Showing 120001 words to 123000 words out of 252835 words

Chapter 41 - HAJAR COMPLETE NOVEL DOCUMENT

zuwa parking space, tana zuwa ta bude front seat ta ajiye basket din ta duƙa tace "kaga fa ni ba ruwana Yaya, gobe ka ƙarasamin gyaran dan Allah..", yace "ke close the door and get lost..", ta turo baki ta rufe ƙofar ta wuce cikin gida, tara saura Nurain ya isa gida, yana shiga main palour ya fara tunanin shirmen da ta masa ɗaxu, sai a lokacin ya sake gasgata tabbas akwai tsantsar yarinta a lamarinta, murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl", kitchen ya shiga ya ɗauki plate with spoon da ruwa da lemo ya ɗora kan basket din hannunsa, da haka ya fito ya haura upstairs. washe gari da safe Hajar ce take sakkowa a hankali daga stairs, takaici duk ya isheta na rashin waya don wayar ce ke ɗebe mata kewa, gashi so take ta kira Umma taji ya jikin Mu'azzam, Still tayi ta ƙurawa hannun kujera idanu tana kallon wayarsa dake kai, ta ƙarewa palourn kallo tana murza slim fingers dinta, a hankali ta matsa ta ɗauki wayar tana kallonta, tinda take bata taɓa ganin waya mai kyanta ba, waya gaba ɗaya glass, juya wayar take a hannunta tana neman ta inda ake kunnata, da sauri ta dubi ƙofa jin an murɗa handle, tini idonta ya faɗa cikin kaifafan nasa, wani irin harbawa zuciyarta tayi, hannunta ya kalla a takaice, tana ganin haka tayi sauri zata ajiye wayar, ai kam garin sauri ta ajiye ba daidai ba, ji kake tass wayar ta faɗi akan tiles, durƙusawa tayi ta ɗauka, tana ganin yadda screen din yayi kwatsa kwatsa tayi sauri ta ajiye a ƙasa ta miƙe tana zaro ido, Nurain ya ƙaraso ya duƙa ya ɗauki wayar, da wayar a hannunsa ya miƙe yana kallon yadda screen din yayi kwatsa kwatsa, har wani numfashi ya ajiye tsabar yadda ransa ya mugun ɓaci, ya ɗago idonsa ya kalleta, tinda take dashi bata taɓa jin tsoronsa irin na yau ba, ƙafarta ta fara karkarwa ta juya da mugun gudu zata haura sama, Nurain yayi wurgi da wayar kan kujera, fixgo hannunta yayi ya juyo da ita, habawa ai tsabar firgita kawai ta tafi luu sai kace wacca aka hankaɗa ta zube a ƙasa......✍️

Plxx share as widely as possible 🙏
💛 HAJAR 💛

{53..}
Tsayawa yayi kawai yana kallonta, taja jiki ta koma can bayan kujera ta rakuɓe ta haɗe kanta da guiwa, tsabar yadda zuciyarsa take tafarfasa kasa cewa komai yayi, kuma baiyi yunƙurin taɓa ta ba, a lokacin idan yace zai taɓa ta to tsaf zai karya ta, Hajar kam ta tsorata iya tsorata har wani karrr jikinta yake, a yadda taga reaction din fuskarsa sai take tunanin yau ba ɗalle mata lips zaiyi ba tsaf zai rabata dasu, ɗago kanta tayi taga har lokacin yana tsaye a kanta, tayi sauri ta ɗora kanta kan knee tana sake takure jikinta, ajiyar zuciya yayi ya figi hannunta ya miƙar da ita tsaya, ƴar ƙara tayi tana zaro ido sai kuma ta fara yarfe hannu, gashi dai ta tsorata kuma tayi nadama amma kuma girman kai bazai barta tace sorry ba, shi kuma a ynxu sorryn ne zaisa ya yafe mata tinda ya lura ba tada shirin faɗa, figarta yayi zuwa cikin palourn, yana riƙe da hannunta ya tura Centre table da ƙafarsa zuwa daf fa kujera 2sitter, zaunar da ita yayi kan Centre table din shi kuma ya zauna kan kujerar suna fuskantar juna, ta haɗe legs dinta waje guda tana kallon ƙafarsa dake sanye cikin soft room slippers, gashi ya saka legs din nata a tsakiyar nasa, ƙoƙarin zamowa ƙasa tayi tana turo baki, da sauri ya mayar da ita ta zauna, zuciyarta na tsananta bugu ta ɗago idonta tana kallonsa, ya haɗe gira ya ɗauki wayarsa dake kan kujerar ya ɗora mata kan laps yace "biyani..", ta ringa kallon wayar ba tace komai ba, yace "uhmm am talking to you young lady, nace ki biyani..", ta juya lulu eyes dinta ta wani ci mur sai kace ita aka