HAJAR

Chapter 37 of 85

Kulsoom ta taɓe baki tace "mu jima da yawa..", ficewa Ruqayyah tayi daga gidan fuskarta a haɗe, da badan Kulsoom ƴar uwarta bace da babu abinda zai hanata danƙara mata baƙar magana, kuma taci sa'a elder sister dinta ce yau da ace itace gaba da Kulsoom to babu abinda zai dakatar da ita daga kwalla mata marii, wai ta ajiye Dearest a gefe wato ta rabu da shi, never ever babu abinda zai sa ta rabu da shi sai mutuwa, tana isa bakin titi ta tari napep zuwa gida.

★Hajar ta gyara ɗakinta fes bayan ta gama cin Noodles da ta dafa, ta rufe ɗakin ta sauka downstairs zata kai plate da cup din da tayi amfani dasu kitchen, gaban sink ta tsaya tana kallon liquid soap dake wajen, ta kunna pampo ta matsa liquid soap din a plate ta tashi foam, sponge ta dauka ta fara wanke utensils din da ta ɓata, tass ta wankesu ta kife a inda ta ɗauka, duk da kitchen din babu datti amma saida ta sake gyarasa, tayi drying hannunta da towel kafin ta fita daga kitchen din, room dinta ta koma tayi zugum sai kace wata prisoner, can dai ta gaji da zaman daƙin ta tashi ta fita, ta kitchen tabi ta fita daga gidan zuwa backyard, through out the day anan tayi zamanta kamar dai jiya sai idan za tayi sallah ne take komawa ciki, bayan ta idar da sallar la'asar ta birkito kayan da ta saka set biyu sai nities da hijab biyu, toilet ta shiga da kayan ta zazzaga detergent a bucket ta shiga wankesu duk da cewa ba suyi wani datti ba, tana gama wankewa ta ɗauraye toilet din ta fito da kayan cikin bucket, can backyard din ta wuce ta shanya kayan jikin flowers, tana cikin shanyar saiga mai gadi da watering can a hannunsa zai bawa flowers ruwan yamma, dan russunawa yayi ya gaisheta ta amsa kafin ta ɗauki bucket din tabar wajen dan ta gama shanyar, tana shiga palour taji kamar ana buɗe main door din gidan, ta ringa kallon ƙofar har aka buɗeta, Nurain ne ya shigo Farooq biye dashi, suna yin ido huɗu tayi sauri ta ɗauke kanta ta wuce zata haura sama taji ance "Amarya..", dakatawa tayi amma bata juya ba, Nurain ya wurgawa Farooq wani kallo kafin ya wuce ya haye sama, Farooq ya ɗaga shoulder ya ƙarasa cikin palourn, a hankali Hajar tace "ina yini..", Farooq yayi murmushi yace "lfy lou amarya.. how are you..", tace "am fine thank you.." da haka ta nufi stairs ta haura sama, Farooq ya zaune kan kujera ya ciro wayarsa daga pocket yana latsawa, after 20mins yana zaune palourn ya daga kai yana kallon stairs, contact ya shiga yayi dialing numbern Nurain har ta gama ringing bai ɗauka ba, babu jimawa saiga shi nan yana sakkowa, Farooq ya ringa kallonsa har ya ƙaraso palourn yace "muje..", Farooq bai motsa ba yace "daga ɗakko paper saika tsaya wanka kuma..", Nurain ya nufi door yace "c^mon let go..", Farooq na fitowa Nurain ya rufe ƙofar da mukulli, shidai Farooq yana so yace wani abun amma dai ya fasa, a tare suka nufi gate, Inuwa dake zaune nan bakin gate din yayi saurin miƙewa har suka ƙaraso, russunawa yayi ya gaidasu duka, shidai bai san lokacin da suka shigo ba sbd a lokacin ya tafi can backyard, Nurain yace "ba wanda yazo..?", Inuwa yace "Eh Alhj..", Nurain yace "Okay, zan sake fita sai na dawo..", Inuwa yace "Allah ya tsare..", Nurain yace "Ameen" ya buɗe ƙofa suka fita gidan da Farooq, motarsa da ya parker