Showing 117001 words to 120000 words out of 252835 words
ƙarasowa ya danna mabuɗin motar da keys din hannunsa, cike da tsiwa tace "bani", ya buɗe front seat ya ciro papern dake aljihunsa ya ajiye kan seat yace "pick it..", ta wani galla masa harara ta wuce ta ɗauka, da sauri ya koma ta bayanta ya turata cikin motar, ta zabura zata bar wajen hakan yasa yayi wrapping dinta a ƙirjinsa, tana shirin kwala ihu ya toshe mata baki, within few seconds ya sakata a motar ya kulle, saida ya zaga driver seat snn ya sake buɗe motar ya shiga, dukan glass din motar ta fara yi tana cewa "malam ka buɗe min ƙofa na fita", Nurain kam resting yayi da kujera yana sauke ajiyar zuciya, a hankali yace "damn it", tana jin ya kunna motar ta kwala wani uban ihu sai kuma ta fashe da kuka ta haɗe kanta da guiwa, shi dai baice mata ƙala ba ya fara driving dinsa, a wani eatery ya tsaya yayi take away snn ya fito, back seat ya buɗe ya ajiye ledar abincin kafin ya shiga driver seat, har suka je gida Hajar bata dena kuka ba, bayan yayi parking motar ya buɗe ya fito, ledar abincin ya ɗauka ya zaga side din da take ya buɗe yace "come down..", a hankali ta zuro ƙafafuwanta ta sakko, ya mayar da ƙofar ya rufe snn ya kulle motar, hannunta ya figa suka wuce ciki, saida ya haura har sama da ita snn ya saketa bayan sun shiga har room dinta, ledar abincin ya ajiye nan kan chest of drawers yace "ba takardar saki kika ce na baki ba toh ai gata nan na baki..", Hajar ta dubi papern da ta dunƙule a hannu sai kuma ta ɗago tana kallonsa, ya ɗaga shoulder ya fita daga ɗakin, da sauri ta shiga warware papern hannunta har na rawa, kawai ta tsinci rubutunta a jiki, wurgi tayi da ita ta sulale ƙasa ta fashe da kuka, ji tayi hijab dinta na ƙamshinsa, ta tashi ta cire hijab din ta shiga bathroom ta wanke fuskarta, sai kuma taji tana son tayi wanka, saida tayo wankan snn ta fito da wata azababbiyar yunwa, tin safe babu abinda ta zubawa cikinta ko ruwa, turo baki tayi ta ringa kallon ledar abincin da ya ajiye mata, ta saka kayan bacci snn tazo ta ɗauki ledar ta buɗe. washe gari da safe Nurain na zaune palourn downstairs yana shan Coffee, ga laptop gefensa yana operating, Hajar ce ta sauko ƙasa da ledar abinci a hannunta, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta, kitchen yaga ta shiga, ya ajiye coffee cup din ya tashi ya bita kitchen din....✍️
you can join my WhatsApp group by clicking the link below
💛 HAJAR 💛
{52..}
Hajar ta ajiye ledar hannunta kan cabinet, juyowa tayi jin motsi a bayanta, ba tare da ya dubeta ba yayi folding hands yana kallon gas cooker yace "kin iya amfani dashi..?", ta kalli gas cooker din sai kuma ta dubesa tace "A'a saika koyamin..", nodding kansa yayi don ya gane kalar amsar da ta basa, now bazai biye mata ba, without looking at her yace "alright.." ya ƙarasa gaban gas din ya ɗauki lighter ya kunna sai kuma ya dubeta yace "like this.. idan zaki rage wuta da ƙarawa duk da control knob din za kiyi amfani.. kin gane..?", ta juya lulu eyes dinta tace "Eh nagane.." yace "fyn" ya bude fridge ya ɗauki raspberry drink na kwali, cupboard ya buɗe ya ɗauki glasscup, har zai bar kitchen din sai kuma ya dakata yace "i told you babu gage a nan duk abinda kika gani a kitchen din nan idan kina so ki dauka kici.." da haka ya buɗe ƙofa ya fita, ta taɓe baki ta riƙe haɓa tace "nida jangwangwan ai dole ka tmbyeni na iya amfani da gas sbd kaje