Showing 111001 words to 114000 words out of 252835 words
ringa tafiya gida da wuri ai yafi son..", ya shafa kansa yace "tom Mami", Compound ya fita ya shiga motarsa, ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Noor, tana picking yace "yi sauri malama", tace "Yaya gani nan..", few minutes saiga tanan ta ɓillo ta can baya da basket a hannunta, ta buɗe front seat ta ajiye basket din ta rufe door, Nurain ya gyara zama ya tada motar. saida ya tsaya wajen suya ya siyi kaza snn ya wuce gida, fitowa yayi daga motar yana amsa sannu da zuwan da mai gadi yake masa, ya buɗe front seat ya ɗauki basket din kafin ya nufi main building din gidan, keys ya ciro daga pocket ya buɗe door ya shiga ya mayar ya rufe still da muƙulli, ajiye basket din yayi nan palour kafin ya haura sama, wanka yayi ya saka Pajamas masu sweat pant masu shegen kyau, downstairs ya sakko da room slippers a ƙafarsa, kamar ce masa akay ya kalli wajen, ya ringa kallon papern dake kan Centre table, haɗe gira yayi kafin ya ɗauki papern ya buɗe a wulaƙance, beautiful handwriting din dake jiki ya fara karantawa.... "malam wai an gaya maka inada wata buƙata ne a wajenka in banda guda ɗaya, kawai ka sauwaƙe mana shine buƙatata..", tsaki yayi ya cukuikuiye takardar ya wurgar da ita, wani irin ƙauri ya fara perceiving, da sauri ya nufi kitchen, yana buɗewa yaja da baya ya toshe hancinsa, gaba ɗaya kitchen din ya gumame da hayaƙi da uban yaji, da hannu ɗaya ya rufe hancinsa ɗayan kuma ya ringa kore hayaƙin har ya samu ya shiga kitchen din, gaban cooking gas ya isa yana ƙoƙarin kashe wutar amma da yake hayaƙi yayi yawa baya gani sosai hannunsa ya jogali tukunya, da sauri ya janye hannun ya riƙe da other din, hkan ce tasa yayi perceiving ƙaurin har cikin lungs dinsa, tini ya fara tari at same time yana ƙoƙarin kashe gas din. Hajar ta saki pillow din hannunta bayan brain dinta ta amsa, shaf ta manta da kayan miyar da ta ɗora akan wuta, bata tsaya bi takan wani hijab ba ta gyara hular kanta ta fito daga room din, da sauri ta ringa sauka stairs har tana tuntuɓe, tin daga palour ta fara tari ga uban hayaƙi da ya rufe mata vision, gadan gadan kitchen ta shiga daidai lokacin da Nurain ya kashe gas din, da sauri ta juya kamar zata sa gudu sbd fitowar da tayi ba shiri, Allah yaso ma kayan baccin riga da wando ne kuma rigar ta saukar mata, tana fita daga kitchen din shima ya fito yasa ƙafa ya banke ƙofar, tana shirin hawa stairs taji an fixgo hannunta, figarta yayi zuwa dining area inda babu hayaƙin sosai, haɗe ta yayi da bango still bai sakar mata hannu ba fighting with his breathing, sosai ya shaƙi hayaƙin shiyasa numfashinsa har yanzu bai dawo normal ba, kiciniyar kwace hannunta ta fara yi tana turesa da iya ƙarfinta, sake matseta yayi da bango ta kasa motsi, heavily yake breathing har zuwa lokacin da yaji dama dama, a hankali take mayar da numfashi ta ɓalla masa harara tace "let go off me, ni ka sake ni..", ita babban tashin hankalinta kayan jikinta, muryarsa ma bata fita sosai yace "from today henceforth karna sake ganinki a kitchen, are you mad fire outbreak zaki ja min a gida, koda