Showing 234001 words to 237000 words out of 299981 words

Chapter 79 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17622

tayi komai,
Sai Umma ke cewa wai bata san ko may mu ke kullawa ba adakin yanzu Asmau ta,wani nace min,
Asmau kance mata Umma kin mata cewa dama Aisha kawata ce muna yara kece dai kika rabamu da ta auri yayana wai kada ta raina mu,
Sai nace kin taba ganin mata ta raina mijin ta aiku mazana ne dolene na baku girman ku,
Tabe baki Umma tayi tace koma may kuke kullawa ai in yai wari muji don mu yan kallo ne,
Sai dai muyi dariya kawai muce Umma alheri muke kullawa mu,
Shigan dare yai muna musalin sha,dayan dare suka,shigo duk a lokacin ina zaune ina jiran shi don nasan da zuwan shi banyi barci ba yadda na saba,
Duk da dare ne ina cikin kwalliya na da makeup a fuskana sai kamshin dake tashi a jikina da dakina mimi tana kwance saman shifidar ta dana tanadar mata a gefe,
Ina jin muryan shi ya shigo namike tare da dan gyarawa na fito waje har lokacin su Umma basuyi barci suna zaune suna kallon hausa film da yaran ta,
Ban damu da suna gurin ba dana,fito nake ce mai sannu da zuwa yaya tare da dan rugumo shi kadan a jikina na karbi yar jakar dake hannun shi ,
Kallon juna sukayi kawai kowa da abinda yagani a idin shi Hamza ko sai faman murmushi yake yana cewa Ran gida baki barci ba ashe ke ma,
Nace nasan kana hanya ina zanyi barci ban ga isowar ka ba lafiya,
Ya tsaya gurinsu sun dan gaisa ya mike don zuwa daki Umma ta bishi da kallo tana cewa har zaka,shige ke nan yace wallahi Umma duk a gajiye nake tun sha daya nake hanya fa,
Allah ya bamu alheri tace don nasan ka,shige kenan bazaka fito ba kuma yace gaskiya kan,
Yana shigowa daki sai kokarin cire a gogon dake hannun shi yakeyi ta bayan shi na zagayo na dan rugumay shi a hankali tare da sauke ajiyan zuciya a hankali,
Nace sannu da zuwa yaya ka tafi kabar mu da kewan ka sai tunanen ka kawai muke yi,
Murmushi yayi tare da dan zagoyo ni muna fuskantar juna yake cewa nima ai kun barni can da kewan ku don ban ko gama abinda nakeyi ba nadawo donku,
A hankali nace mai ruwan wanka yana a bayi don yanzu da ya gyara muna daki har da bayi akai muna a cikin dakin ,
Mun huta da wanka ana kirga cewa munyi wanka kazs munyi da,asuba kuma muna yi da rana wani lokaci har da rana inji Umma wai na faye barnan ruwa da yawa,
Wani lokaci kuma takance wai mace ke nan kullun bata da,aiki sai wanka buta kamar agwagwa,
Yana fitowa nace mai abinci fa yace yana goge ruwa akan shi,
Wallahi Humaira ban iya cin abinci yanzu duk a gajiye nake abinci zai min nauyi mun kuma ci a binci a Jaba,
Nace cikin marairai cewa aiba mai nauyi na girka ma ba don nasan baka son cin abu mai nauyi da,dare sosai,
Ba laifi don ya dan sha perppe soup din kifin da nai mai da yawa ina daga gefen shi zaune ina dan zuba mai ruwa tare da dan jan shi da hira a hankali,
Ya, gama na zuba mai ruwa da sabulu ya,wanke hannun shi na kwashi kayan na nufi dashi dakin Umma ko akwai wanda zaici kada ya lalace idan ya kwana,
Yana waya ko da na iso dana dan saurara sai naji da wani abokin kasuwan ci shine yake fada mai cewa ya iso lafiya yake tambayan ko an kawo motan maganin shukan da ya bayar a shigo dashi zuwa wani kauye,
Kara dan kimtsawa nayi tare da haye saman gadon mu bayan naiwa mimi addu,a,
Har ya karaso bakin gadon da waya a hannun shi yana yi inda ya dan zauna a bakin gado,
Juyowa nayi don jin shi a kusa dani inda cikin dakiyar zuciya na,dan kai hannu a saman bayan shi nadan fara shafawa a hankali,
Ajiyan zuciya naji ya sauke tare da,sallama da mutumin da yake wayan dashi yana cewa sai dai da safe indan mun hadu sai mu karasa maganan,
