Showing 240001 words to 243000 words out of 299981 words

Chapter 81 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17680

tunda ke bai rage ki da komai ba na rayuwa,
Ba dai komai akewa kishi ba sai jijiyar namiji ko tau ai ajikin shi yake ba,a jikin ki ba shi ya sani da bakin auren don shi zai fadi ai ance jiki magayi,
Halin mutum mai kosar dashi, shi da,ya jajibo shi ne zai gasu kina zaune zaki ji shi da ita in har kinyi hakkuri,
Ko murai kada ki wahalan tayar da hankalin ki a,banza don ba bari zaiyi ba idan yai niyya,
Ke da ki kula da kanki da tarbiyan diyan ki, sa mashi ido kawai don ko shiru magana ne Aisha,
A sanyayye nace naji Anty nagode insha Allahu yadda kikace hakan zan yi don baki tabani shawaran da bai min dadi ba a rayuna,
Munyi sallama da ita tana ta kwantar min da hankali ina ce mata babu komai insha Allahu,

****** ********* ******
Kamar ban san komai ba haka na daure na dake da zancen a cikin zuciya na sai dan lalaba kaina nakeyi kada na kasa,
Ya gama ginan gidan sbi komai ya,saka acikin gidan sai kace wani palace ,
Sai da wata matsala da,takunno kai a kan zancen komawa gidan shine,
Umma tace sai ta koma tare da mu amma kuma shi Hamza din ya ce gaskiya ba zai so takoma can ba abar masu gida ba kowa sai su Ibrahim kawai ta daiyi hakkuri ta zauna dasu idan sunyi aure sai ta,dawo gurin shi din,
Da kyat aka samu su liman dasu Baba suka shawo kanta harta yarda amma da sharadin idan taso zata dinga zuwa ta kwana biyu a gurin mú ta dawo, nama dai badon yaso ba yarda,da hakan,
Don haka ranan laraba da zamu tare a,gidan tare da ita muka koma sai da tai mu Sati biyu tadawo gida badon ranta yaso ba,
Ko shi Ibrahim ne yazo ya,sata gaba sai da ya dauke ta suka tafi tare da shi,
Aka barni ni da yarana sai a gidan sai mai gadi don a lokacin shi yana gurin tafiya da kyat Umma tabar mu Sa,ade ta taya ni kwana kafin ya dawo tunda,ban saba da gidan ba,
Ranan da ya dawo da dare ya,mayar da,Sa,ade gida akabarmu daga mu sai yan yaran mu biyu a gidan,
Bayan ya,dawo daga gurin kai Sa,ade ne ina zaune a falon yaran sun gaji da,wasa,sunyi barci a gefe na ya,shigo gidan cikin shigar kanan kaya,
Na kalle shi cikin girmamawa nai mashi sannu da zuwa ledan da ya,shigo dashi nai kokarin tashi na karba sai dai akwai mimi a jikina don haka yske cewa zauna abinki na hutar dake, kada ki tayar min da uwa kin san yazu tana,fara rigiman nan nata ta hana mu shakat,
Shi kan shi ya shiga har kitchen ya dauko plate ya ciro kaza guda daga cikin ledan yazo har gabana inda nake zaune ya zauna a kasa gap da kafafuna na yake ce min bisimillah,
Naso na,dawo yaran nan basuyi barci ba don su samu suma suci shi da zafin shi amma sai wani ya tsayar dani can,
A raina nace wani ko wata kai dai kasani in kaya ne kaji dashi can,
Daga inda nake zaune yake dan miko min nama ina ci muna hira, nan yake fada min cewa yana son bana su sauke farali da Umma insha Allahu,
Nai matukar farin ciki dajin zancen shi inda yake ce ni kuma badi in Allah ya,kaimu sai na tafi na sauke, nima ban lokacin da na kaiwa kanshi dake daidai cinyata runguma,ba ina matukar farin ciki da jin zancen,
Yace min sai dai ina son kija bakinki kiyi shiru kada ki fadawa wa ko sai in har tafiyan ya,tabbata kawai za,aji dan dama ina da pasphot din Umma dashi nake son nai mata amfani na tafiyan,
Zaman mu a,sabon gida zan iya cewa wani irin zama ne da muks dade muna mafalkin shi a,ran mu don so ne da kauna tsan tsan ta muke shimfidawa a gidan,
Wanan karon nai yaye babu ciki a tare dani don haka ban samu wani tsegumi ba,a gurin Umma don tace ina son na cika maigida da "ya"ya mata



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU,IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE YAR UWA,,,



