Showing 36001 words to 39000 words out of 63299 words

Chapter 13 - Auren Huce Haushi Book 2

13 Mar 2025

31840

ita ke Jan sitiyarin motar ai tasan ba'a banza ba tayi irin wannan cikowar tasan ta gane garin.
Sai a Nan Zahrar ke fada musu mahmud din ma baya kasar Yana India an Kai malaminsu Asibiti ya samu matsala a bayansa. Sun jajanta sosai, mayuka da turaruka Zahra ta basu, Aunty safiyar tayi mata Alkawarin kawo Mata wasu kayan Mata dasu tureren mara Mai fitar da oga daga hayyacinsa duk iya yanda ya Kai ga kame bakinsa, Amma Bata fada Mata hakan ba tasan halin kayanta sai taki amfani dashi.
Har gurin mota zahra da Aunty zilai suka rakosu, bayqn sun tafi ciki Zahra ta wuce wanka takeso Dan ki take kamar ya Bata Mata jiki.
Basu Dade suna Hira ba Zahra taga Aunty zilai tana hamma sai tace Mata taje ta kwanta kawai tasan har yanzu da sauran ramuwar barcin a idonta.

*********


Tun karfe shida na safe Mahmud ya wuce asibitin shida Mr salahuddeen, Saida ya jira doctor din yafi son ya Gama da doctor din kafin yaje gurin Baba malam misalin bakwai da rabi doctor ya shigo office dinsa be Jima da shiga ba mahmud ya shiga suka gaisa da yarensu na indianci, sannan yayi Masa bayanin yanzu takwas dai-dai zasu shiga dashi suna tunanin zasu dauki awa goma Sha biyu suna aikin Dan ma lakkar Bata tsinke ba. sallama sukayi ya nufi dakin da Baba malam din yake.
Lokacin da suka shiga har an shirya Baba malam cikin Kayan aiki.
Murmushi ya fara yi da yaga mahmud ya shigo.
Da sauri Shima ya nufe shi Bai taba jin karaya ba irin ta yau daya ganshi kwance sandam babu inda yake motsawa daga kugunsa zuwa kafarsa.
"Sannunka jarimin namiji, ubangiji yayi Albarka Mahmud ko yanzu Allah ya bani abunda bani dashi da namiji, kayi min komai Babu abinda zance maka sai godiya, idan Allah yasa na tashi falillahil hamdu idan Kuma lokacin komawar yayi to muna rokon Allah yasa mu cika da imani, ga Zainabu Nan Dan Allah a kula da ita, ga Kuma makaranta Nan Daman yanzu ni suna ne kawai na me makaranta, Amma kune ke dawainiya da ita, to kada a kasa ko bayan Mana Nan bamu San abinda ubangiji ke nufi da kawoka gurinmu ba shiya barwa Kansa sani, a kula da ibada da Kuma riko da gaskiya, Mai gaskiya baya tab'ewa kayi duk Mai yuwuwa ka koma mahaifarka Dan girman Allah a rage fushi kaji mahmud bashi da kyau ko alama ka Zama Mai yafiya kaima Allah ya yqfe maka kaji, Nima ka yafe min Zaman da mukayi Kona saba maka, Kuma ka rokarmin sauran jama'ar da muka zauna dasu Suma a fada musu na yafewa kowa Nima su yafe min, Abu na karshen da Zan fada maka ga yarinyar nan kaji tsoron Allah a Cikin lamarin ta nasha yin istikhara Ina ganinka a Cikin wata irin wadata Wadda na kan samu kaina da tunanin abun to duk yanda rayuwa ta juya ka kula da Amana ta Fadima marainiyar Allah ce".
Tunda Baba malam ya Fara Masa wannan magqngaun masu Kama da wasiyya jikinsa ke tsuma daga ciki Yana ta faman rokon Allah akan ya rufa Masa asiri kada bawan Allahn nan aikin ya Zama sanadinsa.
"Idon jajur da gani kukan zuci yake ya Kara rike hannun Malam.
"Baba in Sha Allah lafiya za'ayi aikin nan a Gama Kuma ka warke in Sha Allah saika taka da kafarka ka zagaya Asibitin Nan Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w, Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne ya bada nasarar aikin da za'ayi, ai sunce babu wata matsala Mai yawa dama mun zauna a Nigeria anyi aikin".
Kafin Baba malam ya fadi abinda yayi niyya ma'aikatan da zasu tafi dashi sun shigo da gadon da zasu tura shi zuwa theater room din, lokacin da zasu canza Masa gado ya ringa fadin.
"Wash!!! Allah kuyi a hankali bayana bana son ana motsani" .
Da sauri Mahmud ya karaso Yana musu magana da yarensu, da sauri suka mayar dashi suka fita.
Sannu kawai mahmud ke jerawa Baba malam Nan da Nan jibi ya rufe shi.
Kusan mutum bakwai suka shigo suka hadu aka Dora shi a gadon sannan suka tura shi a hankali suka fice daga dakin mahmud na biye dasu, har kofar karshe mahmud ya raka baba Malam Bai tsaya ba saboda dauriya kawai yakeyi Amma Yana Daf da zubar da hawaye.