gidanmu, toh koda nake ƴar malam shehu naje makaranta, koda ilimina ai na kunna shege gas..", Noodles ta dafa ta zauna nan kitchen din taci, tana gama ci ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa ta sha, saida ta gyara kitchen din ta wanke komai snn ta fita, har lokacin Nurain na zaune palourn, daman ko gigin kallon position din da yake ba tayi ba ta haura sama, ya tashi ya shiga kitchen din yana ƴan dube dube, komai na nan a mazauninsa babu alamar anyi girki, ya fito kitchen din ya zauna yayi crossing legs ya cigaba da aikinsa jikin Laptop. Hajar ta kimtsa ɗalinta sama sama kafin ta shiga bathroom, ruwan zafi ta tara a bucket ta fito tana jiran ya kai yadda take so, wayarta dake jone a charge ta cire ta shiga kiran Umma, Umma na picking Hajar tace "Umma ina kwana..", a takaice Umma ta amsa tace "kunje gida lfy..?", Hajar tace "Eh Umma ya jikin Yayan..?", Umma tace "jiki alhmdllh..", Hajar tace "toh Allah ya ƙara afuwa..", Umma tace "Ameen, Allah ya miki albarka..", da haka suka katse kiran, Hajar na shirin ajiye wayar ta tina da ruwan zafin da ta tara a bucket, tsabar sauri bata iya ajiye wayar ba ta tafi da ita bathroom din, ai kam ruwan ya cika bucket din dam, ta zaro ido ta tafi zata kashe, wani irin santsi ne ya ɗebeta suuu tana shirin sulewa a ƙasa tayi sauri ta dafa kan pampo, pressure da ta bayar a pampon yasa wayar hannunta ta suɓuce ta faɗa cikin bucket din ruwan zafin, gwalo ido tayi tana shirin kelayar da ruwan zafin sai kuma ta fasa sanin hakan babu kyau, ga wayarta tsamo tsamo ta lume can ƙasan bucket din, bowl din diban ruwa ta ɗauka ta kanfato ruwan tare da wayar, da sauri ta tsame wayar ta hau bibbigeta a hannu, ta fito daga toilet din still tana bibbige wayar, ta zauna gefen gado tana gogeta da ƙasan rigarta, ta danna switch ta kunnata, sai gashi ta kawo few seconds da kawowarta sai kuma ta fara farfaɗiya daga nan kuma ta ɗauke gaba ɗaya, babu irin dabarar da Hajar bata gwada ba amma waya taƙi kamawa, daga ƙarshe ta ajiyeta kan mirror a daidai saitin AC, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi yanxu idan wayarta bata tashi ba dame zata ringa communicating da ƴan uwanta, bathroom ta shiga tayi wanka da ruwan da ta tara don har ya huce, tana fitowa ta sake gwada kunna wayar amma bata tashi ba, ta gama shiryawa tsaf bayan ta saka wata doguwar riga material wacca akaiwa ɗinkin tsuke baby armless da tail, sai kace wata yarinya haka kayan suka mayar da ita. tanata zaune a ɗaki abin duniya ya isheta ƴar wayar da take rage mata zafi ma ta margaya, a haka har akay sallar Azahar ta tashi tayi, linke dardumar da hijab din tayi ta ajiye, ta gyara hular kanta ta fita daga ɗakin, a hankali ta sauka daga stairs tana jin kamar ta kurma ihu sbd a maƙoshi lalacewar wayar ya tsaya mata, tana kaiwa tsakiyar palour aka buɗe ƙofa aka shigo, tsaye tayi tana kallonsa don ita a tunaninta baya nan, kallon da ta lura yana mata ne yasa ta dubi kanta, wani irin gwalo idanu waje tayi ta ruga da gudu ta koma sama, Nurain ya taɓe baki ya ƙarasa shigowa ciki, yau Saturday babu inda yaje yanxun ma daga masallaci ya dawo, kan doguwar kujera ya hau ya kwanta ya miƙar da legs dinsa, a haka yake amfani da wayarsa, stairs ya duba jin footsteps, lokaci guda ya ɗauke kansa ya cigaba da kallon wayarsa, a zuciyarsa yace what is she covering, Hajar na shiga kitchen ta tattare hijab din da ta zumbula ta