Saiku karanta din en barii kawe...... Khaleesat ta gama Laundry da take a kitchen ta fito, a reading nook din parlon ta tarar da Housemate dinta yana duba textbooks dinsa, cikin few seconds ya dau wanda zai dauka ya dawo cikin parlon yana kallonta yace "Har kin gama kenan" Kai kawai ta gyada masa ta fara tidying din parlon, rana na farko kenan da ta fara ganinsa yayi shiga irin ta Hausa cikin fararen kaya, Taji yace "Hope you are studying well Halysaah" kai kawai ta gyada masa, yace "Alright, till later" Ta ɗan kallesa tace "Are you Nigerian?" Ya buda ido yace "Why do u ask?" Tace "Kawai nayi zatan ko daga Chad kake, or Niger" Dariya yayi yace "Hope it's fine now tunda kin rama?" Hanyar dakinta ta nufa ba tare da ta basa amsa ba, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar parlon, sai bayan da ya fita sannan ta dawo cikin parlon ta tafi gun window ta ɗan bude drapery din jiki tana leka garage, ganin har ya tafi ta ci gaba da aikin da take yi a parlor. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat na kitchen tana girki at the same time suna waya da Abdul, tun 40 mins ago ya kirata suke magana har sannan, duk kwanan nan dai lafiya suke waya da shi, ya kuma ɗan rage mata wasu abubuwan da yake mata, he is being a little caring these days, a rana sai su yi waya sau biyu wani lkcn har sau uku har hakan na bata mamaki kamar dai ba shi ba, yanzun ma shi ne yayi encouraging dinta ta tashi ta fara girkin da take yi don bata yi niyyar girki ba, for weeks now kullum Housemate dinta ke masu takeaway na dinner wani lkcn har l