nan waje ya bude ya shiga, Farooq ya shiga front seat, tada Motar Nurain yayi ya fara driving out of the street, suna hawa main road Farooq yace "Allah yasa dai ba rufe yar mutane kake a gida ba..", banza Nurain yayi dashi kamar baiji ba, Farooq ya sake cewa "kaga idan ma rufeta kake to ka dena dan naji Mami tayi complain akan hakan a asibiti..", still Nurain bai tanka masa ba kawai driving dinsa yake, Farooq ya gyara zama yace "if i were you banza zanyi da rayuwa wllh, tini zan saki jikina with my cutie wifey, the girl is so cute...", Nurain ya ƙara speed din motar kafin ya juyo ya dubi Farooq yace "really, tinda she is cute idan kana sonta sai in saketa kawai ka aureta punk...", Farooq ya haɗe gira yace "you're not serious...", Nurain yace "am jet serious..", da wani irin expression Farooq ya ringa kallonsa ya kasa cewa komai, Nurain ya juyo sukay ido huɗu, ganin reaction din fuskarsa Nurain yayi murmushi, Farooq ya fara latsa wayarsa bai sake cewa komai ba har suka je inda zasu, 40mins suka ɗauka a wajen kafin suka gama abinda za suyi suka fito, bayan sun shiga Mota Farooq yace "dude you have to make this thing serious, container nawa ce zata sauka..?", Nurain yace "three.. next month", Farooq yace "Ohk..", Nurain yace "lokacin da nake India naje China nayi order dinsu, you know shipping zasu jima basu zo ba..", suna zuwa wani junction Farooq yace "drop me here..", Nurain yace "bari nayi dropping dinka gida mna..", Farooq yace "i have another appointment..", Nurain yace "Ohk", Farooq ya buɗe motar ya sauka. Nurain na zaune main palourn gidansu bayan ya dawo daga masallaci sallar isha'i, Noor ta shigo palourn da Laptop dinta a hannu, ta zauna a gefensa tace "Yaya please duba min..", keenly yace "Ohk..", kunna Laptop din tayi ta shiga slide din, duba mata ya fara yi inda akwai gyara sai ya nuna mata ta goge ta gyara, resting yayi jikin kujera ya lumshe idonsa, Noor ta gama typing mistake din da ya gyara mata tace "Ya am done..", yace "get me something to eat first..", tace "tom" ta tashi ta shiga kitchen, abincin da aka dafa na dinner ta zubo masa, ta haɗo da ruwa da lemo ta kawo masa a tray, saida ya gama cin abincin snn suka cigaba, Mami ce ta shigo, tayi still tana kallonsa kafin ta dubi wall clock dake palourn da ya nuna 9:20 dot, Mami ta kalli Plate din abincin da ya gama ci, tini taji wani iri a ranta, sau uku knn, Mami ta ƙaraso kusa dasu tace "Nurain me yasa kake dare ne baka tafi gida ba, i thought ka tafi ma since..", ya shafa kansa a hankali yace "ina dubawa Noor project dinta ne...", Noor tayi saurin cewa "we will continue tomorrow then Yaya, thank you..", Nurain ya miƙe yace "Mami saida safe..", without looking at him Mami tace "Ohh Allah ya tashe mu lfy..", Noor tace "Yaya ka gaida Hajar Please..", ya gyaɗa kai kawai da haka ya fita, Mami na kallon Noor tace "wane yaci abinci..?", Noor tace "Yaya ne", Mami ta wuce part din Abba dan daman nan ta fito shiga, Noor ta kwala kiran mai aiki, Laure ta fito daga kitchen tace "gani hajiya ƙarama..", Noor tace "Please gyara nan wajen", Laure ta dauke trayn ta shiga kitchen. ƙarfe tara da minti arba'in a gida ta yiwa Nurain cause gudunsa ya falfala a mota, kuma yana shiga gidan daman Kitchen ya wuce, yaufa gaba