Showing 141001 words to 144000 words out of 252835 words
hakan shine worst. wayarsa ya ɗauka ya canza flight din daga na safe zuwa dare bayan yayi booking wani seat din, yayi ajiyar zuciya yayi resting da kujera. washe gari ƙarfe goma Hajar na tsaye kitchen tana dafawa kanta breakfast, bayan ta gama ta zauna kitchen din taci snn ta wanke komai da tayi amfani dashi ta fita, palour ta fita ta fara kakkaɓe cuisine tana arranging trow pillows, yamutsa fuska tayi sbd cikinta da ya murɗa a bazata, ajiye duster din hannunta tayi ta haura sama hannunta dafe da cikinta, tasan ma cramps ne yake shirin antayo mata, haka ciwon ya wuni yi mata saidai bai tsawaita ba shiyasa bata wahala kamar yadda yake mata ba, zaune take kan darduma bayan ta idar da sallar magrib, a ynxun ma dai cikin ne ya ɗan murɗa mata, kawai jira take ayi sallar isha'i ta tashi tayi ta kwanta kawai, ƙofar ɗakin aka murɗa kafin aka buɗe aka shigo, ta ɗaga kai tana kallonsa, tini pure men scent dinsa ya bulale ɗakin, yayi sallama ciki ciki kafin ya ƙaraso cikin ɗakin, yana kallonta yace "ki haɗa duk wani abu da kika san zaki buƙata idan zaki wani wajen kwana...", ta ɗago ta kallesa sai kuma ta ɗauke kanta ba tace komai ba, ya kalli tsadadden agogon wrist dinsa yace "you just have 10mins to do that.." yana gama faɗin haka ya juya ya fita, taɓe baki tayi ta jinginar da kanta da gado, after 15mins Nurain ya sake dawowa ɗakin, zaro piercing eyes dinsa yayi ganinta inda ya barta ɗaxu, kawai gani tayi ya shigo ɗakin ya wuceta ya tsaya gaban makekiyar wardrobe din kayanta, buɗe wardrobe din yayi ya ringa kallon ciki sai kuma ya rufe ya buɗe wani section din, boxes din lefe ya gani an jerasu a ciki, ƴar madaidaiciyar box ya sauke ya ɗora kan bed ya buɗeta, cike take da kaya ya zazzage kayan ya barta empty, daga nan ya fara sauke ragowar boxes din, Abaya set uku ya ɗiba ya zuba a empty box din, sai kayan bacci da ya kwashi wajen set shida suma ya zuba ciki, Hajar dai na zaune inda take tana binsa da ido, ya mayar da boxes position dinsu wacca ke kan bed kawai ya bari, ya sake buɗe section din kayanta ya fara janyo duk wnda hannunsa ya fara taɓawa, haɗe gira tayi ta miƙa tace "meye haka wai, ni ka dena taɓamin kaya..", banza yayi da ita har ya gama ɗebar abinda zai ɗauka ya jibga a box din, bathroom ya shiga ya fito da shower gel da spoonge, ya zuge ƙaramin zip na akwatin ya zuba a ciki, daga nan ya wuce gaban mirror, tsaye yayi yana kallon tarkacen kai ya rasa abinda zai ɗauka don mirror din a cike yake da kayan shafe shafe, juyawa yayi ya kalleta for the first time yace "zo ki ɗauki abinda kika buƙata a nan..", with confusion written all over her face take kallonsa, ya haɗe thick eyebrows dinsa strictly yace "Ba magana nake miki ba... you are wasting my time malama..", saukar da idanunta tayi ta isa gaban mirrorn ta fitar da body lotion din da take shafawa sai perfumes guda huɗu, ya kalleta yace "is that all you need..?", turo baki tayi ta ɗauki hair butter da oil tayi drawing drawer ta ɗakko comb, ya kalleta da gefen ido kafin ya kwashe kayan shafar ya zuba a box din ya zugeta ya ɗauka ya nufi door, juyowa yayi yana kallonta yace "get change right away" da haka