SO DA BURI BOOK 2

Chapter 19 of 39

wanda yake sa mana ido yana gayawa wani Abokin shi wai ‘kar a had’a mu da kowa Granpa d’in yayi waya yace a ware mu.’
Inaga yana gudun kar wani ya gane mu ne.

Amman fa kin san zancen duniya ba ya b’uya, wacce irin kunya kike tunanin zamu kwasa idan k’awayenmu sukaji labari?”.

Ajiyar zuciya Mom ta sauk’e kafin tace
“Shikenan ba damuwa, amman kinada tabbacin ba zata kwab’e mana ba ko?”

D’aga mata kai kawai tayi alamar ‘eh’

Shikenan nima zan gwada yiwa Auwal magana, inaga maybe ya taimaka, dan
naga kamar abun ya dameshi.
In kuma yak’i, to ko sark’ata ce zance ya duba ya d’auki d’aya ya saida sai ya kawo kud’in”
Cewar Mom.

“Allah ya shige mana gaba”Mammy tace
Daganan suka ci gaba da maganganunsu, ita kam Ummi tun d’azu bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, ata dalilin allurar da akayi mata.....


Tabbas su Ummi basu kyautaba amman a nata tunanin bai kamata ayi musu haka ba! Hukuncin yayi yawa kuma abunda akai musu d’in tabbas zai jawo mata bak’in jini a wajen y’ay’ansu ne, besides ita tama yafe musu har k’asan zuciyarta……

Tana waennan tunanin suka isa munjibir park, sun sha doguwar tafiya ba kad’an ba, ita Huda jikinta ma duk ya fara ciwo.

Parking yayi duk suka fito, sai da ya gama komai ya siyaawa Sudais ice cream d’inshi, ya d’aura shi a lilo tukunna ya dawo inda take tsaye.
Kallonta yayi kafin yace “Ko kema lilon kike son hawa k’atuwa dake??”
Kauda kai tayi ta girgiza kai, kawai.

Murmushi yayi kafin yace
“Ta kwancen, itace wacce aka saki Mamanki a dalilinta! Matar Abbanki har a yanzu.”

Taji zafin maganar amman ta shareshi kawai…

“Wadda ta bani sak’o kuma, na san daga maganar da tayi mini kin fahimci Mahaifiyar Arshaad da Aaima ce!

D’ayar kuma Mom d’ita ce!

Ummi, ko dan su Sudais da kike pretending kina so, ya kamata ki tausaya mata.

Mammy kuwa ko Arshaad ya kauda kai saboda son da yake yi miki, to ina tausaya miki In Aaima ta dawo dan sam ba za kiji dad’i ba at all.

Mom d’ina kuwa, to be sincere ba ma wani shiri da ita, but blood is thick!
And you should know me by now
I’m capable of anything..

Huda! All you need to do
Is talk to your stubborn father
ya san abun yi…
Idan ba haka ba kuma
Wallahi!
Ni kaina ina jin tsoron abunda zan yi miki!…

A matsayin ki na so called cousin d’ina yasanya nayi
deciding in baki warning first akan in aiwatar da abunda nayi niyya akanki kai tsaye.

Idan kika yi min abunda nakeso to kin tsira
In kuma kika yi taurin kai!
To fa gaskiya i can’t save you from me.

Lastly, kar ki kuskura kiyi mentioning cell d’in da kika je yau, to anyone.”
Ya k’arashe maganar yana kallon cikin idonta.

Da sauri tayi k’asa da kanta…
Tabbas ta hango b’acin rai a cikin idanuwanshi, gashi har colour d’insu ya soma chanza wa.

Bud’e baki yayi zai yi magana yaji an dafa shi ta baya.
Kafin ya juya ita ta zxagayo gabanshi ta tsaya tsakaninshi da Huda.

Murmushi yayi kafin yace
“Har kin iso?”
Yayi maganan yana mai rik’o waist d’inta ya d’an jawota jikinshi.

Yadda Huda ta zabura zaka d’auka ita aka janyo..

D’an jaa da baya budurwar tayi ta d’an juyo tana kallon Hudan kafin tace
“Who’s she??”
Tayi masa tambayar ba tare
data kalleshi ba, da d’an alamun b’acin rai a fuskarta.

Murmushi yayi kafin yace
“Relax! She’s just a cousin, daga k’auye tazo shine Daddy yace In kawota ta ga gari.”

