Showing 243001 words to 246000 words out of 299981 words

Chapter 82 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17651

gane ba zancen yan uwanka kakeyi ba sai na matar ka duk tabi ta shanye ka akowa,
Haba Umma kada fa ki manta da hakkurin da humaira tayi a gidan nan shine fa ake gani kamar ta shaye nine,
Ni dai shiru kawai nayi ina zaune waje da Mama muna hiran mu muna jin zancen su,
Mama tace kada ki damu da zancen ta Aisha ya ci ace yanzu kin saba da halin uwar ku don kishi take da ke haikan,
Nace mama ai babu komai halin Umma na hassada a kaina,ba bakona bane, yanzu,
Mun kai wani lokaci a gidan muka fito zuwa gida sai da ya,tayar da mota yake cewa, kai ni wallahi idan Umma tai wani abin har mamaki take bani,
Na fahinci nine Umma bataso da alheri ba,wani ba taya zatace wai nakai Zarah ko Asmau makka gaki,
Idan ma nai haka ai ita mai min fada ne sosai da tana kaunana da alheri da bata sani hanyan da Allah zai tambaye ni, ba kan cin amana,
Banyi magana ba sai ma kallon titi da na mayar da hankalina a kai tare da dan wasa da hannun yarinya na da nakeyi ina dan mata wasa,

A haka har zancen tafiyan su gabas yataso in da ya sai muna komai da yasan zamu bukata a bayan shi,
Sa,adatu zata dawo gidan mu ta zauna wai sabo da tsaro don Umma tace wai mama bata zama a gida da rana,
Rashin zaman mama da har take fita zuwa kujiba kujiban ta gurin nema kudi don saboda yawan fitinan Umma na da take mata kamar karamar yarinya,
Duk da Hamza ya hana mama yin wanan sana,an amma bata bari ba tafi bukatan ta fita zuwa neman nakan ta gashi kuma abin ya karbe ta sosai,
Dawowan Sa,a datu gidan mu ya kawo muna matsloli da dama a zaman ta gurina,
Don kullun sai tafita wai tana zuwa gurin yan uwan ta yini,
Idan kuma tana gida sai dai ta mike kafa tana kallo ko kwanon da taci abinci bata iya kawarwa sai dai ni mai shi na dauke da kaina,
Sai kuma fita hiran da takegi a kofan gida da dare har wani lokaci mai tsawo nai mata magana amma tai banza dani,
Gashi yarana duk da kanana ne basu da shakat a gurin ta dan abu kadan ta kai masu duka ko zagi,
Wanan bai damay ni ba don nasan diyan tane tana da iko akan su don kaunar mahaifin su ne,
Ranan da tana kallo mimi tazo inda remote yake ta dauka tana daddannawa ta juyo ta kwashe ta da mari sai da yarinyar ta gigice da zafin marin,
Nace haba Sa,a datu may mimi ta sani da zaki mata wanan irin dukan haka yarinya ce ko anjima karawa zatayi,
Tace min ko zaki hana na duke tane zaki gwada min ke ce kika haife ta ko,
Ko don nazo gidan ubansu kike son kiyi min wullakanci dama nima wallahi ban so zuwa wanan zaman ba duk yayane yaja min zuwa nan,
Don dama nasan bason mu kikeyi da dan uwan mu ba kinfi son abarki ke da diyan ki ku mahe gida ku kadai sai abinda ranki yaso,
Nace don nai maki magana akan dukan mimi shine kike kokarin fada min abindake zuciyar ki dani,
Sau nawa kike dukan su ban maki magana ba kona yau naga dukan yai tsanani ne bai dace da karamin yaro ba,
Tace mai da wukar ki a kube Aisha na daina shiga harkan yaran ki har da naki ma na daina,
Nace to dayafi nono fari wallahi
Tun daga ranan ta daina shiga harkan mu ta daina yi min magana ko gaisuwa bamuyi da ita,
Sai nice ma nake kokari kawar da gaba a tsakanin mu nakan dan yi mata magana ta amsa,min a lalace,
Ko shigowa zatayi gidan bata sallama haka ma idan zata fita bata ce min uffan,
Naga zata zubar muna da mutunci a guwa yawan fitan ta da zama a kofan gida har wani lokaci yasani daukan mataki a kan ta,
Nai mata magana akan ta daina,wuce karfe goman dare bata dawo ba,
Sai taso ta zageni don haka na kira Ibrahim nafada mashi irin zaman da mukeyi da ita don ya,tsawata mata,
Bayan yai mata fada ya tafi tafito tana,min maganganu, rashin kunya wai dama dan tallaka bai iya samun guri ba na,samu guri shine har dasu kannen miji nake son na mulka to na tsaya iya mijina da na mallake,
