Babu So

Chapter 18 of 58

ɗin ƙaramar yarinyace da kowa zaita fama dake akan abinda zai amfaneki.....”
    Da ido Abie yay mata alamar tayi haƙuri, ta ɗauke kai da ƙoƙarin barin wajen cikin takaicin ƴar tata. Abie yay murmushi da maida kallonsa ga Shareff da ke faman daƙilar waya kamar bai san abinda ake a falon ba, sake kallon Anam ɗin yayi cikin sigar lallashi “Mamana to Yayanki yay miki ko?”.
       Da sauri ta ɗago tana girgiza kanta, “Garama kowa yamin akan shi yamin Abie”. Ta faɗa cikin zafi-zafi da share hawayenta. Amrah ta taɓe baki da barin wajen, yayinda aunty Mimi da Abie ke dariya.
     “To saboda mi baki son nashi? Bayan tun ɗazu muke nan ana fama dake ga ruwan har sun huce”.
        “Aunty Mimi nidai bana so ke kimun”.
    Aunty Mimi zata kai zaune Shareff da har yanzu bai nuna yasan mi suke ba ya dakatar da ita. “Aunty barta, a canja ruwan dai”. Babu musu Aunty Mimi ta bashi waje ya zauna, ruwan zafin ta ɗauka ta nufi kitchen. Anam kuwa ƙafarta ta shiga ja baya, sai dai ta kasa jan jikinta saboda table daya tokare ta. Shi dai bai kulata ba har aunty Mimi ta dawo da ruwan, Abie kuma dama yayi ficewarsa saboda wayarsa da aka kira. Ganin yanda ruwan ke turirin zafin ya ƙara ɗaga hankalin Anam, cikin marairaicewa take duban Aunty Mimi amma tai kamar bata gantaba itama.
      “Ni wlhy bana son naka!!”.
Ta faɗa da ɗan ƙarfi da son sake jan jikinta baya ganin ya amshi towel babba da ƙarami a hanun aunty Mimi. Babban ya ɗaura akan cinyarsa batare da ko kallonta yayi ba, ƙafin kuma ya saka ƙaramin a ruwan zafin, ƙafar tata ya kamo takai hannu zata rike, wani mugun kallon daya sata janye hanunta babu shiri ya watsa mata,
      “Idan hanunki ya sake kawowa nan saina ɓallashi shima kiyi jiyyarbaki ɗaya”.
   Kamar ta rushe da kuka takeji, sai dai tayi alwashin bazata bar hakan ta faruba insha ALLAH. Yana ɗaura towel ɗin daya naɗoma ruwan akan kafarta dake kan cinyarsa alwashin nata ya zama tarihi, dan da gaske kukan ta sanya musu mai ƙarfi tana ƙanƙame ƙafar aunty mimi dake kusa da ita tana matso masa towel ɗin daga ruwan zafi.
     Sosai yanda takeyi ɗin ke neman sakashi dariya, amma ya danne da ƙyar ya cigaba da daddana mata ƙafar a nutse. Ta haɗa uwar zufa kafin a gama, hatta da aunty mimi da tasha riƙo ta haɗa tata zufar dan ba riƙon wasa Anam tai mata ba. Su Amrah da kukan Anam ɗin ya sasu sake fitowa dole sun kasa daurewa sai dariya suke kwasa, aiko ta wawushi throw pillows ta shiga jifansu da shi. Duk yanda yaso daurewa kasawa yay sai da ya shiga layin ƴan dariya da Abie ma ya dawo yana yin tasa a gefe, Mamie ma dake a kitchen dariyar take kwasa  dan borin Anam dabanne dana kowa.
      Ba ƙaramin ƙuleta dariyarsa tayiba fiye data kowa, shi dai da baisan laifinsa ba bai bartaba sai da ruwan ya huce ya shafa mata man da aka bata a asibiti sannan ya saki ƙafar da kumburin har ya fara saɓewa, sai ga mutuniyar gyangyaɗi na ɗibar idonta. Da ɗan sauran murmushin da bai bar fuskarsa ba yake tambayar aunty Mimi ko taci abinci dan yana son tasha maganinta.
      “Inafa taci, tunda Aysha ta kawota fa takema mutane bore a gidan nan har sai da Mamie ta mata tas. Anam ɗin ya kalla cikin ido, babu zato hararar data wullo masa ta iso garesa. Da sauri ta kauda fuskarta dan batai tunanin zai juyo ba. Abie dake kallosu a gefe yace, “Bara na maidata ɗaki sai taci abincin acan kawai ta kwanta”.
      Dakatar da Abie ɗin yayi cike da girmamawa, dan bai kamata shi yana wajen ba yabarsa yay jigilar ɗaukar Anam ɗin. Cikin matuƙar zaro idanu da suɓutar baki Anam tace, “Wai Yayan ne zai ɗauke ni?”.
       Harara ya wurga mata, ta kauda kai gefe cikin ƙunƙuni take faɗin, “Ni dai ALLAH bana so, garama a nemomin wheelchair........”
    Ranƙwafowarsa kanta na shirin ɗaukar nata ya sata haɗiye abinda take faɗar da sauri tana ƙoƙarin zabura gefe...........✍