Ture hannunshi da yake rik’e da waist d’inta tayi, har yanzu idonta nakan Hudan wadda ita ma ta kasa d’auke idanunta akan su tana kallon ikon Allah, budurwar tace
“Cousin and more, ha?”

Dariya sosai yayi this time around kafin ya matso da fuskarshi dede tata tukun yace
“If she’s cousin and more would I do dis in front of her?”
Ya k’arashe maganan da kissing lips d’inta lightly…..

Da sauri Hudan ta bar wajen tana had’a hanya.

Kujerun data gani a gefe chan taje ta zauna tana haki tana istighfari.

A chaan wajen su Auwal kuwa murmushin jin dad’i budurwar tayi sannan suka shiga sabgogin gabansu..........

A tap d’in wajen tayi alwala, wasu mata manya ta gani da darduma sun shinfida k’atuwa suna zazzaune ga kuloli alamun picnic suka fito, dan haka ta k’arasa tayi musu sallama tace
“Dan Allah tanaso za tayi sallah”
Da fara’a suka tarbeta suka matsa mata d’ayar ta fiddo hijabi a jakanta ta bata..
Bayan ta idar suka yi mata tayin abinci, gorar ruwa kawai ta d’auka ta sha tayi musu godiya a wajen ta ci gaba da zamanta a wajen, tana hango Sudais yanata wasanshi, chan gefe kuma Auwal da budurwarshi an cika musu gaba da kayan kwalama kala kala amman ita ko ruwan sha ya kasa bata…
Ganin bata da abunyi yasa ta bud’e wayarta ta hau karatunta ragowar ruwan da ta sha d’an mitsitsi ta rage ta tofa a ciki..

Sai da aka fara kiraye kirayen sallar Magrib tukunna taga ya taso…
Yana tasowa ta mik’e ta hau sallarta dan ta lura In suka kama hanya yanzu sai sun kusan 40min suna tafiya.

Takaici, kamar ya kifa mata mari haka yaji, ba yadda ya iya shima yaje yayi alwalla yayi iya magribar d’in daya tarar maza sunyi jam’i suna yi.

Tare suka jero da budurwar da Sudais da yaje ya d’auko, suka nufota.

Sallama da godiya ta yiwa matan da suma suketa shirin tashi, ta rik’e hannun Sudais wanda ya iso gareta da sauri suka nufi inda suka yi parking.

Sai da ya k’araso ya bud’e motar tukunna suka shiga
Ita da Sudais suka zauna a baya shi da budurwar suka zauna a gaba.
Sai da suka biya wani gida a lamido crescent flat mai kyau suka ajjiyeta tukunna suka wuce…Abunda ya d’aurewa Hudan kai shine shi Auwal d’inne ya bawa budurwar makullan gidan!

Ita dai batayi magana ba, ta yi shiru kawai tana mamakin shi..
Ko da yace wani ya koma gaba, Sudais ta matsawa ya tsallaka.


A gajiye suka isa gida yana ajjiye su yayi reverse ya sake fita.

A parlourn ta tarar da Arshaad
wanda suna dawowa daga kai Amarya ya had’u da Aslam cikin hira yake gaya mishi ‘Hudan sun fita munjibir da Auwal!’
Ko wanka kasa yi yayi ya taho gidan…
Yana tunanin bin bayan su kenan suka shigo.

Ajiyar zuciyar daya sauk’e lokacin da suka shigo sai da taji, sarai ta lura dashi amman ta d’auke kai tayi wucewarta….ganin yadda ta bawa iska ajiyarshi kuwa hakan yayi mugun bak’anta mishi rai!
At least in tana jin haushinshi ai ko darajar kallo yaci ace ya samu.


Sai da ta raka Sudais d’akin shi tukunna ta nufi side d’inta.


Tana shiga parlourn ta saki jakarta ta tafi da gudu tana ihun murna.
Rungume juna sukayi suna dariya kafin tace “tun yaushe kika zo?”
Dariya itama Sakina tayi tace
“D’azu Abbas yaje da kanshi ya d’auko ni hala ke kikayi mishi kwatance ko?”
“Eh” tace
tana sake hugging d’inta, sannan ta jata suka nufi bedroom.

“Ma shaa Allah,
Ubangiji mai zamani”
Sakina tace.