Guri ya nema ya zauna Yana kallon yanda manyan doctors manya da kananu suke Kai kawo kafin time ya cika suka rufe kofar.
Yana Nan zaune har kusan one hour sannan Kiran Habib ya shigo Masa.
Cikin dari dari Habib ya Fara fadin.
"Yallabai ya maganar zuwa Asibitin ne munji shiru baka fito ba tun bayan da muka dawo daga sallar Asuba".
Tsaki mahmud yayi dama duk ransa ba dadi ga wani sabon salon da Habib ta tarka Wai yallabai.
"Wallahi ka Kara kirana da wani yallabai sai munyi uwar watsi a kasar nan da Kai,ba dai ba barci kuzoyi ba sai kuyi tayi, yanzu Baba malam ya samu good one hour a dakin tiyata, zaka wani ce min maganar Asibiti,kaima wallahi inaga saina kaika Inda zaka Kwana a tsaye kana aiki ko Abinci sai dai kaci a tsaitsaye sannan zaka fashinci namiji Allah yayi ka, ka fadawa dayan ya kawo ku yanzu Ni tun shida Ina nan".
Ya yanke Kiran ya dafe goshinsa da yake Sara Masa.

* *

Karfe bakwai da rabi dai dai Mai a dai daita ya sauke Salma a kofar katafaren gate din gidansu,kudin dake hannunta ta Mika Masa ta wuce da sauri ta shige ciki, ba kowa a harabar gidan ko Mai gadi ma ya shiga sallar insha'i.
Wuf tayi ta shige part din Mama cikin sa'a babu kowa a cikin parlourn directly master bedroom dinta ta wuce, can ta hango Mama ta Zuba tagumi tana zaune duk tayi zumu ba wannan gayun da kwalisa, tunda ta rasa tudun dafawa a Kan sakon da za'a kaiwa Zahra ta shiga halin ha'ula'i tunda Saida aka gindaya mata sharadi ta amince gashi kuma kwabarta na neman yin Ruwa.
Ganin shigowar Salma ko sallama babu yasa Mama ta wani zabura ta taso tana fadin.
" Ke!!! Salma lafiya? Daga Ina kike da wannan tsohon daren? Ina Hameeda Kuma?".
Zama tayi a gefen gado tana sadda Kai kasa tayi shiru.
"Wai ba magana nake Miki ba Dan ubanki kin mayar Dani banza".
Kuka ta fasa Mata Mai cin Rai, Wanda ya firgita 'yar sauran nutsuwar Mama.





[16/02, 8:31 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*


08055362975

09061432330

MAMAN FATEEMAH.

Page 70.

