni a cikin wanan zancen don ansa dai bazan taba yarda ya surka min zuria da jini kafirai ba a gida,
Mama hafsi tace sai ko ki dage da yi mashi addu,a bawai wanan shirmay ba haka,
Sosai tai la,asar nan sukai ta zancen da yar uwar ta har ta dauki shawaran mama zata dage da addua kan wanan abin kun ya,
Sai dai bayan kwana biyu kuma mama Sa,a ta kara zugata ai ta hau fam sai take gani wai ana mata hassadane don kawai ta hadasu fada da yar uwar ta,
Ganin yadda Umma ta sakani gaba ga kuma bakin cikin abida miji ke min yasa mama hafsi zuwa gidan mamana Rahana ta fada mata halin da nake ciki na damuwa akan tazo ta samay ni ta bani magana,
Batare da kowa yasan zuwan ta ba, har ta tafi tadawo ba wanda yasan cewa ta tafi,
Mama Rahana ta samu Ummi da zancen duk hankalin su ya dan daga amma sai suka yanke shawaran kan su kwantar min da hankali sai su bini da addu,a,,
Don namiji idan yai niyar aure ba mahalukin da ya isa ya hana shi yi sai Allah,
****** ********* ******
Yau satin shi daya da tafiya amma ko wayan shi na ya isa lafiya da ya saba bugo muna babu shi,
Gashi tun ba,a kai ko ina ba abinci ya fara muna tsaiko a gidan ba irin yadda muka saba sau uku a yini ba, kamar baya,
Na rasa may ke min dadi a duniyan nan gashi gurin wanda nake dan jin sanyi a gidan yanzu yafi guba daci,
Ina zaune ina tunane hannu yana rike da littafina wanda na dauka don na dan rage tunane dashi,
Amma karatun ya gagara sai tunanen da nakeyi ina cewa, ni Aisha,
Nagodewa Allah na da can ina cewa na huta da fitinar gidan su Ummina, nai aure na a gidan tallakawa yan uwana,
Sai gashi babu jindadin babu kwanciyan hankali a tare dani sai tarin fitina duk safe,
Sam ban taba tsan manin irin wanan sakaiyan haka ba daga gurin Hamza,
Wanda a dacan nake dauka daga Ummina sai shi gurin masu kaunan farin cikina,
Sai gashi ya shigo gari na koma mai kamar wata abin kyama, wanan zuwan, na nisa tare da cewa ina gyara zamana,
Ya Allah ka tausayawa boyar nan taka Aisha da hanyoyin alherika ka sauya min wanan rayuwan bakin cikin danake a cikin sa,
Ina jin muryoyin su Umma da yaranta daga dakina, mama hafsi ne ma banji ta a,waje ba,
Ina a cikin wanan halin ne na tu nane naji murya ana sallama kamar muryan Ummi na,
Shiru nayi nakara saurarawa don na fahinci mai sallamar, kara sallama akayi muryan mamana Rahana ne,
Da sauri na fito waje daga cikin daki ina mata sannu da zuwa, mama cikin nuna farin ciki na, da ga ganin ta,,
Inda Umma take zaune saman tabarma ita da yaran ta mama ta nufa suna gaisawa, saiga mama tafito daga dakin ta hannun ta dauke wani roba cikin fara,a take gaisawa da maman nawa,
Niko ina tsaye daga bayan su duk na matsu su gama gaisawa da mutanen gidan,
Dan jin mama ta mike tana zuwa dakina ina gaba muka,shige,
Umma ta raka mu da harara tana cewa Allah dai ya fiku muna fukai kawai ta Allah ba takuma ba,
Mama dake bayan ta daga tsaye take cewa ikon Allah,
Shigar mu daki na nuna ma mama kujera ina kara kakabewa duk da babu kuran komai a kai nace zauna mama,
Gurin fridge na nufa nadauko ruwa da goran zobo duk da nasan cewa suma sana,an, gidan sune kayan sanyi na gargajiya,
Mama ta dauki ledan ruwan dake gaban ta ta dan huda ta ja kadan sai ta mayar a plate din don yai mata sanyi sosai,
Ina zaune daga gefen ta tadago kai ta kalleni tace Aisha may yasamay ki haka kin ramay kinyi baki duk kin wani lalace a lokaci guda, haka,
Dan dukar da kaina nayi yayin da wani malolon bakin ciki naji ya tokaro min a wuyana,
May ke faruwa ne haka wai Aisha idan baki fada min ba wazaki fadawa damuwar ki,
Sai naji na kasa magana wasu hawaye ne masu dumi suka silalo min daga kumcina,
Ganin na sa kuka irin mai kuna zuciyar mai sauraron ta yasa mama rudewa tana cewa,
Haba Aisha nazo naga lafiyan ki na samay ki a hakan ga daga tambaya kuma kin saka min kukan tashin hankali,
Baki son ina shigowa gurin ki ke nan ko don ba zan zo gurin ki kina min kuka haka ba
Cikin dan sasauta kukana nake cewa, mama ina cikin kunci da bakin ciki ga kuma kuntatawan rayuwa wallahi mama ni kadai nasan halin da nake ciki, a gidan nan,
Yanzu ki share hawayen ki ki daina wanan kukan ki fada min abinda yake faruwa,
Kamar yadda mama tace hakan nayi na dakatar da kukan tare da,share hawaye na,
Cikin kwantar da murya na fara zaiyano wa mama abinda ke faruwa tun farkon zancen da kuma irin yadda yanzu Umma ta sakani a gaba da habaici da gori,
