Sarautar Mata

Chapter 78 of 94

kukan duk wanda ya ganmu a lokacin sai ya yaba muna sai dai makiyin mu, kawai,
Hamza ko duk ya rude har da mikewa yayi yana fadin Umma wani abune ke maki ciwo ko may akai makine wai,
Mama tace ba abinda ke mata ciwo don tun safe lafiyan mu lau a gidan nan da ita,
Kara zama abin tausayi Umma tayi tana marairaice kukan ta duk hankalin su ya daga sai cewa Hamza keyi Umma idan nine nai maki laifi don Allah dai kiyi hakkuri ki yafe min,
Ganin da tayi duk ya kidimay har yana rokon ta gafara sai take cewa, cikin kuka,
Dole ne nai kuka Baba na ganin burina a kan ka ba zai cika ba har na mutu,
Subbahanallahi Umm may akayi kuma wanda ban cika maki burinki ba har zaki mutu baki gani ba,?
Duk gaba dayan mu munyi son muna sauraren burin da Umma ke dashi a kan dan nata da zata mutu bai cika mata shi ba,
Ina zaune sai shan jinin jikina danayi don ina Allah Allah in ba akaina ne gurin nata zai kare ba,
Duk munyi kasake muna kallon Umma wadda harda majina take fecewa don kukan da takeyi gasu Ibrahim duk sun shigo don ganin motanshi a gidan yazo,
Wai mama maynene ana tambayan kikin yi shiru sai sa zukatan mu cikin tashi hankali kikeyi, inji Jibrin dan zafi,
Hamza yakara tausa murya yana lalashi ta saida ta fece wani maji na tace, cikin sanyin murya irin na wanda ke kuka,
In ganka ka,shigo gaidani da matan ka biyu mana Babana kullun bawa idan ya samu ai ya,geadawa Allah yagode ga mata birjit agari kana da wadatan kara aure amma ka zauna da mata guda,
Tsaki suka ja banda hamza da ya dukar da kan shi din bai taba zaton wanan ne abinda mama takewa kuka ba haka,
Murmushi kawai na ita fuska na kakaro a fuskana nace araina Umma kin kai makira ta nan kuma kika bulo min ana zaune kalau,
Kowa na magana shi baiyi magana ba sai can naji ya bude baki cikin sanyin murya yake fadin kiyi hakkuri Umma in har lokacin yin hakan yayi ai zankara mata don ina da gurin yin haka bakiga gidana na mata biyu nayi ba,
Insha Allahu bazan barki har ki mutu ban cika maki gurinki ba nan badadewa ba zan kara mata ,
Kaiyya inji mama wai uwar diya mata ce ke irin wanan maganan haka da baki da diya mace ne sai ace baki san zafin abin ba,
Munzo da niyar yini mukazo amma wanan makircin da Umma ta azamin yasa duk jikina yai sanyi lokacin da yagama zai tafi nima namike ina cewa zamu tafi don tun da Umma tai magana sai ban kara magana ba da kowa, saboda wanan gurin na Umma ya sakar min da kasala ajikina
Gashi inba gyaran Allah ba kalaman da Hamza yaiwa Umma ya sha banban da wanda yasaba mata idan tai maganan yai min kishiya a baya hakan ya tabbatar min da yana gap dayin yanzu,
Ganin nima namike ina cewa yaran suzo mu tafi yasa shi cewa au kun fasa yinin da zakuyi a nan din ne,
Ummm kawai nace mashi tare da tattaro natsuwa na ina ce masu zamu tafi,
Ke Humaira baki fahince ni bane karin auren da nace yayi aiko ke amfanin ki ne ina kwanan baya ce min yayi aiki yai maki yawa a gidan yanzu idan ku biyu ne ai baxaki wahala haka na ba,