.........…..
Luggage din da Zahra ta aje matar ta dauka tana fadin "taso mu shiga,wallahi nayi loosing control dina ne wallahj abun ne da mamaki ban taba tunanin Zan ganshi a irin wannan lokacin dana hakura na sallama".
Jiki ba kwari Zahrar tabi bayanta suka shige ciki, a zaune suka same shi, yaron yana lik'e a jikinsa ya lafe sai Karamar da yake yiwa wasa tana balbala dariya Kamar ba yanzu ta Gama tsandara kuka ba.
Suna shiga matar ta karasa inda ya zauna tana fadin.
"Yanzu ina alkwarin mu? Haka mukayi alkawari da Kai, ka bace bat a cikin duniya ka manta da kowa? Ba waya ba sakon Email? Wallahi ka dauki Alhakin Ammi ba kadan ba, kasan yanda Hajiya Inna ta rude kuwa? Abbie ma ba karamin tashin hankalin ya shiga ba, da farko ya dauka fushin 'yan kwanaki ne Saida yaga tafiyar ta mik"a yasan da gaske ne, har nan ko ya taso takanas ta kano, Wai yasan ko baka fadawa kowa in da kake ba yasan ni dole nasan inda kake".
Hannu ya daga Mata.
"Pls Aisha Dan Allah ki rage surutu, kin bar yarinya a tsaye ki kaita daki ta huta kinsan long journey din da tayo? Ki tayata shiga da kayanta zata nuna Miki abinku na Mata da bakwa iya tafiya Saida tsaraba".
Wata harara ta wurga masa.
"Ai duk Kai ka jawo na manta da ita, sorry sister kinsan abin ne da al'jabi wallahi twins dina ne yayi batan dabo a duniyar nan, nayi kukan rashinsa har naba uku Lada, zo muje".
Wata ni'ima Zahra taji tana shiga jikinta, sai lokacin ta Kare Mata kallo kamarsu Daya Dan dai shi namiji ita mace.
"I am coming".
Ta fada tana haura stairs da sauri.
Tana bacewa ganinsu ya juyo Yana kallon Zahra.
"Precious".
Bata amsa ba Amma ta dago tana kallonsa kafin tayi magana Aishat ta sauko da sauri da keys a hannunta.
"Muje ko bakuwa ni ko introducing dinki Bros Bai yi min ba".
"Kije ki rakata Mana tunda na kawo Miki ita ai magana ta Kare, diyar uban gidana ce Bata da lafiya ne zataga likita, sannan malamina ma Yana Nan anyi Masa aikin spinal cord ne da sauran fractures Daya samu.
Ya fada Yana fuskewa.
Daki ne comfortable yaji komai, na bayan more rayuwa.
Aisha Bata fita ba Saida ta Taya Zahra saka komai a muhallinsa sannan ta fito.
Zama Zahra tayi a gefen gadon tana nazarin maganganunsa, me yake nufi da diyar uban gidansa, Amma zata raka shi taga iya gudun ruwansa Shima namiji ya iya danne abunda ke ransa bare ita mace.
Aishar ce ta Kara shigowa da tray an dora snacks da Ruwa da drinks.
Da murmushinta ta karaso tana fadin.
"Ashe Fateemah ce, sannu da hanya zahra, ya jikin naki nagi Bros yace Baki da lafiya, Ni Sunana Aishat Muhammad Dange, twins din Al-husasain".
"Masha Allah, Aunty nagode kwarai sannu da kokari".

"Lah ba komai, ki Sha ruwan kiyi sallah saiki fito lokacin an shiya muku abinci"
Sallar zahra tayi ta Jima tana addu'ar neman mafita daga wata sabuwar rigimar da take hangowa.
Nan Kan sallayar ta Dan kwanta barci yayi awon gaba da ita.

****
Zaune suke Yana cin abinci ita Kuma tana duba sakonni whatApps har zata wuce salon Faisal saita dawo saboda Basu fi minti goma da Gama ways dashi ba Yana Mata magiyar ta turo da kudi suyi sarin Kaya, ta nuna masa ya jirata zasu shigo ganin jikin Abban nasu sai ayi abinda ya kamata, sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta akan ta duba ita me majiyyaci ai share sako ba nata bane.
Ta maimaita karanta sakon ya Kai sau biyar tana ganin kamar ba gaskiya bane.
Dialing din number Faisal Aunty Surayya tayi, Yana dauka Bata jira komai ba ta jefa Masa tambaya.
"Shin text din daka turo min gaskiya ne".
"Eh wallahi Aunty ko jiya ma yazo gurin Abba mantawa nayi na fada Miki bakiga yanda yake kula da Abba ba kinsan har daki ya canza Mana mantawa nayi na fada Miki ayi Mana godiya gurin Auncle Mustapha".
"Ok shi kenan ina zuwa".
Ta fada tana yanke Kiran.
Auncle Mustapha ta juya tana kallo Wanda Shima ita ya zubawa idanu, batace Masa komai ba sakon ta bude ta Mika Masa.
Yana Gama karantawa ya dago da sauri yana neman Karin bayani.
"Nima shine na Kira Faisal din ya bani tabbacin haka ne, Wai ya Kai wani Babansa ne".
Spoon din ya aje ya mike ya zari hularsa da key din mota ya fice, Surayya na Masa magana hannu kawai ya daga Mata yayi gaba.

