Showing 45001 words to 48000 words out of 178785 words

Chapter 16 - Babu So Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

32840

hakan ta faru ne? Keda ke zaune a kujera?”.
          Fuska ta sake tsukewa matuƙa, taƙi kuma cewa komai sai harar gefen ido data ballama Shareff daya tsareta da idanu shima alamar bukatar son ji.
   “Ina saurarenki ya akai hakan ta faru?”.
          Nan ma ƙin cewa komai tai, sai dai ta ɗago yanzu sosai ta kalli Yaya Shareff har suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi da zamewa ta kwanta tana son maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata. Maheer da bai hakura da son jiba yay ƙoƙarin zagayawa inda ta juya fuska Shareff ya dakatar da shi. “Malam ya isa”.
   Kamar Maheer zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda shigowar Nurse. Sannu tai musu tare da mikama Shareff dake kusa da ƙofa takardar hanunta. “Yallaɓai zaku iya tafiya da ita gida yanzu, ga wannan magungunan sai a saya mata tai amfani da su, ALLAH ya kiyaye gaba”.
    Amsar takardar yay da gyaɗa mata kansa kawai. Sai da Nurse ɗin ta fita sannan ya dubi Maheer dake tambayarsa ko can gida zasu wuce kawai?. Bai ce masa komai ba ya fita a ɗakin, shi kuma Maheer ya koma inda ta juyar da fuskarta.
      Kallonsa tai da faɗin, “Yaya nidai mu tafi gida kawai, bazan koma gidansa ba, kuma wlhy ta kwana da sanin yanda ta zubarmin da jini sai na rama koba yanzu ba”.
        Ɗan zaro ido Maheer yayi da zama a kujerar dake gaban gadon. Kafin ya samu damar cewa wani abu Shareff da wasu Nurse suka shigo ɗakin. Kallonta yake cikin ido saboda yaji abinda take faɗa. Maheer ma kallonta yake sai dai ya kasa cewa komai dan bai fahimceta ba. Da taimakon Nurses ɗin aka kawota wajen mota, tanata mitar ita dai a kaita wajen Mamie. Bai kulata ba, sai Maheer dake lallashinta. Sun tsaya wani pharmacy ya bama Maheer takardar da atm ɗinsa tare da faɗa masa pin......