Zarah nakira tazo gidan nafada mata sai bude baki zarah tayi tanacewa kai Aisha ban son kanan maganganu wanan ai sheri kike son yiwa Sa,a datu,
In har tai wani abin da ba daidai ba ki dauki mataki mana da kan ki basai kin fadawa Ibrahim ba, ki kirani mana inzo ki fada min,
Nace mata tau babu laifi suyi hakkuri amma zan dauki matakin da tace da kaina,
Tun lokacin nafahinci akwai wani sauyi a tsakani na dasu ban sani ba ashe umma ta fada masu wai na hana mijina ya kai su makka don ni ban tafi ba,
Ranan da ta fita tun safe ban sani ba,na kira yan uwan ko tana gurin su suka ce batazo ba har dare nakara kiran Zarah da Asmau sukace min bata gurin su,
Tana dawowa nai mata magana sai cewa tayi ke kin fa isheni tana magana kamar zata make ni,
Sai dai in zaki mutu ne ki mutu yar hassada kawai haka kawai ki sakani gaba da bakin lecture kamar kin aike ni,
Kuma duk tsiyar ki ba zan bar gidan ba tun da ba don ki nake a gidan ba don ba gurinki nazo ba,
Kince na daina kula diyanki nace har kema bani kulawa bana,shiga tsabgarki dana yayan
Gida kuma gidan dan uwanane sai yadda naga dama nayi dole kuma ki dafa ki bani naci koba kyaso,
Takarshe zancen ta cikin tsiwa tare dacjan wani irin uban tsaki tace banza kawai,
Na kalle ta nai murmushi kawai bayan ta,shige dakin ta,
Washegari ma nasan ba fasa fitan zatayi ba don haka na kyale ta,ko shiryo tazo ta,wuce mu zaune a falo tafita abinta,
Tana fita nabi bayan ta sai da tafice daga gidan na kalli tsohon bakaben dake muna gadi nace mashi baba cikin girmamawa,
Nace daga yau duk wanda ya, zai shigo gidan nan bayan karfe goma kowa ye kada ka bude mashi kofa idan bani nace ka bude ba ya amsa da to cikin girmamawa,
Sai sha biyu da yan mintina Sa,adatu ta dawo ta tura kofa get a,rufe yake tai kiran maigadi takafan get din wai ya bude mata gida ta shigo yace mata hajiya ta,ce kadana budewa kowa idan goma ta,wuce na dare,
Tai juyin duniya,tsohon ya bude mata amma fir yaki yana,gudun sabawa umurni na yayi laifi,
Waya ta,daga cikin daren nan takira layina naki dauka ran ta ya baci ta rasa yadda zatayi
Dole takira Zarah ta fada mata karya da,gaskiya wai na hana a bude mata gida,
Itama Zarah tai kiran wayana naki dagawa don ai tace na dauki mataki akan sherin da nakewa kaunan ta,
Gashi dare ne kuma bata son kishiyoyin ta ko mijin ta suji zancen don mijin ya taba mata magana akan Sa,ade din,
Dole badon taso ba takira Ibrahim ta fada mai abin dake faruwa agidan mu sai ko gashi a cikin daren nan yazo yasamay ta tsuru tsuru rakube a kofan get,
Kira daya yai min na fito naba maigadi Umurni da ya bude gidan suka shigo tare dashi suna shiga falo yakai mata wawan mari yana tambayan ta inda tafito a wanan lokacin,
Yai mata mugun duka ya kuma ce min nai mashi dai dai don ya tambayi maigadi yafada,mai time din da,ta,dawo,
Yabani hakuri tare da kara yi min nasiha akan nayi hakkuri kullun zai dinga zuwa safe darana har da,dare ya duba ta,
Tun wanan rana Sa,ade bata sake fita ba don tana tsoron Ibrahim yazo bai samay ta a gida ba yaci uban ta,
Shima Jibrin dayaji sun zo da mama sun mata tas suka kuma samu zara sukai mata cin mutunci a gidan ta,
Duk nasan maganan bai kare ba don in Umma ta dawo akwai magana amma hakan bai damay ni ba saboda nasan haka shine daidai don in wani abu ya samay ta dani za,ai kuka don may ban dauki mataki ba tun farko,,

****** ********* ******
Allah yayi matafiya sun dawo lafiya ana ta murna da farin cikin dawowan su taro na musaman nai masu sai dai shigowan dare sukai muna,
Don haka ba,a samu issashen lokacin tsayawa hira ba bamu dade ba muka shige da mijina muka bar Umma da yarta su ma adakin su din duk wanda yazo taron su ya tafi don dare yayi lokacin,
Tsab na shiryawa dawowan shi don duk wani abu da mace zatayi don taron mijin ta nasa kudina naiwa shiri wanan ranan,