wasa na sake ganinki a kitchen saina sumar dake nonsense" yana kaiwa nan ya hankaɗeta saura ƙiris ta faɗi. da sauri ya nufi stairs ya haura sama don bazai iya ƙara koda 1minute a wajen ba, Hajar tabi bayansa da kallo zuciyarta ta ringa ƙuna kamar zata kama da wuta, zama tayi kan stairs din hawa dining ta haɗe kai da guiwa, after 10mins ta tashi ta haura sama kamar wacca kwai ya fashewa a ciki. washe gari da safe Nurain ya sauko downstairs, ta main door ya fita ya zaga can backyard ya kashe gas cylinder, cikin gida ya dawo bayan ya kashe gas din, ya shiga kitchen to make a cup of coffee, wani tsaki yayi ganin tukunyar dake kan cooking gas, tayi wani baƙi ƙirin ko kyan gani babu, cikin sink ya saka tukunyar ya sakar mata ruwa saida ta cika damm snn ya kashe pampon, ya jona coffee maker. A hankali Hajar ta ƙarasa sakkowa daga stairs idonta ƙur akan keys din dake jikin ƙofa, ta isa bakin ƙofar a hankali ta zare keys din, tana juyawa sukay ido huɗu dashi ya fito daga kitchen da cup a hannunsa, ta haɗe gira tayi sauri ta kunshe keys din a hijab, garin haka ji kake tass muƙulli sun faɗi a kan tiles, kallon keys din Nurain yayi snn ya kalleta, ta wani haɗe rai, yana kallon main door ita kuma ta samu opportunity ta sunkuya ta ɗauki mukullin ta kwasa a guje sai sama, a hannun kujera ya dungurar da Coffee din yabi bayanta da sauri, tana ƙoƙarin rufe ƙofa yasa ƙafa ya banke ƙofar, zaro ido tayi tace "na shiga uku" ta ruga can edge of the room ta boye hannunta a baya, daga bakin ƙofar ya tsaya yace "give me the keys..", ta murguɗa masa baki tace "wllh bazan bayar ba, ni ba tinkiyarka bace da zaka ringa kulleni", ƙofar bathroom ta kalla sai kuma ta kallesa tana banka masa harara, lokaci guda ta tafi da gudu zata shige bathroom din, ganin haka ya taho da speed ya fixgota ya haɗeta da jikin wardrobe, dunƙule keys din tayi a hannunta ta ɓoye a baya, tini ta ringa shaƙar scent dinsa da bata so, ta ɗaga lulu eyes ɗinta ta kallesa, shima kallon cikin idanunta yake da wani irin expression zuciyarsa na tafasa.......✍️
Chapter 49... on Arewabooks..
Click the link below to join my WhatsApp group 👇
💛 HAJAR 💛
{49..}
Thick eyebrows dinsa a haɗe while still staring at her yace "i said give me the keys..", ta juyar da kai gefe tana turo baki tace "ni fa bazan bayar ba..", bata ankara ba taji hannunsa akan nata da ta ɓoye a baya yana ƙoƙarin dawo dashi gaba, ta cije iya ƙarfinta ta sake dunƙule keys din a hannunta, partially ya dubi fuskarta kafin ya murɗa hannun nata ya dawo dashi, ƙara ta fasa ta fara ƙoƙarin fixgewa, tana ji tana gani ya ɓamɓare keys din daga hannunta, ya bita da wani shegen kallo ya juya ya fita daga ɗakin, wani mugun takaici ne ya tokare mata a maƙoshi, ta sulale ƙasa ta rushe da kuka tace "wllh sai na maka rashin mutunci mai wasali, ba dai ni ka murɗewa hannu ba, na rantse da Allah saina rama, dala ba gammo ka ɗakkowa kanka idan baka sani ba saika sakeni zaka cigaba da rayuwa mai daɗi..", taci kukanta ta more ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskarta da ruwa ta fito, fita tay daga ɗakin tana cika ta batsewa ƙiris take jira