       ★★

  Tun bayan fitarsu take auna son kiran Mamah (Gwaggo Halima) sai dai gargaɗinsa akan kai ƙararsa ga iyayenta ko nashi na taka mata birki. Sosai ta kasa zaune ta kasa tsaye balle tsaida shawara. Har cikin ranta tsoro ne da shakku ke cizon zuciyarta dake ayyana mata abubuwa masu dama. Ta rasa miyasa yarinyar nan ke yawan shiga mata hanci ne? Kodai akwai alaƙar da suka jima suna jin tsoron ta kasance ne ta ƙullu tsakanin mijin nata da baƙar yarinyar nan? “Kai ina, wlhy zuciyata bazata iya ɗauka ba”. Ta faɗa a zahiri da ƙoƙarin kauda mummunan zaton dake kawoma zuciyarta farmaki. Ba yau ta fara irin wannan tunanin ba, shiyyasa a koda yaushe take ƙara jin tsanar yarinyar bayan wadda mahaifiyarsu ta cusa musu akan iyayenta da ita kanta, bata son ganin wata alaƙa tsakanin Mijinta da Anam, amma abin tsoron a kullum kusanci take gani a tsakaninsun, kusanci irin wanda tafi shiga tashin hankali da shi a yanzu fiye dana baya.. Tabbas lokaci yayi da zata ɗauki mataki, idan tace mataki tana nufin koma wane irine in har zai nisanta tsakanin mijin nata da wadda takema kallon maƙiyya tun a zamanin tsatson kakanni da suka haɗa kishi.....
       Harta danna kiran Mahmah ta yanke, dan tasan rashin haƙuri da haɗiye abu irin nata, maida akalar kiran nata tayi ga Mommy, bugu ɗaya kuwa ta daga. Ta gaidata cikin ladabi da kwantar da murya. Itama Mommy sai ta amsa da kulawa sosai. Shiru ya biyo baya, Fadwa na tunanin ta inda zata fara...
    Mommy ta katse shirun da faɗin, “Fadwa babu dai wata matsala ko?”. Nan ma shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya da fara kukan da bata san yana makale a makoshinta ba. “Lafiya Mommy”. “A'a Fadwa, ya zakice lafiya kuma kina kuka. Kinga kar kiji komai faɗamin matsalarki kinji, Shareff ne ko?”.
       “Bashi bane Mommy yarinyar nan ce Anam”.
     “Anam!!”.
“Eh Mommy”.
Shiru Mommy tayi zuciyarta na tafasa, taja nannauyar ajiyar zuciya tana mikewa. Falon ta fara zagayawa har lokacin wayar na a kunnenta sai dai ta kasa cigaba da cewa komai kamar yanda itama Fadwa tai shiru. Kusan mintuna biyu sannan Fadwa ta katse shirun da faɗin, “Mommy wlhy ni bazan iyaba. Zuciyata bazata iya ɗaukar cigaba da ganin wannan yarinyar mai ƙirar karuwai na shigomin gida ba. Inba hakaba zan iya kasheta na halaka banza.....”
      Rai ɓace Mommy ta katseta da faɗin, “Shi Shareff ɗinne ya kawota gidan?”.
          “A'a tare da Yaya Maheer sukazo. Yanzu haka daga ta ɗanji ciwon da tana akan sani tayisa dukansu sun kwasheta zuwa asibiti a ruɗe. Kusan awa huɗu kenan har yanzu basu dawo ba. Wlhy Mommy na tsaneta, dan ALLAH nidai ta daina zuwa min gida”.
        Katse wayar Mommy tayi, ranta a matuƙar jagule ta fara laluben number Maheer, harta katse ba'a ɗauka ba, ta sake kira nan ma ba'a ɗagaba. Ranta ya sake ɓaci ta maida akalar kiran ga Shareff. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga, cikin girmamawa a gareta da tausasa harshe na ɗa nagari ga iyaye yay mata sallama da faɗin, “Mommy barka da yamma”.
        “Kuna ina?”
Ta jeho masa tambaya batare data amsa gaisuwar tasa ba. Ɗan jimm yay alamar tunani, sai kuma ya kalli Anam dake kwance cikin kujera idanunta a lumshe. Kamar mai raɗa ko tsoron tada jariri a barci yace, “Pharmacy”.
       “Kai da wa?”.