Hamza sai faman santin rashina akusa dashi yakeyi yana cewa Humaira rashin ki a,wanan tafiyan yai min illa da yawa a can na,zabatun da,rashi ki a tare dani
Nace ai bautan Allah ka tafi yaya ko da atare muke ba abinda zaifaru a can ,
Yace amma in ina ganin ki abin zai min sauki sosai kara shigewa yayi a jikina yana fadin kina da,wani siri a jikin ki daba ko wace mace take dashi ba kina,sa nakanji tankar ke din kifi duk saura mata a komai,
Murmushi kawai nai mashi batare dana tanka mashi ba nasan kayan maman mujaheed ne ke aiki akan shi lokacin,
Washegari tun da,safe nafito nai masu abin karyawa tin da nakaiwa Umma nata dakin da,suke ina gaishe ta naji yadda ta amsa min yasani sanin cewa Sa,ade ta kwashi karya da gaskiya ta fada mata ko,
Sai da Hamza yai barcin shi mai isar shi sanan ya tashi yai wanka ya karya yafito don ya gaida Umma don sun dawo tana mura,
Bayan ya dawo daga dakin Umma alokacin ina kitchen ina guara gurin na,dora abincin rana don nasan ranan muna dabaki agidan,
Ina,shiga dakin na,samay shi ranshi a bace kwarai da gaske da alaman yaji maganganu iri iri a gurin Umma ,
Wanka nashiga nafito na zauna nagyara jiki shiko sai cika yake yana batsewa ya hau sosai,
Ina daura dankwali naji yana cewa, Humaira may ke faruwane bayan tafiyan mu ke da yan uwa na,
Najuyo a hankali cikin natsuwa nace mashi kaman yaya kuma ni dasu babu komai,
Yace Umma ta tareni da wani labarin da banji dadin shi dana,shiga gurin ta dazun,
Ni babu abinda ya faru tsakani dasu in ma akwaishi ka tambayi Ibrahim don shi yasan komai akan idon shi akayi,
Yace tau bari Ibrahim din yazo don ai hardashi dama a zancen,
Yaya zaki sa yaiwa yarinya mugun duka don kawai wani manufa naki na daban,
Da,sauri na dago kai na kalleshi yace idan da wani zai fada min baki son yan uwa na,su mamayni zance karya ne amma sai gashi dan tafiyan da mukayi sa,adatu kawai muka bar maki amma kinyi bakin ciki dazaman ta a gidana ,
Muryan su mama da mukaji tana cewa ina Alhajin yake ne dan nawa nagan shi Allah mun gode ma da ka dawo muna da,su lafiya,
Abinda yasa mikewa ke nan fita zuwa gurin mama yabar ni zaune cikin bacin rai a daki sai daga baya nafito kallo daya mama tai min tafahinci akwai matsala don yadda raina yake hade akan maganan da ya fada min a daki kan yan uwan shi,
Sun gaisa,da mama tashiga gurin Umma tabar su da Ibrahim da Jibrin a falon,
Suma,zuwa sukayi gaida Umma din yana,shiga umma tace dama kai nake jira yanzu Ibrahim don ban gari kasaman yarinya akan wanan mara mutuncin Aiaha kai mata bugun akawo ruwa,
Au haka tace maki Umma ashe ma dana,sani na karya ta kafin ku dawo ki samay ta akare da shegen kafan ta na yawo,
Shigowan su Xarah da Asmau danake ganin sun shirya yin tafiyan a,tare ne lokacin,
Umma batai shiru ba,sai masifa takeyi sai mama ce tace assha yaya ai kamata yayi ki tambaya mai tayi ya,doketa da,bakinan,
May zan tambaya tunda da hadin bakin ki akai mata haka aida bada saninki bane bai kai can yai mata wanan dukan ba hakana,
Jibrin ne yatare ta da cewa Umma yaya zakice haka yarinya tana fita tun safe har karfe dayan dare bata,dawo gida ba,
Umma tace inji Uban wa wanan yar sherin mai bakin halin tsiua ta hada maku gadar zare kun haye wa Aisha ke son gani gidan nan a cikin ku in ba ita da diyan ta da yan uwan ta ba,
Wallahi in tai tsiya sai tabar gidan don ba gidan Uban ta bane itama kuma tabar gidan muga tsiya,, don an bugi diyan ta zata sa yarinya a gaba da tsangwama
Ina diyan dan uwantane sai tafita tabar mu da diyan da,take fada a kan su
Subbahanallahi inji Mama tace amma,wallahi yaya kin bani kunya wanan yarinyar kokarin da,tayi in ba yaba mata ba kuma ba ace mata Allah waddai,
Jibrin yace mama yanzu ya dace ace tun safe Sa,a bata gida kuma ba,wanda yasan in da take zuwa,.