ya fita, Hajar tabi ƙofar da ya rufe da kallo tana sauke ajiyar zuciya, toh meye haka ne wai, kawai sai tayi tunanin ko gidansu zai mayar da ita ne, hakan yasa taji wani mugun daɗi ta ringa fatan Allah yasa haka ne, within few minutes ta gama canza kaya, doguwar rigar Abaya ta saka tayi rolling kanta da veil din Abayar, ko 1mins ba tayi da gama shiryawa ba sai gashi nan ya shigo, daga bakin door ya tsaya yace "ki jirani a compound", ba tace komai ba ta wucesa ta sauka downstairs, ɗakin nata ya shiga ya kashe duk wasu kayan wuta snn ya rufe ya fita, daman already ya kashe electric appliances na palour dana kitchen, freezer da fridge ne kawai ya bari a kunne sbd perishable food da suke cikinsu, tsaye ya ganta a dan nesa da balcony, ya rufe entrance door kafin ya nufi inda mai gadi yake zaune, Hajar tabi bayansa da kallo har ya gama mgana da Inuwa snn ya wuce parking lot, dashare haƙora Inuwa yayi ya cusa uban kuɗin da Nurain ya basa a pocket, tashi yayi ya fara zuge gate. a hankali Hajar ta isa parking space din ta tsaya gaban motar, shiga motar tayi ta fakaici kallonsa tace "gidan mu zaka kaini ko..?", baiko kalleta ba ya sauke handbrake yace "close the door", sai a lokacin ta rufe ƙofar, driving Nurain ya fara yi bayan ya dubi agogon dashboard wnda ya haska ƙarfe takwas da minti ashirin na dare, Flight dinsu na ƙarfe tara ne so he have to make it there kafin time din, haka suka bar gidan Inuwa na ɗaga musu hannu. Hajar tana ganin ya fara sharara gudu tace "kabi a hankali dan Allah, unguwarmu akwai yara da suke tsallaka titi..", without looking at her yace "Ohk" amma bai rage gudun ba, can dai taga samm hanyar da suke bi ba tayi kama da ta zuwa unguwarsu ba, shan kunu tayi tace "where are you taking me...? nan fa ba hanyar gidanmu bace", yana driving dinsa yace "Ohk", Hajar ba ta sake mgna ba tana jiran taga destination din da zasu, suna isa Airport yayi parking wajen da ake ajiye motoci, ya bude booth kafin ya sauko daga motar, sauke box din kayanta yayi da bag dinsa, har ya gama Hajar ba ta fito ba tana zaune cikin mota, tini idonta ya ciko taf da ruwa, toh ina ne nan din ya kawota, itafa gida ta saka ran zai kaita, buɗe murfin motar yayi yana kallonta yace "come down", ta sauke kanta ta fito a hankali tana bin wajen da kallo, key din motar ya bawa wni ma'aikacin Airport din masu kula da motoci, da haka ya dubeta yace "wuce muje", zirr hawayen da suke maƙale idonta suka zubo tayi sauri ta goge da bayan hannu tace "dan Allah cewa fa kayi gidanmu zaka mayar dani..", ya ɗage gira yace "ni mukayi haka dake..?", shiru tayi can tace "toh idan ba gidan mu ba ina zaka kaini da kaya..?", yace "siyar dake zanyi dan naga za kiyi tsada..", zaro ido tayi tace "am not a toy aii..", bag dinsa ya rataya ya nuna mata box din kayanta yace "Ja muje", maƙe shoulder tayi ba tace komai ba, box din ya fara ja ya wuce ya barta a wajen, saida taga ya mata nisa sai kuma ta kyalla da gudu tabi bayansa, tana zuwa kusa dashi ta fashe da kuka tace "kawa Allah da manzonsa kazo ka kaini gidanmu..", ya cigaba da tafiyarsa, tana biye dashi tana kuka a hankali, da haka suka isa departure har aka gama musu checking aka tafi da kayansu za a saka a