Sannan tace “gaskiya wajen nan ya burgeni Huda, over!!
Ina tunanin had’uwar parlourn ashe bedroom d’in har ya fishi? “
Murmushi Hudan tayi tace
“Ni kuma duk toilet d’in yafi burgeni” da sauri Sakina tace “muje In gani” ta fad’a tana cire hijab d’in jikinta dake nan har k’asa.
Suna shiga nan itama tace “gaskiya kam toilet d’in duk yafi had’uwa”
Haka nan suka taru suka dinga hauka, daga su kunna wannan sai su kashe wannan, wani abun ma ba iyawa suka yi ba da karambani suka koya. Babu abunda yafi burge Sakina irin closet dan haka ta fito wajen tana kuma setawa Hudan zaman kayanta kafin ta fito a wanka.

Bata wani dad’e ba ta fito a wankan
tana fitowa tace “itama ta shiga tayi wanka sai ta chanja kayan jikinta, lace d’in zai yi mata nauyi dan garin ana zafi sosai”
Murmushi Sakina tayi kafin tace “Ni fa daga ni sai hand bag d’ina nazo, Ummu daa hanani zuwa tayi fa, sai da Baba ya bud’e mata wuta!Amman tace wai gobe da safe in dawo, har na d’auko kaya set uku tace wai In na tafi da kaya ba zan dawo da wuri ba!
Shi kuma Baba yace tunda Abba ne da kansa ya rok’esa to sai lokacin da kika saba da nan d’in tukunna zan koma!.

Wallahi tun d’azu jikina a sanyaye yake, Mama ma bata san na taho ba, dan Ummu tace bata san da wanne ido zata kalle ta ta fad’a mata ba!
Shinema dalilinta na hanani zuwa tun farko daman.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace
“Ranar dana tafi ya aka yi? Ina ta kiran Ummu bata d’auka.”

“Hmm..
Mama ce ta rikita kowa wai Abba ya aiko an sace ki!
Amman har yanzu a haka su Ummu suka barta basu gaya mata ke kika tafi da kannki ba saboda kar taji haushinmu, kawai dai ance mata kina nan d’in so ta kwantar da hankalinta tunda kina wajen Mahaifinki ne ba wani mugun hannu ba.”

Hawaye Hudan ta goge kafin tace “Sakina wallahi ni ban san ya zan yi ba” ta fad’a tana fashewa da kuka, rungumeta Sakina tayi kafin tace “wallahi Huda ni kaina abun nan yana daure min kai, sai ka rasa ina zaka tsaya, gaba d’aya ni kaina i’m confused, ballantana kuma ke.
Muyi ta addua kawai ki kwantar da hankalinki, kinji?Please”.

Hawayenta ta goge jikinta duk yayi sanyi, sannan ta d’an d’aga kanta
a hankali kafin ta cewa Sakinan “kije kiyi wanka sai ki sa kayana
Inner wears kuma ina da sababbi suma, muyi
sauri dan na san yanzu Abba zai fara kira, lokacin dinner yayi.”

Hijab d’inta wanda ta ajjiye a bedroom Hudan ta fita ta d’auko ta wuce ta sa a washing machine ta fito ta bata towel,
Ita ta tayata wankin dan sai da ta tayata ma shanya kayan data cire suka wanke d’in tukun ta fito ta barta dan tayi wankan.

Sallah ta tarar Hudan tanayi lokacin da ta fito dan haka itama ta nemi hijab ta tayar da sallar.
Sauranta izu d’aya a izu goman daya kamata tayi, dan haka ta hau karatu bayan ta idar….
Tana idarwa tayi addua ta tofa ta had’e ruwan d’azu data shigo dashi dana d’akin waje d’aya!.
Da mamaki Sakina ta kalle ta kafin ta tambayeta
Bayani ta hau yi mata a kan ‘na maman Aslam ne wanda ta basu labarinta….’
“Allah sarki Allah ya bata lafiya, abun tausayi wallahi”
Sakinan tace.

Kayan bacci dukkansu suka sanya, sai suka d’aura hijabai a sama, sannan suka sauk’a dan Abba har ya kirata kamar yanda tayi tsammani.

Sai da ta lek’a d’akin su Sudais, ganin basa nan yasa suka nufi k’asan.

Har Aslam suka tarar a dining d’in da Arshaad amman yanzu ya chanja kaya wanda hakan ke nuni da wanka yaje yayo.