fara tunanin me zata girka, bai ɗauketa wani lokaci mai yawa ba ta fara sarrafa wata haɗaɗɗiyar jollof rice wacca ta zuba mata isasshen kifi da kayan miya exclude tomato. Nurain ya tashi daga kwancen da yake yana kallon ƙofar kitchen din, da hannu ya ja pointed nose dinsa jin wani aroma da yake hudasa, hancinsa ya ringa perceiving aroman ba ƙaƙƙautawa, ji yayi stomach dinsa na shaking ya tashi da sauri ya zura room slippers dinsa ya wuce sama. Hajar na gama girkinta tayi serving kanta a plate, ta juye ragowar a warmer ta haura sama da ita. wajen ƙarfe biyar da minti huɗu tana zaune kan stool tana combing hair dinta, gwara dai ta yiwa kanta qiyamul layli tinda ynxu ba ta gida bare Umma ta taimaka mata, don idan ta bari kanta ya danƙare saita gane kurenta, slowly take combing hair din tana yamutsa fuska, wai ma a hakan saida ta jiƙasa da oil, ƙofa aka buɗe aka shigo tare da sallama ciki ciki da murya mai zurfi, ɗaga kanta tayi sukay ido huɗu dashi, ta haɗe gira ta ajiye comb din hannunta kan mirror tace "nifa ka dena shigo min babu notice..", yayi folding hands dinsa a ƙirji yace "bayan sallamar da nayi akwai wani abu bayan ita ne..?", ta miƙe tsaye tana mayar da gashin daya rufe mata fuska baya tace "Amma dai kasan babu kyau, kai ba muharrami na bane dan haka bai kamata ka ringa shigo min ɗaki babu sanarwa ba..", yace "Ohh really, su iyayen naki basu gaya miki me suka miki ba kafin a kawoki nan din", ta yamutsa fuska tace "me kwa aka min din.. nidae ka dena shigomin ɗaki ehe..", sai kuma ta fara gunguni ƙasa ƙasa tana cewa "hka kurum zai kalleni a bati", zamm yaji abinda ta faɗa don yanada sharp hearing mechanisms, yace "ke!! kinje islamic school kuwa..?", cike da tsiwa tace "A'a jira nake kazo ka kaini aii..", tana ganin ya fara tunkarota tayi baya tana turo baki, ya ajiye wayarsa kan mirror, kafin ta ƙara one step backwards yayi wuff ya cafke hannunta, yace "idan bazaki gaji ba nima bazan gaji ba..", tana jin zai ɗaure mata hannaye a baya ta fara ƙoƙarin kwatar kanta, nan ya gwada mata ba ƙarfinsu ɗaya ba, duka hannayenta ya riƙe da hannu ɗaya ta bayanta, ɗalli ya kaiwa lips dinta yace "do i look like your mate ba..?", tini ta guntse lips din ta mayar dasu ciki yadda bazai iya ɗallesu ba, sakinta yayi yace "da kin cigaba dai..", ja da baya tayi tace "karka sake taɓani dan ni ba ƴar iska bace..", slight smirk yayi yace "ƴar iska ce mna tinda gaki nan zaune gida ɗaya da namiji..", ta gwalo idanu tace "chaɓɗi jamm wllh ni ba ƴar iska bace, dole akamin nake zaune a nan..", wani mugun kallo ya watsa mata ya ɗauki wayarsa ya nufi door, har zai fita sai kuma ya juya yace "thank God wanda suka kawoki sun san ina ne nan din a wajenki which is gidan aure..", habawa ai wani irin tafashe Hajar taji a zuciyarta, tini fuskarta ta canza tamkar wacca aka saukarwa da wahayin mutuwa, zuciyarta ta harzuƙa iya harzuƙa, sosai Nurain ya fahimci wnn sauyin don shima saida yaji tasa azabar da ya faɗi hakan amma ya lura ita har ta fisa shiga shock, muryarta na rawa tace "meye kuma wani aure.. wa aka kawo gidan aure.. kaika sansa wllh tllh ni kam banida wani aure, aure a ina.." sai kuma ta durƙusa ƙasa ta fashe da kuka tace "ƙarya ne wllh Allah, ba wani aure da aka min..", ya taɓe baki yace "Silly girl" yayi fitarsa daga ɗakin. downstairs ya sauka ya fita compound, parking space ya isa ya shiga motarsa ya bar gidan zuwa nasu.