Yace hakane fa Umma itama saukin tane idan nakara din ai ba wani abu bane dama,shi aure bana kowa da kowa bane sai wanda yasan zaiyi adalci a kai,
Sai dai ina gudun nayi nazo ina zaluntar dayan ko a,taru a zalunce ta najawa kaina fitinan kabari shiyasa ni auren ma yafita min akai,
Amma tunda burin kike nan a kaina insha Allahu zan kara auren a zauna lafiya ni dake Umma,
Tace yyawa dan albarka haka nake son ka gurin biyayya yanzu da su biyu ne idan dayan bata zauna ba basai dayar ta zauna muna har daren ba,
Nai masu sallama naja yarana muka fita mamace kawai tai muna rakiya tana fadin Antina ina nan zuwa nai maku wuni yaya yace ai yanzu gwago gudun ki takeyi,
Muna hanya ba,wanda yaiwa wani magana abakin wani shagon sayar da kayan sanyi ya,tsaya yana cewa bari nai maku take away don naga rana yayi baku yi abinci ba,
Sai da ya dawo ya zauna amota yafara tuki yake cewa kai Umma akwai rigima daga shigar mu ta tayar wa kowa da hankali nima na dauka ko wani zance ne can nadaban wallahi,
Ranan haka na wuni sukuku dani ina kullawa ina kwancewa sai faman tunane nakeyi ni kadai a gida,
Sai dare ya dawo cikin anna shuwar shi ban nuna mashi komai ba kuma ban ta da zancen ba don ban mason ayi shi,
Dadare bayan mun gama komai sai barcin shi yake hankali kwance niko na kasa runtsawa sai tunanen abinda Umma tai min yau nakeyi,
Umma shike nan tai min wanan sanadin ta kishiya a daidai lokacin da muke zaman mu na dadi ni da mijina
Amma yanzu zata sa a kawo min wata a cikin gidan nan ta zauna a matsyin kishi a gare ni, Umma bata bukatar zamana a gidan dan ta ko kadan,
Yadda na saba zama ni daya yanzu idan ankawo wata na tabbatar da duk farinciki na zai rushe ne kamar yadda Umma take bukatar gani na,
A haka muka zauna cikin wani bakon yanayi ina lura da tafiyan shi ko zanji wani abu ya taso akan zancen kishiya sai da har zuwa tsawon lokaci ba abinda ya faru shi kake ji,

****** ********* ******
Watarana ya,shigo gida da takardun shi na karba kamar kullun zan shiga mashi dasu daga ciki sai yake ce no dakata ai takardun nakune na tafiyan ku, saudiya,
Ban san lokacin dana juyo ba cikin murna nakai mashi ruguma tare da subantar shi ina cewa kai yayana aiko naji dadi nagode, wallahi, sai faman murmshi yakeyi yana jin dadin yadda nake ta faman yabawa,
Nasake shi ina cewa amma ni dawa keda wanan sa,an rana haka yaya ?
Keda suwa kike son tafiya dama bada sisters dina ba tare na,samo maku sai mama,
Naso ibrahim yabiku kada kuyi tafiya babu namiji a tare daku amma kuma har yanzu ba,a samu kujera ba,
Nakara rugumay shi nace wayyao yaya ka gama min komai don kafitar dani daga zargi wallahi,
Nace wai ashe saudiya na da kwasan manyan bako bana gaskiya yaya ban san irin godiyan da ma zan maka ba,wallahi,
Yace in baki sani ba,aini na sani bari anjima kiga irin godiyan zan gwada maki ai,.