Yana aje wayan yadan juyo gareni tare da sauke ajiyan zuciya yana cewa Hummaira duk kin canz min fa gaba daya,
Kafin nai magana kira ya,shigo a,wayan shi kallon wayan yayi yaga mai kiran shi sai naji yadan ja tsaki ya dauki wayan ya kashe gaba daya yana cewa ban son yawan damuwa please,
Nan na fara mashi sabon sallon da nazo mashi dashi a ranan duk ya susuce min ya koma min kamar wani karamin yaro sai yadda na yi dashi a ranan,
Bayan komai ya dan lafa a tsakanin mu na manne a jikin shi ina cewa yyallabai kafa kwaso gajiya ne nagani,
Ya kamata ka huta haka don ka samu dan natsuwa kafin safe don nasan ko goben ma ba hutawa zakayi ba,
Yace ban tsanmani gobe zan iya zuwa ko ina don ina son hutawa sai a gida nima cikin iyalina koda sau daya ne a,sati,
Washe gari tun da,safe duk da akwai gajiya a jikina ban kwanta ba sai da nafito nai abin karyawa kamar yadda na saba yi a kullun,
Nagama nai wanka na tsala kwalliya na cikin wasu English dress da aka sayo min a,sokoto ta gurin hindatu,
Ina fesa turare naga yadan juya daga gurin da yake kwance hakan yasani gane cewa ya farka ke nan karasawa nayi bakin gadon ina cewa yayana,
A tashi aci abinci ko kada yunwa ya illanta min kai ina gani,
Jawoni yayi zuwa jikin shi ni kuma na biye mai tare da haye ruwan cikin shi ina cewa ka tashi kai wanka ka,karya kaje ku gaisa da mutanen gida,
Yace ai ban gama gaisawa da iyalina ba ma kafin naje gaida na cikin gida,
Nan wani sabon wasa ya fara a,tsakanin mu sai kace kanan yara mun dauki lokaci a hankan cikin wani yanayi na farantawa junan mu rai san,nan yadan sarara min,
Ina daga gefen shi a kwance yake cewa bayan ya,sauke numfashi da karfi yace wai Humaira may ke faruwa ne haka please,
Kaman ya yaya ?
Yace gaba daya naga kin canza min a cikin lokaci guda halin da ban san ki dashi ba sune nake gani a gare ki,
Nace ba abin da ke faruwa canjin yanayi ne kawai yanzu kaunan ka ta girama ta kai lokacin ta shine kawai,
Yace eyyeh kalai naga alaman haka ashe sai na shirya ke nan don yanzu yarinya ta girma nace lalai kam don kana da,aiki ja a gaban ka,
Sauka nayi daga gadon na shiga ban daki ban futo ba,sai da na tsabtace kaina nafito ina cewa ga ruwan wanka can na hada ma kaima,
Sai na samu yana waya yana fadin a lokacin da nake hutawa da iyalina ya dace a bugo min waya,
Ko sau nawa za a kirani inda i a tare da iyalina bazan dauki waya ba gaskiya don haka a bari kawai,
Shan jinin jikina nayi don na fahinci da mace ce yake wayan don haka na wuce gurin mirror ina gyara jikina,
Yana kashe wayan ya juyo inda nake a zaune yana cewa azo a taimaka min na tashi tunda duk kin kashe min jiki,
Kafin nai magana dama duk a kule nake sai muryan Mama naji a falo tana fadin Aisha yar ki fa nono take so kila don ta ki yarda tun dazu kuma taki yin barci,
Don haka na mike zuwa falon don na karbi yarinyar hannun mama kafin na koma ciki har ya,shige bayin don yin wanka,
Sai da ya karya yafita zuwa gurin su Umma don su gaisa dasu tun bai zauna ba Umma ke cewa halan yau baka fitane har kakai war haka baka fito ba,
Cikin dan yamutse fuska tana kaiwa zaune yake cewa wallahi yau banjin cewa zan fita don hutu nake bukatar yi a gida,
Nan ya fara gaishe ta kafin ta furta wani zancen suka shiga hiran yadda al,amari ke tafiya ga,kasuwan cin shi,
Ya dan dauki lokaci a gurin ta din har ya bada sakon asayo mai kashin rago da dan naman ragon ai pepper soup din shi da rana a gida,
Nai aikina na gaji na koma daki na samay shi zaune a falo yana kallo ga kuma waya a hannun shi yanayi cikin jin dadin yanayi,
Nan na zauna gap dashi muna hira nai dan filo da kafadan shi ina kallon TV dake aiki,