Duk yanda Aishat taso mahmud ya Bata hadin Kai suyi magana ya Kiya yace ta Bari sai dare zasu zauna suyi magana sosai.
Abincin ta shirya a table ta nufi dakin da zahra take, samu tayi barci ya dauketa a saman sallar da tayi sallah, Bata tasheta ba dawowa tayi tana fada Masa tayi barci da alama ta gaji.
Shida Abulkhairi sukaci abincin, yayin da Aishat ta dauki Afnan Wadda tayi barci ta haya da ita sama.
Kamar jira ake ta shiga bedroom dinta Kiran sweet heart ya shigo.
Tana dauka ya Fara fadin.
"Sweetie Ina Mahmud din yake Dan Allah?"
Saida taja fasali sannan tace Masa.
"Yana down stairs, wallahi sweet heart kamar Almara nake ganin abin duk na rude Dan Allah kazo kada ya Kara tafiya... Yace matukar na fadawa Abbie ko Ammi Bazan Kara ganinsa ba".
Ta fada tana share hawaye.
"Cool down your temper my sweetie Babu inda zaya, ban tsoro ne kawai yake miki yasan idan yayi Miki haka bazaki fadawa kowa ba, ki jirani zuwa gobe da safe in Sha Allah, ki daina yi min asarar hawayenki a banza, a gurina suna da mahimmanci , ki kyaleni dashi yanzu basai an Jima ba zanyi informing din Abbie gara ayita ta Kare tunda shi Abu baya wucewa a gurinsa".

"Gaskiya dai Kam ki shiga cikin Lamarin kuyi Masa taron dangi, kasan da wata yarinya yazo Wai 'yar gidan uban gidansa ce ya kawota Asibiti, nifa I doubt much akan yarinyar Nan kasan dai halinsa baya sabga da macen daba muharramarsa ba ya kake ganin ze dauko yarinya mace kamar wanna ka ganta kuwa? Allah Ina Jin ta hada iri da Larabawa Dan she is very young and beautiful".
"Just ka bishi a yanda yake so idan na shigo zamu Yara da yaren garinmu rabu dashi".
Basu wani Dade ba yayi Mata sallama Yana Kara kwantar Mata da hankali akan tunda ya kawo kafarsa har gida in Sha Allah komai yazo karshe.

A mota uncle Mustaphan ta karaso gidan duk da babu nisa Amma sai yaga idan yace ze tako a kafa kamar baze zo ba.
Directly part din Ammah ya nufa Don baya son maganar ta fita tun kafin su tabbatar da abunda aka fada, very lucky ya samu yayan nasa general a part din.
Batool ya bude Masa kofa ya shigo tana gaishe shi.
Ya amsa Yana fadin.
"Ina Abbie Amminku take?".
"Tana part din Abbie na cikin nan".
Ok, Bari na kira shi"
Ringing Daya ya dauka Yana fadin.
"Ko Ina kake Mustapha maza kazo Ina son ganinka ina kokarin kiranka naka Kiran ya shigo".
I
"To ai gani a part din Ammi Nima neman ka nakeyi".
Ya fada yana nufar kofar baya yabi corridorn da ze sada shi da part din General din".
Yana shiga da sallama a bakinsa yayi turus ganin Ammi tana shafe hawaye, a sanyaye ya karasa cikin parlourn.
"Lafiya! meya faru?".
"Zauna Mustapha yanzu ne Abbas ya kirani daga Jamaica inda yaje aikin da nake fada maka, wai Aishat ta kiwo shi ga Dan uwansa yazo Yana tare da ita".
Neman guri uncle Mustaphan yayi Yana tabbatar da gaskiyar maganar Faisal.
"To ai Nima abinda ya tasoni kenan na taho, kasan Alhajin su Surayya Yana can Indian an sake Masa gyaran kafa shine suka hadu da mahmud din yaketa dawainiya dasu shine ya fadawa surayyar tayi min godiya kasan ba kowa ne yasan case din da ya faru ba kawai dai an wayi gari ba'a ganinsa duk da zancen duniya baya buya nasar Surayya Bata fada musu komai ba gaskiya, Ammin Yara ki daina kuka ko lokacin da ake cikin tashin hankali ba Wanda yaga hawayenki sai yanzu da asking ya I gaban gashi".
Share hawayen tayi tana fadin "
dole nayi kuka ni kadai nasan dacin Dana ci a lokutan baya da dararen Dana Raya akan ubangijina ya dubi Lamarin yaron nan ya juyo min da hankalinsa gida".
"To godiya ya kamata ki yiwa Allah Daya amshi addu'ar ki ba kuka ba".
Wani murmushi general yayi yana duban Mustapha.
"Ni bansan lokacin data aje karar 'ya'yan fari ba da ko me zakayi musu Bata daga Kai ta dubeka amma yanzu dibi yanda take Kora bayani Kamar ba ita na".
"Kan barta tayi Yaya ai taking jarunta ma ba uwa duka ba, yanzu Yaya kenan za'ayi? Da nida madam zamuje next week amma dole mu raba tafiyar a yau Zan shiga neman visa ko nawa Zan bayar saina samu nan da jibi in Sha Allah Zan tafi Indian Zan kadi shi mu taho gida da izinin Allah. Amma dan Allah kada a fadawa Hajiya Inna wallahi idan taji cewa zatayi kafarta kafa ta".
"Kaje kayi shiri zanyi magana akan visar taka, ka Zama cikin shiri kawai".
Tashi Ammi tayi ta shiga ciki ta barsu suna tattaunawa akan Lamarin.