Dariya kawai nayi tare da kara kankamay shi ina murna da farin ciki sai sambatu nakeyi ina Allah nagode maka Allah yakara daukaka da budi na alheri yaya,
Kafin kwana biyu zancen tafiyan mu kowa yaji sai murna ake muna da fatan aje lafiya a dawo lafiya,
Su Zarah har ni saida sukaiwa godiya sina cewa sun san nice silar hakan don basu zaci ma zai kaisu ba,a lokaci daya haka,,
Muna ta Allah ,Allah lokacin tafiyan mu yayi don an samo wa yaya Ibrahim nashi,
Yai tafiyan shi zuwa lagos ya dawo mun tare shi da murna da farin ciki kamar kullun sbai fita ba sai washe gari ya tafi zuwa gaida Umma,
Ban bishi ba dontun lokacin da tai muna kuka nan ban kara zuwa gidan ba har yau din nan, tai korafin hakan ta barni,
Yasamu nagama girki ya zauna yaci yana wa madina ba,a wai itace tai girkin shiyasa yaji dadin shi,
Ina daga zaune gefen shi sai murmushi nake masu don yana kula min da al,amarin yarinyar sosai kamar shiya haife ta, har makarantan boko ya saka min ita na kudi ita da Jidda suke zuwa,
Sai da yakare na kawar da kayan nadawo na zauna daga gefen shi remote din tv dake aiki ya dauka ya rage karan tare da juyowa inda nake,
Hakan yasa na fahinci magana ce ta musanman yake son yi dani,
Yace cikin kura min ido tun kwanaki naso muyi wata magana dake Humaira sai dai ban samu lokaci bane don tafiyan da nayi,
Na zuba mashi ido ina kallon shi tare da sauraren shi, yace nasan zaki dauki maganan tawa da wani manufa ta daban,
Amma idan kin fahince ni sai kiga maganan ba,wata abin tayar da hankali bane,
Ya dan yi shiru tare da numfasawa yasake kura,min ido cikin natsuwa yace bawani abu bane illa zancen auren da nake son in kara kwanan nan,
Abinda naji azuciyata yafi karfi akirashi da faduwar gaba sai dai a fili na dake ina sauraren shi batare da,na nuna damuwaba a fili,
Nasan ni dake akwai fahintar juna Humaira kan mi a hade yake bamu da,wata matsala a ko wani bangare,
Itama wace zata shigo din ba wai karamar yarinya bace nasan tasan takan duniya sosai, shiyasa na yarda da shigowan ta a cikin mu,
Don haka ban son kiyi wani tunanen ko ban son ki ne nace zan kara aure ko kuma ki dauki wani abu da tsanani har ki bata tsakanin mu,
Kuma ban son kiyi tunanen ko wanine yasani yin wanan auren ban tashi yi ba, kinnsani tun farko ni mutum ne mai ra,ayin hakan,
Banyi bane abaya don ina son in maki adalci sai kin samu natsuwa da kwanciyan hankali, a gidana,
Hmmm yaya ke nan adalcin may kai min ko kuma kwanciyar hankalin may nasamu in akwai shi a gare ni nuna min in gani,
Shiru yayi tare da,dukar da kan shi kasa sai kuma yadago kai yana kallona kara jin haushin shi naji a raina har ban iya boyewa
Namike a zafafe nafara tafiya ina cewa nayi dana sani da auren ka Hamza a rayuwana wallahi,
Ya maimaita kslman Hamza da nace yace Hamza yau Humaira, nace eh Hamza ko ba sunan ka ke nan ba,
Bukatar Umma ya biya ai ban san ta isa ba da tasaka cika mata,burin da tace sai yau tasa ka sakeni saki uku ta zuba ruwa kasa tasha,
Mikewa yayi a lokaci daya ran shi a bace ya nuna ni da yar yatsa yana cewa kada ki fara ki zagar min uwa wallahi yanzu ranki zai baci a gidan nan,
Naga kina son kawo maganan da zata lalata tsakanin mu don ba zan kyaleki ba idan kika zagar min uwa Humaira,
Ki bari mu fahinci al,amarin yadda muka saba saboda kada mutane suyi maki dariya,
Ya kalleshi kasa da sama nace mutane ai sun dade da min dariya tunda ba yau kafara watsa min kasa a ido ba,
Yau ne aure ka ake min dariya a gida da,waje tunda kai ba dan goyon baya bane wallahi nayi tir da zama acikin ku mutanen da ba,su san arziki ba,
Ai kin san bamu da arziki tun farko kika,aure Aisha ,?
