Babu So

Chapter 37 of 58

take ya fice ta sama ƙofarta key, sai da yaga ta shiga toilet sannan ya fice zuwa sashen Fadwa itama ya tashesu. Koda ta fito kai tsaye ƙofar ta nufa, amma wayam babu keys ɗin alamar ya zare. Ta dallama ƙofar harara da murguɗa baki.
       Sai da gari ya ɗanyi sha ya shigo, har sannan tana zaune tana azkar. Batare da ta yarda ta kallesa ba tace masa ina kwana. A taƙaice ya amsa yana kaiwa kwance dan barci ne fal idanunsa. Jin ya fara sauke numfashi ta ɗan juya ta kallesa, ya juya mata baya, amma ta fahimci barci ne ya ɗauke sa. Itama dai ƙarasa azkar ɗin tai ta koma ta kwanta tunda ba wani aikine da ita ba.....

       ★★★★

  Tsabar yanda ta kwana da abubuwa masu yawan gaske a ranta tana idar da salla sashen Gwaggo ta nufa. Burinta kafin su Daddy daga massallaci su shigo ta shige, dan ita yanzu ko ɗakinsa bata zuwa, shi kuma yaƙi ce mata komai akan hakan. Gwaggo na zaune tana lazimi Mommy ta shigo, kallonta kawai take baki a sage, sai dai kuma batai mamaki ba musamman akan sanin halin rashin haƙuri irin nata. Mommy ta gaisheta kamar yanda ta saba, damuwa ƙarara akan fuskarta.
        “Wai Nafisa kuwa anya hankalinki na jikinki? Wace irin rayuwace wannan duk kin firgita kanki akan abinda bai taka kara ya karya ba. Da alama yau ko barcin kirki ma bakiyi ba ko?”.
    “Humm Gwaggo ina naga ta barci nikam, kema kin san babu wani barci dazan iya a wannan halin. Ki duba fa kiga Shareff ya ɗauke ƙafa gaba ɗaya a gidan nan tamkar ya manta dani a raye, ko'a waya baya kirana tumma yanzu kenan za'a rabani da yarona. Maheer ma yaƙi zuwa duk da shi nasa bai cika damuna ba nasan fushin banza da wofi ya sakama ransa bayan ni gata naima rayuwarsa. Gwaggo taya zanyi barci a wannan yanayin to? Na kasa gane kan Shareff sam. Son yarinyar nan yake da yake gudun haɗuwarmu ko yaya ne?”.
        Ƴar dariya Gwaggo tai. “Banda abin Nafisa halin namiji kuma kika manta! Shi yanzu Mustapha a wannan gaɓar bake kaɗai ba kowama zai iya rasa gane kansa ai.....”
    “Gwaggo to saboda mi? Ni wlhy kaina duk ya kulle”.
       “Uhhm haka dai, tunda kin ruɗa kanki ba dole kanki ya kulle ba. Kina tunanin duk ƙin da yakema yarinyar zai kawo ido ya saka mata ne a gidansa”.
    Kaɗan ya rage Mommy ta haɗiye harshenta. Cikin in ina da shiga ruɗani take magana. “Gwaggo wai kina nufin ya kwanta da yarinyar nan?”.
          “Har kuwa ki ganta da ciki nan da watanni kaɗan”.
“Aiki dana tsine masa”.
    “Ki tsine masa! Kinga Usman da Ai'sha sunci riba a kammu kenan. Ki kiyayi harshenki da ambaton tsinuwa ya ƴaƴanki saboda kawai ranki ya ɓaci. Ki koyi nutsuwa a duk lokacin da kikaci karo da abinda bai miki ba. Nafisa idan kikai sakaci k da kanki zaki tabbatar da nasarar maƙiyanki akan ƴaƴanki. Yanzu dakin kwantar da hankalinki tun bayan da akai rikicin farko akan auren nan da yanzu mun kai ga mafita. Mustapha da kike gani hatsabibin yaro ne mai shegen zurfin cikin tsiya da wayo. Gaggawa a al'amarinsa ba shi bane mafita, kuma tsananinki ba shi bane zaisa muci nasarar rabashi da yarinyar cikin sauƙi, musamman da matarsa dama ta kasance shashasha, dan nikam sai yanzu nake dana sanin yin wannan haɗin nasu”.
       Da mamaki Mommy tace, “Wani abun ya faru ne Gwaggo?”.
    “Nafisa ai shiyyasa nace ke ɗin ruɗaɗɗiyar mutum ce, yo banda haka halin Fadwa har wani ɓoyayye ne da zaki kasa ganewa. Duk wani baƙin halin Halima shine tare da ƴarta, kodan shi Mustaphan bamai yawan magana bane da kullum zai zauna faɗa miki matsalarta shiyyasa kike kasa fahimtar halinta?”
           “Gwaggo bawai ban fahimci wasu abubuwa bane, dan ni kaina yawan kirana da takeyi kullum tana kawomin ƙararsa ya mata kaza ya mata kaza yana cimun rai, sannan Aysha ta faɗa min ko abinci sai ta gadama takeyi a gidan sai dai mai-aiki, Shareff da ko'a gidan nan baicin abincin masu aiki”.
      “Humm zatayi abinda yafi haka ni na sani. Amma karki damu zamu fara gyara mata zama. Yanzu abinda nake so da ke ki sassautama zuciyarki komai, ki nunama su Muhammadu komai ya wuce kin ajiye makamanki, shima ɗin Mustapha ki kirashi a waya ya sameki ki nuna masa komai ya wuce. Mu kuma daga nan zamu fara namu yaƙin, badai wata uku shi Ibrahim ya bata ba, to duk yanda zamuyi sai munyi nanda wata ukun tabar gidan, babban fata na dai ace bai taɓata ba. Kai koda ya taɓatan ma ba komai”.
     “Gara dai karya taɓatan Gwaggo, danni bana fatan haɗa kowace sabga da Usman balle shegiyar matarsa”.
    Ƴar dariya kawai Gwaggo tayi da faɗin, “To ALLAH yasa haka. Yanzu dai inaga kima Sakina magana yau taje mana gidan taga yaya zaman nasu yake”.
      “Wannan shawaran yayi gwaggo, bara na sanar mata yanzun nan kuwa”.
     Daga haka suka cigaba da tattaunawa kuma har gari yay haske sannan Mommy ta koma sashenta zuciyarta na ɗan sassauta nauyin da tai kwana biyu. Masu aikinta ta bama umarnin haɗa abincin Daddy. Duk da sun ɗanji mamaki babu wanda yace komai tunda ba huruminsu bane, itako ta shige domin shiryawa tunda dama girkin tane.....