yiwa ɓarnar tace "nawa ce wayar taka ba sai na biyaka din ba..", ganin yadda tayi mganar ba tare da wata nadama ba yasa yaji ta matuƙar basa haushi, wai maimakon tace yayi haƙuri shine har tanada kwarin guiwar da zata tambayi nawa wayar, shi yasan ba tada kuɗin da zata biyasa a yanxu dai, kawai ya faɗi hakan ne to test her yaga irin girman kanta, ɗalle bakin yayi yace "wa ya gaya miki da kuɗi zaki biyani nonsense..", da sauri ta kai hannu ta shafa bakinta, ai kam ta dangwalo jini, tace "kai ka kai ka kai toh idan ba da kuɗi ba da mai ka sayi wayar da zaka dakar min baki haka..?, kuma naga ai ba ina sane na fasa ba.." tana gama faɗin haka ta yunƙura zata bar wajen, ya zaunar da ita da sauri, ƙafafuwansa da ya rutsa nata yasa ya matseta snn ya rutsa hannayenta da hannu ɗaya, kokawa ta fara yi dashi tana gunguni ita lallai sai ya saketa, dan kanta ta haƙura ganin bazata iya kwacewa ba, yace "har yanzu ba kiyi nadama ba young lady..", hijab dinta ya tattaro ya kawosa zuwa laps dinta, zaro ido tayi tana mutsu mutsu tace "malam meye haka... ni ka sake..", ya kalleta ba tare da yace komai ba, hijab din ya zare daga kanta ya sauka a wuyanta, nan da nan ƴan hanjin Hajar suka juya, idonta kamar zai faɗo tana turo baki tace "ka sake ni malam...", kwafa yayi ya cije lower lips dinsa painlessly yana kallon yadda take zabga masa harara, ba tay aune ba ya cire hular kanta, ta fasa ƙara a gigice ta kai masa cixo a hannu, gwaɓe bakinta yayi yace "karki kuskura..", tini idonta ya kawo ruwa jikinta na tsananta rawa, hijab din ya cire gaba ɗaya daga jikinta, wata gagarumar ƙara ta fasa har saida ya runtse idonsa sbd yadda ear drum dinsa yayi beating, he can feel yadda jikinta ke rawa, sbd kayan bacci ne ajikinta shiyasa ta razana sosai, ya ɗalle lips din yace "karki sake min ihu a nan, are you mad, by now kin fahimci da mai zaki biyani wayana..", wani numfashi ta sauke tamkar zata shiɗe ta fara girgiza kai, tama kasa yin magana tsabar yadda take shivering, bata sake firgita ba saida taji ya ɗaga ƴar rigarta sama, ta muskuta baya tana ƙoƙarin fixge kanta, janyota yayi da ƙarfi har kusancinsu yafi na da, bakinta na rawa sai kace an jona mata shocking tace "wayyoh Allahna na shiga uku na lalace... nifa ba ƴar iska bace..", sosai tayi mugun basa dariya amma ya shanye yace "nima ba ɗan iska bane amma saina fanshe wayana..", wnn furucin da yayi ba karamin ɗaga mata hankali yayi ba, hannunsa ya zura cikin rigarta, idonta yayi wani farrr sai kace wacca zata suma kafin ta kwallara ƙara da iya volume dinta tace "Allahumma ajirni fi musibati... na shiga ukuna..", ya ɗago kansa yana kallon yadda hawaye ya wanke fuskarta tass, gashi kuma tayi jajir sai kace jan ƙosai, a gigice tace "yi haƙuri don Allah, dan girman Allah kayi haƙuri", idonta a runtse bama ta kallonsa, yayi ajiyar zuciya kafin ya ciro hannun daga rigarta yace "maimaita..", lips dinta na rawa tace "kayi haƙuri dan Allah..", ya gyaɗa kai yace "ni sa'an kine da zaki ringa min rashin kunya..?", ta girgiza kai har lokacin bata buɗe idonta ba tace "A'a wllh kai ba sa'ana bane ka girmeni..", yace "good.. zaki sake min rashin kunya..?", nan ma ta girgiza kai tace "A'a wllh har abada bazan sake ba.. kayi haƙuri don Allah..", yana sakinta tayi baya luuu zata fada kan glass din center table din, fixgota yayi yace "open your eyes..", a daburce ta buɗe idon, samm taƙi yarda ta haɗa ido dashi, ta yayibi hijab dinta da ya wurgar kan carpet ta lulluɓe jikinta, a miliyan ta haura sama har tana zabga tuntuɓe, yabi bayanta da kallo yace "Silly girl..", wayarsa da ta faɗi nan kan carpet ya sunkuya ya ɗauka, ya ringa jujjuyata a hannunsa kafin ya tashi ya haura sama da ita.

