About this Novel

 

Story Preview

*FAKE DADDY*
_💞Mahaifin Bogi💞_

*Love and romantic story*


Mom Islam



Page 1-2


Ruwan sama na sauka a hankali, yana gangarowa kan gilashin ƙofar babbar fadar Sarki Sheyk Rayyan Al Kaito, attajiri ne wanda har hayakin numfashinsa kuɗi ne.
Shi ne mutum mafi ƙarfi a Japan, kuma duk wanda ya taɓa ganin fushinsa, ba ya son sake ganin sa.
Yau kam zuciyarsa a cike take da ɓacin rai,

"Ni mahaifinta..!!!"

Ya maimaita kalmar cikin ƙaraji,

"Ashe har akwai wata ƴar talakawa da zata danganta sunana da nata?"

Ɗan sandan dake tsaye a gabansa ya sunkuyar da kansa, yanajin kamar iska ma ta daina wucewa a hancinsa,

"B...Barkanka da Yamma mai girma sarki Yarinyar dai tace kaine mahaifinta, tana a offishinmu.."

Ɗan sanda ya faɗa ƙirjinsa na dukan uku-uku, saboda ƙafafunsa suna neman gaza ɗaukarsa, sakamakon wani irin kallo da Sheyk Rayyan Al Kaito yake yi masa,

Shiru ne ya cika falon,

Ana iya jin ƙarar agogon bango da yake bugawa, bayan shi babu wani sauti dake tashi a babban parlon masarautar,

"Ina buƙatar a kawomin yarinyar"

Cewar Sheyk Rayyan Al Kaito,

Ya faɗawa ɗan sandan muryarsa na ɗagawa cikin sauti mai ƙarfi,


Acan offishin ƴan Sanda, Hana ce a zaune, jikinta sai karkarwa yakeyi, idanunta sun kumbura sosai saboda kuka, sai dai har yanzu kalmar mahaifi da ta faɗa yana yawo a kunnenta,

Lokacin da ƙofar ofishin ta buɗe, iska mai ƙarfi ta cika gurin, ilahirin jami'an tsaron dake a zazzaune wasu suka miƙe tsaye saboda girmamawa wasu kuma suka durƙusa,

Hana ta miƙe tsaye, idanunta suka haɗu da nasa, id

Continue reading →

Reader Reviews

Login to leave a review.

No reviews yet — be the first.

Da Bazarmu Team

More Novels You May Like