ɗaya bai sha coffee ba shiyasa yake jinsa moody, kuma bazai iya bacci bai sha ba, ya buɗe Cupboard ya ɗakko Coffee powder yana sake duba expire date, coffeen da ya sha da safe was the worst coffee ever da ya taɓa sha, shine yake duba expire date wai ko powdern tayi expire shiyasa yaji na safe da ya hada rotten, still dai wani sabon pack din ya buɗe cause bai yarda ba kar yaje daga powdern ne, da sauri ya dubi window ganin kamar mutum ya gifta, ya ƙurawa windown ido yana mamakin abinda ya gani, ƙofar kitchen wacca ta fita ta backyard aka buɗe, rumgume da kayanta da ta wanke ta shigo, ta ɗan firgita ganinsa a kitchen din sai kuma ta haɗe rai ta wuce, ta buɗe ƙofar shiga cikin gidan ta shiga palour, Nurain ya ringa kallon ƙofar backyard din, jinjina kansa yayi ya fita kitchen din, ya haura sama ya shiga part dinsa, drawer da ya ajiye kaff spare keys din gidan ya buɗe ya ɗauki guda ɗaya kafin ya fito ya koma kitchen din, ya gama making coffee ya juye a cup, ya matsa gaban ƙofar backyard din ya zura key din ya kulle, saida ya tabbatar ta rufe gamm snn ya cire key din, ya ɗauki Cup of Coffee dinsa ya bar kitchen din bayan ya kashe lights....✍️

yan Arewa ku rungumi sorry yau 😅🌝
💛 HAJAR 💛
by Feenerh feeche

{48..}
Washe gari tinda Hajar ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba sbd da wuri ta kwanta jiya, tana kwance kan carpet ta rufa da duvet da wayarta ta buɗe Alqur'anin tana karantawa, sai ƙarfe bakwai da rabi ta ajiye karatun, linke duvet din tayi ta maida kan bed, shima pillow da ta tada kai ta mayar dashi gado, bathroom ta shiga dan yin wanka, minti ashirin ta ɗauka tana wankan kafin ta fito ɗaure da towel da yazo mata har guiwa, sai ƙamshin tsadadden showel gel da tayi wanka ne ke tashi a ɗakin, gaban mirror ta tsaya kafin taja stool ta zauna, body lotion ta janyo ta fara rubbing a jikinta, a hankali take shafa man tunani iri iri na amsawa a brain dinta, da sauri ta dubi ƙofa jin alamar za a shigo, ido huɗu sukay da Nurain, yana riƙe da handle din ƙofar, Hajar ta zaro ido kafin ta fasa ƙara ta fara kare jikinta, ya ɗauke kansa fuskarsa a murtuke, da wani irin zafin nama ta tashi daga kan stool din ta wafci hijab dinta ta saka, ƙarasa shigowa ɗakin yayi ya ajiye pen da jotter din hannunsa, da haka ya doshi ƙofa zai fita, Hajar da jikinta yake mugun rawa sbd tinda take babu wani namiji da ya taɓa ganinta a haka, har ruwa idonta ya kawo, da kyar tace "malam ka dena shigo min haka nan without notice...", fita yayi daga ɗakin, ta bisa da sauri ta tsaya bakin ƙofa tace "kai da Allah da ka shigo min babu sallama...", tana kallonsa ya shiga part dinsa, ta juya ta koma ɗakinta zuciyarta na tafasa, wani irin yamutsa fuska tayi sbd kawai ƙamshinsa da ya bari ne ke tashi a ɗakin, ƙamshin da sam baya mata daɗi, ta ɗauki freshner ta hau feshe room din amma duk da haka pure men scent dinsa bai disashe ba, Shafa man da bata ƙarasa ba knn ta buɗe wardrobe ta ɗauki kaya ta saka, har ta gama shiryawa zuciyarta ba ta dena tafasa ba, knn yaga bati, a fili tace "shi ya isa yaga bati, wllh Allah ban yafe ba..", gaban mirror ta koma ta ringa kallon jotter da pen din da ya ajiye, ta taɓe baki kafin ta ɗauki biron, rubutun da bai wuce 5lines tayi ba ta yage papern tayi folding