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko



*_ALLAH ka gafartama iyayrnmu_*😭🙏🏽
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_18_*

..........Sosai idanunta ke faman marmari ga ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a cikinsu.
      “Juwairiyya!! Wlhy! wlhy! daga yau na sake ganin yaron nan ko wani ya ɗaukeki a motarsa koya kaiki gida sai na miki mugun dukan da zaki kasa tashi, kuma ki koma gidana da zama stupid kawai”. Ya ƙare maganar da ture fuskar tata gefe.
     So take ta fashe da kuka amma tana ƙoƙarin son dannewa, sai dai hakan bai hana rawar jikinta bayyana ba. A tsawace ya sake faɗin, “Get out of my car! Kafin na marmashe ƙashinki anan stupid”.
     Da sauri ta ɓalle murfin ta fice tamkar mai jiran umarnin nasa dama. Yaja dogon tsaki da figar motar yay gaba, badan titi bane da sai ya bula mata ƙura, murfin ma sai da yay gaba kaɗan yaja abinsa ya rufe.
     Duk yanda taso ƙoƙarin danne komai hakan ya gagara. Dole ta samu wani dutse a gefen titin ta zauna ta fashe da kuka. Duk abinda kaga Anam ta zauna yima kuka lallai ya taɓata sosai, dan tsiwarta da giringiɗishi bai cika barinta maida abu serious ba, ga kuma yanayin rayuwar data tashi a ciki, ita kaɗai a gidansu sannan a ƙasar da kowa kansa ya sani kawai.
     Ring da wayarta ta farane ya sata share hawayenta ta daga dan tasan su Mamie ne, a kullum tana waya dasu a irin wannan lokaci da kuma in zata kwanta. Video call ne, dan haka ta shiga son ɓoye damuwarta da murmushin farin cikin ganinsu. “Good morning my sweetheart”.
        Dukansu babu wanda ya amsa mata, dan duk da ƙoƙarin da take na ɓoyewa idanunta sun tabbatar musu tayi kuka. Abie yaja numfashi a hankali yana sake kafeta da ido. “Mamana mi yake faruwa da ke? Waya saki kuka? Ko baki da lafiyar ne har yanzu? A ina kike nan?”.
      A karan farko ta saki murmushi dan jin tambayoyin mahaifin nata a jajjere. Samun kanta tai da kasa faɗar gaskiya duk da ƙarya ko ɓoye-ɓoye ba halinta bane, ta sake share hawayen da suka ciko mata ido tana murmushi, “Abie ba komai fa, kawai kewarkuce har yanzu ALLAH. Kuma a wajen aiki nake ban dai shigaba ka gani”. Ta juya masa wayar yanda zai iya hango gate ɗin wajen.
     A jiyar zuciya suka saki shida Mamie, kafin su shiga lallashinta duk da ita Mamie a ranta bata gama yarda da cewar har yanzu kewar tasu bace. Amma sai ta barta a hakan dan tasan Anam da rashin ɓoye-ɓoye koma miye wataran da kanta zata sanar musu. Sai da suka tabbatar sun sakata farin ciki tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ba sannan sukai mata sallama Mamie na faɗin ta gaida mata Yaseer. Farin cikin waya da iyayenta ya taushe abinda Shareff yay mata ta shiga wajen aikinta da walwala kamar yanda ta saba ko yaushe.