Kallon Anam ɗin ya sakeyi suka haɗa idanu, a marairaice ta janye tana kauda kanta gefe. Numfashi ya ƙara saukewa, cikin sake tausasa harshe yace, “Ni da Maheer ne....”
      “Dawa kuma?”.
Ta tare numfashinsa tun kan ya ƙarasa. Bai iya karya ba, shi mutumne kai tsaye koda ace gaskiyarsa zata ja masa laifi ko matsala zai faɗa ya amsa hukuncin daga baya. Dan haka yace, “Mommy da Juwairiyya ne da taji ciwo”.
       A fusace tace, “Waye Juwairiyya kuma?”.
     A hankali yace, “Anam”.
“Kusameni kai da Maheer”.
Ta faɗa tana yanke wayar. Tsirawa wayar ido yayi kamar mai son ganin Mommyn a ciki, sai kuma ya ɗan girgiza kansa ya ƙara kallonta ya ɗauke kansa yanama motar key saboda hango Maheer na fitowa. Baicema Maheer ɗin komaiba ya canja hanyar zuwa gidansa zuwa amsa kiran Mommy. Shima Maheer ɗin baiyi magana ba a tunaninsa mitar Anam ce ta sashi canja shawara.
      Gidan su Anam ɗin ya fara tsayawa, sai dai bai shiga da motar ba yay parking a ƙofar gate. Kusan atare suka fito shi da Maheer. Maheer ɗinne ya buɗe mata murfin yana faɗin, “Kefa yau kin zama gimbiya sai dai a ɗaukeki ko?”.
       Kanta ta jinjina masa tana murmushi duk da hango mugun kallon da Shareff ya watso mata. Tana ƙoƙarin miƙa masa hannu duk da tsokanarsa dama tai niyyar yi su Abie suka fito shi da baƙon abokinsa da suka jima basu haɗu ba. Hannun Maheer ya janye ya nufi su Abie ɗin kamar yanda Shareff yayi. Abie dake kallonsu fuska ɗauke da murmushi ya riƙo hanunsu su duka yana kallon abokin nasa. “Waɗan nan yarana ne, Babana Al-Mustapha muna kiransa Shareff. Architect kuma Shugaba mai mallakin companyn da nake maka bayani, sai Barrister Maheer”.
      “Masha ALLAH yaran albarka”.
Murmushi duk sukayi suna mai rissinawa da gaishesa. Ya amsa cike da kulawa yana riƙo hannayensu shima. Albarka ya dinga saka musu kafin ya juya ga motarsa dake fake a gefe yana faɗin, “Ato ga ɗan uwanku ma ai tare muke da shi sai ku gaisa ko”.
       A tare duk suka kalli motar, dai-dai da fitowar Anam daga mota itama cikin matuƙar son nuna dauriya sai dai ta kasa taka ƙafar ta nema zubewa. Da sauri Shareff ya nufeta saboda ratsa kunuwansu da siririyar ƙararta tayi, ya riƙota dai-dai ta kusa kaiwa ƙasa.
    “Ance ki fitone?”.
“Nifa na gajine ga zafi a motar”.
Kamar zaiyi magana sai ya fasa saboda idanun su Abie dake kansu, yayinda kunnuwansu ke jiye musu bayanin da Maheer ke musu na cewar ciwo taji a ƙafa.
          Ƙoƙarin ɗaukarta Shareff ɗin yake yi tai saurin ja da baya cikin zare idanu da bugawar ƙirji sakamakon ganin wanda batai zaton gani ba.
    “W...waya kawoka gidanmu?”.
Ta faɗa idonta kar a kansa kamar yanda shima ita ɗin yake kallo. Su kuma su Abie su dukan suke kallo. Tattausan murmushi ya saki yana mai janye idanunsa cikin na Shareff da yay wani irin mugun kicin-kicin da fuska, akan fuskarta ya maida cikin ɗaga kafaɗa yace, “Ina tare da Daddyna ne. Amma badan nasan nanne gidanku ba Beauty ”.
        Sau ɗaya ta kalli abokin Abie ɗin ta maida kanta ta duƙar. Cikin sake faɗaɗa murmushi Alhaji Abu kalla ya dubi ɗan nasa da ƙyau. Kansa ya shafa yana mai kauda kai da sakin ƙaramar dariya. Alhaji Abu Kalla yay ƙaramar dariyar shima da ɗauke idonsa ga ɗan nasa ya maida ga Abie da shima dai murmushin yake da sonjin ƙarin bayani..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽


[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO.. 👉🏻AREWABOOKS🫶🏻_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_17_*


........Kasancewar Abie a wajen ya sashi ƙin cewa komai ya ɗauketa gaba ɗayanta ya haura sama aunty Mimi biye da shi. Ɗakin Mamie suka nufa kamar yanda Aunty mimi tace.
     Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfin gaske lokacin da yake ajiyeta akan gado, dan tunda ya ɗakkota ta ɗauke numfashinta da rumtse idanu zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Shi ɗimma dake ƙoƙarin dannewar tashi zuciyar bugu take da gudu a ƙirjinsa har numfashinsa na seizing. Ajiyar zuciyar ya sauke tamkar ita, sai dai tasa ta fitane a ɓoye. Sallamar Mamie ta sashi haɗiye abinda ke masa kaikawo, tray ɗin hanunta ya amsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Mamie da kanki”.
      Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, ta harari Anam dake kwance lamo tana sauke ajiyar zuciya. “Mai rakin tsiya yanzu waye yaji daɗin? Nikam zanga yanda zaki ƙare lokacin rainon ciki balle ranar haihuwa, mijinki dai yaga takansa ai”.
     Dariya aunty Mimi ta sanya, yayinda Anam ke tura baki gaba, taɗan saci kallon Shareff sai ko idonta cikin nashi. Sosai ya sarƙeta da su, sai da ƙyar ta samu damar fisgewa tari mai alamar sarƙewar yawu na kufce mata. Wani irin yanayi data kasa bama fassara ta karanto a cikin ƙwayoyin idanunsa, hatta da tsigar jikinta yamutsawa ta shigayi, ga tarin yaƙi tsayawa har sai da Aunty Mimi ta tadata zaune tana bubbuga bayanta. Kamar ba shine sanadin komaiba cike da basarwa ya miƙama Aunty Mimi ruwan, a baki ta saka mata, sai da tasha sosai kafin tarin ya lafa idanunta har sunyi jajir. Sannu Mamie tai mata tana ƙoƙarin ficewa domin nuna kara garesu tunda dai duk suna ƙoƙarin nuna kulawa gareta bai kamata ita saita tsaya ba.
     Yana daga tsaye har Aunty Mimi ta bata umarnin fara cin abinci bayan ta ɗaura mata tray ɗin akan cinyarta. A hankali ta fara cin abinci, sai ƙunƙuni take a zuciyarta na zamansa ɗakin. Oho bai san tanayi ba, dan babu alamar zai fita ɗin. Aunty Mimi ta miƙe ta fita saboda kiran mijinta daya shigo mata a waya.
       Shiru ɗakin bakajin motsin komai sai na ƙarar spoon da take juyawa a plate, dan gaba ɗaya tama kasa cin abincin yanda ya kamata, tarasa mike damunta, kunyarsa ko haushinsa, dan abinda ya faru a gidanta ɗazun ya gagara barin zuciyarta. Jin shiru kamar baya ɗakin ya sata ɗan ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka sake haɗa ido. Kanta ta maida ga abincinta tana sake tsuke fuska.
     (Sai kallon tsiya) ta faɗa a ranta. Kamar yaji mitake faɗa ya zura wayarsa a aljihu yana ɗan jan siririn tsaki. “Baki iya komai ba sai kallon mutane laziness”.
     Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa idanunta cike da tsiwa. “Toni da baka kalleniba zaka san ina kallonka ne.....”
       “What!”.
  Ya faɗa cikin ɗan kausasa murya da waro idanunsa kanta sosai. “K! Wai yaushe na zama abokin wasanki ne a gidan nan?”.
       Ƙin cewa komai tai, sai dai bakinta a sama kamar zai taɓo silin. A ranta ko addu'a take aunty Mimi ta dawo kafin ya fara zazzabga mata maruka. Ganin yana matsota tai saurin faɗin, “Amma matarka ɗazun datai iskanci agaban mutane baka hukuntata ba sai ni, kuma jinina da aka zubar sai na rama”. Ta ƙare maganar wasu zafafan hawaye dake nuna tabbacin abun na ranta kamar zanen dutse har yanzu suka shiga rige-rigen sakkowa. Cak ya tsaya yana kallonta, kuka take sosai kamar wadda aka doka, kusan tsahon minti guda da wasu sakanni ta gagara tsaidasu. A hankali ya rumtse idanunsa, tare da furzar da ƙaramin huci daga bakinsa. Shiru bashi da alamar cewa komai balle lallashinta, itako sai ƙara matso hawayen take wani baƙin ciki da takaicinsa na sake hasalata, tabbas da ace lafiyar ƙafarta ƙalau ɗakin zata bar masa....
       “K sau nawa ina hanaki tarayya da wannan yaron amma kika maidani sauna? Bayan shi ba muharraminki ba itako *Matata ce!*”.
     Karan farko da tunda ta fara kukan ta ɗago jajayen idanunta tana kallonsa cikin tsakkiyar ido. Shima kallon nata yake a tsakkiyar idon......
       Ita ta fara janyewa cikin ƙunƙuni tana faɗin, “Ni dai baza'a rabani da masoyina ba”.
Sosai kalaman nata suka daki ƙirjinsa. Sai dai kafin yay wani yunƙuri aka dakatar da shi.
“Mike faruwa anan?”.
   Aunty Mimi dake shigowa ta faɗa cikin dariya. Ita ta fara janye nata idanun, batare da tace komai ba ta zame ta kwanta. Shima numfashi ya ɗan fisga, cikin yanayi kamar mai borin kunya ya ɗaga kafaɗarsa. “Nothing Aunty. Zan wuce gidane goodnight”. Kafin ta samu damar cewa wani abu yayi ficewarsa. Da kallo ta bisa har ya fice, kafin ta juyo ga Anam dake faman sauke ajiyar zuciya.
     Komai batace mataba, sai da ta tadata zaune ta bata abincin da kanta tare da magungunanta sannan ta fiskanceta da ƙyau. Kai tsaye tace, “Mamana kina son Shareff ko??!...”
        “God for bid Ummie”.
  Ta faɗa cikin tarar numfashin Aunty Mimi da saurai.
    “Sure?”.
“Yes Ummie”.
Yanda ta bada amsar da ƙwarin gwiwa yasa Aunty Mimin haɗe fuska tana mata kallon sama da ƙasa. Cikin rashin wasa tace, “To *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!”*.
        “Kishi kuma Aunty? A dalilin mi zanyi kishinsa?”.
     Ko amsa ɗaya Aunty mimi bata amsa mata ba, sai dai ta kafeta da ido ganin hawaye na ciko mata ido. cikin ɗan ɗage kafaɗa tace, “Okay fine kwanta kiyi barci”.
    Kwanciyar tayi, tana ta faman ALLAH ya kiyaye ta so wannan mutumin a zuciyarta, a fili dai bakinne kawai ke motsawa babu sautin fitar magana......