HAMZA ne zaune a falo yana rike da waya a hannun shi magana yake akan wasu kayan da za,a shigo mashi da,su daga kwatano,
Nafito daga daki acikin shigar dagon riga ta matan Niger style din rigar yai matukar kabar jikina, tunda na shigo falon gaba daya ya mayar da hankalin shi a kaina,
Ya zuba min idanuwan shi sai kace mara gaskiya ya motsa bakin shi don yakirani sai kuma ga waya a kunnen shi da hannun yai min alamar danazo inda yake,
Kitchen zan shiga sai na juya zuwa gurin shi alama yai min da na zauna a gefen shi,
Ina zama ya dauki hannun shi guda ya rike min hannuwana yana dan murwa a hankali yana wayan shi ,
Shiru nayi daga gefen shi ina sauraren wayan da yake yi da abokin sana,ar shi,
Sai da ya gama wayan yadan sauke numfashi shi ya juyo gareni yana cewa Rangida, ashe aikin nan bai maki yawa ba ke kadai ga gyaran gida ga, luran yara ga kuma girki duk ke kadai,
Nace sai kace ba yar Umma nake ba wace tai aikin mutum kusan bakwai a gida daya har tsawon wasu shekaru sai wanan na mu kadai ne zai min yawa,
Ya ce Nop ciki daga hannun shi da juya kan shi ina bukatar ki huta yanzu tun da Allah ya hutar damu,
Don haka ki samo wata da zata tai maka maki da wanan aiki ko tsohowa ko kuma yarinya,
Murmushi nayi tare da dan kwantan da kaina a kafadar shi nace kaidaine kake ganin shi aiki amma ni aguri na wanan ai ba aiki bane,
Yace na sani amma ina son ki samo wacce zata taimaka maki da ko da gyaran gida ne ke sai a barki da dawainiya na dana yara,
Nace harda girkin ma ni ce zanyi abina da kaina don ban son wata tai maka girki bani ba,
Yace cikin lushe idanuwan shi tare da dan sunsunan wuyana nima nafi da son hakan ai amma so nake ki huta ki kula min da wanan jikin naki da kullun yake koma mawa kamar ta under age,
Murmushi nayi ina under age inda Jidda da Mimi suka fito yace kece ke ganin haka ni kullun kamar bakece kika haife suba nake gani,
Mikewa naso yi don zuwa duba girki da na dora a gas sai yariko min hannu yana cewa ina kuma zaki muna magana nace na,dira abinci a wuta don ka,samu kaci kafin kafita don nasan in kafita sai dare,
Ya lumshe idanuwan shi yana cewa kuma gaskiya kika fada don ko nafita din ba wani abu nake ci ba sai fura da dan snacks,
A hankali nayi wata yar sanyanyar ajiyar zuciya nace nasan haka wallahi don nakan ga yadda kake cin abinci idan kadawo shiyasa ma yanzu nake kokarin tashi da wuri na girka maka,,
Bayan ya kammala cin abincin shi ne ya mike tare da dan shafan gaban rigan shi yana,fadin kin dai kusa sani katon tubi Humaira wanan irin abinci da kike tula min a gaba,
Ai nan da yan kwanaki nakara kiba ba kadan ba don dadin dakike bani,
Nace cikin murmushi kiba,ai ga,dan Africa kamar ruwa,ne don sai guda,gudane basu kiba idan sun kai age din yin kiba yanzu aikai da,sauran ka sosai,
Yace lokacin da mukai aure ana cewa dani dake duk mun yi kanana sosai yanzu gashi har mun kai ga,diya,biyu cikin ma bamu haihu ba da wuri, murmushi kawai nai mashi cikin dan jin kunya
Mikewa nayi na bishi har zuwa kofa ina mashi adawo lafiya,