Sai wasa yake da hannun mimi dake shan nono a jikina tana washe baki irin na yara ,
A kai, mashi sallama yafita bai shigo ba yana waje da,wani abokin tafiyan shi suna magana,
Koda ya shigo nake gabatar mai da abinci don baici ba har zuwa lokacin yake ce min nazo mu zauna muci tare nace mashi dadai yaci don ni nashs furan gora gurin Jibrin,
Yace ke da ke shayarwa mai fura zai maki Humaira kawai ki zo ki zauna munci a binci kafin Ummana ta tsotse ki,
Nace cikin murmushi wallahi ko bai mata wuya indai mimi ce don tsotso gare ta har na,sayarwa,
Munci abincin sosai don ni kaina naji dadin cin da nayi don cikina ya dauka sosai,
Umma ranan sai mamaki takeyi don fmganin sauyin danta gashi a cikin gida amma bai fito gurin ta ba kamar yadda ya saba yi in yana gida yana dakin ta suna hira har da,dariyan ta,
Niko a lokacin ina daki zaune ina hadiyan zuciya yadda Umma ke bukatan gani na,
Amma yanzu ni da kaina sai nake jina wata wasai dani ban tare da wani kunci a raina don yana tare dasu,

A haka nake ta takona ina cusa kaina agurin mijina kullun kurciyana yana da da baiyyana a fili, kwaliya na nakeyi ina gyara ko ina na jiki na don kada aga damana,
A daidai wanan lokacin ni kaina nasan ban taba samun dama ko freedom din na mallakan mijina ba tun auren mu sai yanzu,
Hamza wanda yai tafiya zuwa sokoto don karbo takardun shi da yai karatu amfanin shi sun taso gare shi,
Kwaliyan dogon riga nayi tare da dan daura gyalen kayan a kaina na daure gashi na dasu, idan har na tsaya cesa nayi kyau ma bata lokaci ne,
Kallona Hamza keyi yana karawa watakila jin yake kamar ya rungumay ni a gaban kowa, ta lashe tun kan lokacin yin hakan yayi muna,
Takardun na karba na,shiga daki dasu har na kai kofa cinkin dan ga mutse fuska yake cewa tsaya na dauki wani file a ciki ya tako zuwa dakin mu yabar su Umma a gurin,
Ji nayi ya matsoni a jikin shi abinda yasani murmushi ke nan ya kalleni yana cewa Humaira gaskiya wanan shigar taki a cikin gidan nan ya fara sani wani yanayin ki shi kin san fa bani kadai bane namiji a gidan nan,
Yana fadi yana dan kara matse ni a jikin shi tare da dan sun sunan wuyana a hankali,
Na daga ina cewa haba dai yaya su ina ruwansu dani tunda ba mallakin su nake ba,
Kara jawoni a jikin shi yayi yana matsewa da karfi yana cewa,
Kina kuwa kallon yadda kika koma kuwa madubi murmushi nayi nace wanda dai nayi don shi in ya kalla zai fada min, ai
Kuma in dai kai ka gamsu dashi ai shike nan don badon wani nayi ba don ka kawai nayi,
Na gamsu ma ai shi yasa har yau naji kishin yan uwana ya kamani gashi yanzu kurciyar ki sai dada fitowa yake a fili kin koma kamar wata yar sha bakwai fa,
Nayi dariya tare da kokarin cire jikina daga rikon da yai min don na,aje takardun dake hannun na ina cewa,
Kai yaya yanzu fa ashirin da biyu nake cif, yace Uhmmm humaira wallahi kamar yar sha bakawai yanayin ki yake nunawa a fili,
Nace yayin dana duka ai kaima yaya yanzu duk kurciyar ka ya fito ka koma kaman wani mazaunin abuja can don dai kawai ansan cewa a nan kake da zama da babu wanda zai ce ba,a birnin taraiya kake zaune ba, ga wani mutunci da kwar jini da kakeyi wa kowa a fuska,
Shiyasa yan mata suke ta faman kawo maka harin don suma,suzo su kwashi nasu garan,sai dai kuma kwalelensu wallahi,
Hamza ya kyalkyace da dariya tare da kamoni yana cewa ai kin tare kofa yanzu kan babu guri din duk wace ta kawo kanta gulma tazo,
A kusan tare muka fito daga dakin muna dariya Umma tana ganin fitowan mu cikin raha ta,wani bata ran ta a lokaci guda kamar an mata mutuwa,
Ni dai nasan ganin da Umma tai muna muna,dariya ne yasata bata ran ta,