Har karfe dayan dare don may Aisha hankakinta,bazai tashi tunda amanan ta aka bar mata ,
Nan suka kwashe duk irin tsiyan da tai ta tsula min suka fadawa Umma dashi yaya din da yau ya zauna,
Yacd ga,zarah nan data fada maki may kika ce bacewa kikayi ta dauki mataki ba,
Ta dauki matakin kuma shine za,a ce tai laifi haba Umma ku dinga tsaya ku binciki magana kafin ku dauki mataki,
Don kawai kuna kin yar mutane sai kusa mata karan zuka haka, wallahi haka babu kyau gaskiya
Kayauuu Hamza ya kwashe Sa,adaru da mari da duka a lokaci guda yace sai ya halakata,
Ina jin su wanan yafadi nashi wancan ma yafadi ban shigo gurin su ba na kyale su karshe ma nashige daki don takaici na fara kuka,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA,BA KADA KI KARANTA,HAKKIN WASU PLEASE DON YIN HAKA CIN AMANA,NE,,,,,



Ko da ya daina dukan ta ranshi a,bace yayi shiru ns dan lokaci mai tsowo saboda ran shi yai matukar ba ci a lokacin sauraren kalammin kowan su yake a lokacin,
Sai can Umma tace naji anyi laifi tana zuwa gidan Audi bata fada mata ba amma kums kuma ku kwantar da hankalin ku kuyi nazari,
Kun san fa ita Aisha yanzu baku gane ta,bane ita so take duk wanda zai shigo gidan daga ni uwar ku haku yayana indan zamu mami mijinta sai dai mu yarda ta mayar damu talolo kamar yadda,ta mai da shi mijin nata ,
Da,sauri suka,daga suna,kallon Umma gaba dayan su don jin may tace, a kaina da dan uwan su,
Hamza daga inda yake zaune yana tuku buri da,jin haushi zan tukan su, ya dago kao ya,dubi Umma sai mama hafsi ce tace wai wa kike nufin tamayar solobiyo shi Hamza din ko wa wai,
Umma cikin hasala tayi maza tace eh shi din mana kin ko san yadda take wa Su yaran nan Sa,adatu bazata yarda a ce a juyata tun da ita ba sakariya bace, irin su, kuma ba wurin ta tazo ba bakuma don ita ta zauna gidan ba,
Don dai gida ba nata bane ita da "ya"yan ta da yan uwan ta da zata kama bakin ciki da hassadan duk wanda yace yazo zama a gidan
Gida dai nakane da zata kama bugun kirji tana kafa masu doka yadda ran ta so,
Hamza ya katse Umma da cewa nata ne Umma b bugun kirji takeyi ba tun da itace matar gidan,,
Amma tunda kince ba wurin Aisha tazo ba ta ba har kin fada da bakin ki yau din nan Sa,adatu ta tattara tabar mata gida tunda ita ba boyar ta bane da tana zaune za,ai mata komai kuma babu ragowa ko mutuci akan ta,
Tabar mata gida fakace Hamza ta kira sunan shi abinda ban taba jin tayi ba,
Yace da karfi eh Umma kema ai kin fadi da bakin ki ba wurin Aisha Sa,a ta zo ba towurin watazo ni dai ba mazauni gida bane itace ke cikin gidan ta zaune,
Yaya za,a zo a zauna a gida ace wai ba wurin matar dake cikin gida akazo ba wurina akazo ni mazauni gidane ko kuwa ?
Umma ke kin san Humaira bata ta adawa da yan uwana inda bata damu da halin da zata fada ba sai ta saka mata ido tayi yadda ranta ke so bata damu ba,
Kin koga tasan a gurin ta ke take fita yawo dole hankalinta ya tashi ta dauki mataki,
Inda haka kawai ta saka ta a gaba ba wani dalili ma kwari kin san nima bazan kyale Humaira ba yau a gidan nan,
Ai naga dukkan su gasu nan kin san lokacin da suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login