****** ********** ******
Kamar yadda Umma tai alkawarin zuwa ta kwana biyu a gurin mu hakan ne kuwa don wataranan laraba da dare muna zaune a falo muna kallo sai mu kaji ana nocking din kofa,
Muryan Umma ce tana fadin ko babu kowa ne a gidan ana,sallama ba,wanda ya karba muna,
Jibrin ne yashigo ya kawo ta ya shigo yana,min raha irin yadda muka,saba dashi,
Sai Sannu da zuwa nakewa Umma na karbi kayan ta hannun shi ina ta,farin ciki da,ganin ta,
Na mata iso da firin zama ta zauna tana bin gidan da kallon yadda yasha gyara ga kamshi ta ko ina a lokacin Hamza yana dagi don bai dade da dawo ba,
Na shiga na,sheda mashi zuwan ta, ya juyo yana cewa cikin bata fuska Umma kuma da daren nan haka waya,kawo ta, nace mai Jibrin ne,
A tare muka fito dashi lokaci guda yana murmushi yake cewa Umma da daren nan kika taso ,
Tace tau tun rana nake jiran yaran nan sukawoni suna min yawo da hankali shiyasa da dan neman nan ya,shigo cin abinci yanzu na datse shi,
Ai ban ma san kana gari ba da kai zance kazo ka dauko ni, zama yayi suka fara hira da Jibrin yana mashi zancen komawa makarantan da yai mashi,
Ina can ina kokarin kawo wa Umma abinci da Jibrin sai da na aje abincin ta bude taga,may na,dafa,
Tuwon alkama nayi da miyar kubewa danye sai ta,dan bata fuska tace ki aje min kila anjima naci Jibrin yace anjima kuma umma keda yanzu kikagama cin abinci,
Nace wa Jibri kai yaya na zubo maka ne zakaci yace a koshe nake naci tuwon mama na koshi wallahi,
Abinci kike dafawa haka da yawa ke kadai a gida Aisha ?
Hamza yace ni aikin ne ma yai mata yawa ita daya nake gani shi yasa nace ta samo yar aiki ta taya,
Hummm,ummm, inji Umma yar aiki kuma kodai kayi aure ga gida da girma ace wai mace daya ce a cikin shi,
Murmushi Hamza din yai mata yace aure ba yanzu Umma don ina da,abubuwa a gaba da zan yi,
Ban tsaya jin su ba na dauki kayan abinci na,zan mayar kitchen take cewa nai maganan abinda bata so ai kaga zata gudu,
Ko bakiso sai wata tashigo gidan nan don bazaki zauna ke kadai ba ,
To ai Umma ke kadai kika zauna a gidan Baba don may wai kike son aiwa Aisha kishiyace tana zaman lafiya da mijin ta,
Anshi naka taiwa Jibrin dakuwa da hannun ta tace ai da na zauna ni daya ban samu wuri irin haka ba,
Kai Umma fadi gaskiya don dai kowa yasan da,baban mu na,da rai yana da,wadatan shi sai dai aga abu a gurin ki,
To kai sai ka zauna da mace daya in ka tashi auren amma,shikan sai ya kara wata gidan nan takara daga kai tana bin gidan da kallo,
Kaina ya daure da,wanan irin kiyayyan na Umma a kaina ni dai abin wani lokaci yana damuna sosai don ban san,
Da dare muna daki dashi ina zaune a bakin mirror ina gyara jikina yake cewa cikin dan jan tsuki,.
Wai ni ban san wanan abin na Umma da bazata iya zama da yar uwan ta da yara a gida
Nidai ban tanka mashi ba sai yake kwata kwata na fahinci Umma bata son zaman lafiya na wallahi,
Don bata fahinci irin yadda rayuwan yanzu yake ba da take wani matsawa wai nai aure aure ba sai mutum ya,shirya yin shi ba zai yi, ya,sake jan wani tsakin yana juyawa,
Yace ita gashi taci nata rayuwan ba wanda ya damay su da zaman ta ita daya ,
Jin nayi shiru yasa shi juyowa inda nake yana cewa yaya ina magana kin kyaleni kin san ban son ina magana ai min shiru ko
Niyi dan murmushi tare da,mikewa daga inda nake ina cewa kayi hakkuri ka bar wanan magana yaya,
Don kasan ni ban da baki magana akan kan wanan zancen tun da ni ake son kawai kishiya,
Saboda zamana a gidan nan ni kadai ya kai wa Umma ko ina shine yasa take son ka kawo wata wace zamu zauna tare muci arziki da ita don ni yai min yawa ni kadai,
Yai murmushi don ya fahinci raina yana a bace akan maganan Umma don hakan ne nai shiru,
Yace naji amma ai ko na kara auren in da Umma ce bazaman lafiya zasuyi da wata din ba,
Kamar nace hakane mana don Umma kishi take da matan ka,,
Na hawo gadon tare da dan fara matsa mashi kafan shi a hankali har na,soma yi mashi abubuwan da na san sun fiye mishi wanan magana muhinmanci a yanzu,