dinta, da papern a hannunta ta sauka downstairs, ta wurga takardar kan Centre table tace "wnn kaɗai nake buƙata a wajen ka malam..", kitchen ta shiga dan samawa kanta abinda zata ci, ta buɗe fridge tana kallon fresh vegetables dake ciki, ta rufe fridge din kafin ta buɗe freezer wacca take cike da nama da chicken ga kuma fish duk frozen, shawara ta yanke akan cewa anjima za tayi stew saita ajiye a fridge ta ringa amfani da abarta na ƴan kwanaki, ruwan shayi ta tafasa ta soya kwai guda biyu da haka tabar kitchen din, bata haura sama ba ta zauna nan palour, Centre table da Tv stand da kujerun duk sunyi ƙura, tin ranar da Hafsah ta gyara palourn rabonsa da ganin tsintsiya, taɓe baki Hajar tayi tace "uhmm tinda ba ubana ne ya zuba ba babu abinda ya shalleni..", ta ɗauki kofin shayinta ta fara sha tana gutsirar kwai, tana gama cin abincin ta tashi ta shiga kitchen, ta wanke kwanukan da ta ɓata ta mayar dasu position dinsu, tin kafin ta gama wanke wanken ma take kallon ƙofar backyard, Alla alla take ta gama ta fita can ta ɗan sarara, bakin door din ta isa ta murɗa handle, sake murɗa handle din tayi da ɗan ƙarfi jin ƙofar taƙi buɗewa, lokaci guda ta saki handle din ta kafawa ƙofar ido, shiknn a kulle take, sosai ranta ya ɓaci dan zaman backyard din nan sosai yake rage mata kaɗaici, ranta duk ba daɗi ta bar kitchen din, main door ta ringa attempting buɗewa itama dai a rufe. tinda aka kawota gidan duk wnn ranar tafi mata zafi, baccin rana ma kasawa tayi, babban abinda yafi tsaya mata a rai bai wuce na safe da ya shigo mata ba, bayan tayi sallar la'asar ta kira Umma, gaisawa sukay Umma ta tambayeta ya take, Hajar dai tace lfy amma dai a ƙasan ranta ba haka bane, har Sabra ta tambaya tana cewa yaushe za a kawo mata ita, Umma tace mata ba yanzu ba, da haka suka kashe wayar.

★Nurain na zaune bisa executive kujera dake office dinsa bayan ya gama attending last patient, ƙofar office din aka buɗe aka shigo, ya ajiye plastic heart like da yake wasa da ita ya ɗaga kai ya dubi wanda ya shigo, lokaci guda ya haɗe thick eyebrows dinsa, da sauri Haleema ta shigo office din itama gaba ɗaya a ruɗe take, ta kalli Ruqayyah tace "Maam please get out..", ko kallonta Ruqayyah ba tayi ba ta isa gaban table tana kallon Nurain tace "i can stand any humiliation as far as zaka saurareni Dearest....", Nurain ya maida dubansa ga Haleema yace "amm me na gaya miki ne...?", with due respect Haleema tace "don't let her in..", Calmly as if speaking to himself yace "bayan nan..?", Haleema tace "call security..", ya gyaɗa kai yace "good.." kafin ya ɗauki heart din da ya ajiye ya cigaba da wasa da ita, Haleema ta fita daga office din da sauri, Ruqayyah ta zauna kan ɗaya daga kujeru biyu dake gaban table din, kallonsa ta ringa yi babu ko ƙiftawa, kifa kanta tayi da table din ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "na haɗaka da Allah, na haɗaka da manzon Allah, please talk to me Dearest, ko scolding dina kayi that will be better amma...", ta kasa cigaba da maganar tana kuka sosaii, a hankali yayi baya da kujerarsa ya tashi salum alum ya nufi door ya buɗe ya fita, Ruqayyah ta ɗago kanta ta bisa da kallo da jajayen idanunta, Office din Dr Marwan ya wuce, Dr Marwan na kallonsa yace "is there any problem