*_Idan kinason ci gabada karanta wannan lbrn ki tuntubeni ta wannan number a WhatsApp_*
*_09013718241_*
*_Dont read this book if you are not married, Mature content contained in it, Reader discretion is advised, You read at your own risk._*
🅿 *1*
*_Bazanci gaba dasa number ba course masu fita dashi Allah ya isa kuma ban yafe ba duk wacce ta fitarmin da buk saboda bake kadai kika biya ba faqat_*
Da mugun gudu motar me qirar Ferrari ta shigo makarantar Adon Bayero University wadda suke Kira da new set birki ta taka da sauri tare da furta “ya Salam na bigeshi wlh na bigeshi rahama" tana fadin haka ta balle murfin motar ta fito da sauri wata kyakkyawar budurwa ce chocolate color wadda da gani babu tambaya kasan tanaji da kanta kuma tana tashen rashin kunya duba da yanayin shigarta.
Riga da wando ne farin jeans da jar riga three quarter ta hade gashinta na fulanin asali ta daure a baya ta dora wata hula me kamar nadin gammo a kanta tsakiyar kanta a waje ta zuba zobunan gold qafa da hanu sai daukar ido takeyi kamar walqiya duk wani lafiyayyen namiji idan yaganta a yanda take sai yaji yarr a jikinsa yanda take takawa duwaiwakanta na juyawa hips dinta yana daukan hankalin maza duk inda kyau yake Samha takai a kirata kyakkyawa.
Da dan sassarfarta ta qarasa ta tsuguna gaban kyakkyawan farin saurayin takai hanunta zata kamoshi ya kuwa daga hanu ya dauketa da wani lafiyayyen mari ta dafe gurin da sauri ta dago ta dubeshi