    ★★

   A hankali yake driving ɗin tamkar baya so ko kuma shi kaɗaine a titin, motoci da yawa sai sun masa horn yake ɗan kaucewa ya basu hanya su wuce, ga kiran Fadwa dake faman shigo masa waya babu ƙaƙƙautawa. Sai da tai wajen bakwai baida alamar ɗauka, ana takwas ɗinne ya fisgi wayar a fusace daga change daya sata yakai kunne. Sai dai baiyi magana ba dan inhar ransa ya ɓaci baya son ya ringa cewa komai....
      “My son!”.
Muryar aunty Mimi tazo masa a bazata. Da sauri ya cire wayar a kunensa ya kalla. Tabbas Aunty Mimi ɗince ba Fadwa ba. Yawu ya haɗiye da ƙoƙarin saisaita kansa. “Yes small Mom ko nayi mantuwa ne?”.
      “Da alama tunda ka tambaya ƙila kayo ɗin”.
  Ƴar dariya yayi yana shafa kansa da lanƙwasa kan motar ya shiga layin gidansa. “Aunty kenan, da alama magana kike nema dai kawai”.
         “Kusan hakan, sai dai kai tsaye zan yita, kamar yanda nayi a ɗayan ɓangaren”.
      A hankali ya tsaida motar a ƙofar gate, sai dai baiyi horn ba. “To ina saurarenki mamana!”.
        “Babana kana son Anam ko?!”.
    Da ace ruwa yake sha ko cin abinci babu shakka sai ya ƙware dan abinda Small mom ɗin nasa ta faɗa yazo masa a baza. Ya haɗiyi yawu da sauri jin maƙoshinsa na ƙafewar danshi. Yay ƙoƙarin saisaita kansa kai tsaye yace ni da nai aure sati guda kuma”.
     “Ba labarin aurenka nake tambaya ba, dan nima ban manta lissafin ba. Ka bani amsata kawai”.
          Steering ya ɗan daka yana cije lips, cikin son kauda mata dukkan wani tunani babu ko gargadar murya ya bata amsa.
     “Aunty ni matata kawai nake so, bayan ita babu wata a raina”.
        Shiru Aunty Mimi tai, sai kuma ta saki murmushi mai sautin da har yaji, cikin dakewa tace “Sure?”.
     “Babu kokwanto a maganata Mom”.
“Okay fine. To amma *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!*”.
        “Kishi kuma?! Sai dai na zuminci”.
     Ƴar dariya aunty Mimi tai da faɗin, “Lallai kam”. Tana yanke wayar.
      Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka yay baya luuu jikin sit ya kwanta, idanunsa da suka canja launi ya lumshe, tsahon mintuna ya kasa horn balle yunƙurin shiga gidan. Ga kiran dake shigo masa waya da baya raba ɗayan biyu Fadwa ce amma ya kasa yin komai. Sai da ya sake shafe kusan mintuna goma sha biyu har mai gadi ya gaji da leƙowa ransa fal mamakin lafiya sannan yay masa horn.
       Da ɗan gudunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login