jirgi, sai kace wata jela haka take biye dashi tana kuka mara sauti, gashi har lokacin ba ta fahimci nan din ina ne ba, ya amsar musu tickets snn suka wuce filin jirgi don har jirginsu ya fara boading, sai a lokacin Hajar ta fahimci a inda take bayan taga manya mayan Aeroplane da suke a parke. da haka tabi bayansa suka shiga jirgi, seat dake kusa da window ya samu ya zauna ita kuma ta zaune seat din dake gefensa, babu jimawa aka fara announcing jirgi zai tashi, passengers suka fara fastening seat belts, Nurain ma yayi fastening nasa, ganin ba ta saka nata ba yace "ke.. ba kiji abinda akace ba..?", ta kallesa da idanunta da suka ɗan haura tana twisting pink lips dinta, ɗauke kansa yayi bai sake kallonta ba, har jirgin ya hau runway bata saka belt dinta ba, slight hiss yayi ya ɗaura mata da kansa ya koma ya zauna da kyau a seat dinsa, habawa ai jirgi na takeoff Hajar taji wani zimmm ya tsarga mata, ƴan hanjinta suka baro ciki sukay ƙabe ƙabe a kirji, ba ta san lokacin da ta ruƙunƙumesa ba, saida jirgin yayi labelling snn ta sakesa, ta jingina da seat dinta tana jin wani iri, ji take kamar za tayi amai, ta jima bata dawo daidai ba, throughout the journey idonta biyu, shi kam tinda ya kwama headphones a kunnensa ya saka karatun Alkur'ani ya lumshe ido, lokacin da jirgin zaiyi landing Hajar tafi shiga yanayi a kan lokacin takeoff, bayan ruƙunƙumesa da tayi saida ta kifa kanta a ƙirjinsa, a hankali ta fashe da kuka tace "na shiga uku na lalace", haka sauran passengers suka fara fita daga jirgin, Nurain ya cire headphone din kunnensa ya rage murya yace "ɗagani malama..", a hankali ta sakesa tana turo baki, ya ɗan kalleta kafin ya cire belt ya tashi ya wuceta zai fita, bin bayansa tayi da kallo sai kuma ta goge fuskarta ta tashi ta bisa, luggage dinsu ya amso musu da haka kuma suka fita wajen airport din, Cab ya tsarar musu suka hau suka bar Airport din, after a ride of about 30mins drivern Cab din yayi parking cikin wani danƙareren hotel wnda daman shine location da Nurain ya basa, Nurain ya biya mai Cab kuɗinsa da haka ya wuce zuwa reception, wani worker ne ya shigar musu da kayansu, ID card da wata paper Nurain ya nunawa receptionist din, tini ta gane manyan baƙin da akay musu booking ne tin last week, Keycard ta ɗakko ta basa harda ɗan russunawa, ya amsa yace "thank you", tayi saurin cewa "my pleasure sir", ta elevator suka haura zuwa room din nasu dake 15 floor, workern dake riƙe da luggage dinsu ya ajiye daga bakin ƙofa snn ya bar wajen, Nurain ya saka Keycard ya buɗe room din, the room is huge and luxury with big bathroom, Hajar dai tayi tsaye bakin ƙofa tana ƙarewa room din kallo, Nurain ya ɗauki jakar kayansa ya buɗe closet ya saka, bathroom ya shiga ya ɗauro alwala, ya fito yana jan hannun rigarsa, kallonta yayi yace "are you a soldier..?", tayi rolling eyes tace "yess", prayer mat da ya gani a cikin closet ya ɗakko ya shimfiɗa ya kalli direction din da akay indicating a jikin wall, har ya idar da sallar Hajar na tsaye inda take, Atm card dinsa ya ɗauka ya nufi ƙofa yace "excuse me Captain..", ta ɗan matsa kaɗan, ya kewayeta ya fita, saida ya rufe ƙofar ta fahimci fa ita kadai ce a nan din, ƙarasawa cikin ɗakin