Tun sanda Mama ta dawo gidan namu da sunan yi muna kwana biyu ban samu wani cikakken natsuwa ba kuma,
Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun min karanci saboda a kullun Umma zancen ta shine ita dai ni gida yai muna girma ni da "ya"yana burin ta bai wuce taga raina ya baci ko an dagula min lissafi nayi bakin rai,
Gashi duk yadda zata sa yaya ya bata rai a kaina sai Umma ta kirkiro shi,
Gashi idan hiranta ya tashi takan ta yaba irin rayuwan da tayi da nata mijin da irin yadda tasha gaban yan uwan shi da kowa da yake tare dashi,
Shekarun ta yana karuwa mugun halinta yana kara baiyyana a fili,
Shi kuma Hamza sai Umma bata kusa yakan yi korafi akan halinta na takura min yakan yi kokarin kwantar min da hankali akan halin ta, yace wai girma ne ke sata yin hakan,
Gashi wanan zuwan taki tafiya gida tace ita bama san ranan tafiyan ta ba,
In anyi maganan tabar yara agida sai tace aida uwar su ta barsu har Sa,adatu sai da ta dawo gidan da zama,
Wata rana nai muna sakwara da miyar taushe da naman rago sai da taci takoshi tana santi,
Zuwa yamma sai cikin ta ya rude tafara haraswa da kewayawa da dan ta yazo yana tambayan abinda taci sai cewa tayi nice naja matashi nasan bata son doya amma nai muna sakwara taci shi ya jawo mata rudewan ciki,
Wata kila tafadi hakane don yai cikina da masifa sai yake cewa to ke umma da baki so ai sai kiwa Humaira magana ta sake maki wani abinci,
Tace wane ni nasata canza min abinci tace nazo gidan ta na saka tagaba da fitina kadai san halin yaran yanzu,
Juyawa yayi inda nake zaune yana ce min may yasa baki girka mata nata daban ba Humaira yanzu gashi kin ja mata matsala irin haka,
Raina yai matukar baci ya gama fadan shi ya fita ita kuma ta,shige daki da yar ta ina jin su suna dariya,
Daki na,shiga ranan sai da nai kuka mai isata ina hadiyan zuciya ni kadai sai yarana dake kallon yadda nake kuka,
Ibrahim ne yashigo gidan yaga bani falo yai ta kwada min kira sai da na fito sama sama nake gaida shi kallo daya yai min yafahinci nayi kuka
Yace yau kuwa lafiya Aisha cikin muryan da ya dashe min don kuka na furta mai babu komai yaya Ibrahim,
Yace Umma ko nasan dama hakkuri kikeyi da ita har ma,shi mijjn naki nasan baida yadda zaiyi ne amma insha Allahu yau takai karshe don gida zasu kwana wallahi,
Fita yayi don ban ma tsan manin ya shiga gurin ta ba inda take,
Dan wani lokaci sai gashi ya dawo ya shiga gurin ta yana cewa yazo daukan tane su koma gida don mama bata da lafiya gida ya koma shiru,
Kin zuwa tayi sai da Ibrahim din yace mata idan bata bishi sun koma gida ba zai fadawa Baba lawal tasan zafin Baba lawal don haka bashiri suka fito ya kwashe su sai gida,
Sai dare ya dawo gidan yake tambayan ina Umma nace sun tafi yaya Ibrahim ya, zo ya dauke ta, yace sai Ibrahim don shi kadai zai iya sata gaba ta koma gida,
Wanan dalilai danake lisafawa maki akan umma sai suka sa aurena ya zamo auren da a daidai lokacin da mutane ke ganin ina jin dadi da farin cikin shi sabod nasarorin da zahiri ya nuna ina ciki,
Nikuma da nake a cikin matsalolin nasan yanzu nake zaman aure da fuskantar kalubalin rayuwan aure daga uwar mijina,
Sai duk da halin da nake ciki ban taba yarda wani ya fahinci ina cikin wani halin rayuwan aure ba,
Iyayyena ne idan na,fada masu hakkuri su kan bani suce dama duk wata mace mai aure tana tare da kalubalin aure don haka inyi ta hakkuri kawai don rashi hakuri ga rayuwan aure a yanzu shike kawo yawan mutuwan aure,
Dadin abin kawai ina samun sauki a gurin mijina da yan uwan shi,

****** ********* ******
Har lokacin tafiyan su gabas yazo ranan da aka,fada mata tare muka tafi da Hamza don yafads mata zancen tafiyan su din,
Tai murna tayi farin ciki sai kuma daga karshe tai mashi adduan tare da,cewa Allah yasa badi kuma ya kai mata zarah da Asmau,
Yace Umma bakice Humaira ba sai ki kawo zancen Zarah da,Asmau kuma ,
Yanzun dai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login