      *_MALAYSIA_*

“Humairah waye naji kina faɗin Mamana ta gaida miki?”.
Cikin rashin damuwa Mamie tace sirikinka ne duk da dai naga ɗiyar taka bata son a gane hakan.....”
Cikin sauri ya ɗago yana kallonta, har ya kasa dannewa sai da ya ambaci “Suruki kuma?”.
Ƴar dariya Mamie tai, “Eh bashi kake fatan ganiba daman?, bayan shi ma ai akwai wasu. Yaron nan Muzzaffar da kuma wani abokin Shareff Jamal. Amma naga hankalinsu yafi zuwa ɗaya da Yaseer ɗin nan kamar”.
Jin shiru baice komaiba ta ɗago ta kallesa, kallonta yake kamar mai nazari ko tunani, ta ɗan taɓashi, ajiyar zuciya ya sauke. “Abien Anam akwai matsala ne?”.
Kai ya ɗan jinjina mata yana gyara zamansa, “Babbama kuwa Humairah, miyasa tun muna Nigeria baki sanar min hakan ba.”
Sosai maganar tasa ta sakata kafesa da ido dan mamaki, amma ta kasa cewa komai. Fahimtar hakan ya sashi jinjina mata kai, “Basai kin tambayeni komai ba Humairah, amma idan lokaci yayi ko baki tambayeni ba zan baki amsa da kaina”.
Gaba ɗaya kanta ya ƙara ɗaurewa ita kam, sai dai rashin sabo dayi masa dagiya yasa ta kasa cewa komai ta bisa da kallo kawai ganin ya miƙe yana kai waya kunensa. Yana gab da shigewa ɗakinsa taji ya ambaci sunan Yaya (tasan Daddyn Shareff yake kira da hakan). Jitai kamar ta tashi ta bisa amma sai ta dake kawai, zata bisa a sannu dan tasan dalilinsa na son hana Anaam ɗin tsayawa da samari bayan kuma duk fatansu kenan ita da shi tunkan ta wuce Nigeria.....