Gashi yabzh idan yana gida baida lokacin zama a gurin ta kamar yadda yakeyi da can baya,
Ganin yanayin fusksn ta a lokaci guda yasa shi dan zuwa gurin ta yana cewa Umma lafiya dai ko cikin son jin may yasamay ta
Ta dan girgiza kanta tana cewa ba abin da ya samah kawai dai daurowa ne,
Umma idan da,wani abune da ke sakaki damuea ki fada min kawai a san abin yi,
Cikin bata rai Umma tavmce niko keda abinda ke damuna Hamza
Yanzun ace kana da halinks kana da budi amma zaka zauna haka da mata guda kamar laya sai yadda tayi damu a cikin gida gaba dayan mu ni daku,
Kasake nayi ina,wa Umma kallon mamaki tare da sauraren zancen ta tana cewa ni dai a rayuwa nafi bukatar na gan ka da mata biyu a gidan nan don kara samun kwanciyar hankalin ka, da natsuwa,
A cikin zuciya ta nake cewa sai dai kuwa ki mutu mama don Hamza mijin humairane kawai,
Umma ai komai dan lokaci nd idan anyi hakkuri lokacin hakan yana tafe I,
Ka sake nayi ina sauraren su shi da mahaifiyar shi duk jikina,sai ya mutu saboda bacin ran da nake ji a lokacin,
Kalaman da Hamza ya mayarwa Umma su wajen bata amsa sun tsaya min a rai sosai
Don a,wasu lokuta yakan bata amsa dacewa mama har kin manta da,abinda Sadiya tai maki a gidan nan,




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON YIN HAKA CIN AMANA NE,,,,,


Ginan gidan Hamza keyi nagani na fada a cikin garin Jega, inda nan surutun jama,an gari ya fara na irin yadda ake zargin duk wani sabon matashi mai kudi,
Har dan yan kan kai wasu sunce ma Hamza din duk sun san cewa ya na sana,a neman kudi irin ta zamani kala kala, cikin gari da kewan yan garin har kasan kurmi da kasashen ketare mafi kusa, yana business yanzu duk da karancin shekarun shi,
Yan kasu yan uwan shi suka shiga bata mashi suna suna cewa wai karamin yaro da bai gaji arziki ba a ina ya samu kudi irin haka masu yawa,
Sai dai ance ba duk aka taru aka zama daya a duniya don mafi yawan mutane sun san irin sana,ar shi yana saurin kawo kudi a duniya in har kana da jari a hannun ka,

Ni a bangare na na fitar da zancen wata Biba can don naga basu waya da ita hakan yasa nasan cewa basu tare yanzu duk a kwai yan matan dake kawo mashi hari da zawarori agari har ma da,wani gari,
Hankalina yanzu a kwance yake ga,yarana sai girma,suke abin su kuma Uban su da yan uwanshi su na marukar son yaran,
Umma ce kawai nake da matsala da ita wanan kuma nasan rashin gamon jini ne tsakani da ita don banga abinda nake mata ba wanda tai hatting dina haka da yawa,
Don iyanzu nasan duk abinda zan mata bani fari a gurin ta sai taga laifi na,
Don haka ni ban damu da irin kiyayyan da take nuna min ba kan zamana da danta a gidan,
Don nasan cewa nakafa sayena a cikin zuciyar shi da gidan ta don duk diyan ta na saye zuciyar su gurin ktautatawan rayuwa,
Da taimakon Allah da nawa gashi yanzu har an saka ranan auren Asmau da saurayin ta Abdul,
Sai faman shirye shiryen buki mukeyi a gidan inda duk wani shawaran ta bai wuce ni da yar uwarta zarah,
Mama hafsi kuma har gobe tana matukar nuna min kaina don ko itace ta haife ni ko Hamza abin ya tsaya a nan,
Irin yadda na dage a gurin auren Asmau akan dan uwanta yai mata duk abinda ya dace uba yaiwa yarshi idan zatayi aure yakara sa man farin jini a gidan don ba wani ya fada min banice da kaina naji suna zancen, a daki basu ma san zan ji su ba,
Umma take cewa wai ina dafa kifi daruwan shi su basu gane ba szi Zarah take cewa haba Umma bafa wai kanta takewa amfani da abinda take karba Asmau ce fa ake wa sayyan nan,
In ba don ita ba kuna ganin cewa yaya zai tsaya ya kashe wanan kudin haka wa Asmau ne kin san halin shi fa gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login