★Ƙarfe Shida da rabi Ruqayyah ta fito wanka, bayan ta gama shafe shafenta ta buɗe wardrobe ta ɗauki doguwar rigar atamfa ta saka a jikinta, palour ta fita ta shiga kitchen ta haɗa thick tea ta fito, bread ta ɗauka a kan dining ta shafa masa strawberry jam sbd rashin appetite da ta tashi dashi, slowly take cin abincin tana turawa da kyar, da kyar taci slice biyu na bread din shima jam din ne ya taimaka mata taci, ta shanye tea din shima daman ba mai yawa ta haɗa ba, room dinta ta koma ta bude bedside drawer ta ɓalli 2tablets of paracetamol ta sha da bottle water dake kan mirror, daga nan ta saka hijab din da ta fito dashi ta ɗauki handbag dinta ta fita, ta shiga room din Momy ta tarar bata nan, she knows tana part din Daddy kawai ta juya ta fita compound, bayan ta bar layin gidansu ta samu wani pos ta cire cash sbd na jikinta ba zasu isheta ba, ta tsari napep ta shiga, bayan tafiyar 20mins ya ajiyeta a motor park, Ruqayyah bata shiga ko wace mota ba sai wacca taga ta kusa cika, tana shiga motar ta tashi cause itace ta cike wajen mutum ɗaya daya rage, ƙarfe takwas suka isa Zaria, wayarta ce ta fara ringing, ta cirota daga handbag ganin mai kiran tayi sauri ta ɗaga, from the other side Momy tace "kina ina Ruqayyah, na duba room dinki bakya nan..", Ruqayyah ta haɗiyi yawu tana neman ƙaryar da zata rangaɗa, jin shiru Momy tace "ba kya jina ne..?", Ruqayyah tace "Momy gidansu Meema naje..", Momy tace "da safiyar Allah kika je musu gida..", Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya bayan sun gama waya da Momy, bayan tafiyar almost 2hrs suka iso garin Kaduna, ta biya kuɗin motarta snn ta fito daga motor park din, napep ta tare, ya tambayeta ina zata tace "Malali..", yace "Malali wacce..?", Ruqayyah tace "Malalin har nawa ce ni Ruqayyah..", ya gaya mata, taɓe baki tayi tace "toh muje dai wataqila na gane idan mun shiga garii", da kyar Ruqayyah ta iya gane gidan bayan sun gama gallafiri tsakanin unguwanni, mai napep kam ya cajeta kudi da yawa, ta fello haƙƙinsa ta basa ita dai tinda ta gane gidan ai mgana ta ƙare, almost 3yrs fa rabonta da zuwa wata kaduna, wani gida mai bakin gate wanda yake da manyan bishiyar dogon yaro a gabansa ta isa, tayi knocking door, few seconds mai gadi ya buɗe mata, shiga compound din tayi ta wuce main building din gidan, sai a lokacin taji fargata tazo mata, ta dake ta shiga da sallama. yaran da suke zaune palourn su uku suka ɗaga kai a tare suna kallonta, kamar yadda bata ganesu ba suma haka basu santa ba, babban cikin kawai