        ★★

    Kusan ƙarfe takwas ta farka. Ganin har yanzu shi barcinsa yake hankali kwance sai ta koma ɗayan ɗakin tai wanka ta shirya a can. Ganin har lokacin baida alamar tashi saita nufi falo ta gyara duk da ba wani datti bane ba. Yunwa takeji matuƙa, dan haka ta haɗa tea ta dawo falon tai zaman sha tana buga game a waya. Koda ta kammala a falon ta cigaba da zama tana game ɗin har kusan ƙarfe tara.
     “Wai mutumin nan bazai tashi bane? Koya manta yau monday akwai office?”.
   Ta faɗa tana kallon agogon dake falon, miƙewa tai kanta tsaye ta nufi bedroom ɗin. Mamaki ya ƙara kamata ganin har yanzu dai a kwance yake, (Lallai babu lafiya) ta ayyana a ranta tana ƙarasawa gaban gadon, dan ita dai a sanin datai masa na rashin wasa da aiki inda ƙalau yake babu yanda za'ai yakai yanzun yana barci. Fuskarsa ta ɗan tsurama ido dan kwance yake a rigingine. Lumshe idanu tai da sake buɗewa a kansa, ita shaida ce Shareff ƙyaƙyƙyawa ne, ƙyawu irin na masu kwarjini da cikar haiba bawai na fitar hankali ba. ALLAH ya bashi dukkan kamala ta cikakken mutum tamkar wani babba. Baida yawan hayaniya, sannan bai da yawan fara'a. Mutane da yawa kance mata yanada sauƙin kai da daɗin zama, sai dai ita har yanzu bata ganinsu tattare da shi, dan zata iya bugar ƙirji tace babu wadda yatsana a rayuwarsa ƙila sama da ita, ta rasa minene laifinta a gareshi. Ta taɓe baki da juya idonta, a fili ta furta “Yo karya soni ɗin nima ai ba son sa nake ba humhh”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki ta juya zata bar wajen a bazata taji an riƙota. A firgice ta juyo dan ta tsorata, sosai idanunta suka firfito waje dan batai zato ko tsammanin shi ɗin bane tunda taga barci yake. Idanunsa ya ɗan rufe ya sake buɗewa a kanta tare da fisgota ta faɗo kansa.....
      “Wayyo Yaya zaka karyani ne?”.
Komai baice mata ba, sai dai kafeta da idanunsa dake a yanayin wanda ya tashi barci. Ƙoƙarin son zame jikinta take a nasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora hanunsa a bayanta ya tallafeta da ƙyar a saman jikinsa, fuskarta dake a gab da tashi ta kautar gefe saboda yanda yake kallonta tsigar jikinta har tashi take. Ɗayan hanunsa yasa ya maido fuskar tata a saitin tasa har yana jin saukar numfashinta.
       “Kina yin miye tsaye a kaina?”.
   Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta tura baki da ƙara ƙoƙarin janye fuskarta dan bazata iya jurar kallonsa ba. “Ni to mizanyi? Kawai nazo tadaka ne dan naga lokacin office yana wucewa”.
      Agogon dake ɗakin ya ɗan kalla tare da maido idanunsa a kanta lokaci guda. “Dama ango na zuwa office ne?”.
    Sosai ta yatsine fuska tamkar wadda aka faɗama wani mugun abu. sai kuma ta taɓe baki da sake yunƙurin barin jikin nasa........✍