a taɓata ta sauke kwandon bala'i, downstairs ta sauka ta nufi kitchen tana cewa "duk abinda kace kar nayi toh yanzu na fara yinsa a gidan nan, dani da kai naga wanda zai sumar da wani, dan wllh tllh ni kaɗai nasan irin ayar da zan gasa maka a hannu..", plate ta ɗauka ta buɗe bucket din dubulan dana chin chin ta zuba, ta fito daga kitchen din, tsaye tayi tana kallon cup din Coffeen da ya ajiye a hannun kujera, Cup din ta ɗauka tana kallon coffen, ta gyaɗa kai ta haura sama da Kofin, a kan mirror ta ajiye plate da cup din taja stool ta zauna, taci dubulan da chin chin dinta tayi nak tana korawa da coffee, sosai combination din ya mata dadi sbd the coffe is creamy and yummy gashi babu sugar sosai sai hakan ya bada wani armashi. Nurain ya ringa kallon inda ya ajiye Coffeen sa wayarsa a kare kunne yana magana da Farooq, zagaye ya ringa yi yana duba each sofa a palourn, Farooq yace "are you listening..?", Nurain yana sake duba hannun kujeru yace "yeah", Farooq yace "alright" ya cigaba da bayanin da yake masa, after 5minutes suka gama wayar, Nurain ya shafa cikakkiyar sumarsa yace "damn it i misplace my coffee" da haka ya haura sama to get ready for work, dakatawa yayi da zuge glass door da ya fara ya kalli ƙofar ɗakinta da ta buɗe ta fito, idonsa ya sauka akan cup din dake riƙe a hannunta, ya ringa kallonta har ta ɓace masa bayan ta sauka ƙasa, slight hiss yayi ya juya ya shiga room dinsa, ƙarfe tara dot ya fito bayan yayi wanka ya shirya hannunsa riƙe da briefcase, ya sauka downstairs ya shiga kitchen ya ɗauki basket din abinci da yazo dashi jiya, bayan ya rufe main door ya isa parking space, ya shiga motarsa ya kunna, a booth ya saka basket din ya koma ya shiga motar tana gama warming ya fara driving ya fita daga gidan Inuwa na ɗaga masa hannu. sai ƙarfe uku Hajar ta fito ɗakinta zuwa kitchen, duk wnn lokacin ba ta ji yunwa ba sbd breakfast din yau ya riƙe mata ciki, ji take dama zata sake samun wnn creamy coffee din, saida ta gama jajjaga attaruhu da Albasa ta zuba a ƙaramar pot ta ɗora kan gas, ta ɗauki lighter ta kunna gas din amma babu wuta, ta canza wani shima dai wuta ba tazo ba, ta koma ta jingina da jikin cabinet tana tunanin yanxu yaya knn, me zata bawa cikinta, ta ringa kallon gas cooker din sai taga ashe akwai electric head ajiki har guda biyu, ta tuna lokacin da take gidan Anty Jamilah dashi ai take amfani most of the time sbd unguwar akwai nepa sosai, Hajar tayi ajiyar zuciya a bit relief, tana murɗa control knob din electric stove din luckily for her sai gashi ya kama, tinda a jone yake da wuta, wani dadi ne ya ratsa Hajar, tini ta hau yin girkinta, cikin kayan gararta ta farke buhun shinkafa ta ɗebi yadda zai mata ta dafa, bayan ta gama dafa shinkafar da ƴar sauce ta palm oil, gaba ɗaya ta juye a plate ta zuba Sauce din akai, ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa da haka ta fita zuwa palour, da kyar ta iya cinye abincin, ta kai plate din kitchen, saida ta wanke komai da tayi amfani dashi ta mayar mazauninsa snn ta bar kitchen din ta haura sama, cikinta ɗam ɗam dan ji take ita da abinci kam sai gobe kuma.