   ★★★★
 
Sauraren sakatariyarsa kawai yake batare da yana fahintar abinda take faɗa masa ba, idanunsa ma gaba ɗaya nakan kula ɗin daya shigo dashi, wadda baya raba ɗayan biyu Anam ce ta manta ta...
     “Kinga jeki zan nemeki”.
Ya faɗa cikin katse sakatariyar da ke faman zuba bayani cike da yanga da kwarkwasa. Bataso hakan ba, sai dai sanin shi sam baya wasa yasata bin umarninsa. Sai da ta fice da kusan minti ɗaya ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi, yakai bayansa kwance jikin kujerarsa yana mai lumshe idanu. kusan mintuna uku ya ɗauka a hakan kafin ya bude idanun, kular ya ɗauka ya buɗe. Ya tsirama abinda ke ciki idanu tamkar mai irgawa ko lissafa abinda aka sarrafashi da shi. Abincine irin na ƴan ƙasar malaysia, shima yana bala'in son sa a lokacin da ya rayu acan, ko yanzu kuma da yake a Nigeria yakan je takanas ya siya a inda yasan zai samu. Hannu yakai ya ɗauka spoon ɗin dake ciki ya ɗiba dan tabbas wannan ɗin da gani an masa haɗi da girki na musamman ne. Sosai ya lumshe ido lokacin da yake taunawa, koda ya haɗiye sai ya sake ɗiba yakai baki, kamar da wasa sai gashi ya cinyesa tas dan dama bai karyaba ya fito gidan, shayi kawai ya sha, shima sai da Fadwa ta ɓata rai dayin korafin ganin saurin da yake faman yi duk da ta fahimci shi mai fitar wuri ne office sannan ya sha a tsaitsaye ya barota tana tura baki gaba.......
      Shigowar Fharhan ta sashi ture kular gefe yana goge bakinsa da tissue. Fharhan dake kallon kular da murmushi ya kai zaune yana faɗin, “Ɗan gatan madam, abincin ma sai an baka kazo office kuma ba gayyatar masu tayaka ci ka kulle office kai kaɗai”.
     Murmushi kawai yay yana miƙa masa hannu sukai musabaha. “Kai ka cika sa ido wlhy, ka hucema kanka takaici kai auren kaima sai a ringa baka kana zuwa da shi kana hanamu”.
       “A'a karka damu alhaji, ai abun bana gori bane muna hanya da iznin ALLAH”.
    “Haka muke so ai muma. dan kun ishemu a tituna”.
        Dariya sosai Fharhan yake da maganar ta Shareff, yace, “Kaima yaushe kabar titin. Ba komai zan rama”.
          Shima ƴar dariyar yayi. Cikin komawa serious yace, “Yanzu nake duba saƙonka ta email ai. Mutanen nan ya zasu mana haka kuma?”.
    “Wlhy nima abin ya ɗauren kai, jiya badan karna takurakaba da a daren zanzo na sameka gida tun shigowar saƙonsu, na kira wayoyinka kuma duka switch up”.
            “Mtsoww! Kabari kawai, wlhy ban san madam ta kashesu ba sai da asuba na gani. Amma gaskiya abun nan nasu yayi tsauri, anya kuwa bazamuce mun janye ba”.
     “Amma janyewar sai nake gani kamar akwai matsala Musty. Sakamakon company na buƙatar babban aiki irin wannan a halin yanzun, na biyu mun riga munyi zama da su har munyi signing akan agreement ɗin, kasan kuma turawan nan dai musamman chines ɗin nan da basa wasa da damarsu”.
      Huci ya ɗan furzar yana mai komawa jikin kujera ya kwanta. Har ga ALLAH abubuwa masu yawa ne ke masa kaikawo a cikin rai. Amma duk sai ya haɗiye abunsa yana sake fuskantar Fharhan dake kallonsa. “Ni gaskiya da tafiyar ta zama nine dole zanyi shine matsalata Fharhan”.
      “Oh saboda amarya?”.
Hararsa Shareff yayi, “Ko saboda ita ma ɗin ai inada hujja”.
   “hhhh hakane ango kafa ɗan ɗana. To mizai hana kaje da ita kawai”.
            “Zan so hakan nima, sai dai bazai yuwu ba”.
    “Mi yasa?”.
Shiru kamar bazai amsa ba, sai kuma ya girgiza kansa da furzar da iska ya sake komawa jikin kukera ya kwanta yana ɗan juyata. “Ina hasashen Fadwa nada shigar ciki, sai dai ko ita kanta bana jin ta sani. Yin tafiya da ita a irin wannan gaɓar zai iya zama haɗari”.
         “Masha ALLAH! Alhmdllhi. Lallai wannan angon da gaske sharp shooter ne. ALLAH ya inganta mana”.
      Shareff ya ɗan murmusa da faɗin “Amin” akan laɓɓa. Cigaba da tattaunawa sukai, daga ƙarshe dai shawara ta zauna akan shi zaiyi tafiyar tunda dai wata uku ne kawai insha ALLAH.
       Bayan fitar Fharhan ya buƙaci shigowar sakatariyarsa, daga haka ya cigaba da ayyukansa har zuwa lokacin break....