tayi ta zauna kan couch, tanata zaune a wajen sai kuma ta tashi ta shiga bathroom tayi alwala, ta fito ta kalli inda ya kalla tayi sallahr Isha'i, Sai 11 ya dawo a lokacin Hajar ta gama cika famm da tsoro, yana shigowa ta miƙe tace "ni karka sake barina ni kaɗai..", ya ajiye ledojin da ya shigo dasu kan carpet yace "are you a kid..", sai kuma ya nuna mata ledar abinci yace "take your dinner..", daga haka bai sake kallonta ba ya bude closet ya dauki Pajamas dinsa ya shiga toilet ya saka, yana fitowa ya matsa gaban makeken bed din da ya sha white bedding ya ɗauki pillow da ƙaramin duvet, kan couch ya hau yayi kwanciyarsa. Da asuba Nurain ya farka, vision dinsa na daidaita ya fara surveying kan gado with his sleepy eyes, wayam yaga bata nan kuma babu alamar an hau gadon, can ya hangota ƙasan carpet ta dunƙule waje ɗaya, har yayi sallah yayi wanka ya shirya bata farka ba don ba ita tayi bacci ba sai wajen 3 na dare, before 7 ya gama shirinsa, har ya kai bakin door da bag din laptop dinsa a hannu sai kuma ya dawo, ya ringa kallonta ganin ta takure kanta ya dawo da baya ya ɗauki duvet din da ya rufa ya lulluɓa mata, da haka ya fita daga ɗakin ya rufe, A restaurant din hotel din yayi mata order both breakfast and lunch, ya gaya musu room din da za a kai da kuma time, shi kuma anan ya zauna yayi breakfast din, da ya gama ya wuce babban conference hall dake hotel din inda a nan za ake duganar da training din.....✍️
💛 HAJAR 💛
{62..}
Bai daɗe da fita ba Hajar ta farka daga baccin da take sakamakon cramps din da yake sukarta a cikin baccin, ta yamutsa fuska ta miƙe zaune tana kallon duvet din jikinta, muttsuke idonta tayi ta kalli couch din ɗakin, ta fara yaye duvet din sai kuma ta tsaya tana kallonsa, a hankali ta kai duvet din hanci perceiving the scent, ta taɓe baki gami da yin wurgi da duvet din kafin ta tashi a hankali, ƙarewa ɗakin kallo kawai take sai kace mai neman wani abun, walking like a chameleon ta isa bakin ƙofar toilet, she want to use it amma kuma tana tunanin may be yana ciki tinda dai bata gansa a ɗakin ba, kara kunnenta tayi da jikin ƙofar wai ko za taji wani sound, ɗipp ba taji anysound ba don haka ta samu courage din murɗa handle, ta shiga toilet din tana jin kamar ana mata ruwan allurai a cinye, daman tin tini haka cramp yake wahalar da ita, ganin she is still clean kawai ta ɗora alwala ta fito, ta gyara rolling dinta da ya sakwarkwace wajen bacci da yin alwala kafin ta kabbara sallah, tana idarwa ta kalli ledojin dake kan carpet har lokacin, turo baki tayi ta fara buɗewa, rolls din satchet of white coffee ta gani wajen uku sai milk sai kuma black coffee, taɓe baki tayi ta janyo wata ledar, anan taga toothbrush and toothpaste da detergent, zamewa tayi ta kwanta ta ringa twisting toes dinta shallow in pain, after 40mins lokacin ma takwas ya gota taji ana knocking door a hankali, ta tashi zaune tana kallon ƙofar, saida aka sake knocking snn ta miƙe ta isa bakin ƙofar, tana buɗewa waiter dake riƙe da park din Abinci cikin leda yace "good morning maam..", tace "morning..", ya miƙa mata ledar hannunsa yace "here is your order", kallon ledar ta tsaya yi bata amsa ba, waiter yace "gashi fa Maam", sai a lokacin