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_53_*



.........Da sallama ta shigo ɗauke da madaidaicin tray mai ƙyau, a samansa  madaidaiciyar butar shayi ce da kofinta ɗaya, sai tea spoon da sugar a ƙaramin bowl. Sai kuma plate dake rufe da robar ruwa ɗaya duk da tasan za'a iya samun ruwan a sashensa. Kaɗan ya juyo daga kallon tvn da yake ya ɗan dubeta, sai kuma ya ɗauke da amsa sallamarta akan lips. Gaba ɗayansu haushinsu yakeji dan kowacce da kalar laifin datai masa, sai dai yafi ganin sassaucin na Fadwa akan wannan tsiwatacciyar yarinyar da har yanzu maganganunta na ɗazun basu daina masa zafi a zuciya da ruhi ba.
      Ita dai da bata san yanayi ba ma koda ta gama zuba shayin ɗan ɗagowa tai ta dubesa da zata saka sugar. A taƙaice yace, “biyu” ya cigaba da kallonsa. Baki ta ɗan taɓe itama ta jefa masa biyun ta saka cokali. Plate ɗin datai warming sauran naman jiya daya kawo da dare ta zubo a ciki ta buɗe masa, sai sauran meatpie ɗinta da shima dai baiyi komaiba kasancewar a fridge yake shima dai tayi warming ɗin nasa.
      “Bani waya a bedroom”.
Ya faɗa dai-dai tana ɗagowa alamar ta kammala aikinta. Ganin yanda yake tsume-tsumen fuska ta wuce salin-alin batare da tace komai ba. Babu jimawa ta fito da wayar a hannu. Harya fara cin abincin hankalinsa rabi a tv. Nanma dai tana bashi tai ficewarta tabarsa.
       Motar da bata san kota wacece ba take shigowa gidan. Bata san wani a gidansu da motar ba, dan haka tai wucewarta batare da maida hankali ba dan maybe baƙin Fadwa ne kona mai gidan...

     “Kinga kallon da yarinyar can taima motarmu ta watsar kuwa Sakina?”.
     Hajiya Luba ƴar uwa ga Mommy kuma mahaifiya ga Bibah ta faɗa idonta akan Anaam dake shigewa sashenta. Aunty Sakinar ma kallon nata take, tai ƙwafa da ɓalle murfin motar ta fita. “Yaya Luba ba dole tai mana kallon banza ba tunda wanda ya kawota gidan ya nuna mata tafimu, yo ta fimu mana tunda ya zaɓeta sama da umarnin uwarsa ma”.
    “To aikuwa zasu ci ubansu daga shi har ita, dan zamu sauke mata abinda ke kanta yanda uwarta ta mallake ubanta mu anan AL-Mustapha yafi ƙarfin haka. Jiba yanda take yawo da wata ƴar iskar shiga dan ALLAH”.
        “Duk dama ta samu ai ke dai Yaya Luba, muje dai”.
Wanda ya kawosu babban ɗan Aunty Sakina ɗinne, ya girgiza kai duk zuciyarsa babu daɗi, dan shi dai baiga abinda yarinyar tayi ba suke cusa mata wannan zagin, shikam harma ya fara tausayin Yaya AL-Mustapha wlhy.