★Maama na kallon Maimuna da take ƙoƙarin saka hijab tace "wai ina zaki a haka Mainuna.. jifa fuskarki ko gama saɓewa ba tayi ba..", Maimuna da tayi ɗaurin ɗan kwali har goshi tace "kai Maama ba fa daɗewa zanyi ba, nan nan zanje na dawo..", Maama tace "nan nan ina..?", Maimuna tace "kai jaraba" ta ciro wata fatattakakkiyar dari biyu daga bra ta linƙawa Maama a ƙirji tace "yanzun nan zan dawo..", Maama ta dafe ɗari biyun tace "karki daɗe", Maimuna ta ƙarasa saka hijab dinta ta fita, bayan ta saka takalmanta dake bakin ƙofa tayi soro, can ta gangara cikin lugunsa har ta ɓulla wani lungun, daga nan tayi tafiyar da bata wuce ta minti biyar ba sai gata a wani kango wanda aka zagayesa da blocks sai gate na langa langa, tin kafin ma ta ƙarasa cikin kangon ta fara jin warin kayan zuƙe zuƙe, haka nan ta dake ta shiga kangon, su biyar ne a zaune a kangon matasa dasu babu wanda ya haura ashirin da bakwai a cikinsu, wanda ya fara hangota ya cire cigarette da yake zuƙa yace "ke ubanki kika kalla anan...?", Maimuna tace "ƙwage nake nema..", wani daga can gefe wanda ya fisu shekaru bakinsa baƙi ƙirin ya kalleta a wulaƙance, Wiwin dake hannunsa ya yiwa mummunar zuƙa ya fesar da hayaƙin ta hanci da baki tamkar salansar tsohon babur yace "ke yarinya yane... kin kawomin kanki ne dan na tuɓeki..?", Maimuna tace "haba ƙwage ai kasan nafi ƙarfin ka... harƙalla na kawo maka..", Ƙwage ya tashi ya matsa kusa da ita yace "meye..?" yana cigaba da busa wiwi, ta fara lalube cikin hijab dinta ta ciro kuɗi masu ɗan kauri a ƙalla zasu kai 10k ta miƙa masa, wurgar da ragowar wiwin yayi ya murjeta a ƙasa ya amshe kuɗin, Maimuna tace "kasan Mu'azzam ɗan gidan gini..?", Wani ne ya taso yana kallon hannun Ƙwage yace "kai wnn yaron fa nunar rana take nufi, ke ba ƴar gidansu bace ai naga yayanki ne..?", Maimuna tace "Eh ɗan kishiyar Baabarmu ne..", yace "A'a malama baabarki dai ba tamu ba..", Ƙwage yace "kai zan feɗe ka da rai nace ka sako bakinka ne..?", Bisi ƙwale yace "haba gorun goruba naga harkar nan tare muke yinta ai karka mana eh yane faa..", Ƙwage yayi kwafa yace "ina jinki", Maimuna tace "Shi nunar ranar Mu'azzam nake so ku masa dukan tsiya..", Ƙwage yace "Au abin sauƙi, ai ko cewa kikai mu ƙaddamar masa wllh a yau sai yaro ya ziyarci barzahu..", Maimuna tace "ku lakaɗa masa na jaki..", zuciyar Maimuna ba tada maraba da kindirmon nono sbd fari haka ta koma gida, tana shiga ɗaki ta cire hijab ta bage akan gado, Maama ta bita da idanu tace "har kin dawo...?", Maimuna tace "gashi kin gani", Maama tace "sai naji kamar kina warin Wiwi", a hasale Maimuna ta miƙe zaune tace "wiwi kuma Maama..?", Nabilah dake zaune ɗakin tana tsince shinkafa tace "nima naji wllh...", harara Maimuna ta bisu da ita ta koma ta kwanta tana jan dogon tsaki. Da yamma Umma na zaune bakin murhu tana kwasar tuwo, Mu'azzam ya shigo gidan da sallama, ya durƙusa gaban Umma ya gaisheta, da fara'a ta amsa masa tace "an dawo lfy ya aiki..?", yace "Alhmdllh Umma, yau mun gama da gidan ma har an biya mu zuwa jibi zamu tafi Katsina wani aikin..", Umma tace "toh alhmdllh, Allah ya temaka..", yace "Ameen Umma ga wnn.." ya ajiye mata ledar da ya shigo da ita, tace "toh madallah, Allah yayi albarka, ga can abincinka a ɗaki", yace "toh" ya tashi ya shiga ɗakinta ya ɗauki warmern abincinsa, daga nan ya shiga ɗakinsu, Maimuna dake laɓe jikin window tana leƙensa tayi kwafa ta koma ta zauna, Umma ta gama kwashe tuwon ta ɗauka ta kai ɗaki tare da ledar da Mu'azzam ya kawo