Nadauka a lokacin ko ku yan mutnci ne ai sai yanzu na fahinci ko ku suwaye,
Na tako har gaban shi nace ka,sake kawai ka huta da,wahalana da,akecewa na shanye ka,
Yace baki shaye ni din bane Humaira wana ke gani da mutunci in bake ba yafada cikin murmushin takaici,
Ya zo ya gwautani ya wuce nasha gaban shi nace wallahi sai ka,sake ni don ba zan zauna akara kawo wace zata sani agaba da,tashi hankali ba,
Hankade ni yayi ya fita daga gidan yabarni nan na tsuguna a gurin tare da rushewa da wani irin kuka bai ban tausayi,
Bai, madina tazo ta dafani idon ta taf da hawaye tana cewa kiyi hakkuru Anty ki kyale shi don Allah,
Rugumota nayi ajikina muka shiga rusa kukan a tare ba mai ba,wani hakkuri sai nice ma nagaji na kyale gudun karnajawa yar mutane ciwo,
Bai kara kula harkata,ba nima ban kara bi takan shi basai zaman doya da,manja muka shiga yi,
Bai saba ba don haka yahe ya fadawa mama hafsi a,asirce tazo tai min magana ita da anty hindatu,
Lokaci guda sukazo lokacin kwana hudu daya fada min zancen auren nashi,
Ina ganin su nasan sun san da zancen zaune nake a,falo dagani sai rigar barcin dake a jikina tun safe da zani,
Tun shigowan Hindatu tafara cewa may ye haka Aisha may ye kika mayar da kanki haka kamar wata bakauya can,
A take idanuwa suka ciki da hawaye nace muryana na,shirin kuka Anty may naiwa Hamza da Umma,arayuwan su suke min wanan azaban haka may ne masu anty,
Dafani tati tace kinga idan kina son muyi magana mai kyau tau share hawayen ki ki saurare ni,
Don wannan kishi naki yafi kama da irin kishin jahilan mata ba matan da,sukan kan su da addini ba,
Ita fa kaddara ai yarda da ita shine sharadi na cikan imanin bawa don komai da kikaga bawa yayi mukadddarine a gare shi, mai kyau da mara kyau sai ka,rugumay ta idan tazo maka,
Aisha mayye acikin wanan zance bafa wanan karon bane farkon kishiyar ki, may zai hana ki natsu ki nazarin wacan artabun da kuka sha wancan karon ki san ta ida zaki bullo mashi,
Amma kinzo kina wanan irin ta da hankali haka kamar wace bata da,wayo,
Don Allah Aisha ki natsu ki kwantar da hankalinki ki fahinci mijin ki ku zauna lafiya kada wace za,a kawo tazo ta samu kuna fitina har ta samu kafar da zata rainaki,
Mamahafsi dake gefen mu ta ce ni Aisha na,rasa ina hankalinki da,wayon ki, ya shiga ne wai,,
Da har kika rufe ido kinawa mijin ki wanan tujaran cikin nuna,rashi ladabi da tarbiya,
Shiru nayi don zancen su ya fara,ratsa,min zuciya nan suka sani gaba da fada da nasiha har saida nasauko,
A,karshe suke ce min na yi hakkuri na kara tausar zuciyata sun san hakan akwai zafi amma idan nai hakkuri komai zai wuce
Gashi duk mijin ki ya tayar da hankalin shi don kin ki kwantar da hankalin ki ga buki na karasowa saura Sati daya da yan kwanaki,
Da sauri na dago kaina nace satifa kikace mama, mama tace eh sati mana bakin ki kwantar da hankalin ki ku fahinci juna da shi ba,
Kin ba yan uwan shi da uwar shi dama sun shige maki gaba tare dasu yake aiwatar da shirye shiryen shi an barkina nan kina ta haukan ki ke kadai,
Ni don ansan ina,tare dake komai ba,ayi dani Aisha ina dai jin wanda yazo min a kunne na,
Mama yanzu ashe har auren yazo ban sani ba mama wallahi hamza ya cuceni yaci amanata wallahi,