        ★★★★

  Duk da bata ɗauki gargaɗinsa da muhimmanci ba sai ta kasa sakewa da Yaseer gaba ɗaya yau. Kullum shike fita da ita su ciyo abinci a inda yasan za'a samu abinda take iya ci. Amma yau saita ɓoyema ganinsa. Daga salla ta maƙale a massallaci taƙi fita. Sai ma ta ɗauka alkur'ani tahau karantawa.
       Sai da ta daidaici lokaci yaja sosai sannan ta fito. Kamar jira tana fitowar wani abokin aikinta yazo ya sanar mata tana da baƙo. Da mamaki take kallonsa dan bata tunanin wani zai iya zuwa wajenta a yanzu. Daga Muzzaffar har Dr Jamal bata tunanin ganin wani anan, garama Muzzaffar yakan zo idan ya daidaici sun tashi yace zai ɗauketa sai dai bata taɓa yarda ba. Kamar bazata je ba sai kuma taga gara taje dai taga wanene.
        Turus tayi lokacin data iso taga mai kiran nata, zaune yake a cikin mota sai dai ƙafarsa ɗaya na waje dan ƙofar a buɗe yake..........✍🏻


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107 ko


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/28, 11:42 AM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_19_*

.......... Ɗagowa yay daga latsa wayar da yake yana kallonta, dan ƙamshin turarenta da takunta ya sanar masa da zuwanta duk da ta kasa magana. Idanunta ta ɗauke daga kallonsa tana faɗin “Good Afternoon”.
           “Ni kike ma gaisuwa kina juyar da fuska?!”.
    Juyowa tai Idanu cike da ƙwalla tana kallonsa. “Ni wlhy Yaya ban san mina maka ba duk kabi ka tsaneni ka takura ni. Komai nayi a duniyar nan a wajenka ban iyaba”. Ta ƙare maganar da sakin siraran hawaye.
         Kallonta kawai yakeyi ko ƙyaftawa babu. Ji tai kallon ya sake saka mata jin haushinsa, juyawa tai da nufin barin wajen.....
     “Kika bar wajen nan sai ranki ya ɓaci”. 
    Idanunta ta rumtse tana jin wasu zafafan hawaye da sukafi na farƙo na neman kufce mata. Ita kam ta rasa mita tsarema bawan ALLAHn nan a duniya, tana fatan watanin nan bakwai da suka rage mata su maza suzo ta kammala abinda ya kawota tabar ƙasar nan, dama tun farko abinda ta gujemawa kenan amma su Mamie suka kasa fahimtarta. Haɗiye hawayen tai batare data barsu sun zubo ba sannan ta juyo garesa, yana a yanda yake har yanzu, sai dai idanunsa masu kwarjini da kaifin dake hana ƙarfin halinta tasiri na nan tsaye kanta ƙyam har yanzu. Kasa jurar kallonsa tai, tai ƙasa da nata, shima sai ya janye nasan, juyawa yay kujerar gefensa ya ɗakko ledar dake ajiye. Miƙa mata yay kansa tsaye.
     Ledar ta fara kalla tare da hanunsa dake ɗaure da agogo da zoben azurfarsa da ya jima yana birgeta, har addu'ar damar sace zoben ta taɓa yi a zuwa na karshe da tai kafin wannan.... Saurin ɗagowa tai tana kallonsa jin ya kamo hanunta cikin nasa, ya wani sake ƙanƙance idanu cike da salon kallon da a duk sanda ya jefeta da shi yake firgitata, ta fara son zame hanun a hankali dan gaba ɗaya lakar jikinta neman daina aiki takeyi, kanta ta fara juya masa tamkar mai ciwon wuya, tana son zare idanunta daga cikin nasa amma yaƙi bata damar hakan nan ma, sai kawai ta sakar masa kukan karya.
    Hanun nata ya saki a hankali bayan ya saka mata ledar, kamar wadda ake control da remote fitt ta ɓace a wajen. Tsabar sauri har tintiɓe tayi ALLAH dai ya taimaketa bata faɗi ba ta dafe gate.
           Murmushi ya saki mai ɗan sauti daga ƙirjinsa yana kauda kansa. Ya maida ƙafafunsa cikin motar tare da rufeta yabar wajen.

Itama koda ta shiga sai da ta samu jikin wata mota ta huta tare da share hawayen ƙaryarta sannan ta buɗe ledar. Shawarma ce da ice-creem sai yogurt da robar ruwa. Haka kawai sai kuma ta samu kanta da sakin murmushi. A fili tace, “Ga rashin mutunci ga kirki idan yaso”. Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da

Download complete TXT · Novel page