ta gane tace "Mujaheed..", yayi yaƙe ya gaisheta duk da dai bai santa ba, sauran ma suka gaidata, kan kujera Ruqayyah ta zauna tana raba idanu, courage dinta ma duk ya fara narkewa, Ruqayyah ta kira ƴar macen, yarinyar ta taso ta tsaya gefenta, Ruqayyah tace "ya sunanki..?", yarinyar tace "Hanan..", Ruqayyah tace "ina Mamamki..?", Hanan tace "tana gidan mu, ni jiya aka kawoni nan wajen Mammah..", Ruqayyah ta gyaɗa kai bata kai ga cewa komai ba aka buɗe wata ƙofa, wata dattijuwa ce ta fito da tray a hannunta an ɗora masa cups uku tana mita "wnn wane irin rikici ne, na gama ɗawainiya da iyayenku kuma yanzu na ɗora da taku, dan bala'i duk sati sai a kawomin ƴaƴa wai weekend, iyayen ku nacan suna tiƙar bacci ni an barni da tashin sassafe da guntuwar hamma..", sai kuma tayi shiru ganin Ruqayyah tana ƙanƙance ido, Ruqayyah ta zamo ƙasa tace "Mammah ina kwana..", Mammah ta ajiye trayn da ta haɗowa jikokin nata shayi tana kallon Ruqayyah da kyau, Mammah ta riƙe haɓa tace "Ruqayyatu hala dai ɓatan kai ki kayi ko..?", Ruqayyah tayi murmushin yaƙe tace "A'a Mammah zuwa nayi na gaisheku..", Mammah tace "toh sannu da zuwa daga kanon kike..?", Ruqayyah ta gyaɗa kai tana murza fingers, kitchen Mammah ta koma ta fito da plate din dankali da kwai ta ajiyewa jikokin nata da har sun afka kan shayin da ta ajiye musu, daga nan ta zauna suka gaisa da Ruqayyah da kyau tana tambayarta Daddyn ta. ƙarfe biyu da rabi Mammah ta shiga ɗakin da aka sauki Ruqayyah tace "kinci abincin..?", Ruqayyah tace "Eh naci..", Mammah tace "toh kixo ku gaisa da mijin naki, ni tsautsayi ne ma ya sani na kai kishiya har ɗaka..", Ruqayyah dai tayi murmushi ta tashi tabi bayan Mammah, ɗakin Kawu wanda yake ƙanin mahaifin Daddy Mammah ta kai Ruqayyah, kana ganin dattijon kasan sun haɗa dangantaka da Daddy don kamar shi ya haifi Daddy sbd resambulance, da ladabi Ruqayyah ta gaida Kawu, ya amsa yana tsokanarta a matsayinta na jikarsa, Ruqayyah ta duƙar da kai tana wasa da ƙafarta, a hankali ta shigar da ainahin abinda ya kawota Kaduna, Kawu ya gyaɗa kai bayan sauraronta yace "toh ko so kike ki zama tsohuwar guzuma babu aure ƴar nan.. naga tsohon naki gata zai miki..", Ruqayyah ta fara sharar hawaye tace "Kawu wllh wnda zai auramin ne banaso..", Kawu ya jinjina kai yana kallonta da kyau yace "ja'ira daman ba zuwan Allah da ma'aiki kikay ba, ashe takakkiyarki ce ta kawoki". kafin magrib Ruqayyah ta iso kano, a galabaice tazo duk tayi wani wiƙi wiƙi, daman ba wata lfy ta samu ba kuma shine ta tarki uwar tafiya.