      Suko sashen Fadwa suka fara nufa, a falo suka sameta zaune tana shan lemun fata, mai-aikinta zaune daga ƙasa itama. Kallon sukeyi na wani horro film sai dai sam hankalin Fadwa ba gaba ɗaya yake akan film ɗin ba. Maman Abu ta miƙe tana musu sannu da zuwa. Da ƙyar suka amsa mata, bata damuba ta nufi kitchen ɗakko musu ruwa dan ba yau ta saba da halinsu ba tunda sanda tana can gidan su Fadwa ɗin ma suna zuwa babu kalar wulaƙancin da basa gani su masu aiki a wajensu su a dole ƙanen masu gida (Karku manta suma ƙanen uba suke ga Fadwa, kuma ƙanen uwa ga Shareff).
       “Baki da lafiya ne?”.
   Aunty Sakina ta faɗa idonta fas akan Fadwa. Kanta ta girgiza mata kawai. Baki aunty Sakinar ta taɓe. Hajiya Luba ta karɓe da faɗin, “Ciwo ya wuce baƙin cikin miji da kishiya mai kama da karuwai, k yanzu nan Fadwa har waccan ƴar tsefatar yarinyar ce zata razanaki ki koma haka firingau-firingau ido luhu-luhu. Kuka kenan kika zauna kinayi kamar wata sakara?”.
     Hawayen da taketa riƙewa ne suka silalo mata. Aunty Sakina da Hajiya Luba suka ɗauki sallallami da tafi kamar waɗanda sukai gamo. Ita dai Fadwa kanta a ƙasa tana hawayenta.
  “A to wlhy aiki ya ganki kuwa, yima kishiya kuka. Kishiyarma wadda bata wuci a sati ki kaɗa shegiya ba tabar gidan saboda ke ɗin shashashar ce kika zauna kinamata kuka. To bara kiji, idan zaki dawo cikin hankalinki ki dawo, a duk zuri'armu babu sakarai. Balle ke da mijin nan naki tako ina jininki ne, da ubansa da uwarki uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, da ubanki da uwarsa iyayensu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Gaba da baya aka tsaga jikinku jini iri ɗaya za'a gani, itako fa miye haɗinsa da ita banda ɗiyar ɗan uban ubansa, dalla malama sharemin waɗan nan banzayen hawayen ki tashi ki rakamu sashen shegiyar”.
     Hawayen Fadwa ta share, sai dai kuma tuna yana gidan yasa ta kasa tashi. “Aunty yana nan fa a gida”.
    “Shi wa ɗin?”.
Cewar Hajiya Luba.
“Shareff! Yau bai fita aiki ba wai hutu ya ɗauka harna sati ɗaya”. Ta ƙare faɗa da rushewa da kuka tabbacin abinda ke cin zuciyarta kenan tun ɗazun.
     Cikin riƙe baki Aunty Sakina tace, “Iyee wato sati guda, amma uwarsa nacan ko sau ɗaya baije ya gaisheta ba. Shiko dai Al-Mustapha yayi asara. Aini namaji daɗin samun nasa a gidan zanfi jin daɗin cin uban shegiyar yarinyar a gaban nasa sallamamme kawai. Tashi muje ki kaimu, kuma karna sake ganin waɗan nan hawayen banzar kema shashasha”.
     