★Ruqayyah na kwance kan gado tunani iri iri ke yawo a brain dinta, babu abinda take tunawa sai time din da sukay sharing da Dearest, ba ƙarya sun zuba soyayya mai danƙo mara algus, soyayyar da take ganin zata kaisu ga aure, soyayyar da take ganin bazata taɓa mutuwa ba, toh me yasa wnn soyayyar take ƙoƙarin tabarbarewa ne..?, me yasa dearest zai gaya mata magana mai zafi irin wnn, wai yana da aure, shin yanada auren ne ko kuma kawai so yake ya ƙuntata mata, a lokacin da ya gaya mata wnn mummunar kalmar tayi tunanin zuciyarta ta buga ne don ji tayi tamkar an ɗauki wuƙa mai shegen kaifi an tsagata gidan biyu snn aka barbarɗa mata gishiri, tin shekaran jiya batada wani kuzari tana kwance ne kawai a ɗaki, jiya ma ko aiki bata je ba duk da cewa tanada night duty, wasu hawaye suka cika mata idanu, lokaci guda suka fara bin gefen fuskarta suna shiga ramin kunnenta, door akay knocking kafin aka murɗa handle aka shiga, da sauri Ruqayyah ta goge hawayenta ta miƙe zaune tana kallon Momy da ta shigo, Momy ta dubeta tace "ya jikin..?", Ruqayyah tace "da sauƙi sosai..", Momy ta gyaɗa kai tace "Ohk sannu your father is calling...", Ruqayyah ta ɗan zaro ido tace "Momy lfy..?", Momy ta nufi ƙofa tace "idan kinje kya ji.." ta buɗe ƙofar ta fita, sakkowa Ruqayyah tayi daga kan gadon ta saka hijab dinta ta fita, palourn Daddy ta shiga da sallama tana rarraɓewa tamkar munufuka, kanta a ƙasa ta zauna kan carpet a hankali tace "Daddy ina yini..", Calmly yace "lfy..", tayi shiru tana wasa da laushin carpet, Daddy yace "Ruqayyatu..", sai a lokacin ta ɗago kanta tace "na'am Daddy..", Ruqayyah na kuka wiwi ta fita daga palourn bayan Daddy ya sanar da ita ya amshi kuɗin aurenta da Dauda, fagam fagam ta wuce room din Momy tana kuka, Momy dake gyaran wardrobe ta ajiye gogaggun kayan hannunta tace "ke lfy kike gursheken kuka haka...?", Ruqayyah ta jingina da bango tana kuka sosai tace "Momy na shiga uku na lalace da rayuwa, wllh da na auri Dauda gwara na mutu..", Momy tace "ce miki akay auren Daudan za kiyi ne..?", Ruqayyah ta tsagaita kukan tace "Daddy ne ya amshi kuɗin auren Dauda..", Momy ta tsuke ido tace "Daddyn ne ya gaya miki haka..", Ruqayyah ta gyaɗa mata kai, Momy ta fita daga ɗakin, zaman dirshan Ruqayyah tayi a ƙasa ta ringa rafsa kuka tamkar wacca uwarta ta mutu, after like 10mins Momy ta dawo ɗakin ranta busu busu, don basu wanye da Daddy ta arziƙi ba, cewa yayi yaga alamar so take ta shiga tsakaninsa da ƴaƴansa, duk wani hukunci da yayi ƙoƙarin zartarwa saita kawo nata tawilin wnda ada ba haka take masa ba, shi ya gaji da zama da Ruqayyah a gida ɗaya aurar da ita zaiyi, goɗai goɗai da ita me zai hana a aurar da ita tinda tanada manema ba babu ba, Momy ta zaune gefen gado tana jin tinda take da Daddy basu taɓa samun matsala kamar yau ba, Ruqayyah ce causative agent, tin farko ita taja komai don haka she must harvest what she planted, Ruqayyah ta rarrafa gaban Momy tayi kneeling tace "Momy kin basa haƙuri ko..?, ya haƙura bazai aura mim Dauda ba ko..?", tureta Momy tayi tace "na gaji Ruqayyah, kawai ki haƙura ki auri Daudan shine zaman lfy na da kuma naki..", daɓas Ruqayyah ta koma ta zauna ba shiri tana girgiza kai, ta wawaki ƙasa ta miƙe ta fita da gudu ta bar ɗakin, dole ta nemawa kanta solution, don wllh tllh bazata auri Dauda ba, safa da marwa ta ringa yi a ɗakinta tamkar wacca ta shirgawa sarki ƙarya, wata babbar dama ce tazo mata kwanya, shi kaɗaine zai iya dakatar da Daddy, gobe goben nan zata kama hanyar Kaduna da yardar Allah, yanzun ma dan yamma tayi ne da babu zai hanata ɗaukar hanya.