Yaji tahowa amman bai d’ago ba, dan babu abunda yake sosa mishi zuciya irin yadda ko kallon inda yake bata yi.

Sai da suka k’araso tukun Abba yace “a’a inyee! Yau ga annuri a fuskar princess, duk a dalilin Sakina, irin wannan murmushi haka?!”
Ya fad’a yana murmushi
kafin yace “bismillah ku zauna mana”

A hankali suka fara k’ok’arin jan kujera…
Yana shirin d’agowa ya ga da gaske Sakinan ce jin abunda Abba yace, yaji tace “Ya Arshaad Ina wuni.”
Da sauri ya d’ago, ya d’an zaro ido alamun mamaki, sai
kuma ya fara murmushi yace
“Lafiya, Alhamdulillah.
Ashe kece da kanki!
Welcome, ya gida?”

“Alhamdulillah” tace kafin ta d’an turo baki tace
“Ai gani nayi da farko ka wani had’e rai ko kallon inda muke ma bakayi ba”
Dariya yayi kafin yace
“Hankalina baya wajen ne,
sorry”
Itama murmushi tayi ta sake gaida Abba da Aslam wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba!
Tunda suka sauk’o ma ta lura bai ko kallesu ba…
Tana ganinshi tashi d’aya ta fahimci shine Aslam.
Lokacin da Hudan take zuzuta mata kyawun Aslam d’in bata yarda ba, dan har ta fara tunanin wani abun a tare da Hudan na daban,
but yanzu kam tagani itama!
“Tubarakallah!”
Ta fad’a a k’asan ranta.

Cikin nutsuwa taji Hudan suna gaisawa da Abba wanda yake zaune a opposite d’insu shi da Aslam. Da kulawa yake tambayanta hope taji dad’in ganin Sakina? Is she happy now? Taji dad’in zuwa munjibir park d’in? Ba wata damuwa ko?……
Murmushi Hudan tayi duk tana ta binshi da “Alhamdulillah komai Alhamdulillah..”

Abun yayi matuk’ar burge Sakina a ranta tace “yau ina Baba da Umma suzo suga gatan da akewa Huda, suga yanda Abbanta yake janta a jiki yana lallab’a ta”
Wani farin ciki ne taji ya lullub’eta, tabbas tana yiwa Hudan murna da baiyyanar Mahaifinta!
Itafa sometimes ji take a ranta kamar ma tafi Hudan farin ciki.

A hankali taji sun gaisa da Aslam, taga ita Hudan ta d’an samu darajar kallo a wajenshi tukunna yace “lafiya” da d’an mitsitsin bakinshi.

Har an fara serving ta mintsili Huda da k’arfi ta k’asa k’asa inda ba za a gani ba.
“Ouch” tace, a hankali sannan ta juyo tana kallon ta, harara Sakina ta zabga mata k’asa k’asa tace “shi ba zaki gaidashi ba???”
Itama Hudan hararar ta maida mata ta cigaba da zuba abincinta!
Mintsilinta Sakina ta sake yi, kafin tace
“Wallahi ko ki gaisheshi ko kiyi ta karb’ar ruwan mintsili kala kala!”
Dai dai nan wayar Abba tayi k’ara …
Excusing kanshi yayi ya mik’e ya d’an koma gefe yana amsa wayar dan it’s a very important call ba zai yiu yayi ignoring ba.

Kamar jira Sakina take, nan ta sake sakar mata wani sabon mintsinin da sai da tayi k’ara mai sauti sosai this time around har su Aslam sai da sukaji suka juyo suna kallonsu…
Sudais kuma ya fara kyalkyala dariya dan shine a kusa da Sakina yana kallonta tun d’azu!

Ganin da Huda tayi Sakina ba zata hak’ura ba yasa ta juya, kujera biyu ne tsakaninta da Arshaad d’in dan haka ta d’an kalleshi tace “ina wuni”
Sai da ya sake tamke fuska tukun yace
“Lafiya”
Yanajin haushi a ranshi, wato gaisuwar ma sai ta ga dama zata yi, kuma shine na k’arshe! Har su Sudais sai da ta gama kulawa tukunna shine last!

Tashi Sakina tayi daga kan kujerarta ta dawo ta gefen Hudan side d’in da Arshaad yake ta zauna kafin tace
“Am i missing something here???”
Tayi musu maganar tana juyowa ta kalli wannan ta kalli wannan.