mata, ta buɗe ledar taga lemo da Ayaba sai kuma ɗan tsire ne ciki, murmushi tayi ta ajiye kan mirror, Sabra ce ta shigo da gudu tana haki tace "Umma Yaya ya dawo...?", Umma tace "ba zaki dena guje gujen nan ba ko dan kinga Addarki ba tanan ne?", Sabra tace "ya haƙuri Umma", Umma ta shafa kanta ta ɗauki lemo ɗaya Ayaba ɗaya ta bata tace "zauna kici". Mu'azzam na alwala bakin rariya zai wuce masallaci dan daf ake da kiran sallar magrib, yana idar da alwalar ya fita daga gidan, bayan Umma ta idar da sallahr Isha'i tana zaune kan darduma tana lazimi, sallama akay daga soro, Maama da ƴaƴanta babu wanda ya amsa Nabilah kuma da ta ɗan fara shiryuwa sallah take, ga Baba ma baya nan ya fita masallaci, Umma ta ajiye carbin da take lazimi ta fita, daga bakin ƙofar soron ta tsaya, bata kai ga magana ba Naseer ya shigo, gaisawa Sukay da Munkaila wanda shine yayi sallamar, Munkaila yace "ina Baban naku..?", Naseer yace "yana masallaci..", Munkaila ya numfasa yace "toh muje da kai, ban san me ya haɗa Mu'azzam da fitinannun yaran nan ba gashi can sun sassara sa, yanzu haka dai an wuce dashi emergency..." ganin Umma kawai sukay a soron tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un.. wane Mu'azzam din.."
★Nurain yayi parking motarsa a wani babban eatery, fitowa yayi daga motar ya shiga eatery din, a vacant table na two sitters ya zauna, tini waitress ta kawo masa food menu, bayan ya gama order abinda yake so waitress din ta tafi kawo masa, dice watermelon da Orange juice aka fara serving dinsa as a starter, gently yake sipping orange juice din yana latsa wayarsa, Tamkar ɓera a buta hka ta shigo Eatery din tana rarraba idanu, tana hangosa ta nufi table din da yake zaune, ta ja kujera ta zauna gami da zuba masa idanu, ajiye glass cup din lemon yayi ya fara shirin miƙewa, da sauri ta riƙo hannunsa tace "dan girma Allah listen to me ko sau ɗaya ne..", fasa tashin yayi da sigar ko in kula murya ƙasan maƙoshi yace "what..?", duk da Ruqayyah taji haushin yadda yayi treating dinta these days amma bata nuna ba, gyara zama tayi tana kallonsa tace "Dr dan Allah don't take grudge against me, ba wai na tafi bane sbd bana son na aureka, ba a fahimce ni bane from the start..", keenly yace "Ohk, then stop following me..", Ruqayyah ta haɗiye kukan da ya taho mata tace "shknn, nasan har yanxu fishi kake dani Dearest..", yana latsa wayarsa yace "not at all..", tace "nagode da ka tsaya, har yanzu ban canza daga Ruqayyahn da ka sanni ba, i still remains your first love and only kuma your wife to be, zan aureka Dearest, a shirye nke ko yanxu ma kaje wajen Daddy za ai mana aure Dearest..", a lokaci na farko da ya ɗago kansa ya kalleta kafin ya dauki orange juice yayi sipping yace "Ruqayyah..", murya na rawa tace "Na'am", yace "a lokacin da nayi dating dinki kinsan duk abinda na bari na barsa knn", ta gyaɗa kai idanunta na ciccikowa, yace "snn kin san banida ra'ayin auren mata sama da ɗaya..", nan ma ta gyaɗa masa kai tace "amma why are you saying that bayan baka da aure..?", ya girgiza kai yace "you are wrong" da haka ya kira waitress yace ai masa packaging abincin da yayi order, Ruqayyah dai ta kasa mgn cause tana buƙatar concrete explanation, wayarsa ya saka a pocket ya tashi zai biya bill, cashier ya nufa ya biya bill din ya amshi ledar abincin ya nufi exist, da sauri Ruqayyah tabi bayansa tace "wllh Allah ban fahimci me kake cewa ba, kuma baka bani enough time na maka bayani ba..", yayi ajiyar zuciya yace "i don't like