      Anaam na kwance cikin kujera tana buga game suka faɗo mata ko sallama babu. Da farko tayi kamar ta share dan Fadwa ce ta fara shigowa, sai dai ganin su Aunty Sakina ya sa ta tashi zaune tana danne sosuwar da zuciyarta tayi akan shigo mata kai tsaye da sukai. Ta san aunty Sakina dan sun taɓa zuwa gidanta ita da Aysha. Daga Hajiya Luba har aunty Sakina bin falon suke da kallo baki a taɓe, sai dai acan ƙasan ransu razani ne na gaske, dan ko makaho ya shigo ya laluba yasan annunama duniya yariyar ƴar gata ce.....
       Cigaba da game ɗinta tai domin basu dama su gama kalle-kallen, saiko da sukai iya iyawa sannan suka juyo gareta.
    “Oh lallai, ga ƴan iska sun shigo ko?”.
Aunty Sakina ta faɗa murya a sama. A karan farko Anaam ta saki murmushi, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi tana kallonsu, cikin hausarta dabai gama nuna ba ta gaishesu kamarma bata fahimci harzuƙowar aunty Sakinar ba..
          “Uhm lallai kam Shareff ka amshi ruwan dafa kanka. Wato k a dole ƴar bariki”.
     Sarai ta fahimci abinda Hajiya Luban ta faɗa, dan kuwa zuwa yanzu Alhmdllhi hausa ta fara zauna mata a brain da harshe da ƙyau saɓanin farkon zuwanta. Amma sai tai kamar bata fahimci komai ba, fuskarta da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Aunty ku zauna Please bara na kawo muku ruwa”. Bata jira cewarsu ba ta nufi kitchen.
     “Babbar b*r* uba kai. Wai wannan yarinyar tana nufin bama tajin mi muke faɗa ko mi?”.
   Fadwa da batace komaiba tun shigowarsu tana kuma daga tsaye dan bata zauna ba tace, “Hummm! Tana jin komai sarai iskanci ne kawai fa Aunty. Ni dama kun barta dan ALLAH kawai....”
        Harara Hajiya Luba ta zuba mata. Shigowar Shareff a bazata ta saka Fadwa haɗiye abinda zata faɗa babu shiri da risinar da kanta ƙasa, wani yawu mai kauri ya wuce muƙut a maƙoshinta ƙirjinta na bugawa.
        Idanunsa ya janye a kanta da ƙarasowa cikin falon hannayensa duk biyu a cikin aljihun wandonsa.
   “Oh dama kana gidan?”.
Aunty Sakina ta faɗa tana hararsa.
Duk da sarai ya jita sai bai amsa ba, sai da yakai zaune cikin kujera da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya dubesu. “Barkanku da safiya aunty kune a gidan namu?”.
     Sosai ransu ya sosu da salon rainin wayonsa su duka. Sai dai kafin wani yace wani abu a cikinsu Anaam ta fito ɗauke da tray shaƙe da kayan ciye-ciye da ruwa da lemo. Itama dai ta ɗanji wani iri na ganin nasa, amma saita fiske abinta ta ajiye tray ɗin a gabansu tana murmushi. “Aunty ga ruwa to....”
        A matuƙar harziƙe Hajiya Luba ta tura tray ɗin da ƙafarta tana ballama Anaam harara. “Tunda shine ya kawomu ba, k ki kama kanki wadda ta haifeki ma a tafin hanunmu take balle ke kanki...”
     “Juwairiyya bani lap-top dana bari a ɗakinki”. Shareff ya katse hargowar Hajiya Luba tamkar bai ji mima take faɗa ba. Tsamm Anaam ta miƙe batare da tace uffan ba, ba kuma ta kalli sashen da Shareff ɗin yake ba balle Fadwa ta ɗauka wayarta ta wuce bedroom.
         “Oh ke ko ga mahaukata suna magana dole ka sata aika. K! Fadwa shaƙomin ƴar iskar yarinyar can na nuna mata wacece ni dan ubanta”.
     Muƙutt Fadwa ta haɗiyi yawu da ƙyar a karo na biyu domin jin umarnin Aunty Sakina tamkar saukar aradu bisa kai. Ta ɗan saci kallon inda Shareff ke zaune a harɗe har yanzu kai kace baima san wainar da ake toyawa a falon ba. Kanta ta girgiza a hankali, so take tayi magana amma ta kasa motsa lips ɗinta sai kawai ta juya da sauri ta bar falon ma gaba ɗaya. (Tabbas Fadwa nada kurari da hayaƙi, amma kuma tanada tsoro bata cika iya jure hatsaniyar faɗa ba. Idan mai karatu bai manta ba kokuma ya lura da ƙyau zai fahimci Anaam ta fita tsiwa, saboda a lokuta da dama takan takaleta faɗa amma a ƙarshe Anaam ɗin ke tsigeta itako sai tai laƙwas. Tabbas a cikin raunanan halayanta wannan yana ciki rashin juriyar hatsaniya, a wani fannin kuma zamu iya kiransa haƙuri😜).
      Daga aunty Sakina har Hajiya Luba baki suka saki uwa sakatar sakarai dan al'ajabin Fadwa. “Oh ni Sakina ato lallai Fadwa

Download complete TXT · Novel page