★Abba na kallon Nurain yace "ranar Monday zaka amso mna passport din..?", Nurain yace "tom Abba.. zuwa wani lokaci Visa zata fita..?", Abba yayi resting da kujera yace "bazata wuce nan da 3weeks ba insha Allah..", Nurain ya gyaɗa kai yace "harda Hajiya ne..?", Abba yace "yeah..", Nurain ya jinjina kai yace "alright.. can i excuse myself..?", Abba yace "sure", tashi Nurain yayi ya bar great room din, bayan sallar isha'i Nurain na zaune palourn Mami, Mami tace "dan ma dai angama processing komai ne aida da Hajar zamu wuce..", Nurain ya kalleta bai dai ce komai ba, Mami ta numfasa tace "Son i hope all is well..", ajiyar zuciya yayi yace "yeah Mami..", Mami ta ringa kallonsa don yayi losing weight, ba haka yake ba, tace "toh cut down on coffee yasa kana ramewa fa..", ya zaro ido yana shafa fuskarsa yace "Mami coffee ne zai ramar dani", tace "toh idan bashi ba mene ne, bayan ma kullum anan sai kayi ƙat da abinci..", dariya yayi wacca ta tsaya iya throat, Mami ta kalli Tv tace "toh ga gaskiya..", Noor ce ta shigo da box din doughnuts da tayi order a hannunta, ta ajiye box din tace "Mami ga doughnut..", Mami ɗauki one piece cikin pieces shida dake cikin box din mai filling din foam milk with chocolate, Noor ta ɗauki box din ta ajiye kusa da brother dinta tace "Yaya fa..", ya girgiza kai yace "A'a", tace "toh na kawo maka cake" bata jira cewarsa ba ta tashi ta fita, da plate ta dawo palourn mai ɗauke da variety na cake, akwai red velvet with whipped cream, milk coconut cake, sai kuma chocolate cake, miƙa masa plate din tayi ya amsa yana kallon abin ciki, spoon dake gefe ya ɗauka ya fara ci a hankali, Noor ta zauna gefensa tana cin doughnut ita kuma tace "Yaya ya kaji cake din...?", yace "not bad..", tayi murmushi tace "nifa nayi..", yace "gashi nan kam har kin fara shirga kiba tinda kin durfafi cin wnn tarkacen..", ta zaro ido tace "aikam basa sa kiba Yaya.." sai kuma ta fakaici kallon yadda yake cin cake din tace "Yaya na dakko system din..?", ya ajiye plate din yace "Au bribery aka bani knn.. toh am leaving..", ya tashi ya yiwa Mami sallama, kafin ya nufi door ya kalli Noor, ta fakaici kallon Mami tayi sauri ta ƙifta masa ido, fita yayi daga ɗakin, yana fita da kamar minti biyar Noor ta ɗauki plate din cake da ya ajiye tace "bari na mayar da abuna fridge.." ta tashi ta fita tana kallon Mami da wutsiyar ido, da sauri ta wuce kitchen ta zuba abinci a warmers ta jera a basket, ɗaukar basket din tayi ta buɗe ƙofar kitchen din ta baya ta fita, ta zagaya