Dr..?", Nurain yace "not at all, how is the patient..?", Dr Marwan yace "alhmdllh he is recovering gradually..", Nurain ya gyaɗa kai yace "how about his vital..?", Dr Marwan yace "great, Khaleel ya duba not too long ago", Nurain bai sake cewa komai ba yayi resting jikin kujerar, after few minutes of silence Dr Marwan yace "naji ana maganar Seminar wacca za aje Abuja nan da 1month, all thoracic surgeon must be there..", Nurain yace "am not going..", Dr Marwan yace "why..?", Nurain ya ɗaga shoulder yace "kawai.." da haka ya dubi wrist watch dinsa, tashi yayi ya yiwa Dr Marwan sallama, yana fita daga department din ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Haleema, tana picking yace ta kawo masa briefcase dinsa yana parking lot, da haka ya kashe kiran ya cigaba da tafiya zuwa inda ya parker motarsa, buɗe motar yayi ya shiga, babu jimawa saiga Haleema da briefcase din tasa, ya amsa ba yabo ba fallasa yace "thank you..", tace "am so sorry sir about what happened, i tried to stopped her...", ya ɗaga mata hannu yace "it's okay..", tace "thank you sir", murmushi kawai ya mata ya sauke handbrake yaja motar yabar harabar hospital din, driving kawai yake saman titi amma bai san inda ya nufa ba, lokaci guda yayi murmushi yace "ironlady..", yana zuwa wani roundabout ya juya kan motar, yana zuwa gidan ya danna horn, mai gadi ya buɗe masa gate ya shigar da motar, fitowa yayi daga motar bayan ya gama parking, ta baya yabi inda direct nan ne zai kaika part din Hajiya, da sallama ya shiga palourn Hajiya, Hajiya na zaune kan darduma ƴar dattijuwar mai aikinta tana yanka mata papaya, Hajiya ta kalli Nurain ta saman kantamemen glasses dinta tace "ywwa ga likita ma Allah jefomin daga sama, Usuman cikina ne ya ɗaure kwana biyu ban kewaya ba, toh duk ya dameni ji nake kamar anyi min jeren marmaroni a kyuiɓi ko isasshen bacci bana samu, dana gaji da azaba shine nasa Umaru ya kwaso min gwanda kwallo uku, na sha kwallo guda da safe yanzu ma gashi ana yankan wata zan shanye, da daddare in Allah ya kaimu a yanke min gudar da ta rage itama na shanye, ai idan nayi hakan na huta da jarabar basir din nan, ba kaga da yaya na shanye wacca aka yankan da safe ba, cikina har baya kamar zanyi amai amma kuma ai lfy nake nema, yanzu haka har na fara tararrbin yadda zan shanye wnn..", Nurain yayi still yana sauraronta kafin ya samu waje ya zauna yace "karki sake shan wata ta safen is Okay..", Hajiya tace "Allah ko idan na sake sha zan iya tsurewa knn...?", ta dubi mai aikin tace "ke Asabe maza fita da ita duk warinta ya cikan hanci, kije can ki shanye rabonki ce", mai aikin ta ɗauki plate din papayan tayi waje da ita. Hajiya tace "na ganawa kaina azaba har yanxu gyatsar wnn aba nake, kai ina jin ma harna koma ga mahalicca na bazan sake shan gwanda ba duk ta gundureni", Nurain yace "ba kya jin komai daga wnn...?", tace "A'a ƙalau nake Usuman, haka kurum nace maka wani waje na min ciwo ka samu hanyar da zaka fara zuba min allurai..", yace "toh shknn tinda lafiyar ki ƙalau..", Hajiya tace "toh madallah ya gyatumar taka.." sai kuma ta tsuke baki tace "ji wani sakarci nida zan fara tambayarka matarka kuma na tafi wani wajen, Mami ai ba gida ɗaya kuke kwana ba yanzu..", shi

Download complete TXT · Novel page