Mama tana jin haka tace amma ko anyi dattijiwar kawai matar danka zaka saka a gaba kamar kishiyar ka haka,
Mama ma ta rasa may zata ce sai kawai tai tsuki ta ja bakin ta tai shiru nadan wani lokaci,,
Can murya a raunane take cewa, Aisha abinda nake so dake shine ki kwantar da hankalinki ki ki saurari may zan fada maki,
Cikin sauri na kara mayar da hankalina a gare ta tafara cewa,
Dama shi zaman aure dan hakkuri ne Aisha zo mu zauna zomu sabs haka rayuwan aure yake,
Shi namiji tundai namijin bahaushe baki raba shi da bakin aure aure,
Walau tun kurciyan sa ko kuma zuwa girman sa wani kuma haka zaitayi a cikin rayuwan shi,
Don haka banga dalilin da zai sa ki tayar da hankalinki ba har kina batun illantawa rayuwan ki haka,
Ba mace daya, ko uku zai kawo lokaci guda babu abinda ya damay ki,
Don nagaba yai gaba nabaya dole sai biya don dai kece uwargida sarautar da sai macen da Allah yazaba ta rike wanan sunan mai daraja zata rike shi, a gida,
Don haka maza share hawayen ki ki gyagije kinuna ke yar arzikice bata tsiya ba,,
Daga Hamza din har uwar wace bata san mutunci ba ki fita batun kowa ki koma ga Allah,
Nuna mata cewa Allah yafisu yafi sherin su kuma,
Ke dai ki dage ki dinga kaiwa Allah kukan ki banda rashin kunyawa kowa kiyi masu ladabi da biyayya irin yadda kika saba Allah na tare da masu hakkuri insha Allahu,
Cikin murya maiban tausayi tare da gyada kai na ce na gode mama Insha Allahu zanyi yadda kikace mama,
Takara dacewa zamu dage da maki addu,a insha Allahu,,
Mun dan dauki lokaci da mama mukai sallama da ita ta,sallami su Umma da mama inda na rakata har bakin kofan gida sai da ta fita na juyo zuwa cikin gida,
Allah dai ya tsare min wanga yaro daga duk wani kuli da tofe tofe da za ai mai,,
Allah ya sauka yaya wanga, bakar dabian bai yi ba,wallahi,
Nikan tun zuwan mamana sai naji na koma wata wasai dani ban tare da wani kunci ko kadan kamar yadda nake ji a baya,
Sai na koma harkoki na kamar yadda na saba yi a baya can,
Sai naga hakan kuma baiyi wa mama dadi ba tafara nuna bacin ranta a ganin ina walwala ba bacin rai a tare da ni yasa Umma kokarin ganin na shiga kuncin ta ko wani hali, amma hakan bayi ba,,
Daga gurin practical na wuce zuwa gurin hindatu don bata da lafiya tana fama da lalurar karamin ciki a jikin ta,
Irin cikin nan mai wahala take fama dashi ga miyau ga amai komai bata ci sai, dan kafa koshi mai dan zafi wai,
Hindatu duk ta bi ta wani ramay ta koma kamar wata yar kauye wai ko wanka bat iya yi da sabulu sai dai ta,watsa ruwa kawai ta tashi,
Na tausaya ma yadda na samay ta ga dakin ta duk ya wani yi kura ko ina kaya ne birjik, a dakin,
Dole na cire hijjab dina na tsaya na gyara mata dakin ya koma tsab dashi wankin da ta tara nace zan dawo nai mata a cikin weekend insha Allah,
Sarakuwar ta mama itace take fama da dawainiyar komai yanzu na gidan su har girki mama din na samu a kitchen tana masu girki,
Da sharan gida idan yai datti takumakula da Haidar dan Anty hindatu din,
Abin gwanin ban sha,awa, don zakace yarta ce ta cikin ta take a cikin wanan halin ,
Kadan kadan zata shigo tace sannu hindatu ya jikin naki kina son abu kaza kina son ai maki kaza,
Hakane zatai ta shigowa tana duba Anty hindatun wace ke kwance sai faman tsriga miya take a wani roba mai dan girma,
Yadda nai Alkawari da aka shiga weekend bamu da wani aiki sosai a asibiti sai na dauki permission na dawo gidan ta nai mata wanki tare da kara gyara mata daki tas,a da gida ranan nai mata girki sai dai ban tsaya na ci ba na wuce zuwa gida,
Nabar gidan bada jimawa ba maigidan ta Mansur ya iso gidan tun daga waje yake mamakin irin yadda gidan yasha gyara haka, tas
A ranshi yana tunanen ko Hindu din taji sauki ne har ta samu karfin yin wanan aikin haka duk da kuma ai bai fada mata cewa yana hanyaba,
Sai gashi ga mamakin shi gida yayi wani tas dashi ga kamshi yana tashi, tun kofan shigowa,
Ya,shigo gidan da yar fara,ar shi don rabon da ya ga irin haka kusan wata uku kenan,
Sai dai yana shiga yai turus a kofan don ganin hindu din kwance a cikin corido din dakin su, yasa a kasa ko riga babu a jikin ta,
Ya karasa gurin ta a cikin nuna damuwar shi a gareta yana tambayan ta, ya jikin nata ya dan zauna daga, gefen ta yana dan taba jikin tayana wani tambayan ta acikin nuna damuwan shi da kulawa a gare ta,
A haka mahaifiyar shi tafito ta,samay su tana mashi sannu da zuwa,
Sun gaisa da mama, yake ce