Don Allah kibar wanan haukan Aisha ki natsu inji hindatu yanzu ki saurari maganan karshe da zaman maki,
Idan yadawo tunda ya nemo mii muzo gareki ki kwantar da hankalinki ki fahinci ina ya dosa ta yadda zaki mayar da komai da yan uwan shi keyi a ba,tare da keba,ki nuna masu ke din kin kai komai yaddawo a hannun ki ki wanke kanki,
Nan ta fada min duk yadda zanyi har suka tafi bai dawo gidan ba sai dare yadawo,
Lokacin muna zaune falo da yarana ina cikin kwaliyan material pink color da,golding,
Yarana,munci kwalliya dasu sai wasan su sukeyi a sanyaye yashigo gidan don yasan ba sannu zai samu ba gare ni dan dama a gurin madina in tana falon
Amma ga mamakin shi sai yaji ina mashi sannu da zuwa, hakan yadan bashi mamaki maimakon ya shige yadda ya saba sai yadawo falon ya zauna yana wasa da yaran shi,
A sanyaye cikin murya mara sanyi nake cewa abinci fa yaya yace cikin murmushi in Rangida tabani zanci mana tunda kun barnimaraya dake da yaran ki
Ban bashi amsa ba na shige kitchen na hado mashi, abinci nakawo mashi yana ci ina zaune daga gefen shi yana satar kallona a hankali,
Sai da naga yai rabin abincin nake cewa yaushe ne auren naka za,ayi,
Dagatar da cibin da zaikai baki yayi yana cewa kin sauko ke nan daga fushin naki, dan gutun murmushi nayi iya fuska kawai,
Yace koke fa Humaira yaushe rabon da nagan ki haka duk kin wani hargitsamu ga baki daya kin hanamu shakat a gida nida yara baki dayan,
Yau da kikasake koke bakiga gidan naki ya dawo normal ba kamar baya humaira ban son ki tayar da hankaliki akan wanan zancen kamar yadda kikayi,
Kin barni a maraya banda abikin shawara dole naje gurin su zarah na nemi shawaran su,
Saida na hade yawun takaici tukun nakakaro murmushi ina cewa ai yanzu komai ya wuce sai muyi yadda kace,
Sannu a hankali nake tambayan shi yana fada min abubuwan da akeciki ni kuma ina kafa nawa dokar ina rushe nasu,
Washegari da safe zaifita inajin zarah ta bugo mai waya sai ya bata ansa dacewa tazo ta samu humaira asan yadda za,ayi,
Komay tace mashi sai naji kawai yai murmushi yace nadai ce kuzo gurin ta bashike nan ba,zata baku komai da za,a bukata,
Ya juyo inda nake zaune yake cewa Zarah ce zasu zo su samay ki sai ku tsara yadda za,ayi,
Nai mashi adawo lafiya har ya kai kofa sai kuma ya dawo inda nake zaune ya dawo ya tsuguna daidai tsawona yana fadin a dai kara hakkuri please,
Ban son naganki a damuwa ko kadan idan har kinga nayi ba daidai ba ki nuna min kuskure na nace naji kawai yamike yafita,

****** ********* ******
Sun shigo gidan suna wani hura hanci sai nafito ina ce masu, a sannun ku da zuwa ashe kuna,tafe,
Sai wani bina da kallo sukeyi suna yatsunar fuskan su cikin yan harare harare,
Saida suka zauna muka gaisa sama sama dasu zarah tace gamu mun zo ance dole sai mun ganki tunda kece shi,
Murmushi nayi nace zarah aiko kin ji dadi tunda,kaunar ki ta zama yadda kike so,
Wani harara ta bakado min na wasa tace aini wallahi yanzun kifi karfina Aisha nadan rugomo tanace sai anty na,
Nan muka wasance naciki na ciki ga kowan dole ba don sun soba muka tsara yadda za,ai komai, a tare,
Sai yamma nya,dawo sai dai

Download complete TXT · Novel page