ta amsa ta mayar da ƙofarta ta kulle, jingina tayi da ƙofar, after few seconds ta bude ƙofar tana leƙa waje wai ko za taga waitern ta tambayesa whereabout din wnda take jira tin dazu, wayam taga long Aisle din mai ɗauke da ƙofofi rututu, idonta yayi rau rau ta juya ta koma ɗaki, a kan couch ta zauna ta fara buɗe ledar, Irish ne da kidney sauce sai golden yam, ga bottle water da lemon kwali, tashi tayi ta dauki ledar da ta ga toothpaste da toothbrush, without second thought ta farke brush din ta matsa masa paste ta shiga toilet, bayan ta gama brush ta kuskure bakinta da mouth rinks da ta gani gefen sink, fitowa tayi ta zauna taci lafiyayyen breakfast dinta, kuma sosai taci abinda don ya mata dadi, saida ta gama ci ta ajiye ragowar snn ta fara tunanin wanka, sai a lokacin ta dubi box ɗinta dake bakin ƙofa tin daren jiya, ta janyo box din ta shiga da ita cikin ɗakin sosai, a hankali ta zuge zip tana kallon kayan ciki, ta harari kayan bayan ta tina ydda aka haɗasu, zaro ido tayi ganin harda undies sai kuma ta juyar da kai tana turo baki, sponge da shower gel dinta ta ɗauka ta shiga bathroom, tayi amfani da towel din da ta gani a jikin hanger, bayan tayi wanka ta fito ta shirya abinda, zaune tayi kan couch ta idonta ƙif akan ƙofa, tunani iri iri ya ringa zuwar mata ka, toh ko dai nan ya kawota shi yayi tafiyarsa, da sauri ta miƙe ta isa gaban closet ta buɗe, tana ganin bag dinsa taji wani mugun relief, tayi ajiyar zuciya kafin ta rufe closet ta koma ta zauna, ƙarfe sha biyu cleaner mace ta shigo ta gyara ɗakin, Cleaner ta gama aikinta ta fita, Hajar dai ta gaji da zama ta kwanta, saida taga har biyu na rana ta gota amma babu alamar zai dawo, da sauri ta miƙe jin anyi knocking door, har tana harɗewa sbd sauri taje ta buɗe door din, tayi turus tana kallon waitern da ya kawo mata breakfast, this time around ma ya gaisheta kafin ya miƙa mata ledar hannunsa, ta amsa tana jin wani ƙululu ya tsaya mata a throat, har waitern ya juya zai tafi tace "dan Allah ji mna..", ya juyo yana kallonta baice komai ba, da kyar ta ƙaƙalo mganar tace "emm dan Allah wane yace a kawo min wnn...?", yace "daga restaurant ne..", tace "Amm shi ina wnda yace a kawo..?", yace "sorry maam but i don't know aikina kawai shine delivery..", wani irin saki guiwarta tayi tace "Okay" da haka ta rufe ƙofarta, ko buɗe abincin ba tayi ba ta ajiyesa kan mini fridge dake ɗakin, saida tayi sallahr la'asar snn ta ɗan ci abincin kaɗan, tin daga cin abinci sai ciwo kuma ya motsa, ta ringa murƙususu a kan carpet, gashi idan baizo ba toh fa cramps din bazai lafa ba, daga yazo mgana ta ƙare, da kyar ta samu ya lafa mata, ta jingina da jikin gado ta ɗora kanta a guiwa, after few minutes ta ɗago kanta ta kalli door, gani kake sharr sharr hawaye sun fara gudu a cheeks dinta wani na bin wani.
★Ruqayyah ce zaune a Nurse station ta zabga uban tagumi, yau tana shigowa hospital direct office dinsa taje taga baya nan, tin ranar Tuesday last week da tazo bata sake zuwa ba sbd bata jin daɗi, sai yau ne ta samu tazo wajen aikin, Nurse Jiddah ce ta iso station din, tapping Ruqayyah tayi tace "Rukky yada zabga tagumi haka..?", Ruqayyah exhale heavily bayan ta fito daga duniyar da ta