★Bayan sallar la'asar Hajar ta buɗe ƙofar ɗakinta a hankali, saida ta gama ƙarewa corridor kallo taga babu kowa snn ta fito, walking slowly ta sauka downstairs, zuciyarta ta ringa bugawa cause ba ta son encounter dashi, luckily for her ta tarar babu kowa a palourn, da sauri ta shige kitchen ta dafa Noodles sharp sharp ta fito, tana rufe ƙofar saiga footsteps ana sakkowa ƙasa, ta ɗaga kai ta kalli stairs din, suna yin ido huɗu tayi sauri ta juya masa baya tana turo baki, runtse idonta tayi ta wawaki handle ta murɗa ta koma kitchen din ta rufe ƙofar, jingina tayi da ƙofar tana mayar da numfashi, kawai abinda ya mata yau da safe ke mata yawo a brain, idan ta tuna sai taji tamkar ƙasa ta tsage ta shige, bayan kamar minti goma ta buɗe ƙofar ta leƙa, ajiyar zuciya tayi ta fito ta haura sama bayan hancinta ya cika da ƙamshinsa da ya bari a palourn. washe gari Nurain ya fito daga room dinsa ya gama shirinsa na fita aiki, har zai sauka sai kuma ya duba tsadadden agogon dake wrist dinsa, ƙarfe tara da minti biyu, ƙofar room dinta ya buɗe ya shiga, Hajar dake zaune gefen bed ta ɗago ta kallesa, tin ɗazu ta tashi tayi wanka ta shirya, so take ta fita amma kuma ta kasa, tana ganin shine ta tashi da mugun gudu ta shige bathroom ta garƙama lock, Nurain ya haɗe thick eyebrows dinsa ya ringa kallon ƙofar bathroom din kafin ya juya ya fita, yana zuwa hospital din patient huɗu yayi attending suka shiga meeting, akan Seminar da nan da 3weeks zata zo akay meeting din, shi dai baiso ba kwata kwata, don har dashi acikin wadanda zasu, duk yadda yaso ya noƙe kar yaje amma haka Dr Mansoor yace ai shine zaiyi representing thoracic surgeon, bbu yadda Nurain ya iya hka ya fito meeting din under probability don yace sai yayi tunani tukun, baima koma office dinsa ba kawai ya bar hospital din, saida ya biya aiken da Abba ya masa na amso passports snn ya wuce gidansu, da yamma ya shiga wajen Abba ya kai masa saƙon tinda ya dawo a lokacin, da sallama ya shiga great room din, yana zama saiga Abba nan ya fito daga bedroom, bayan sun gaisa Nurain ya ajiye envelope din da ya shigo da ita yace "gashi Abba..", Abba ya buɗe envelope din ya fara ciro passports din, Nurain na kallon passports din yace "harda Noor ne..?", Abba yace "yeah..", Nurain ya gyaɗa kai yace "amma exams din fa..?", Abba yace "kafin nan ta gama ai, tace nan da 2weeks zata gama exams din..", Nurain yace "alright.. bari na wuce mosque..", Abba yace "Ohk" da haka ya tashi ya shiga bedroom to perform ablution. da misalin karfe takwas da rabi na dare Nurain na tsaye jikin motarsa yana jiran Noor, hannu na dukan cinya Noor ta fito compound din ta isa bakin motar tana kallonsa tace "Mami ta hana na zuba maka abincin wai kaci a gida..", kasa cewa komai yayi ya tsaya yana kallonta, Noor da taga reaction dinsa weird tace "Yaya wai Anty Hajar din bata iya girki bane..?", yace "just cut it good night...", motarsa ya shiga ya bar gidan with speed, yana zuwa gida yayi refreshing kansa ya sakko downstairs, cup of Café latte ya haɗama kansa, da cup din a hannunsa ya fita balcony ya zauna kan kujera dake wajen, slowly yake sipping coffee, kira yaga yana shigowa ta jikin smart watch dake hannunsa, daman yau duk dashi yayi amfani wajen calls, airpods ya ciro daga pocket dinsa ya saka one ear, Calmly yace "yeah sister..", from the other side Sakeena tace "brother tataccen mai kirki how are you..?", yayi murmushi don ya fahimci ba'a take masa yace "am fine alhmdllh..", tace "toh Yayi.. ya Hajar..?", yayi sipping coffee yace "kin bar mijinki shi kaɗai ni zaki hanani bacci nan haka..", tace "Yah c^mon bani amsana...", yace "ohh she's fyn..", tace "good..", dariya yayi yace "are you alone..?", tace "yess yess", ya sake yin wata dariyar yace "toh don kar kije kiyi ihu ki razana mutane...", tace "toh nidae ka gayamin mene..?", yace "hmm wai daman Umrahn babu ke za a..?", Sakeena ta miƙe daga kan kujerar da take kwance tace "bangane bani ba, harda ni mna..", Nurain ya gyara airpod din kunnesa ya ɗauki cup of coffeen sa ya shiga ciki, Sakeena tace "tafiyar tazo ne..?", yace "A'a ban sani ba fa, nida babu ni to what concern me da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login