*****
Saida zahta tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, wanka ta shiga tana fitowa lokacin magariba ta kusa kawo jiki, tayi mamakin dogon barcin da tayi.
Lotion kawai ta shafa sai roll-on da tasa sure sai body midt da normal turaruka da take amfani dasu designers na kamfanin Alharamaini, rigar atamfa ta saka simple style A shape ta yafa Karamin gyale sai tayi wani sansanyan kyau, a hankali ta bude kofar ta fito tana takunta gentle ta shigo parlourn Aishat ta gani a zaune da Abulkhairi a gefenta tana koya masa homework, kafin tayi sallama har sansanyan kqmshinta ya jewa Aishat.
Dago Kai tayi tana amsa sallamar da Zahra tayi.
"Masha Allah!"
Abinda Aishat ta fada kenan Dan babu karya yarinyar ta hadu ta ko Ina macece ga asalin kyau Dan gaske, murmushinta Mai kayatarwa zahra tayi Mata tana fadin.
"Sannu da hutawa Aunty".
Hannu Hanan ke dagowa Zahra tana zillo daga cinyar mamanta.
Daukarta tayi tana Zama daga dayan gefe Kan wata kujerar.
"Yauwa sannu, Zahra ko?"
Kaita gyada Mata alamar eh.
"Kinsha barcin gajiya, ga abincinki can Kan table muje kici kin kwanta da yunwa, bro yace na fada Miki yaje Asibiti sai dare ze dawo".
"Ok, nagode kiyk zamanki Bari muje da 'yar gidana Aunty ki bani ita Dan Allah Ina sonta".
Dan murmushi tayi idan mijin da Zaki aura ya amince ki dauka Ni tawa Mai sauki ne na Baki".
Gaba tayi tana dariya kasa-kasa ta nufi dining din save da Afnan.


Sun Dade suna Hira da Aunty Aishat har barci ya Fara Kama Zahra sannan tayi Mata sallama ta nufi inda akayi Mata masauki, bayan ta wuce Aishat da Dade tana auna Lamarin Zahra a zahiri Sam batayi Kama da yarinya marar tarbiyya ba ko masu budedden idanu Amma tayiwa tafiyarsu da Dan uwanta Question mark, idan ta tuna da irin warning din da yayi Mata kafin ya bar gidan.
"Gata Nan amanace a gurinsa shi yasa na kawo ta Nan inda zata zauna safe, ki kula sosai nasan halin sayyid a Kan mata duk da kince yayi tafiya to Koda za'a samu akasi yazo bana nan, to ki fada masa yarinyar nan da mijinta Dan muna komawa za'ayi bikinta ya dauke idonsa daga kanta idan Kuma ba haka ba za'a iya samun matsala.
"Maji ma ganj, an binne tsohuwa da Rai"
Ta fada a fili.
A Nan taci gaba da Zama tana jiran ta inda Dan uwanta ze bullo, wurin Sha Daya da minti goma ya bude ya shigo gidan, ya yi mamakin ganin Aisha Ido biyu.
"Ashe dai Hali yana nan, yanzu Dan Allah bakiyi barci ba".
"Naka wasa ne kana tunanin Zan iya barci banji komai daga gareka ba Nima ban Amayar maka da abinda ya faru bayan baka nan ba".
"To ai shikenan Bari nayi wanka na fito inaga kwanan zaune zamuyi yau".
Ya shige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login