Page 1-2
Ƙarfe goma na dare. Driving yake yi, cikin yanayi na damuwa gami da rashin walwala shimfiɗe a saman fuskarsa, Hannunsa dake ɗaure da agogon hannu yasa ya shafi sumar kansa, yana jan dogon tsaki mtswww, yaci gaba da driving ɗin yana tsaki lokaci-lokaci, wani wawan birki ya taka sakamakon yin ido biyu da wata ƙaramar yarinya da yayi wacce bazata wuce shekaru takwas a duniya ba, kuka takeyi iya ƙarfinta, tana tsaye a gefen hanya bakinta na fitar da jini, yayinda jikinta yake ta karkarwa, Habibullah ya haska ta da fitilar motar, kana yai parking a nesa da yarinyar, jiki a sanyaye ya ƙarasa inda yarinyar ke tsaye, cikin taushin murya yace "ke..me kikeyi anan?"
Bakinta na rawa tace "an...an...anty..an...ti.. Hanifah ce tace ina jirata tana zuwa, kuma har yanzu bata dawo ba"
Habibullah ya ƙarewa yarinyar kallo cikin tausayawa yace "meye sunanki, wacece Hanifah?"
Hawaye nabin kumatun yarinyar, sai rawar sanyi takeyi, kasancewar garin yayi sanyi sosai, dan ba'a daɗe da ɗauke ruwan sama ba, kuma har yanzu ana yayyafi kaɗan-kaɗan, yarinyar tace "Hurrah.."
Bai sake tambayarta ba, ya ɗagata cak ya rumgumeta a jikinsa ya sata a cikin mota, kana ya zagaya shima ya shiga mazaunin Driver, kafin ya yiwa motar key yace "zaki iya gane gidanku?"
Hurrah tace "eh" bayan yayiwa motar key, a hankali ya hau hanya, driving yake yi amma ƙirjinsa na dukan uku-uku, shi kansa ya rasa dalilin da yasa yake fuskantar hakan, sunyi nisa sosai, Habibullah ya ɗan juyo ya kalleta har yanzu tana rawar sanyin yace "wace