“Eat!”
Arshaad yace sannan yaci gaba da cin abincin shi.
Dawowar da Abba yayi ne ya katse mata maganganun da suka taso mata don haka tayi shiru…
Luckily aka sake kiran Abba a waya dan haka ya mik’e yace “bara ya shiga wajen Daddy”

Ba a jima ba Aslam shima ya mik’e, da sauri Hudan ta mik’e ta mik’a mishi Goron ruwan hannunta
Opposite yau ma suke dan haka ya kalle ta yace
“thankyou!” a hankali yana kallonta.

Bata san daliliba! Dan kwata kwata sam sai ta kasa janye idanunta daga nashi. Tunda Mama ta kawota duniya ko a tv bata tab’a ganin kwayar ido mai kyan nashi ba! Shape d’in Idon kansa abun son ka kalla ne! Komai na idanun nasa masu kyau ne
Itakam wata rana zata tambayeshi ‘me yake shafawa eyelid d’insa?’ Dan wani haskene yake fitowa daga wajen .....
Dukda yadda zuciyarta ta tsananta bugu hakan bai sanyata ta d’auke idanunta daga kansa ba kuma baisanya ta sakar mishi robar ruwan da ta mik’a masa ba!

“GOOD NIGHT Sakina!!”
Suka ji Arshaad ya fad’a da d’an k’arfi!

Da sauri Aslam yayi firgigit, ya janye robar da mugun k’arfi, sannan ya juya yayi hanyar fita. Har ya fice daga parlourn bai yarda ya sake juyowa ba.

Hudan ita kam kunya ce gaba d’aya ta lullub’eta.. Ashe har Arshaad da Sakina sun mik’e
su shuraim kuma suna shirin fara hawa bene ita bata ma sani ba!.

Yana shirin barin wajen Sakina tace “pls mana”
Tana d’an karkartar da wuyanta.

Murmushi yayi yace
“she’s busy rn, let it go kawai.”

A hankali Sakina tace
“Plss”
Tana had’e hannuwanta biyu waje d’aya alamun rok’o.
Ajiyar zuciya ya sauk’e ya d’an ja ya tsaya.

Hudan na ganin wucewar su Shuraim sama ta juya itama zata bar wajen.
Hannu Sakina tasa ta rik’eta.
Ba tare data juyo ta kalleta ba tace
“Sakin mani hannu plss, bacci nake ji”

Jin abunda tace ya sake tunzurashi
don haka kawai ya fice fuuu!! Ko sauraron Sakina bai sake yi ba.

Haushi Sakina taji ta saki mata hannu suka haura sama…
Har suka shafa addua suka kwanta suka ja bargo ba wanda ya yiwa d’an uwanshi magana...........

BULAMA ✍️


So da Buri
Free Book
44


Tun Asuba Hudan ta sauk’o ta fara kula Sakina, dan ita ta tasheta ma sallar Asuba.

Sakina kuwa har suka yi wanka suka shirya, aka je aka yi breakfast aka dawo bata kula Hudan.nKo tayi mata magana ma sai dai tayi mata banza:

Hankalin Hudan bai tashi ba, sai da taga Sakina ta saka kayanta waenda tazo dasu chap ta shirya, tace mata “sai sunyi waya”.
Da sauri ta shiga gabanta ta tsaya dan har ta kusa k’ofa,
kafin tace
“Ban gane ‘sai munyi waya’ ba!
Me hakan yake nufi?”
Ba tare data kalletaba tace
“Tafiya zan yi”
Cikin rashin jin dad’i Hudan tace “Akan Ya Arshaad kikayi fushi dani haka har kika yanke hukuncin tafiya ki bar ni??
Kin san kuwa me yayi min?”

D’ago dara daran idanuwanta Sakina tayi, kafin tace
“Nasani Hudan, sanin abunda ya had’akun ne ma har yasa kike fushi dashi hakan ne zai sanya in tafi..
Jiya baki b’ata min rai sosai ba
amman dana san dalilin fad’an naku wallahi bakiji yadda raina ya b’aci ba.”
Cikin takaici da son fahimtar da ita Huda tace
“Sakina Jalila fa yaje........”

Cikin katseta Sakinar tace
“Na fad’a miki fa, na sani.
Jiya mun yi chatting da shi sosai ya fad’amin komai!
Haba Huda,

Download complete TXT · Novel page